Gobir Rumbun Wakokin Makadan Baka: Ibrahim Hassan Bagwashe Mashigin Waka (1985-)

    Citation: Gusau, S.M. (2024). Gobir Rumbun Waƙoƙin Makaɗan Baka: Ibrahim Hassan Bagwashe Mashigin Waƙa (1985-). Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 33-46. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.005.

    Gobir Rumbun Waƙoƙin Makaɗan Baka: Ibrahim Hassan Bagwashe Mashigin Waƙa (1985-)

    Sa’idu Muhammad Gusau,
    Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

    Tsakure: An bibiyi rayuwar Malam Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe ne, wanda a bisa tsarin zahiranci ya zamanto matattari na rumbun wasu mabambantan matanonin waƙoƙi na makaɗan baka na Hausa. A falsafar Ibrahim Gobir dangane da waƙar baka, ya samar da guruf-guruf daban-daban a Manhajoji na sada zumunta waɗanda suka haɗa da Manhajar WhatsApp da ta FaceBook da ta Instagram da dai sauran makamantansu waɗanda ake amfani da salula da nau’o’in wayoyin hannu da Kwamfutoci da dai sauran dangoginsu. Misali a WhatsApp ya buɗe Guruf wanda ya kira Diwanin-Waƙoƙin-Baka inda yake da mabiya sama da ɗari biyu da tamanin (280 followers), yayin da a Instagram yana da mabiya kimanin ɗari shida da saba’in (670 followers). A waɗannan manhajoji ana isar da wasu waƙoƙi ko hotuna waɗanda makaɗan baka na Hausa suka aiwatar a daɗaɗɗen lokaci da a halin da muke a ciki. Waƙoƙin bakan nan na Hausa sun shafi waƙoƙin Sarakuna da na jamian mulki, da na yansiyasa da na sojoji da na attajirai da na maaikata da na Shaihunan Malamai da na mafarauta da na ‘yantauri da na dabbobi da na tsuntsaye da na da na sauran masu sana’o’i da na gulabe da na garuruwa da da na sauran al’umma. Ta haka ne mabiya waɗannan guruf-guruf suke isar da saƙonnin tambayoyi dangane da wasu muhallai waɗanda sukan shige musu duhu a zubi na layuka ko ɗiya na matanonin waƙoƙin baka. Sau da yawa ma, sukan nemi bayanai game ko fashin baƙi na wasu ƙanana ko manyan maanoni ko manufofi na furucin matanoni na waƙoƙin baka. Haka kuma a kan kawo sunaye da tarihin rayuwa da hotuna na wasu makaɗan Hausa, marigaya da rayayyu, tsofaffi da manya da matasa da yara, maza ne ko mata, daɗa shahararru ne ko fitattu ko masu tasowa. Sannan akan kawo wasu kayan tarihi da na al’adu waɗanda suke jejjefo su a cikin matanoni na waƙoƙinsu da hotuna na wasu makaɗan baka. Sukan gabatar da kacici-kacici, musamman kan tarihin rayuwar wasu Sarakuna na Gobir da na wasu Sarakuna a Ƙasar Hausa.

    Fitilun Kalmomi: Gobirawa, Makaɗan Baka, Ibrahim Hassan Bagwashe

    Gabatarwa

    Jinsin Hausawa, Gobirawa, jinsi ne na mutane masu ƙwazo, masu fafutuka a kan dukkan abubuwan da suka sa a gaba, ko hankalinsu ya karkata a kansu. Ta haka, suka zama masu bajinta, masu sa kai, masu kwarjini, masu jaruntaka, masu juriya. Ta wani gefe kuma, suka zama masu azanci, masu nuna hazaƙa, masu basira, masu zalaƙa.

    A muƙalar nan, za a waiwayi rayuwa ta wani matashin Bagobiri, mai yawan ƙwazo, sha turmuza, mai ɗaga hannu ya yi kirari. Haka kuma matashi ne mai tarbiyya, mai biyayya, mai haƙuri. Mutum wanda ya karkatu da himmatuwa a cim ma maslaha mai janyuwa i zuwa ga bunƙasuwa da ilmantar da al’ummar da yake a cikinta. Wannan gwarzon Bagobiri kuwa shi ne Malam Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe, mawaiwayi, matattari, mafaɗaɗin rumbu da rudu da matanoni na waƙoƙin mabambantan makaɗan baka na Hausawa waɗanda suke rerawa da sadarwa ga al’ummar Hausawa bisa kowace kusurwa ta Ƙasar Hausa.

    Ba abu ne kawai na jan hankali ba, rayuwa ce bisa zahiranci, wadda aka gani, aka tabbatar, aka shaidar a ƙasa da kuma a salkunan gidaje na masu bin diddigi cikin ganowa da fahimtar waƙoƙin makaɗan baka na Hausa.

    Mutane, musamman ma waɗanda aka ambata a baya, za su zaƙu ainun, kai har ma su cika su tumbatsa, irin ta kwari ko randa ko tulu, domin su ɗanɗani ko su lashi wani basɗi na tarihin rayuwar wannan mutum wanda yake a gaɓarsa. An raɗawa wannan takarda batu da aka sarƙa masa kalmomi: Gobir Rumbun Waƙoƙin Makaɗan Baka, Ibrahim Hassan Bagwashe Mashigin Waƙa (1985-).

    Ƙananan batutuwa a wannan muƙala sun haɗa da:

    ·         Asali na jini da Salsalar Ibrahim Gobir;

    ·         Haihuwa da Tasowa ta Ibrahim Hassan;

    ·         Matsayi na Ilimin Alƙur’ani da na Boko;

    ·         Durmuya a Waƙoƙin Baka na Hausa da sa-kai a wasu kafafe da Manhajojin Sadarwa;

    ·         Garin da Ibrahim Hassan Gobir yake zaune yana Gudanar da Kasuwanci da Sauran Hidimomi;

    ·         Aure da Kafa Usra.

    A siga ta wannan rubutu kuwa an karkata ainun a tattaunawa da lura da tsinkaya, tun ma ba ta ɓangarorin da suka danganci al’amura na hada-hadar Malam Ibrahim Hassan Gobir ba. Har wa yau kuma, an bi ta turbar yin bayanai da sharhantawa da kuma ta tantance rayuwa ta wasu kadadu na tattakin Hausawa. Bisa jumla, wannan muƙala za ta yi magana ne game da rayuwa ta Ibrahim Hassan Gobir tun daga asalin zuriyyarsa zuwa yau.

    Asali na Jini da Salsalar Ibrahim Gobir

    Asali na Jinin Ibrahim Hassan

    Asali na jini na Ibrahim, jini ne da ya samo shi daga jini na Gobirawa,[1] a ɓangaren Sarkin Gobir Hassan Ɗanhalima, Sabon Birni (1864-1871).

    Domin haka, iyaye da kakanni na Ibrahim suna daga cikin Gobirawa waɗanda suka ba wa Hassan Ɗanhalima, Sarkin Gobir na Sabon Birni goyon baya a zucci da zahiri kuma a yaƙazatan, har wa yau kuma daga kakannin na Ibrahim akwai wanda Sarkn Gobir Sabon Birni Umaru Jari-Kada (1904-1915) ya naɗa shi Sarkin Ɗiyan Gobir a Sabon Birni.

    Salsalar Ibrahim Gobir

    Taƙaitacciyar nasaba ko salsala ta Ibrahim Gobir ita ce:

    Nasabar Uba: Hassan Ibrahim shi ɗa ne na Alhaji Hassan da ake kira Bakwai ko Babari ɗan Hillo Giwa, ɗan kuma Sarkin Ɗiya wato kakan Ibrahim na biyu.

