Habaici A Wasu Wakokin Makada Sa’idu Faru

    Citation: Sulaiman, M., Agigi, A.M. & Madawaki, S.A. (2024). Habaici a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 349-354. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.049.

    Habaici a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    Na

    Maimunatu Sulaiman

    Department of Hausa Language.
    Zamfara College of Arts and Sciences (ZACAS)
    maimunatusulaiman7@gmail.com
    (+234) 08032145373

    Da

    Aisha Muhammad Agigi

    Department of Hausa Language.
    Zamfara College of Arts and Sciences (ZACAS)
    aishamuhammadagigi@gmail.com
    (+234) 08062243738 

    Da

    Saifullahi Ahmed Madawaki
    Department of Hausa Language.
    Zamfara College of Arts and Sciences (ZACAS)
    madawakisahmed@gmail.com
    (+234) 07068818980

    Tsakure

    Makaɗa Sa’idu Farusanannen mawaƙin baka ne na ƙasar Hausa. Wanda ya ƙware sosai wajen kiɗan fada.Yana da hikima ta tsara magana da ke kambama wanda yake yi wa waƙa. Manufar wannan maƙala ita ce: fito da wasu kalamai na habaici da Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a cikin wasu waƙoƙinsa, da auna nauyin waɗannan kalamai na habaici da yake yi domin fifita wanda yake yi wa waƙa a kan masu adawa, sannan kuma da bayyana matsayin waɗannan kalamai na habaici a al’adance. Za a yi amfani da hanyar hira da ma’abota ilimi musamman kan abin da ya  shafi waƙar baka. Haka kuma za a yi amfani da hanyar sauraron wasu daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Farudomin samun hujjojin gina wannan maƙala. Baya ga waɗannan kuma,  za a yi amfani da hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da kundaye da mujallu da maƙalu da aka gabatar domin ƙara wa juna sani duk domin samun hujjoji da za su gina wannan maƙala. Hanyar  da aka  ɗora aikin a kanta kuwa, ita ce mazhabar waƙar baka Bahaushiya. Wannan bincike ya gano cewa mafi yawan waƙoƙin makaɗa Sa’idu Farusuna ƙunshe da habaici. Sannan kuma nauyin wannan habaicin yana tasiri ga zukatan masu sauraro. A mizani na al’ada kuwa ana danganta wannan habaici da ƙazafi ko ƙirƙira wani abu ga wanda ake yi wa wannan habaici. Haka kuma yin wannan habaicin yana nuna nauyin yadda makaɗin ke kallon masu adawa ko abokan hamayyar wanda ake yi wa waƙa.

    Gabatarwa

    Makaɗa Sa’idu Farumawaƙin baka ne wanda ya shahara a fagen kiɗan fada. Yana da hikima ta tsara magana da ke kambama wanda yake yi wa waƙar, da kuma yin habaici ga abokan hamayyar ubangidan nasa. A cikin tubalan ginin waƙoƙinsa yakan yi amfani da habaici, wato wasu maganganu da yake faɗi a fakaice domin rataya wa wani mutum ko wasu mutane ba tare da fitowa ƙuru-ƙuru ba, wajen bayyana wannan mutum ko waɗannan mutane. Ganin yana yawaita amfani da waɗannan hikimomi ne  ya ƙarfafa gwuiwar wannan bincike domin  fito da  habaice-habaicen da ya yi a cikin wasu waƙoƙinsa, domin huce takaicin abokin gabar ubangidansa, da kuma nuna matuqar girman da ubangidansan yake da shi. Wannan maƙala tayi azamar bada tata gudunmuwa kan taron ƙarawa juna sani da Jam’iar Gwamnatin Tarayya ta dake Gusau jahar Zamfara ta shirya domin karrama makaɗa Sa’idu Faru, lura da tarihi na neman shafe ƙwazon da makaɗan baka sukayi musamman shi makaɗa Sa’idu Faru. Daga cikin hikimomin nasa na waƙa sai kuma ɗauki habaici domin bada tamu gudunmuwa.

    Hanyoyin Gudanar da Bincike

    Wannan muƙala ta yi amfani da hanyar karance-karancen bugaggun littafai da kundayen bincike da mujallu da muƙalu da aka gabatar a taruka daban-daban na ilimi. Haka kuma, antattauna da ma’abota ilimi musamman abun da ya  shafi waƙar baka. Harwayau, an yi amfani da hanyar sauraron wasu daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Farudomin samun hujjojin gina wannan muƙala. An samo waɗannan waƙoƙi ne a zauren da aka buɗa don ƙarawa juna sani kan taron da za’ayi kan waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. Haka kuma an nazarci waƙoƙin nasa ta hanyar saurarensu a kaset da aka naɗi waƙoƙin.

