Ticker

6/recent/ticker-posts

Dadaddiyar Sana’ar Fatauci Da Hausawa a Idon Duniya

Daɗaɗɗiyar Sana’ar Fatauci Da Hausawa a Idon Duniya

Haruna Umar Maikwari

Department of Hausa Language.
Federal College of Education (Technical) Gusau
maikwariharuna@gmail.Com
(+234) 07031280554

Da

Muhammad Sani Lawan

Sule Lamiɗo University, Kafin-Hausa, Jigawa State
mslawan@gmail.com

Tsakure

Fatauci sana’a ce da ta daɗe a ƙasar Hausa. Wannan sanaa ta sadar da Hausawa da sauran alummu na duniya da yawa. Hausawa kan bar ƙasar Hausa su shiga wasu ƙasashe musamman masu maƙwabtaka da su domin sayar da kayan su. Sukan ɗauki kayan gona da na kiwo da sauran kayan da ƙasar ke samarwa su kai a wasu ƙasashe su sayar su kuma sayo na ƙasashen can su kawo su a ƙasar Hausa su sayar. Yin wannan sanaar ya daɗa fito da Hausawa a idanun duniya. Manufar wannan maƙala shi ne ta bayyana yadda aka gudanar da fatauci a ƙasar Hausa da hanyoyin da aka bi wajen yin wannan sanaa da kuma irin fice da alummar Hausawa suka yi a idon duniya sakamakon wannan kasuwanci na fatauci. Hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da wannan maƙala kuwa sun haɗa da karance-karancen bugaggun litattafai da kundayen bincike da mujallun ilmi daga cibiyoyi daban-daban na ilimi. An zaɓi a ɗora wannan maƙalar a kan ra’in Bourhis (Interraction). Wanda wannan ra’i ya nuna irin cuɗanya da Hausawa suka yi da wasu al’ummu ta hanyar wannan kasuwanci na fatauci. Sakamakon wannan bincike ya bayyana cewa Hausawa sun yi kasuwancin fatauci a ƙasashe daban-daban musamman maƙwabtan ƙasashe. Haka kuma wannan fataucin ya ƙara fito da Hausawan a idon duniya sakamakon cuɗanya da suka yi da wasu al’ummu na cikin duniya.

1.1 Gabatarwa.

Hausawa sun kasance al’umma ne masu yawo a ƙasashen duniya. Wannan yawo mafi yawansa fatauci ne ke kai su. Yayin da wasu kuma neman wani abu, wasu kuma aiki, wasu kuma yin hijira ne ke kai su. Ko ma dai yaya abin yake, al’ummar Hausawa sun shiga duniya kuma duniya ta sansu. Wannan maƙalar za ta mayar da hankali ne a kan daɗaɗɗiyar sana’ar nan ta fatauci. Kasancewar Hausawa ba su yadda da zaman banza ba, ya sa suka rungumi kauswanci. Wanda shi kasuwancin shi ne ya haifar da fatauci daga wannan ƙasa ko nahiya zuwa wata. Wato a nan mutum ya fitar da kuɗinsa ya sayi kadara sannan wani lokaci ya fitar da wannan kadarar ya sayar shi ne kasuwanci. Mai irin wannan harka shi ake kira ɗan kasuwa, in mace ce akan kira ta da ‘yar kasuwa. Kasuwanci ba ya yiwuwa sai da jari. Jari shi ne ake amfani da shi wajen sayen kadarar da za a sayar. Ɗan kasuwa dole ne ya riƙe jari domin ya riƙa jujjuya shi Zarruk (1982:38). “Kasuwanci wata harka ce mai saurin samun kuɗi ko rasa su (Madabo, 1979:23).

 Tun fil azal Bahaushe yana gudanar da kasuwancin sayen wani abu ya sayar ko dai a gidansa ko a garinsu ko a maƙwabtansu ko ma ya ƙetara wata ƙasa da yake maƙwabtaka da su. Wannan nau’in kasuwanci na barin ƙasa zuwa wasu ƙasashe domin saye da sayarwa an fi saninsa da fatauci.Buƙata ta saye da sayarwa na abubuwan amfani suka haifar da fatauci. Wannan jinga za ta yi tsokaci a kasuwanci domin a fito da fatauci a fili, sannan a bayyana yadda ya kasance fitacciyar sana’ar da ta fito da Hausawa a idon duniya.