    Malam Hassan, Mahaifin Ibrahim Gobir[2]

    Sunan Mahaifiya

    Mahaifiyar Ibrahim Hassan Gobir ita ce: Rabi. Rabi, uwa ce ma-ba-da-mama, wadda ta kula da ɗanta Ibrahim, kuma ta daɗa taimaka wa mijinta Malam Hassan a tsayar da tarbiyya da koya wa Ibrahim dabarun zaman rayuwa. Rabi ta ƙarfafa wa Ibrahim ainun a yayin karatunsa da a hidimominsa na yau da kullum.

    Malama Rabi, Mahaifiyar Ibrahim Gobir Bagwashe

    Mazaunin Farko na Magabatan Ibrahim

    Kamar yadda aka riga aka bayyana a Ƙarin Bayani na 1, kakannin Ibrahim sun iso, suka kafa mazauni na Birnin Tsibiri, suka ci gaba da zama. A zamanin Mulki na Sarkin Gobir Bawa Ɗangwanki (1936-1958) a Tsibiri sai wata matsala ta haɗa su da Hassan Ɗanhalima, wani fitaccen Ɗandaladiman Gobir.

    Daga nan ne Hassan Ɗanhalima ya nemi Abdurrahman Ɗanyan-kasko ya ba shi mazauni, sai ya baro Tsibiri, ya je, ya kafa Birni nasa a Fadamar Kanwa. A tasowar ce Hassan Ɗanhalima ya tafo da iyalinsa da jama’arsa har kuwa da kakanni na Ibrahim Bagwashe. A shekara ta 1945, ruwan sama ya ci ƙarfin Birnin Fadamar Kanwa, musamman ma yana a kware ne. mazauwa Fadamar Kanwa suka tashi suna barin birnin, har kuwa gami da shi Hassan Ɗanhalima jagaban jama’a. Sarki Hassan Ɗanhalima ya koma Sabon Birni, Birni wanda yake a kan tudu. Su kuma kakanni na Ibrahim suka tashi, suka je Katsira, ƙauye wanda yake gabas da Sabon Birni, kimanin tazara ta tafiyar kilomita huɗu (4).

    Dukkan abubuwan da aka yi ba a daina su ba, magabatan Ibrahim sun ci gaba da gudanar da hulɗoɗi tsakanin Katsira da kuma Sabon Birni har kuwa a yayin da ta zama Ƙaramar Hukuma, a cikin Jihar Sakkwato ta yau.

    Sabuwar Masarautar Sabon Birnin Gobir

    Sabuwar Masarautar Sabon Birnin Gobir

    Haihuwa da Tasowa ta Ibrahim Gobir

    Haihuwar Ibrahim Bagwashe

    Allahu ya ƙaddari samuwar ɗan’adam bisa umumiyya ta hanyar haihuwa a tsakanin tsatso na uba da uwa a kuma matsayi na ma’aurata, miji da mata. A bisa tsari na addinin Musulunci, jinsuna da ƙabilu na mutane tun a farkon zaman duniya sukan fito a tsakani na uwa da uba (Dubi Hadisi na Abu-Huraira, Ruwayar Tirmizi, Hadisi na 3955 a cikin littafi na Sunani al-Tirmizy (?) da kuma a sura ta Al-A’araf (7), aya ta 172. A kuma dubi ƙarin bayani na 172: ‘Ka kuma tuna lokacin da Ubangijinka ya fitar da zuriyyar ‘yan’adam daga tsatsonsa… (Rijiyar Lemu, M. S. U. (1442/2021) Fayyataccen Bayani na Ma’anoni da Shiriyar Alƙur’ani, Juzu’i na 2. Sh.:387. Amman: Bayinat Centre for Ƙur’anic Studies).

    Malam Hassan (Mahaifi) da Malama Rabi (Mahaifiya) su ne suka haifi jariri a matsayinsu na miji da mata. Sannan suka raɗa masa suna Ibrahim[3]. An ba shi suna na Manzo, mai daraja, domin ya albarkatu da kyawawan halaye na mai wannan suna, Annabi, Manzo Ibrahim, Halilul-Lahi.

    An haifi Ibrahim a zaman na gari ko mazauni da ake kira Katsira, wanda yake a nahiyar gabas da garin Sabon Birni na Hassan Ɗanhalima a Ƙasar Fadamar Kanwa. A yau Katsira[4] ƙauye ne wanda yake da nisan Kilomita huɗu (4) daga Sabon Birni, Ƙaramar Hukuma a cikin Jihar Sakkwato, kamar yadda aka faɗa a baya kaɗan.

    Matsayi na Neman Ilmin Alƙur’ani da na wasu Ƙananan Littattafan Musulunci da kuma na Boko

    Neman Ilimin Addinin Musulunci

    Tun da Hausawa suka karɓi addinin Musulunci, suke bibiyi hanyoyi na karatu da tilawar Alƙur’ani, mai girma da kuma koyo na sauran fannoni na addinin Musulunci. Sannan Hausawa sun saduda tare da mayar da hankali a hidimta wa Alƙur’ani, mai tsarki, da bibiyar gwadabu na Shari’ar Musulunci.

    A lokacin da Ibrahim ya tasa, ya fara gwadawa da iya furta muhimman ƙwayoyin sauti na Hausa gwargwadon iyawarsa, sai iyayensa suka sanya shi Makarantar Zaure ta koyon karatu da tilawar Alƙur’ani, mai daraja. Ya bi sahu na koyo da ƙididdige babbaƙu da farfaru (Baƙaƙe da wasulla) tare da haddace wasu ayoyi da ƙananan surori na Littafin Alƙur’ani, mai nassi na Ilahi.

    Haka kuma akwai wata al’ada wadda mazauna wasu ƙauyuka da tungage, musammanmahaifa suke ƙarfafawa, kuma suke giramawa a harka ta koyon karatun Alƙur’ani wadda suke tura yaro, ya fita, ya bar ƙauyensu, ya je garin Mungunu na Ƙasar Maiduguri, ya yi satun Alƙur’ani. Za ya fara cim ma karatun Zuƙu, sannan ya sauki Alƙur’ani, mai girma. An tura Ibrahim Gobir ya je Mungunu, ya sami shekaru uku (3), ya yi karatun Zuƙu[5] na allo, ya sauki Alƙur’ani, mai tsarki a matsayin karatun allo.

    Kazalika kuma bisa al’ada ta zamantakewa, a matsayin Bagobiri mazaunin Ƙasar Hausa, Ibrahim Hassan Gobir, ya karanci ƙananan littattafai na furu’a tare kuma da fahimtar shika-shikai da hukunce-hukunce na addinin Musulunci gwargwadon bukata.

    Ilimin Boko

    Bayan ilimi na makarantun addinin Musulunci, Ibrahim ya kuma yi karatu na Makarantar Firamare a mahaifarsa Katsira daga shekara ta 1993 zuwa shekara ta 1999.

    Daga nan kuma Malam Ibrahim ya zarce da karatu na ilimin boko a Makarantar Sakandaren Gwamnati[6] ta Sabon Birni daga 1999 zuwa 2005.

    Duk da Ibrahim Hassan Gobir bai zurfafa karatunsa na ilimin Turai ba, yana matuƙar fahimtar harshen Ingilishi ta hanyar magana da rubutawa da kuma sadarwa[7]. Wannan kuwa ya wanzu ne saboda kazar-kazar da faɗi-tashin da yake ta yi a cikin al’ummu nau’i-nau’i, da yin mu’amaloli da mutane masu harsuna daban-daban.

