𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya balaga amma ba ya sallah, ko za a ci yankansa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa
Barakaatuh.
Abu na farko da ya kamata mu fahimta shi ne: Wanda
ba a cin yankansa shi ne cikakken kafiri wanda ba musulmi ba. Amma har
ahlul-kitaab ya halatta a ci yankansu, kamar yadda Allaah ya ce
وَطَعَامُ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ حِلٌّ لَكُمْ وَطَعَامُكُمْ
حِلٌّ لَهُمْ
Kuma abincin waɗanda aka ba su littafi halal ne a gare ku, kuma abincinku
halal ne a gare su. (Surah Al-Maa’idah: 5).
Kuma malamai sun yarda cewa, kalmar: ‘abincinsu’ a
nan ita ce: Yankansu. Haka Ibn Katheer ya ciro wannan fassarar daga magabata
irin su: Ibn Abbaas, da Abu-Umaamah, da Mujaahid, da Sa’eed Bn Al-Jubair, da
Ikrimah, da Ataa’u, da Al-Hasan, da Mak-huul, da An-Nakha’iy, da As-Siddiy, da
Muƙaatil. Sannan kuma ya ce
وَهَذَا أَمْرٌ مُجْمَعٌ عَلَيْهِ بَيْنَ الْعُلَمَاءِ: أَنَّ
ذَبَائِحَهُمْ حَلَالٌ لِلْمُسْلِمِينَ؛ لِأَنَّهُمْ يَعْتَقِدُونَ تَحْرِيمَ الذَّبْحِ
لِغَيْرِ اللَّهِ، وَلَا يَذْكُرُونَ عَلَى ذَبَائِحِهِمْ إِلَّا اسْمَ اللَّهِ، وَإِنِ
اعْتَقَدُوا فِيهِ تَعَالَى مَا هُوَ مُنَزَّهٌ عَنْ قَوْلِهِمْ، تَعَالَى وَتَقَدَّسَ.
Kuma wannan al’amari ne da aka yi ijma’i a kan shi
a tsakanin malamai, cewa: Yankan ahlul-kitaab halal ne ga musulmi. Domin suna
da aƙidar cewa haram ne yin
yanka domin wanin Allaah. Kuma ba su ambatar komai a wurin yankan nasu sai dai
sunan Allaah kaɗai, kodayake
kuma suna ƙudurce mummunan
abu ga Allaah Ta’aala, irin abin
da ya tsarkaku kuma ya ɗaukaku daga gare
shi. (Tafseer Ibn Katheer: 3/40).
A ƙarƙashin wannan muke
fahimtar cewa, cikakken kafiri ko mushiriki mai haɗa Allaah Ubangijin Halittu da halittunsa, kamar mai
bautar rana ko wata ko taurari ko kwazazzabai ko duwatsu ko bishiyoyi ko aljanu
ko Mala’iku ko Annabawa ko Waliyyai ko dabbobi da makamantansu, wanda kuma yake
kiran sunansu ko duk wani wanda ba Allaah ba a wurin yankansa, shi ne wanda bai
halatta a ci yankansa ba. Ubangiji Maɗaukakin Sarki ya
ce
وَلَا تَأْكُلُوا مِمَّا لَمْ يُذْكَرِ اسْمُ اللَّهِ عَلَيْهِ
وَإِنَّهُ لَفِسْقٌ
Kuma kar ku ci daga abin da ba a ambaci sunan
Allaah a kan shi ba, kuma lallai shi ɗin fasiƙanci ne. (Surah Al-An’aam: 121).
Musulmin da ba ya sallah - muddin dai ba musu ko
jayayya yake yi da wajibta ba - shi ma, idan ya yi yanka da sunan Allaah, ba za
a ƙi cin yankansa ba.
Kodayake nassoshi sun siffata shi da kafirci da mushirikanci, amma kuma wannan
a babi ne na razanarwa da tsoratarwa daga mugun aikinsa, in ji malamai.
Musamman kuma da yake idan aka ware musulmi daga kafirai, a cikin musulmi za a
saka shi ba cikin kafirai ba. Sannan kuma idan aka tambaye shi addininsa,
musulunci zai faɗa, ba kafirci
ba.
A taƙaice dai, tun da ya halatta a ci yankan ahlul-kitaab wanda bai yarda ya
jingina kansa ko a jingina shi ga addinin musuluncin da Annabi Muhammad (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kawo ba, to ina kuma ga musulmi mai saɓo wanda ya yarda da Allaah shi ne Ubangiji, Annabi
Muhammad shi ne Manzon Allaah, kuma musulunci shi ne addinin gaskiya?! Illa dai
ya kasa tsayar da wani shisshike ne daga cikin shikashikansa, wanda kuma a kan
hakan ne malamai suka saɓa wa juna a kan
musuluncinsa?
Abu ne dai sananne a wurin malamai muhaƙƙiƙai cewa, mutum ya yi kuskuren shigar da kafiri a
cikin musulunci ya fi sauƙi a kan ya yi kuskuren fitar da musulmi daga cikin musulunci!
Allaah ya shirayar da mu ga samun kyakkyawar
fahimta a cikin addininmu.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.