1.1 Manufar Bincike

Babban manufar wannan bincike ita ce ƙoƙarin fito da sana’ar fatauci su kansu Hausawa masu sana’ar. Lura da cewa wannan sana’a ta fatauci daɗaɗɗiyar sana’a ce, kuma al’ummar Hausawa sun kasance suna yin wannan sana’a don haka wannan manufar za ta haɗa da:

i.                    Fito da yadda ake gudanar da sana’ar fatauci.

ii.                  Bayyana irin kayan da ake fatauci daga ƙasar Hausa zuwa sauran ƙasashe.

iii.               Bayyana al’ummar Hausawa da matsayinsu a idon duniya ta fannin wannan kasuwanci (fatauci).

1.2 Ra’in Bincike

An zaɓi a ɗora wannan maƙalar a kan ra’in Bourhis (Interraction). Wannan ra’in yana bayani ne kan cuɗanya da wasu al’ummu. Wani Bature mai suna Bourhis shi ne ya assasa wannan ra’i kuma ya bayyana cewa, ta fuskar hulɗa da cuɗanya tsakanin wata al’umma da wata ana samun wata al’umma ta yi tasiri a kan wata. Wannan hulɗa kuma kan iya zama sakamakon fatauci ko hijira ko yawon buɗe ido. Bourhis ya ƙara da cewa, ana samun cuɗanya ta fuskar karɓar horo. Wato mutum ya samu horo kafin ya tsunduma cikin sha’anin rayuwar wasu. Wannan maƙalar za ta mayar da hankali ne wajen duba cuɗanya tsakanin Hausawa da wasu al’ummu musamman waɗanda Hausawan suka taras a garinsu a ta dalilin fatauci.

1.3 Dabarun Bincike

An bi muhimman hanyoyi guda uku domin tattara bayanai yayin gudanar da wannan bincike. Na farko shi ne lura (observation). An duba yanayin fataucin kaya da Hausawa kan ɗauka daga Arewa su kai Kudu.

Hanya ta biyu da aka bi domin tattara bayanan wannan bincike ita ce, karance-karancen bugaggun littattafai da kundayen bincike da mujallu da aka buga na ilmi. Wannan shi zai taimaka wajen kammalar wannan bincike. Waɗannan hanyoyi su ne za su taimaka wajen gina wannan maƙala.

2.0 Kasuwanci

 Hausawa sukan yi wani kirari cewa, “Kasuwa a kai maki dole” ta la’akari da wannan kirari za a fahimci, kasuwa wata matattara ce ta al’umma inda mutane na nesa da kuma na kusa suke taruwa don gudanar da harkokin saye da sayarwa. Ta haka ne kuma kasuwa ta zama wata mattara ta saduwa da jama’a inda suke ƙulla zumunci da sauran harkokin zaman duniya a dalilin saye da sayarwa. Domin haka kasuwa ta kasance daga cikin manyan hanyoyi da Hausawa suka sami cuɗanya da baƙi. Tun kafin wannan zamani al’ummar Hausawa suna da irin nasu tsari wajen tafiyar da harkokin kasuwanci. A ƙasar Hausa, kasuwanci da aka fara sani da ya haɗa al’ummu iri daban-daban daga garuruwa waɗanda ake tafiyar da harkokin kasuwanci, shi ne ta hanyar “ba-ni-gishi-in-ba-ka-manda” ko kuma ciniki da furfure kamar yadda wasu al’ummomi suke kiran sa a ƙasar Hausa da kewaye. A irin wannan kasuwanci ana musanyar abubuwan sayarwa ne, misali, manomi ya ba masaƙi kayan noma don shi ma ya karɓi kayan saƙa, ko kuma manomi ya ba makiyayi (kayan gona) don ya karɓi wata dabba. An daɗe ana yin irin wannan tsari na cinikayya a ƙasar Hausa har zuwa wajen cikin ƙarni na 18 a inda aka shigo da hanyar yin amfani da kuɗi wuri don yin saye da sayarwa a ciki da wajen ƙasar Hausa. (Mu’azu, 2013:33)

 Haƙiƙa wannan ya taimaka matuƙa wajen sabunta wata irin sabuwar dangantaka da sauƙaƙa mu’amala da sauran al’ummu a tsarin kasuwancin Bahaushe don haka aka rinƙa samun cuɗanya da gwamatsuwar baƙin al’ummu iri daban-daban a ciki da wajen ƙasar Hausa. Haka kuma kasancewar ƙasar Hausa kamar yadda aka gani tana da tsari na shugabanci, da tarbiyya, da mulki musamman a ɓangaren tsarin dukiya, to sai al’ummu iri-iri suka yi ta kutso kai, kuma nu’amala ta kyautatu.