    Durmuya da Cakuɗuwa da Waƙoƙin Baka da sa-kai a wasu Kafafe da Manhajojin Sadarwa

    Tun Ibrahim yana ƙarami ya kasance mai ƙauna tare da mayar da hankali a sauraron waƙoƙin da makaɗan baka na Hausa suke rerawa, suna sadarwa ga al’ummar Hausawa. Kamar yadda za a lura, Ibrahim ya tashi a cikin babban gida na al’umma ta Gobirawa waɗanda suke a ko da yaushe a zazzaune a cikin gidajen gandu. Gidan su Ibrahim ya ta’allaƙa da hidimomi na Sarauta da jagoranci bisa harkoki na jama’a. Mu’amalolin da suka ci gaba da yi ke nan a zama na Katsira da a Sabon Birni da dukkan farfajiya ta Ƙasar Fadamar Kanwa da ta Daular Gobir ta Birnin Alƙalawa. A gabansa, masarta da makaɗan baka da masu kirarin baki da dangoginsu suke ta aiwatar da basirori da azance-azance da zalaƙoƙi, suna rerawa da sadarwa ga majiɓinta ayyukan nasu na hikimomi da fasahohi na harshe da na aiwace ko aikace.

    Ibrahim Bagwashe ya taso a durmuye a cikin hikimomi da fasahohin nan tun kuwa a zango na karatun Firamare da na Sakandare da kuma a halin ƙuruciya da yarinta. Ta haka hikimomin suka kutso a cikin tunaninsa, suka ja hankalinsa sosai ainun, ya karkatu haiƙan zuwa sauraro da sauwara su da haddace su, tun ma ba waƙoƙin makaɗan baka ba.

    Haka kuma, Ibrahim ya janyu zuwa sabga ta ji da sauraro na shirye-shirye da wasu gidajen Rediyon na lokutan da suke sanyawa, suna gabatar wa jama’a masu sauraro. Gidajen Rediyon kuwa su ne kamar Gidan Rediyon Rima, Sakkwato a shirye-shiryensa na waƙoƙi da kaɗe-kaɗen Hausawa, musamman shirin da Malam Ahmad Isa ya yi ta gabatarwa.

    Ga kuma Gidan Rediyo na Kaduna, musamman NBC Kaduna wanda ya yi ta gabatar da shirye-shirye na zaɓe daban-daban musamman da Alhaji Halilu A. Getso da Alhaji Ibrahim Maigandi da sauransu suka yi ta gudanarwa. A cikin shirin ne suka yi ta zaɓo tsofaffi da sababbi na waƙoƙin baka da makaɗan Hausawa iri-iri suka aiwatar suna jiyar da masu sauraronsu.

    Ire-iren shirye-shiryen Gidajen Rediyo nau’i-nau’i, Ibrahim ya yi ta sauraro waɗanda suka ta’allaƙa a kan waƙoƙin baka na Hausa.

    Himma ba ta ga raggo, a falsafar Ibrahim Gobir game da waƙar baka, sai ya cim ma wani zango na yin tsimi da tanadi daga kuɗaɗen da ake ba shi ya yi tara[8] a Makarantar Firamare. Ta haka ne ya yi ta ƙoƙarin sayen kasa-kasai na waƙoƙin baka yana mallakarsu. Ibrahim ya tattara mabambanta waƙoƙin baka masu yawan gaske. Ya kuma sami wata natsattsiyar dama a gidansu ta yadda mata wato iyayensa da yayyensa, sun riga sun mammallaki Rediyoyi masu kaset[9]. Sai kuma ya sami wata faraga wadda suka ba shi sauli da yake amfani da rediyoyin na mata, yana sassaka kasa-kasan yana ji, yana sauraro, yana kuma rirriƙewa, musamman a duk lokacin da ba ya wani aiki.

    Sannu-a-hankali, mutane na haujin mazaunin Ibrahim Gobir suka fahimci malakar da Allah ya ba shi a ƙwanƙwance matanoni na waƙoƙin baka. Wannan ne ya janyo, mutane, tsofaffi da manya da ma yara da sauransu, suka dinga yi wa Ibrahim tambayoyi, yana amsa musu bisa dace dangane da wasu muhallai waɗanda sukan shige musu duhu a zubi na layuka ko ɗiya na matanonin waƙoƙin baka. Sau da yawa ma, sukan nemi bayanai game da tarjama ko fashin baƙi na wasu ƙanana ko manyan ma’anoni ko manufofi na furucin matanoni na waƙoƙin baka. Waƙar baka ta shiga rayuwar Ibrahim Gobir ta kuma sami gindin zama, ta yi zamne daram.

    A yau da goben rayuwa, Hausawa a Ƙasar Hausa suka sami shigowar wasu sauye-sauye daga zuwan baƙin[10] na wasu baƙin abubuwa da kayayyaki da sauransu. sai kuma aka cim ma zango na isowar kafofin sada zumunta a hanyoyin sadarwa na yanar Gozo[11] da kuma suka shigo da wasiɗar manhajoji iri-iri[12].

    Kafar WhatsApp

    Alami na Kafar WhatsApp

    Alami na Kafar WhatsApp

    Malam Ibrahim Hassan Gobir ya yi wata gagarumar huɓɓasawa ta buɗe Guruf a WhatsApp mai suna: Diwanin - Waƙoƙin - Baka[13].

    An fara fito da babbar madosa da manufa ta wannan Guruf a yayin da aka ɗora masa hoton wata ƙungiyar masarta wadda ta ƙunshi makaɗa na ganguna da masu bushe-bushe.

    Makaɗa da Mabusa Masu Nuna Alamun Guruf na Diwanin-Waƙoƙin-Baka

    Makaɗa da Mabusa Masu Nuna Alamun Guruf na Diwanin-Waƙoƙin-Baka

    Guruf na Diwanin-Waƙoƙin-Baka, wani muhalli ne wanda aka keɓe shi domin rayawa da adanawa da bunƙasa ayyuka na al’umma, ciki kuwa har da waƙoƙi da ayyuka na makaɗan baka na Hausa a cikin wannan al’umma ta masu ruwa da tsaki a shirye-shiryen manhaja ta WhatsApp.

    An ƙididdige za a samu aƙalla masoya da mabiya wannan Guruf na Diwanin-Waƙoƙin-Baka ɗari biyu da tamanin (280). An kuma ayyana wa wannan Guruf wasu Jagorori, masu gabatar da abubuwa nasa, da suka haɗa da:

    i.        Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, Jami’ar Bayero, Kano

    ii.      Alhaji Ibrahim Mohammed, Ɗanmadamin Birnin Magaji

    iii.   Hajiya Bilkisu Yusuf Ali, Kano

    iv.   Malam Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe Sabon Birni, Abuja

    v.      Alhaji Sama’ila Gobir, Sarkin Rafin Sabon Birni, Abuja

    vi.   Malam Hussaini Dogo, Sarkin Yaƙi

    vii. Malam Jafar Jafar Ɗanjarida

    viii.           Alhaji Ibrahim Musa Ɗanƙwairo, Maradun, Abuja

    ix.    Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, Kano

    x.      Malam Ibrahim Shira, BASU, Gaɗau, Bauchi

    Wasu abubuwan da ake bijirowa da su a Guruf na Diwanin-Waƙoƙin-Baka sun ƙunshi:

    a.Ilimantarwa da fahimtarwa da adana wasu Waƙoƙin Baka na Hausa waɗanda Makaɗan Baka suke ta saka himma a rerawa da sadar da su;

    b.                  Sunaye da tarihin rayuwa da hotuna na wasu makaɗan Hausa, marigaya da rayayyu, tsofaffi da manya da matasa da yara, maza ne ko mata, daɗa shahararru ne ko fitattu ko masu tasowa;

    c. Wasu kayan tarihi da na al’adu waɗanda suke jejjefo su a cikin matanoni na waƙoƙinsu da hotuna na wasu makaɗan baka, kamar:

    Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina

    Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina

    Alhaji Muhammadu Sarkin Taushin Katsina da Jama’a ko Ƙungiyarsa

    Alhaji Muhammadu Sarkin Taushin Katsina da Jama’a ko Ƙungiyarsa

    Wata Kawa ta Dabboin Layya a Sallah Babba irin ta Gobir da Zamfara da Katsina da Kabi da Sakkwato

    Wata Kawa ta Dabboin Layya a Sallah Babba irin ta Gobir da Zamfara da Katsina da Kabi da Sakkwato

    Wata Tanda Babba ta yin Masa/Waina

    Wata Tanda Babba ta yin Masa/Waina

    d.  Text Box:  

    Janar Murtala Ramat Mohammed, Makaɗa da yawa sun yi masa waƙoƙi

    Hotuna na wasu manyan Turaku na Al’umma da masu jarunta da kuma mutane waɗanda suka yi fice har aka jefo maganganu ko ɗiya a wasu waƙoƙin baka na Hausa.

