Diyam Dan Goje

    Daga

    Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.

    Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya*** ***

    Shin Wane Ne Mai Diyam Ɗan Goje Da Dakta Mamman Shata Katsina Ya Yi Wa Waƙa?

    Sunansa na yanka shi ne Halilu, sunan Mahaifinsa Abdullahi. Ya samu laƙabin Mai Diyam a cikin sunansa ne saboda an haife shi a lokacin damina, watau kamar yadda Hausawa ke kiran ɗansu da aka haifa a wannan lokaci da laƙabin "Anaruwa", to shi Halilu saboda Mahaifiyarsa Bafulatana ce sai suka kira shi da "Mai Diyam".

    An haife shi a garinsu na Ƙaura Namoda, hedikwatar Masarautar Ƙaura Namoda dake Jihar Zamfara ta Nijeriya a shekarar 1919.

    Ya samu laƙabinsa na biyu watau "Ɗan Goje" daga sunan ƙanen Mahaifinsa da ya tashi a hannunsa da ake kira Alhaji Yahaya Goje Ɗan Auta.

    Ya soma sana'ar  tuƙin mota tun yana da shekara 15 a duniya, kenan tun a shekarar 1934 domin ita ce sana'ar da ya taras ƙanen Mahaifin nasa, Alh. Yahaya Goje Ɗan Auta ya na yi.

    Ta wannan sana'ar ne suka haɗu da Dakta Mamman Shata Katsina har so da ƙauna ya shiga tsakaninsu wanda shi ne sanadiyar ya yi masa wannan Waƙar.

    Ya ci gaba da wannan sana'a ta tuƙin mota har zuwa kusan wafatinsa, ya rasu Ranar Asabar, 12/01 /2012  ya na da shekaru 93 a duniya sanadiyar jinyar da ya yi fama da ita. Ya bar matan aure 2 da 'ya'ya maza da mata 19 da jikoki 73.

    Allah ya jaddada masa rahama, amin.

    Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.
    08149388452, 08027484815.
    birninbagaji4040@gmail.com
    Laraba, 28/08/2024.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.