3.0 Fatauci

 Hausawa mutane ne masu sha’awar fatauci da ci-rani zuwa ƙasashe kuma na kusa da na nesa a sassan Gabas da Yammacin duniya, ballantana kuma ƙasashen Afrika baƙar fata. Ashe kenan Hausawa suna yin fatauci da tafiye-tafiye, a inda wannan ya ba su damar cuɗanya da mutane daban-daban. Ta haka ne Hausawa suka yi mu’amala da Larabawa da mutanen Ashanti a ƙasar Ghana da mutanen Saliyo da na Dahome da kuma hulɗoɗin da suka yi da Buzaye da Larabawa da sauran ƙabilu daban-daban, alal misali idan aka dobi fatauci a ƙasar Hausa, ‘yan kasuwa a ƙasar Hausa suna yin fataucin kayayyaki daga wannan ƙasa zuwa garuruwan Adar da Azbin da Nufe da ƙasashen Larabawa da kuma Gwanja. Bayan sun sayar da kayyayakin su a can, sai kuma su sayo wasu kayyayaki daga waɗannan ƙasashe su kawo ƙasar Hausa, don su sayar. Ire-iren kayyaykin fataici da suka riƙa saye daga ƙasar Hausa suna kai wa waɗannan ƙasashe sun haɗa da kayayyakin sutura irin waɗanda aka saƙa aka kuma tura su da baba da dabbobi da kuma daddawa, haka kuma suka saye kayayyaki irin su bindigogi da sauran kayan dangin alburusai da riguna girken Nufe da kayan ƙarau daga ƙasar Nufe. Suna kuma sayen balma da kanwa da dabino da wake da ɗan waken Azbin da awaki da tumaki da raƙumma daga ƙasashen Adar da Azbin da kuma Borno. ‘Yan ƙasar da suke zuwa fatauci Kudu wato ƙasashen Yarbawa da Gwanja suna sayo gero don kawowa ƙasar Hausa da maƙwabtanta da Arewa don sayarwa (Sallau, 2010:17).

 Wannan sana’a daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa. Fatauci shi ne sayen abinci ko wani abu, da yin sufurinsa ko jigilarsa daga wani wuri zuwa wani wuri, da niyar sayarwa. (Alhassan da Wasu, 1988:53).

 Bayan fatake a ƙasar Hausa, akwai kuma fatake daga waɗansu ƙasashe da suka ziyarci kasuwanni da ke ƙasar Hausa don yin saye da sayarwa, alal misali, Buzaye na kawo raƙumma da tumaki da awaki da dabino da kanwa. Idan sun sayar sai su saye hatsi dangin dawa da gero da ire-iren kayyayakin da ake saƙawa na sutura kamar mayafai da sauransu. Haka kuma suna sayen ƙuli-ƙuli da ‘ya’yan kurna da garin ɗorawa da shuni da baba don kaiwa kasuwannin ƙasashensu su sayar.

 Don tafiyar da harkokin kasuwanci a cikin kwanciyar hankali fatake suna yin ayari babba wanda ya ƙunshi ‘yan kasuwa da matsara waɗanda suke tafiya cikin ƙungiya zuwa kasuwanci na kusa da na nesa don gudanar da harkokin kasuwanci.

 Akwai hanyoyi da dama waɗanda fatake suke bi a ƙasar Hausa don zuwa kasuwannio na kusa da na nesa. Ire-iren waɗannan hanyoyi sun haɗa da waɗanda suke zuwa kasuwannanin da suke Arewaci da kuma waɗanda suke zuwa kasuwannnin da suke Kudanci a ƙasar Hausa. (Mu’azu, 2013:34-35)

3.1 Hanyoyin da Fatake Kan Bi Zuwa Sana’arsu ta Fatauci

 Akwai wasu hanyoyi da fatake kan bi idan za su wajen harkokin kasuwancinsu. Su waɗannan hanyoyi sun haɗa da:

1.                  Hanya ta farko ta fara daga garin Sijilmasa ta ƙasar Morocco zuwa ƙasar Murtaniya ta biya ta Taghata zuwa Taodeni zuwa Tumbuktu zuwa Katsina ta ƙare a Kano.