    Janar Murtala Ramat Mohammed, Makaɗa da yawa sun yi masa waƙoƙi
    Janar Murtala Ramat Mohammed, Makaɗa da yawa sun yi masa waƙoƙi

    Sarkin Daura Alhaji Muhammadu Bashar

    Sarkin Daura Alhaji Muhammadu Bashar

    Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari da Chief Olusegun Okikiola Obasanjo

    Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari da Chief Olusegun Okikiola Obasanjo

     e.Wasu hotuna da aka tsartsarmo bayanansu a wasu waƙoƙin baka na Hausa:

    Wani Yanayi na Gona a Ire-Iren Gonaki da Makaɗan Noma Suke Waƙewa

    Wani Yanayi na Gona a Ire-Iren Gonaki da Makaɗan Noma Suke Waƙewa

    Ustaz Nasiru Wada Waziri Khalil

    Ustaz Nasiru Wada Waziri Khalil a zaune a Ɗakin Heinrich Barth na Kayan Tarihi a Birnin Agadez, Jamhuriyyar Nijar

    Wasu Ɗalibai Masu Koyon Hausa a Wata Jami’a ta Ƙasar Sin (China) Suna yin Ɗanin Rerawar Waƙar ‘Jaruma’ ta Hamisu Yusuf Breaker, Kano

    Wasu Ɗalibai Masu Koyon Hausa a Wata Jami’a ta Ƙasar Sin (China) Suna yin Ɗanin Rerawar Waƙar ‘Jaruma’ ta Hamisu Yusuf Breaker, Kano

    f.  Har wa yau kuma, wasu magoya bayan Guruf na Diwanin-Waƙoƙin-Baka sukan kaɗo ko zayikke da wasu hotunan makaɗan baka na Hausa masu yin amfani da zallar kiɗa[14], su dinga ɗora furuci na muryoyin kalmominsu, suna rerawa tare da sadar da waƙoƙi:

    Wani Bello Makaho yana ɗ

    Wani Bello Makaho yana ɗora furuci na muryar kalmominsa a wani amon kiɗa yana rera waƙa (28/7/2023)

    g.                  Har wa yau kuma, wasu magoya baya na wannan guruf sukan fito da wasu halaye da makaɗan baka na ƙasashen Afirka da na wasu nahiyoyin duniya suke gudanarwa domin a daɗa ƙaruwa da hikimomi da basirorinsu.



    Wani soja na Jamhuriyar Nijar a Ɗakin Sitidiyo yana rerawa da sadar da waƙar baka[15]

    Wani soja na Jamhuriyar Nijar a Ɗakin Sitidiyo yana rerawa da sadar da waƙar baka[15]

    Ga wani misali kamar wannan:

    Wani Mutumin Ƙasar Guinea Conakry yana kaɗa wani abin kiɗa, yana rera waƙar baka[16]

    Wani Mutumin Ƙasar Guinea Conakry yana kaɗa wani abin kiɗa, yana rera waƙar baka[16]

    Kafar Facebook

    Kazalika, wani ƙoƙari da kazar-kazar na Malam Ibrahim Gobir, Bagwashe ta fuskar daɗa rayawa da cusa ƙauna da bibiyar waƙoƙin baka na Hausa sun janyo ya shiga, ana damawa da shi a kafa ta Facebook.

    Alami na Kafar Facebook

    Alami na Kafar Facebook

    i.  A kafa ta Facebook, Ibrahim Hassan ya kakkawo wasu waƙoƙi da makaɗan baka na Hausa suka aiwatar a daɗaɗɗen lokaci da a halin da muke a ciki. Waƙoƙin bakan nan na Hausa sun shafi waƙoƙin Sarakuna da na jami’an mulki, da na ‘yansiyasa da na sojoji da na attajirai da na ma’aikata da na Malamai da na Shaihunan Malamai da na sauran Al’umma. Wasu daga waƙoƙin na makaɗan Hausa da Ibrahim yake ta kawo su a Facebook sun ƙunshi:

    ·   Wasu waƙoƙin Dr. Alhaji Mamman Shata, Katsina;

    ·   Wasu waƙoƙin Zabiya Gumsu Maiduguri;

    ·   Wasu waƙoƙin Makaɗa Idi Ɗangiwa Zuru;

    ·   Wasu waƙoƙin Makaɗa Jatau Kamba;

    ·   Wasu waƙoƙin Binta Zabiya Katsina;

    ·   Wasu waƙoƙin Zabiya ‘Yardaudu;

    ·   Wasu waƙoƙin Sale Nadingim;

    ·   Wasu waƙoƙin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo, Maradun;

    ·   Wasu waƙoƙin Malam Yahaya Makaho, Kaduna;

    ·   Wasu waƙoƙin Dr. Aminu Ladan Abubakar, Sarkin Ɗiyan Gobir;

    ·   Wasu waƙoƙin Buda Ɗantanoma Argungu;

    ·   Wasu waƙoƙin Hamza Caji, Kano;

    ·   Wasu waƙoƙin Muhammadu Dodo Maitabshi, Bakura Sakkwato;

    ·   Wasu waƙoƙin Abubakar Akwara Sabon Birnin Gobir; Wasu waƙoƙin Mamman Sodangi Katsina;

    ·   Wasu waƙoƙin Nadada Sabon Birnin Gobir;

    ·   Wasu waƙoƙin Sarkin Tabshi, Salihu Jankiɗi Gusau, Sakkwato;

    ·   Wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Maidaji, Sabon Birni;

    ·   Wasu waƙoƙin Nagelo Kano;

    ·   Wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru;

    ·   Wasu waƙoƙin Nageda, Kano;

    ·   Wasu waƙoƙin Aliyu Gurso, Tatatu Mafara;

    ·   Wasu waƙoƙin Alhaji Abdurrahman, Sarkin Kotso, Kano;

    ·   Wasu waƙoƙin Hadiza Potiskum;

    ·   Wasu waƙoƙin Zabiya Tagoje;

    ·   Wasu waƙoƙin Zabiya Hamma Zariya;

    ·   Wasu waƙoƙin Zabiya Hauwa Ƙanƙara, Zariya

    ·   Wasu waƙoƙin Zabiya Tani Kerawa, Zariya;

    ·   Wasu waƙoƙin Zabiya Hafsatu Kanuri, Sakkwato.

