Ba Zan Iya Zama Da Kishiya Ba, Shin Ya Halatta In Nemi Mijina Ya Sake Ni?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum.. Don Allah ina da tambaya ne. Shin Idan na ce ma mijina ya sake ni saboda ya yi aure ni kuma ba zan iya zama da matar ba domin ni ina da kishi. Shin ina da laifi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Ƙarin aure, wani abu ne wanda Allah ya halastashi bisa bayinsa maza muminai, bisa sharudda guda biyu. Wato mutukar mutum zai iya yin adalci atsakanin matansa, kuma mutukar zai iya ɗaukar ɗawainiyarsu ta ɓangaren saduwa da kuma abinda rayuwar yau da kullum take bukata. Kamar yadda Allah yayi isharah Ƙarara acikin Alƙur'ani

    ...فَانكِحُوا مَا طَابَ لَكُم مِّنَ النِّسَاءِ مَثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَلَّا تَعُولُوا  

    "KU AURI ABINDA RANKU YASO DAGA CIKIN MATAYE BIYU-BIYU, KO UKU-UKU, KO HUDU-HUDU. IDAN KUKA TSORACI KO BAZAKU IYA YIN ADALCI BA, TO (KU AURI) GUDA ƊAYA KO KUMA (KU ZAUNA DA) ABINDA DAMSHINKU YA MALLAKA (WATO KUYANGI).. .." (Suratun Nisa'i ayah ta 3).

    Don haka Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya Ƙara aure, Sahabbansa ma mafiya yawansu basu zauna da mace guda kacal ba. Don haka ki kwantar da hankalinki kiyi hakuri kibi mijinki yadda zaku samu zaman lafiya da albarkar aure.

    Abu ne sananne cewa ku mata kiluna da tsananin kishi akan abubuwa da dama, amma babu kamar akan mazajenku. Wannan ba laifi bane tunda hali ne wanda yake gine azuciyar Ɗan Adam. Kuma an riwaito halaye na kishi daga wasu da yawa daga Salihan mataye tun daga kan matayen Fiyayyen Halitta (Sallallahu alaihi Wasallam) har zuwa na Sahabbansa da tabi'ai. To amma wannan kishin bai kaisu zuwa ga neman sakin aurensu ko neman hana faruwar abinda tun tuni Allah ya Ƙaddarashi kuma ya halastashi ba.

    Ya kamata kiji tsoron Allah kiyi hakuri ki zauna da Maigidanki Kasancewar rabuwarki dashi zata iya janyo illoli ga rayuwarki ko rayuwar yaranku da kuka haifa dashi. Kuma zama da kishiya tamkar taimakekeniya ne wajen aikata aikin alkhairi (wato shine kulawa da maigida) kamar yadda Allah yayi umurni;

    ...وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَىٰ وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ...  

    "KU TAIMAKI JUNA BISA AYYUKAN KIRKI DA TSORON ALLAH, KADA KU TAIMAKI JUNA BISA AYYUKAN ƁARNA DA KETARE IYAKOKI..." (Suratul Ma'idah aya ta 2)

    Kuma maimakon ki samu labarin cewa maigidanki yana neman matan banza, ai gara ki samu labarin cewa zai Ƙara aure ɗin.

    Kiyi hakuri ki bashi haɗin kai, ki taimaka masa wajen kulawa da iyalansa har dake aciki. Amma idan har kinga cewar ba zaki iya yin hakuri ki jure ba, babu laifi ki nemi KHUL'I daga gareshi. Wato ki bashi sadaƙin da zai isheshi ya auri wata matar, tare da dukkan abinda ya kashe alokacin da ya aureki. (Amma wannan agaban alƙali ake warwarewa).

    Amma dai ki sani cewar hadisi ya inganta daga Sayyiduna Thawban (rta) baran Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa "Lallai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace "DUK MATAR DA TA NEMI SAKI DAGA GUN MIJINTA BA TARE DA WANI LAIFI BA, (WATO BA TARE DA LAIFIN DA GIRMANSA YAKAI HAKAN BA) TO ƘAMSHIN ALJANNAH YA HARAMTA GARETA" (Imam Abu Dawud ne ya ruwaitoshi).

    Anan nake Ƙara baki shawarar cewa kiyi hakuri ki zauna lafiya da mijinki da kuma abokiyar zamanki. Hakika Allah yana tare da masu hakuri. Kuma yana bayar da lada mai yawa ga duk wanda yayi hakuri ya jure musiba dominsa. Amma tabbas idan har kika matsa wa mijinki akan sai ya sakeki domin ba zaki iya zama da kishiya ba, to fa Allah yana iya jarrabarki kuma bayan kin bar gidan.

    Jarrabawar nan tana iya zuwa miki ta kowanne ɓangare (ba fata nakeyi miki ba, amma abu ne da yakan faru). Kodai Allah ya jarrabeki da tsananin baƙin jini, ki kasa samun wanda ma zaizo gidanku yace yana sonki, ko kuma duk wanda zaizo sai kiga bai kai koda rabin matsayin mijinki na baya ba. Ko kuma duk wanda zaizo wajenki sai kiga shima yana da mata ɗaya ko biyu ko uku. Su ɗinma masu zafin kishi irinki. Kinga idan hakan ta faru, keda kanki zaki gwammace gara ma gidan mijinki gidan Uban 'ya'yanki. Shi kuma watakil sannan ya sake Ƙara wani auren, kuma hankakinsa ya kwanta, zai ce ba ya bukatar ki dawo gidansa. Kinga daga nan kuma rayuwarki zata shiga wani sabon salo maras daɗi.

    Kiyi hakuri ki jure ki zauna  ki kire yaranki. Kina da wasu darajoji agun mijinki wanda ita amaryar bata dasu. Misali: - Kin rigata shiga gidan, kin rigata zama dashi. - Kinfi ta sanin halayensa, don haka zaki fi ta sanin yadda zaki zauna dashi lafiya. - Kece uwargidansa kuma 'ya'yansa. Ita kuwa bata da kowa agidan. - Kin rigata aure. Don haka watakil kinfi ta iya girke-girke kala-kala, sanin hikimomin zaman aure, da sauransu. - Kinfi ta sanin 'yan uwan miji, da makobta da abokansa da dukkan jama'arsa.

    Don haka kiyi kokari ki fita yawan tsafta, kwalliya, hakuri, kulawa da bukatun maigida, da sauran hanyoyin tattali da zama dashi lafiya.

    WALLAHU A'ALAM.

    DAGA ZAUREN FIƘHU 07064213990

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.