2.                  Hanya ta biyu ta fara daga garin Tarabulus ta ƙasar Libya ta bi da Air zuwa Katsina ta ƙare a Kano

3.                  Ita kuma hanya ta uku sai ta faɗa daga ƙasar Masar ta bi ta Fezzam a ƙasar Morocoo zuwa ƙasar Kanem_Borno ta bi ta Kano ta kuma ƙarashe a Katsina.

4.                  Hanya ta huɗu ita ma ta fara daga ƙasar Masar ta bi Darfur zuwa Waday zuwa Kanem-Borno zuwa Kano ta ƙarashe a Katsina, (Ibrahim, 1982:74)

Waɗannan hanyoyi ba fatake kaɗai ne suke amfani da su ba har sauran ƙabilun Afrika. Sun ƙara da cewa, Fatauci muhimmin abu ne a ƙasar Hausa, da yadda jama’ar wannan ƙasar take cuɗe-ni-in-cuɗe-ka a junanta da kuma sauran ƙasashe. Bayan haka Fatauci yana cikin manyan dalilan da suka yaɗa Hausa, kuma Hausawa suka yaɗu a ko’ina a Afrika ta Yamma. Zango – zango (unguwannin Hausawa) da ake samu a kusan kowane birni na Afrika ta Yamma, babban sanadinsa fatauci ne.

 A cikin ƙasar Hausa kuwa, kusan a kowane gari akwai fatoma, watau mai masaukin fatake, idan sun yada zango a garin da yake.

3.2 Fasalin Fataucin Hausawa

 Yanayin fataucin da Hausawa suka yi a wasu ƙasashe suna da yawa. Wasu suna ɗaukar kayan abinci, wasu su ɗauki kayan masarufi. Kaɗan daga cikinsu su ne:

3.2.1 Fataucin Jakkai

  A cewar su Alhassan (1988:54) sun kalli fataucin jakkai kamar haka; “ Masu ɗora wa jakkai kaya niƙi-niƙi daga wani gari zuwa wani, don sayarwa su ne ‘yan fataucin jakkai. Yawancin waɗannan fatake sukan yi ta zirga-zirgarsu ne ƙungiya-ƙungiya kuma suna da wuraren da suka yada zango, inda suke yin rurrumi ko rage rana. Suna da madugu (jaji) wanda ke yi masu jagora mai kuma farin jini a gare su. Da kuma a garin da suke.

 A wancan lokaci fatake sukan ɗauki kaya na kasuwancinsu masu yawa su ɗora a kan jaki, su kora. Galibi akan samu madugu wato wani da yake da jaki mai ƙwari kuma mai hankali wanda ya san hanya wanda ba ya shirita, wanda zai shiga gaba a bi shi a baya. Sai su saka shi a gaba su kuma su biyo baya ana tafe aka kora jakkai har a isa inda ake buƙatar a isa. Idan kuma lalura ta yada zango ta zo akan yada zango a inda aka san akwai wani mai masaukin fatake wanda ake yi wa laƙabi da Fatoma. Sun riƙa yin tafiya suna yada zango har su isa inda za su sayar da kayansu.

 Madugun yakan tafi tare da zabaya wadda ke yi wa mutane da dabbobi kirari. Kuma yakan tafi da wani ƙwamemen jaki horarre wanda ke kata ya yi kuka da ƙarfi a duk lokacin da aka yi kusa da gari, saboda sanarwar isar ayarin madugunsu. Jaki aka fi amfani da shi a wajen fatauci, ko da yake wasu fatake suna amfani da raƙumi da takarkari. (Alhassan, 1988:54)

3.2.2 Sodori

 Sodori sana’a ce ta sayarda bisashe. Ana sayensu ana sayarwa don riba. Dabbobi su ne kamar shanu, da tumaki, da awaki, da raƙuma, wani lokaci ma har da jakkai da dawakai.

 Wani jiƙon kuma, fatake sukan niƙi gari su yi tafiya mai nisan gaske. Saboda haka sai mai gida ya ba ‘yan kore ko ‘yan fasaƙwauri bisashensa, su kai masa inda yake buƙata. Shi kuma sai ya hau doki ya tarar da su can, ya sayar da bisashensa. (Alhassan, 1988:54)

 Idan muka lura da abin da su Alhassan suka faɗa dangane da Sodori za mu ga cewa, ita wannan sana’a ta sodori sana’a ce da ta ta’allaƙa ga sayar da bisashe zalla, wato duk wani abu da ba bisashe ba in an kai shi kasuwa da nufin sayarwa ba Sodori ba ne. Wannan sana’a ga bisashe kacal ta ta’allaƙa.