     

    ii.   Tabbas, a Kafa ta Facebook, Ibrahim yakan kuma gabatar da kacici-kacici, musamman kan tarihin rayuwar wasu Sarakuna na Gobir da na wasu Sarakuna a Ƙasar Hausa. Sannan yakan gwamawa da ambaton sunaye da hotuna na wasu kayan tarihi na al’adun Hausawa;

    iii.Akwai kuma wasu lokuta da yake jefo hotuna na lokacin salloli, babba ko ƙarama, sannan yakan aika gaishe-gaishen salla-babba da na salla-ƙarama, da wasu bukukuwa na hidimomin aure ko suna ko makamantansu;

    iv.Yakan kuma yi gaisuwa ta ta’aziyya da ɗora hotuna kamar ta’aziyyar rasuwar Auwal Garba Ɗanbarno;

    v.   Ɗora gaishe-gaishe na taya murna da nuna ƙauna ga abokai da masoya da ‘yan’uwa da ire-irensu;

    vi.Na kuma lura Malam Ibrahim, matashi ne wanda ya kasance a ƙarƙashin shiriya ta Allahu, duk kuwa da yanayin himma da kazarniya nasa. Domin haka, a Kafa ta Facebook Ibrahim ya nace matuƙa a wajen yi wa iyaye, uwa da uba addu’a. Allah ya yi musu rahama, ya gafarta musu, kamar yadda suka yi masa kyakkyawar tarbiyya, suka ɗora shi a kan turba ta ilimi da kuma suluki na darajantawa da girmama manya da magabata;

    Ya Allah ka Shayar da iyayena, Uba da Uwa, ka kuma shayar da su daga tsarkakan Gulabe na Aljannah (Ibrahim Gobir Bagwashe)

    Ya Allah ka Shayar da iyayena, Uba da Uwa, ka kuma shayar da su daga tsarkakan Gulabe na Aljannah (Ibrahim Gobir Bagwashe)

    vii. Ibrahim ya zamanto mai son maganganun barkwanci, musamman na tsakanin jinsunan Hausawa, masu wasa da juna da ambaton al’amura domin tuna baya. Kazalika, na fahimci, ba mutum ne mai yin fushi da ire-iren kalamai na barkwanci da ake gaya masa ba. Karanci wasu kamar haka:

    a.‘Zan zaɓi Katsinawa, cikinsu kuma babu Waziri, babu Magajin Gari a cikinsu’ (Ibrahim Hassan, Afrilu, 2023, Facebook).

    b.            ‘Kere baban Sanda, a riƙa, a saɓa, a laga, a jingina, a dogara, a wurwura, a zungura, a jifa’ (Katsina, Bashir Abubakar, 15/9/2023, Facebook).

    c. ‘Kwanan baya na ji kana cewa mutane masu kiran ka da masu yi maka Teɗt ba ka dubawa su yi haƙuri. To, me ya sa suke kiran ka ne?’(K/Soro, Murtala Sulaiman (28/5/2023) Barkanmu da salla, Facebook).

    d.           ‘Lokacin ana ƙauye ba a zo birni ba’ (Ƙ/Soro, Bello (28/6/2008), Facebook).

    e.‘Bagobiri ba lissafi. To, mene ne dalilinka na rashin ɗaukar? An yi ma yawa! To…’ (Shinkafi, Bello (11/6/2023): Ibrahim Hassan Gobir, Facebook).

    f.  ‘Wanga gaye ya samu harka. Motoci kake sayarwa haka?’ (Kurfi, Mainasara Yakubu (11/6/2023): Ibrahim Hassan Gobir, Facebook).

    Kafa ta Instagram

    A bisa agalabiyya ta Kafa ta Instagram, akan ɗora hotuna ne na mutane da na abinci iri-iri da na kayan abinci da ma’aska da makitsa da mawaƙa da makaɗa da ma’aurata da waɗanda suka rabu a aure da masoya da maƙawabta da masu cakirewa da masu wuce-gona-da-iri da ‘yanwasa na kwaikwayo da na finafinai (‘yan fim) da duwatsu da gulabe da ƙasashe da birane da garuruwa da sauran abubuwan da mabiya Instagram suke ɗoɗɗorawa. Manhajar takan keɓe kadadu da za a iya sassaka waɗannan nau’o’in hotuna na abubuwa da aka bayyana a baya.

    Alami na Kafa ta Instagram

    Alami na Kafa ta Instagram

    Ta lura da bi’ar manhajar nan Ibrahim Hassan Gobir ya shige ta, ya shagaltu sosai, ya ɗora hotuna da wasu dangogi na hidimomi da abubuwa na ‘yan’uwa da abokan arziki, tun ma hotuna na wasu makaɗan baka na Hausa kamar Sani Aliyu Ɗandawo Yawuri da na ɗansa Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo Yawuri. Ya kuma sassaka hotuna na wasu ‘yan wasannin kwaikwayo a fejinsa kamar Rabilu Musa Ɗan’ibro.

    A mazaha ko manhaja ko Kafa ta Instagram, Ibrahim Hassan Gobir yana da mabiya kimanin ɗari shida da saba’in (670).

    Garin da Ibrahim Hassan Gobir Yake Zaune yana Gudanar da Kasuwanci da Sauran Hidimomi

    A wani lokaci da Ibrahim Gobir ya kai wani zango na neman ilimi na Alƙur’ani, mai tsarki, sai ya ci gaba da tambayoyi da neman fatawoyi na daɗa fahimtar hukunce-hukuncen ibada na addinin Musulunci. Kuma a daidai zangon ne ya sami tushen karatun boko na Firamare da na Sakandare, sannan ya janye shamaki, ya zama mai wayewa. Daga nan ne ya tsunduma a fahimtar makamar rayuwa ta yau da kullum.

    Ibrahim Bagwashe yana cikin gudanar da rayuwarsa a gida a tsakanin Katsira da Sabon Birni da tafiye-tafiye na buɗe ido da ƙaruwa da makamar zamantakewa, Allah, cikin ikonsa da yardarsa, sai yayansa, masoyinsa, Alhaji Hassan Atace, wanda yake zaune a Abuja yana tafiyar da kasuwancisa, ya nemi ya je da Ibrahim Abuja, ya riƙa masa al’amuran saye da sayarwa. Ilai kuwa, magabata suka tsayar da shawara, suka aminta da a yi haka.

    Alhaji Hassan Atace, Abuja

    Alhaji Hassan Atace, Abuja

    Area 1 Shopping Centre, Garki, Abuja

    A yau, Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe, yana zaune ne a Abuja, yana ta gudanar da harkoki na kasuwanci, musamman saye da sayarwa. Yana a tare da ɗan’uwansa cikin zumunci da amanar Allah da kiyayewarsa. Allah ya ci gaba da tallafa musu, ya ɗaukake su.

    Aure da Kafa Usra

    Allahu ya ba Malam Ibrahim Bagwashe damar ya yi aure domin ya cikasa wata muhimmiyar sunna ta Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama ta kafa usra[17] wato iyali, ya daɗa cikasa rumbun ‘yan’uwa, ya samar da nasaba maɗaukakiya, mai ɗimbin daraja, mai albarkatu.

    Iyali na Ibrahim ko mata tasa da ya aura, sun zauna da ita cikin aminci da mawadda. Allahu ya yi wa matar Ibrahim rasuwa ran 14/1/2022. Allah ya jiƙan ta, ya gafarta mata, ya yafe dukkan kura-kuranta.

    Har wa yau kuma, Allah ya azurta Malam Ibrahim Gobir da samun ɗa namiji wanda aka raɗa wa suna SAMA’ILA. Muna addu’a, Allahu ya daɗa shirya shi, ya ɗora shi bisa turba mai nagarta ta salihan bayi. Ya kuma sami tarbiyya da albarka kuma ya kasance mai ƙauna da yi wa iyayensa da dukkan magabatansa addu’a[18].