3.2.3 Fataucin Ƙasa

 Mutanen da ke ɗaukar kaya a ka daga nan zuwa can suna talla, suna sayarwa su ne ‘yan fataucin ƙasa. Misalin fataken ƙasa kuwa shi ne, ‘yan aruguma masu sayar da ƙorai da sayo goro daga Gwanja a ƙasa, domin jaki ba ya zuwa Kurmi saboda ƙudan tsando

 Ana yin fatauci da tsirfa da saisaina don neman abin masarufi da taimakon ƙasa. Ana yin sa hanyoyi daban-daban, kamar zuwa a sayo wani abu da ya ƙaranta daga wani agri a sayar, saboda musayar yanayi da ƙaruwar arziki da ilmi da sane-sanen halayen rayuwarmu ta farko da kuma ta ƙarshe. (Alhassan, (1988:54-55)

 La’akari da abin da su Alhassan suka faɗa game da Fatauci Ƙasa, za a iya cewa wannan nau’in fatauci ya ta’allaƙa ne ga masu ɗaukar kaya su yi tafiyar ƙasa daga wani gari ko wata ƙasa zuwa wata.

3.3 Wasu Hanyoyin Cuɗanyar Hausawa da Baƙi

 Masana da manazarta sun tabbatar da ƙasar Hausa tana da kyakkyawan yanayi da sararin noma. Noma ya zama muhimmiyar sana’a wadda take samar da nau’o’in abinci na ci da na sayarwa. Ga albarkar dabbobi da tsuntsaye na gida da na daji, sannan kuma ga ma’adanai tun daga azurfa da tagulla da tama da ƙarfe har ya zuwa kwalli da dalma da kanwa da gishiri da kuma duwatsu iri-iri da marmara da sauransu. Wannan ya sanya jama’a daga ko’ina suke sha’awar zuwa ƙasar Hausa don ciniki da samun abubuwan rayuwar yau da kullum.

 Tarihi ya tabbatar da tun da jimawa, a ƙasar Hausa akwai mazauna Hausawa nau’i biyu; wato masu sarauta da kuma talakkawa. Masu sarauta su ne mutane waɗanda suke jan ragamar al’amurran jama’a kuma sun haɗa tun daga kan Mai’unguwa zuwa ga sarki. Waɗannan su ne sahu na farko a tsarin jagoranci da Hausawa mazauna farko. Su kuwa talakawa su ƙunshi sauran jama’a waɗanda ba masu sarauta ba kuma sun haɗa da masu sana’o’i da malamai da masu ayyukan sauƙi da kuma sauran rukunin jama’a. (Smith, M.G. 1959)

 Baƙuwar al’umma wadda ta fara shugar Hausawa kuma suka cuɗanya ainun su ne al’ummar Larabawa, musamman idan zancen shigowar Bayajida a ƙasar Hausa ya tabbatar, to, yara daga cikin Larabawan na farko da suka fara haɗuwa da Hausawa, (Gusau, 2008:48-49)

3.4 Fatauci a Ƙasar Hausa

 Al’ummar Hausawa sun gudanar da wannan kasuwanci na fatauci, kuma sun kasance suna kai kayan gona da na sana’o’insu na gargajiya a wasu ƙasashe da suke maƙwabtaka da su. Wannan sana’a ta fataucin kayan gona da na sana’o’in Hausawa na gargajiya ta daɗa fito da Hausawa a idon duniya kuma ta bunƙasa Hausawa.

3.4.1 Fataucin Fata

Ngaski, (1991:115) ya bayyana cewa, “Daga cikin kayan fata da Hausawa ‘yan kasuwa suka shigo da su zuwa ɓangaren Gwanja, sun haɗa da takalman faɗɗe da salifa da ƙananan jikuna”. Wannan ya nuna kena Hausawa sun jima suna kai kayan sana’arsu a Gwanja wato ƙasar Legas. Haka kuma ya ƙa ra da cewa, “Kayan da suka fi fice na Hausawa tare da abokan kasuwancinsu na Kudu su ne kayan masaƙu”. A taƙaice dai Hausawa suna kai kayan sana’arsu a Kudu kuma wannan yana daɗa ƙara yaɗuwarsu da yin yawa a wasu yankuna da ba na Hausawa ba. Adamu, (1991:113)

3.4.2 Fataucin Kayan Gona Da na Saƙa

 Hausawa sun kasance masu noma albarkatun gona. Kamar yadda Adamu (2010:27) ya bayyana cewa, “ƙasar Hausa ƙasa ce da Allah ya albarkace ta da amfanin gona, inda ake shuka nau’o’in abinci daban-daban da suka haɗa da gero, da dawa, da maiwa, da wake, da dankali, da rogo, da gyaɗa, da wasu kayan masarufi masu ɗimbin yawa”. Babu shakka waɗannan kayan gona ana noma su a ƙasar Hausa, kuma idan an noma a wancan zamani akan ɗabi na ɗiba a kai sauran a wata ƙasa a sayar domin a sayo wano abu da za a zo da shi nan a ci riba.

3.4.3 Fataucin Gishiri

 Wannan sana’a ta daɗa ƙara fito da Hausawa a idon duniya, saboda sun kasance suna ɗaukar gishiri su kai wasu ƙasashe musamman ƙasashen Larabawa. Al’ummar Larabawa suna zuwa ƙasar Hausa domin kasuwanci musamman sayen gishiri, ko bayi. Wannan sana’a ta haɗa hulɗa tsakanin Hausawa da Labarawa, kuma wannan hulɗa ta haifar da fitowar Hausawa a duniya, domin kuwa sun karɓi addinin musulunci, kuma sun ari mafi yawan lamomi na Larabci.

 Ba Kudancin Nijeriya ba hatta ma da wasu ƙasashe masu maƙwabtaka da Nijeriya Hausawa suna gudanar da kasuwancinsu na Fatauci a can musamman a ƙasar Ghana, da Libya, da Nijar, da Togo, da Mali da Sauransu. Duk wata ƙasa da ƙasar ta Hausa ta yi hulɗa da ita ta kasance abokiyar hulɗa ga ƙasar Hausa. Kuma fita da nau’in kayan da Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da shi, ya zama wani babban jakadan ƙasar ga ƙasar da ba su da wannan abun.

4.0 Fatauci da Al’adun Hausawa

 Abin da ake nufi da al’ada shi ne, hanyoyin gudanar da rayuwar ɗan Adam ta yau da kullun. Al’ada abu ce, da ta shafi rayuwa tun ranar gini, tun ranar zane. A cewar Bunza, (2006:7) ‘’Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan’Adam ce tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa.” Shi kuwa Ɗangambo, (1987:5) cewa ya yi: “Al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa, wadda akasarin jama’a na cikin al’umma suka amince da ita.” Gusau (2010:2) ya bayyana al’ada a matsayin “Tafarki wanda wata al’umma take rayuwa a cikinsa dangane da yanayin abinci da tufafi da muhalli da rayuwar aure da haihuwa da mutuwa da wasu hulɗoɗin rayuwa kamar maƙwabta da sana’o’i da kasuwanci da shugabanci da bukukuwa da sauran abubuwa waɗanda suke da alaƙa da haka”. Wani masani mai suna Ibrahim (1982:iii) yana ganin “al’ada” tana nufin: “abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya”. Ta haka al’ada ta shafi yanayin rayuwar al’umma da harkokin da take gudanarwa na yau da kullum. A taƙaice, al’ada wata abu ce wadda ta shafi abin da rai ya riga ya saba da aiwatar da shi har ya zamar masa jiki.

 Hausawa fitattu ne a sha’anin kasuwanci/fatauci, idan suka ɗauki fata, ko kayan masaƙa, ko kayan gona, ko dai wani abun amfani da ake yi ko sarrafawa a ƙasar Hausa suka kai a ƙasashen Kudu inda ake samun goro sai su sayar su sayo goro su zo da shi. Adamu, (1991:110) ya bayyana cewa “Hausawa ‘yan kasuwa tun a farkon ƙarni na sha huɗu suka iso a babban wurin samar da goro, ko da yake daga bisani watakila ya biyo bayan isowar wangarawa’yan kasuwa ne zuwa ƙasar Hausa”.