    Sama’ila Ibrahim Hassan Gobir

    Sama’ila Ibrahim Hassan Gobir

    Kammalawa

    Bayanai sun gabata a wannan takarda wadda aka kawo ƙwarya-ƙwaryan jirwaye na tarihin rayuwar Malam Ibrahim Hassan Bagwashe, Katsira, Sabon Birnin Gobir. Ta haka aka tattaro muhimman abubuwan na tarihin mutum, matashi mai ƙwazon gaske, mai kazar-kazar, mai ƙoƙari da fafutukar kalato tarihin magabata a Ƙasar Hausa da waƙoƙin baka na Makaɗan Hausa. An yi nazarin nan ne a ƙarƙashin batu: ‘Gobir Rumbun Waƙoƙin Makaɗan Baka: Ibrahim Hassan Bagwashe, Mashigin Waƙa (1985-).

    A wannan batun ne aka bibiyi bayanai masu yin nuni kan asali na jini da nasaba ko salsala da mazauni na magabatan Ibrahim da haihuwarsa da tasowarsa da iliminsa na Alƙur’ani, mai gima, da na boko da durmuya da sa-kai nasa a tanadi da sauraro da haddace waƙoƙin baka na Hausa da kuma shigar Ibrahim cikin wasu kafofin sadarwa na WhatsApp da Facebook da Instagram. Sannan da yanayi na kafa usra ta Ibrahim Bagwashe da kuma bazamarsa a cikin hidimomi na kasuwanci a mazauni na Abuja.

    Haƙiƙa, an yi wannan rubutu ne domin a daɗa cusa himma tare da mayar da hankali a kulawa da tattarowa da adanawa da kiyaye turasu na adabi da na al’adu da na addinin Musulunci da al’ummar Hausawa ta yi matuƙar jimawa da ƙanƙame su.

    Kiyaye maganganun hikima na magabatanmu na da da na yanzu da tattalin gudanar da su, kyawawan abubuwan zamantakewarmu ne a matsayinmu na al’umma ta Hausa. Dukkansu hidimomi ne da ake tafiyarwa a yau da kullum da ma sauransu da suka shafi Hausawa. Waɗannan halaye ne da za a dinga riƙe su, ana ci gaba da yaɗa su, ana daɗa tattalinsu da inganta su, musamman ma yadda suka kasance sulukin rayuwar Hausawa.

    Na daɗa lura tare da gane Ibrahim Gobir ya zama zakaran-gwajin-dafi wanda ya kuma yi fice da zara, duk da matsayinsa a shekaru, a hidimta wa adabi na waƙoƙin baka na Hausa. Wani misali da Ibrahim Gobir ya assasa, ni ma na yi nuni a kansa, ba kamar azamarsa da kulawarsa kan waƙoƙin baka. Ashe bai zama wajibi ga kowane matashi, ya nutsu, ya dinga bibiyar waƙoƙinsa na Hausa a mabiyu masu inganci ba, ba tare da ana yi musu ɗaukar-sakainar-kashi ba.

    Wani abin la’akar a nan kuma shi ne, tun-ran-gini, ran-zane, ake tsarawa da aiwatar da shirye-shirye a gidajen rediyoyi na da can, musamman a Arewacin Nijeriya da suka danganci zaɓe[19] da a wasu shiraruwa waɗanda suke tsattsarma waƙoƙin baka na Hausa. Waɗannan Gidajen Rediyo na da can kuwa su ne kamar NBC, Kaduna ko Rima Rediyo ko NBC, Kano ko NBC, Katsina da sauransu. Ire-iren gidajen rediyoyin nan bisa zahiri sukan shayar da masu sauraro wasu waƙoƙin baka ta bin wannan tsari ko siga:

    ·   Waƙoƙi na tsofaffi da daɗaɗɗun makaɗa, maza ko mata, kamar na Sarauta da na Sarakuna. Daga bisani suka shigo da na ‘Yansiyasa da na Sojoji masu riƙe da muƙaman Gwamnati.

    ·   Waƙoƙi na sauran manyan Makaɗa, maza ko mata, kamar na mafarauta da na ‘yantauri da na attajirai da na sauran masu sana’o’i da na Malamai da na manyan mata da wasu manyan ma’aikata da na dabbobi da na tsuntsaye da na gulabe da na garuruwa da sauransu.

    ·   Waƙoƙi na matasan makaɗa, maza ko mata kamar na soyayya da na wasannin kwaikwayo da makamantansu.

    ·   Waƙoƙi na makaɗan bege, yawanci maza da suka ƙunshi waƙoƙin Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, da na Sahabbai da na dukkan Ahlul-Baiti[20].                  

    A yau kuwa, masu shirye-shirye a Gidajen rediyoyin Arewa da Nijeriya har kuma gami da wasu tashoshin Hausa a Gidajen Rediyoyin Ƙasashen Waje sukan keɓantu, musamman da:

    ·   Waƙoƙin makaɗa matasa, maza ko mata, tun ma ba waƙoƙin da su da kansu suke nuna suna buga su a ɗakunan Sitidiyoyi ba. Ire-iren waɗannan waƙoƙi na matasa, su ne a yau rediyoyi suka fi tsarmawa a shiraruwansu a bisa agalabiyya. Wasu daga cikin waƙoƙin sun fi karkata a kan soyayya ta tsakanin ‘yanmata da samari da a cikin finafinai da wasannin kwaikwayo, ana yi kuma ana raye-raye ko da tsalle-tsalle. Wasu waƙoƙin kuma suna gwada wasu al’adun gargajiya da na bukukuwan aure da makamantansu.

    ·   Haka kuma akwai waƙoƙin wasu manyan makaɗa da mawaƙa, maza da mata, waɗanda suke bubbuga su a Gidajen Sitidiyo. Sannan Gidajen Rediyoyin sukan ɗoɗɗora su a sa’ilin aiwatar da wasu shirye-shiryensu.

    Takardar nan tana yi wa wasu masu aiwatar da shiraruwan rediyoyi a yau da masu sauraron waƙoƙin Hausa, su ajiye budurwar zuciya a gefe, su fahimci waƙoƙin baka bisa halayya da ma’anoni ko saƙonni, manya da ƙanana, da makaɗan baka suke ɗora asali na aiwatar da su. Sannan kuma a dinga ware waƙoƙi masu nagarta bisa wata fa’ida, sannan su kuma fitar da waƙoƙi ballagazazzu ko na sharholiya ko na zage-zage, musamman ta la’akari da fuskar zaɓen kalmomi da tsara furuci mai alfanu bisa tarbiyya ta shari’a da sunnar Manzon Rahama, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

    Alhamdu Lillah, ina yi wa Malam Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe wanda ya tsamo ni a cikin dubbai ya ba ni dama in rubuta tarihin rayuwar nan tasa. Ina matuƙar godiya ainun. Ina daɗa gode wa Allahu, mai kowa, mai komai, wanda ya ba ni iko da sauli na haɗa wannan talifi.

    Ni’imomi dukka Allah ne yake ba da su ga wanda ya so. Muna daɗa tsarkake Allahu a kan hikimomin da ya bai wa Ibrahim Hassan Bagwashe har ya sami azama ta raɓuwa da matanonin waƙoƙin baka na Hausa, kuma yana amfanar da jama’a, yana zazzare ɓatagarin su daga ɗimbin salihansu.

    Allahu ya daɗa yin tsira da aminci ga Manzon Allah, Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wa sallama. Muna roƙon Allahu, tabaraka wa ta’ala, ya tashe mu a ranar Mahshar a inuwar Manzon Rahama, Manzon Jiƙayi. Ranar da ba wata inuwa sai kawai inuwa tasa. Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammadin, kama sallaita ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima Fil-alamina Innaka Hamidun Majidun. Allahumma salli ala Muhammadin, wa Ashabihi, wa Zurriyatihi, wa Ahli Baitihi, wa sallama taslima. Muhammadur Rasulullahi, sallallahu alaihi wa sallama.

    Manazarta

    Alƙur’ani, mai Tsarki.

    Al-Tirmizy (Babu Shekarar Bugawa) Sunan al-Tirmizy

    Adamu, M. (1987)The Hausa Factor in West African History. Zaria: Ahmadu Bello University Press & Ibadan: Oxford University Press, Nigeria.