 Wannan ko shakka babu Hausawa sun kasance maciyan goro kuma sha’anin goro ya yi matuƙar tasiri a harkokin Hausawa na al’ada. Misali ɗauki aure, ko zanen suna, duk waɗannan duk wanda aka yi sai an tanadi goro. Don haka ba abin mamaki ba ne a san Hausawa da cin goro. Kuma a yunƙurinsu na zuwa Kurmi sayen goro ko wannan na ƙara fitowa da su a wasu ƙasashe da ba nasu ba.

5.0 Fatauci da Tattalin Arziki Hausawa

 Kalmomi guda biyu ne suka tayar da kalmar tattalin arziki, watau, “tattali” da “arziki (Mika’il, 2015: 3). A ra’ayin Auta (2006:194) kalmar “tattali” kalma ce mai nuna rainon wani abu har ya kai ga ya girma. “Arziki” a wannan wurin yana nufin samun “dukiya” ko wani abin mallaka.

 Haka kuma a wata ma’anar an bayyana “tattali” da tanadi ko kula ko ririta ko adana wani abu ko ajiye wani abu don yin amfani da shi nan gaba. Ita kuwa kalmar “arziki” na nufin tajirci ko dukiya ko samu ko hali ko kuɗi ko wadata ko sukuni ko daula ko abin hannu ko hannu-da-shuni (C.N.H.N, 2006:432;19).

 Idan muka lura da ma’anonin waɗannan kalmomi za mu fahimci cewa, in aka haɗa su za su gina kalmar “Tattalin Arziki”, wadda ita kuma wannan kalmar ta “tattalin arziki tana nufin “kula da abin da aka mallaka ko rainonsa ko ririta shi da ba shi kyakkyawar kulawa domin bunƙasa da cin gajiyar da ake samu tattare da wannan abin. Su kuwa masana da manazarta sun kalli wannan kalmar kamar haka:

 Ibrahim (1981:5) ya bayyana ma’anar “tattalin arziki da cewa, “Tsari ne na sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomin da Allah ya yi wa ɗanAdam domin samar da muhimman abubuwan buƙatu da rarraba su ga jama’a masu buƙata”. Umar (1983:5) shi ma cewa ya yi, “Tattalin Arziki tsari ne na sarrafa wasu abubuwa domin samun abubuwan rayuwa”.

 A fagen nazari kuwa, tattalin arziki tsari ne na sarrafa albarkatun ƙasa da sauran ni’imomin da Allah ya hore wa mutum, domin samar da muhimman abubuwan da ɗan Adam yake buƙata a kuma rarraba su ga jama’a. Don haka wajibi ne ga ɗan Adam ya yi huɓɓasa ta yadda zai sarrafa wasu abubuwa don ya kai ga biyan waɗannan buƙatu. Sai dai mutum ƙashin kansa, ba zai iya wadatar da kansa da dukkan abubuwan da yake buƙata ba, don haka tilas ya dogara ga ‘yan uwansa wajen samun waɗannan buƙatu kamar yadda suma suke dogara da shi (Umar, 1983).

 Ɗaukar kayan gona da sauran albarkatun ƙasar Hausa na sana’o’in gargajiya kamar kayan masaƙa fatar dabbobi da kayan ƙira da gishiri da kanwa da dai sauran kayan da Allah ya albakaci ƙasar Hausa da shi zuwa sayarwa ya ƙara taimakawa wajen haɓakar tattalin arzikin ƙasar Hausa. Kuma kayan da su fatake suke ɗaukowa na wata ƙasa da babu a nan suna taimakawa wajen bunƙasa hanyoyin more rayuwa.

6.0 Fatauci da Harshen Hausa

 Masana da Manazarta da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar harshe. Ga dai wasu daga cikinsu.

 Lado (1964), ya bayyana ma’anar harshe da cewa, shi ne “Rai ko zuciyar duk wani tunanin ɗan Adam musamman dangane da abin da mutum yake yi, game da ƙabilarsa da kuma yadda shi kansa ya ɗauki kansa”. Haka kuma wani masanin kimayya mai suna Bloorn Field ya bayyana harshe da cewa, shi ne, “ ‘Yan gunagunin da mutane ke yi don bayyana manufarsu ga masu saurarensu”.

 Rufa’i (1979:18), ya nuna cewa, “harshe wani tsari ne na furuci wanda ɗan Adam yake amfani da shi don sadarwa tsakaninsa da wani ɗan Adam ɗin”.