    Augi, A. R. (2021) The Gobir Factor in the Social and Political History of the Rima Basin C. 1650 to 1808 AD. Makurɗi, Nigeria: Aboki Publishers.

    Gusau, S. M. (1:2009; 2:2014; 3:2018; 4:2019; 5:2020; 6:2022) Diwanin Waƙoƙin Baka 1, 2, 3, 4 , 5, 6. Kano: Benchmark Publishers Limited; Kano: Century Research and Publishing Limited; Kano: WTPress, Commercial Printing and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (1996) Makaɗa da Mawaƙan Baka na Hausa I. Kaduna: Fisbas Media Services.

    Gusau, S. M. (2008) Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2013) ‘Mizani Tsakanin Waƙoƙin Hausa na Baka da Rubutattu’ a cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture: The 1st National Conference: (Ed. Yalwa L. D.; Gusau, S. M.; Ibrahim Birniwa, H. A.; Abdulƙadir, M. Y.; Chamo, I, Y.; Kano: CSNL, Bayeru University & Zaria: ABU Press Limited.

    Gusau, S. M. (2014) Makaɗan Hausa Jiya da yau. A cikin Garkuwar Adabin Hausa: A Festchrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

    Gusau, S. M. (2014) Waƙar Baka Bahaushiya. BUK Inagural Lecture No. 14. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Gusau, S. M. (2016) ‘Ɗani a Waƙoƙin Baka na Hausa’ A cikin Journal of Hausa Poetry Studies. Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

    Gusau, S. M. (2016) Makaɗa da Mawaƙan Hausa 2. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2021) Rayuwa da Jajircewar Alhaji Dr. Aminu Ladan Abubakar, Alan Waƙa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2022) Fannin Falsafa a Ilmance. Kano: WTPress, Commercial Printing and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2023) Dauloli a Ƙasar Hausa. Kano: WTPress, Commercial Printing and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2023) Jagoran Nazarin Waƙar Baka (Sabon Tsari). Kano: WTPress, Commercial Printing and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2023) Nazarin Al’adu da Adabi a Rayuwar Hausawa. Kano: WTPress, Commercial Printing and Publishing Limited.

    Muhammad, A. S. (2012) ‘Nazarin Ayyukan Makaɗa Sa’idu Maidaji Sabon Birni (1938-2000)’. Juzu’i na 1&2: Kundin Digiri na Biyu (M. A.). Zaria: Sashen Harsuna da AL’adu, Jami’ar Ahmadu Bello.

    Rijiar Lemu, M.S.U.  (1442/2021) Fayyataccen Bayani na Ma’anoni da Shiriyar Al-ƙur’ani, Juzu’i na biyu (2). Amman: Bayinat Center for Ƙur’anic Studies

    Salihu, A. A. (1978) ‘Kaɗe-Kaɗen Hausawa da Bushe-Bushensu da Kayan yin su’ a cikin Makon Hausa 13. Kano: Ƙungiyar Hausa, Jami’ar Bayero.

    Usman, Y. B. (1981) The Transformation of Katsina (1400-1883) Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited. ISBN 978 125 016.

    Tattaunawa Da Wasu Mutane

     

      Suna

    Gari

    Shekara

    1.

    Malam Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe

    Katsira, Sabon Birni  & Abuja

    2023

    2.

    Alhaji Ibrahim Alhassan

    Sabon Birni & Kano

     2023

    3.

    Alhaji Magaji Funtua

    Funtua

     2023

    Wayar Hannu

    4.

    Alhaji Haruna Suleiman Gobir

    Sabon Birni & Kano

    2023

    Tsakure Na Wasu Bayanai Da Hotuna Daga Wasu Kafofi Na Sadarwa

     

     

       Sunan Kafar Sadarwa

    Shekara

    1.

    Kafar Sadarwa ta WhatsApp, na Guruf Diwani­­­­­­ – Waƙoƙin - Baka

    2023

    2.

    Kafar Sadarwa ta Facebook, Shafin Ibrahim Hassan Gobir

    2023

     


    [1] A tarihance, ana bayyana Gobirawa mutane ne masu kuzari, masu ƙama da ƙarfin jiki. Sannan kuma a shirye suke a ko da yaushe bisa ko-ta-kwana. Gobirawa masu zafin nama ne. Wasu masu tarihi na rubuce sukan bayyana Gobirawa Hausawa ne, masu taɗi ko magana da harshen Hausa, kuma a cikin harshen Hausa ne suke gudanar da hulɗoɗinsu na zamantakewa a kuwa kowane ɓangare na rayuwarsu, kamar gudanar da al’adu da maganganu na hikima da balagar harshen Hausa.

    Idan kuwa an amince Gobirawa Hausawa ne, ashe sosai haƙiƙa suna daga cikin mazauna na farko a Ƙasar Hausa, wuri wanda ya zamanto a yankin Arewaci na Afirka (Adamu, M. (1987) Zaria: ABUPress, Sh: 6-7). Gobirawa suna cikin zama na Ƙasar Hausa ne saboda jaruntakarsu da shaja’o’i da bajintarsu da ƙirkizarsu suka tsiri yin ƙaura zuwa wasu ƙasashe tsofaffi, musamman a Afirka ta Gabas da ta Tsakiya da wasu Arewacin Africa da Yammacin Afirka.

    A wata ruwaya da ake badawa, an nuna Gobirawa, sun baro birnin Gubur da yake a cikin Ƙasar Saudiyya, a ɓangarn Afirka ta Gabas daga Tsakiya, suka biyo ta wasu manya da ƙananan garuruwa masu kuwa yawan gaske. Daga nan ne a kwana a tashi,a cikin yaƙi da zaman lafiya, suka iso Gwararrame har zuwa Tsibiri da Gobir Tudu, zuwa Alƙalawa, zuwa Fadamar Kanwa ta Sabon Birni. A kuma tattaunawar da na yi da Ibrahim Hassan Gobir, Laraba, 26/7/2023, ya kawo wata ruwaya da yake faɗin:

    ‘Kakanninsu Gobirawa sun taso daga Gubur, suka miƙo hanya tiryan-tiryan, a shirye cikin ɗaga jijiyoyin jiki, har suka iso Alƙalawa, sai kuma suka je, suka kafa Gwararrame da Birnin Lalle da Birnin Kunya, har kuma aka dawo Tsibiri. A Tsibiri ne aka sami wata matsala tsakanin Sarkin Gobir Bawa Ɗangwanki da Ɗangaladima Gobir a Tsibiri, Hassan Ɗanhalima (Saurari waƙar ; ‘Jikan Jari Ginshiƙ’i ta Nadada Sabon Birni da Sa’idu Maidaji). Daga nan ne Hassan Ɗanhalima ya je ya sami Abdurrahman Ɗanyankasko, Sarkin Musulmi, ya nemi ya ba shi mazauni. Abdurrahman Ɗanyan-Kasko ya ba shi dama a sake ta ya shaci wurin da zai ishe shi da jama’arsa a Ƙasar Fadamar- Kanwa. Wannan ne ya kawo kafuwar Fadamar-Kanwa wadda Hassan Ɗanhalima ya Sarauce ta. Hassan Ɗanhalima ya yi dukkan waɗannan yawace-yawace da kakannina har zuwa 1945 da ruwa ya malale Fadamar-Kanwa, aka koma sabon wuri bisa tudu wanda aka kira Sabon Birni (Domin a ƙara samun fashin baƙi tare da warware wasu matsaloli a dubi: Gusau, S. M. (2003) Dauloli a Ƙasar Hausa. Kano: WTPRess, Commercial Printing and Publishing Limited)’.

    [2] Allahu ya albarkaci Alhaji Hassan da samun ‘ya’ya, maza da mata, kimanin talatin (30). Daga cikinsu akwai yayye da ƙanne na Ibrahim Bagwashe. Daga cikinsu, akwai Alhaji Salihu Bakwai da Alhaji Shu’aibu Nagoshi da Alhaji Shu’aibu Kabo da Alhaji Hassan Atace, Abuja da sauransu.

    [3] Iyaye da ‘yan’uwa da abokai ba su karkata wajen sa wa Ibrahim wata alkunya ba. An ci gaba da kiran sa kai tsaye da sunan da aka raɗa masa na Ibrahim. Sai dai akwai wasu ƙalilan waɗanda suke yi masa laƙabi da Bagwashe ko Iro ko Ibro ta hanyar taƙaita ƙwayoyin sauti na kalmar Ibrahim.

    [4] Kamar yadda aka nuna, wasu masana tarihi, suna ganin an raya tunga ko ƙauyen Katsira a 1945, a shekarar da ruwan sama ya tayar da Birnin Fadamar Kanwa.

    [5] Karatun Zuƙu, shi ne almajirin Alƙur’ani tun daga matsayi na Ɗankuludo ya bibiyi baƙaƙe da wasulla da ayoyi da surori na Alƙur’ani har (114), ya iya karanta su cikin zubin Larabcinsu ba tare da lalle sai ya iya tarjama su ba. Wannan wata fassara ce ta karatun zuƙu.

    [6] Wato Government Secondary School (GSS) Sabon Birni.

    [7] Wato Performance and Communication.

    [8] Wato break da Ingilishi.

    [9] Wato Recorder.

    [10] Kada a manta a Ƙasar Hausa an sami zuwa na wasu al’ummu baƙi, da suka shisshigo dangane da wasu lokuta da ƙarni-ƙarni mabambanta kamar Fulani da Larabawa da Turawa da Barebari da Nupawa da Yarbawa da Igbo da sauransu da yawa.

    [11] Yanar-Gizo ko Intanet.

    [12] Manhajoji ko kafofi sun haɗa da kafa ta WhatsApp ko Facebook ko Instagram ko Twitter ko YouTube ko sauransu waɗanda ake amfani da salula da nau’o’in wayoyin hannu da Kwamfutoci da dangoginsu.

    [13] A mahanga ta zahiri, Malam Ibrahim Gobir ya samo batun nan ne daga suna na wani Littafi na Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau: Diwanin Waƙoƙin Baka. A yau wannan littafi yana da juzu’o’i guda shida (1(2009); 2(2014); 3(2018); 4(2019); 5(2020) & 6(2022).

    [14] Haƙiƙa, amon murya da na kiɗa su ne suke haɗuwa su samar da waƙar baka ta Hausa. Waɗannan abubuwa biyu (2) suke gamuwa har a iya rera waƙar baka, a kuma sadar da ita. A yayin da ake furta kalmomi a matsayin muryar waƙar baka, wajibi ne a daidaita nauyin kiɗa domin mai sauraro ya gane ƙananan saƙonni na kalmomin da ake rerawa. Amma a lokacin da ake so a harraka mutane da kiɗa, sai shi kuma makaɗi (wato mai furucin muryar waƙa) mai yin furucin murya ya tsahirta.

    [15] Ɗakin Sitidiyo, ɗaki ne wanda ake zuba wasu na’urori da Turawa suke yin su, suke kuma ajewa a ɗakuna da suke kira Sitidiyoyi. Ta amfani da na’urorin ne suke daidaita amo ko sauti na kiɗa. Ke nan Sitidiyo ɗaki ne wanda yake ƙunshe da kayayyaki na yin kiɗa da daidaita amo kamar ganguna da kwamfutoci da miksoshi da bigiloli da tasoshi da tsintsiyoyi da mikirifofi wato amsa-kuwa ko lasifikoki da madangantansu.

    [16] A yau, a Ƙasar Hausa da Nijeriya, makaɗa masu aiwatar da waƙoƙin Hausa na baka sun daɗa laƙantar amfani da ɗakin Sitidiyo. Yanzu ta kai, makaɗi yakan rubuta zubin waƙar ne wato ta harhaɗawa da zaɓen kalmomin waƙa (composing), sannan ya karanta su da furuci na muryarsa (voicing). Daga nan ne zai tafi, ya shiga Ɗakin Sitidiyo, sai Makaɗan Sitidiyo, su ƙirƙira wa furucin na muryar waƙa, kiɗa (Sound/Voice), su kuma sarrafa shi gwargwadon nauyi da zaƙin kiɗan da ake bukata. Bayan haka, sai su ɗora murya ta furuci na mai waƙa (Jagora). Idan kuma ana son waƙar ta zama ta Ƙungiya, sai a daɗa ɗora murya ta masu karɓi (‘Y/Amshi) daga furuci na muryar jagora, sai a sarrafa muryar tasa ta zama muryoyi na wasu mutane (miɗing). Na’ura ta Miksa, ita ce jagora wajen sarrafa na’urorin sitidiyo. Na’urar ce kuma take yin wannan aiki, ba mai shiryawa ko aiwatarwa ko rubuta waƙa ba, wanda kuma zai iya zama makaɗi da kansa, ko wani mai tsara kalmomin waƙa. Ta wannan sabuwar hanya ce ake bi a samar da Rauji na waƙar baka. A dinga sauraro kamar ko daidai-wa-daida da Rauji na waƙoƙi na makaɗan baka na asali da wasu suke kira Makaɗan Gargajiya.

    To, mene ne matsayin wannan sabon tsari na fitar da Rauji? A fannin nazarin waƙar baka tun daga farko zuwa yau, idan aka sarrafa na’urori a Sitidiyo, aka samar da irin raujin nan sabo, bai share Jagora da ‘Y/Amshi ba, suna nan a matsayinsu kama da kafin zuwan na’ura. Domin haka, idan za a wakilce su a takarda, dole a rarrabe yanayi na rubuta su zuwa waƙoƙi na ƙungiya da waƙoƙi na kaɗaita, kamar haka:

    a)       Ƙungiya:       Jagora:-----------

    :‘Y/Amshi:--------

    b)       Kaɗaita:        Jagora:-----------(kawai).

    [17] Usra, kalma ce ta Larabci wadda take nufi da iyali na mutum waɗanda suka haɗa da matar aure da ‘ya’ya da jikoki da jikan jika da kama-kunne da tattaɓa-kunne da sauransu (http://en.bab./a/dictionary/malay-english/usrah ko kuma https://www.wordhippo/arabic-word).

    [18] Muna taya murna da yi wa Malam Ibrahim addu’a, Allahu ya daɗa aura masa mata saliha ta gari, mai biyayya, mai kiyaye sirri da amanonin mijinta. Mata wadda za ta zama mai kunya, mai kara, mai kiyaye ibada da hidimominta na gida. Mai kyawawan hasloli, musamman a mu’amaloli na zaman aure.

    [19] Zaɓen yi wa masoya gaishe-gaishe, ba na ‘yantakara a Siyasa ba.

    [20] Akwai wasu ayyuka da Gusau, S. M. (2008:448; 2023:26; 2022: 152-174; 2021: 48-50) ya gabatar waɗanda ya yi bayanai a kan makaɗan baka na Hausa inda aka rarraba su bisa dangantakoki na waƙoƙinsu, aka saka su a kadadu guda uku da suka haɗa da (i) Makaɗa masu yin waƙoƙin bege (ii) Makaɗa da Masarta masu waƙoƙi da kirari da kaɗa taken Sarauta ko fada (iii) Makaɗa masu waƙoƙin jama’a, na mutanen da ba a (i) ko na (ii) suke a ciki ba.

    Download the article:

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.