 Bolinger (1975:14) yana ganin cewa, “harshe wani tsari ne na sadarwa wanda ake furtawa don isar da saƙo haɗi da abin da mai magana ya ji ta hanyar harhaɗa ko gwaggwama sautuka bisa ga tsararren shiri wanda kan haifar da ma’ana”.

 Harshen Hausa ya yaɗu/watsu a duniya, kuma wannan yaɗuwa/watsuwa ba ta rasa nasaba da fatauci. Abin nufi dai a nan kashi 99% na watsuwar/yaɗuwar harshen Hausa fatauci na sanadi. Hausawa sun fantsama cikin sha’anin fatauci kuma suna zuwa har ƙasashen larabawa ba wai Afrika kawai ba. Kuma duk inda suka samu kansu, sai cuɗanya/sadarwa ta samu, wannan ya ƙara fito da al’ummar ta Hausa a idon duniya.

7.0 Kammalawa

 Yawace-yawacen da Hausawa suka yi na harkokinsu na kasuwanci (Fatauci) ya daɗa taikama masu wajen ƙara yaɗuwarsu a cikin duniya, musamman Afrika ta Yamma. Idan aka lura da yadda lamarin kasuwanci ya kasance musamman kamar yadda masana da manazarta suka kalli sha’anin kasuwanci, za mu ga cewa ba wani abu ba ne kasuwanci illa fatauci, wato sana’ar can da ta fato tun zamani mai nisa, wanda zai yi wuya a ce ga lokacin da aka fara ta a ƙasar Hausa. Duk lokacin da Bahaushe ya ƙulle kayansa na sayarwa ya ɗora a kan wani abun sufuri ko ma ya je da ƙafafunsa to baya da bambanci da farke. Kuma yanayin sana’ar ana iya kiranta da suna fatauci, sai dai ya kasance wani abu ya shiga na zamananci ba kamar yadda aka saba ba a wancan zamani. Fatauci ya taimaka wajen fito da al’ummar Hausawa ta hanyar al’adunsu da tattalin arzikinsu da kuma harshensu. Haka kuma waɗannan kaya da Bahaushe ya kai ya sayar suna a matsayin jakadun ƙasar Hausa wanda shi zai daɗa fito da ƙasar a idon duniya.


 

Manazarta

Abdulƙadir D. (2011) “Gyara Kayanka: Tasirin Al’adun Hausawa ga Ci Gaban Ƙasa” a cikin Studies In Hausa language, Literature and Culture. Kano: Jami’ar Bayero.

Adamu, (2010) “The Major Landmarks in the History of Hausaland”. The Eleventh  Inaugural Lecture. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.

Adamu, M. (1991) Hausa Factor In West African History, (Tasirin Hausawa a  Afrika ta  Yamma. Zariya: Ahmadu Bello University Press.

Alhassan, H. Da Wasu (1988) Zaman Hausawa. Lagos: Academy Press

Bunza A.M (2006), Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nig. Lmt Lagos

CNHN (2006), Cibiyar Nazarin Al’adun Nijeriya Jami’ar Bayero Kano.

Funtua da Gusau (2010), Al’adu da Ɗabi’un Hausawa da Fulani El-Abbas Printers and Concepts Kaduna

Faruk A (2017) “Nazarin Biɗau a Cikin Ƙagaggun Labaran Hausa” Kundin MA Hausa Studies UDUS.

Gusau, S.M. (1999) “Muhimman Garuruwan Ƙasar Hausa: Waiwaye a Kan  Tarihin  Kafuwarsu a Taƙaice”. The West African Journal of Language,  Literature and  Criticims (A Multilingual Bi-lingual) Vol. 1 No. 2

Ibrahim, M. S. (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci a Kan  Rayuwar  Hausawa ta Gargajiya”. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Jam’iar  Bayero.

Madabo M.H (1979) Ciniki da Sana’o’i a Ƙasar Hausa Annuri Printers and Publication D/Rimi.

Mu’azu, A. (2013) Baƙin Al’adu a Ƙagaggun Littattafan Soyayya na Hausa. Zariya:  Ahmadu Bello University Press

Sallau, B.A. (2010) Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna:  Najiu  Professional Printers.

Smith, M.G. (1959) “The Hausa System of Social Status” in Africa Vol. XXVII.  No. 1.

Yakasai, S.A (2012) Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Garkuwa Media Services Limited. Sokoto.

 

Post a Comment

0 Comments