    Mazhabar da aka Ɗora Aiki a Kai

    An ɗora wannan muƙala ne a mazhabar waƙar baka Bahaushiya. Wannan mazhabar ta fi raja’a ne da bayar da ƙarfi wajen bayyana (tarihi, asali, da salsalar waƙar baka ta Hausa da zurfafa bayani kan turke da ayyana tubalan ginin turke da yanayin sassarƙuwar adabi da al’adu a waƙar baka da nazarin awon baka da adon harshe da kuma aiwatar da harshe.) Gusau, S.M (2015:23). Kasancewar aikin nan yana da alaƙa da wannan mazhaba yasa aka ɗora aikin akanta. Hakan ya sa aka gano mafi yawan waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Farusuna ƙunshe da habaici. Sannan nauyin wannan habaicin yana tasiri ga masu saurare.

    Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru

    An haifin Makaɗa Sa’idu Farua garin Faru a cikin ƙaramar hukumar Maradun, Jihar Zamfara wajajen shekara ta 1932. Ana kuma yi masa laƙabi da “Ɗan Umma” Wanda matar ƙanin ubansa ta sanya masa, saboda baya faɗin sunanta, sai dai yana kiranta Umma. Sunan mahaifinsa shi ne Makaɗa Abubakar mai Kotso ɗan Makaɗa Alu mai kurya. Ke nan Makaɗa Sa’idu Faru ya gaji Kiɗa da Waƙa daga mahaifinsa, wanda shi kuma ya gadane daga mahaifinsa. Mahaifiyarsa, Halimatu mutuniyar Banga ce da ke masarautar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara. Duk da yake Makaɗa Sa’idu Farubai samu ilimin Muhammadiya mai yawa ba, amma ya yi karatun Allo gwargwadon hali da ya taimaka masa wajen sanin addininsa. Bai yi karatun boko ba, domin haka ne ya buɗe idanu da sabgar gidansu wato Kiɗa da Waƙa tun yana ɗan karaminsa. Yana da misalin shekara Bakwai (7) aka fara fita yawon kiɗa da waƙa tare da shi, da ya kai kimanin shekara goma (10) ya soma amshin waqa a ƙungiyar kiɗa ta mahaifinsa tare da sauran ’Yan uwansa. Da yaga kamar ƙarfinsa ya kawo a shaanin kiɗa da waƙa, sai ya dakatar da mahaifin nasa daga wannan sabga, ya ɗauki jagorancin ƙungiyar ya ci gaba da gudanar da waƙoƙin sarakuna kamar yadda ya taras a gidansu. Bayan soma cin gashin kansa, waƙar da ya fara yi ita ce ta dagacin garinsu, wato Sarkin Yamman Faru, Ibrahim Abubakar. Misali:

    Jagora/Y/Amshi: Bi da maza Ɗan joɗi na Rwahi,

    : Iro magajin Shehu da Bello,

    Jagora: Dawaya kora ɗimau na Wakili,

    ‘Y/Amshi: Dawaya kora ɗimau na Wakili,

    Jagora: Dawaya kora ɗimau na Wakili,

    ‘Y/Amshi: Dawaya kora ɗimau na Wakili,

    : Uban S/gida Bello da Yari,

    Jagora: Ruwa da Kada…

    ‘Y/Amshi: Ɗibgau na Magaji,

    : Sai tsohon wawa ka shigas su,

    Jagora: Kai ak ko yau ko gobe Maradun,

    ‘Y/Amshi: Kai ak ko yau ko gobe Maradun,

    : Turawa sun bada Wasiƙa,

    Jagora/Y/Amshi: Babu mazan da ka ja maka,

    : Jikan Atto bani Usumanu Atiku,

    Jagora: Hasken fitila…

    ‘Y/Amshi: Ba ɗai da wata ba,

    : Tamraro hasken ka subahin,

    Jagora: S/yamma inai maka fata…

    ‘Y/Amshi: Ya Allah ya yi ma tabaruka,

    Jagora: S/yamma inai maka fata…

    ‘Y/Amshi: Ya Allah ya yi ma tabaruka,

    :  Don girman Lawali da Risala,

    : Don hasken Yasin da Muqama,

    : Bi da ɗan Joɗi na Rwafi,

    : Iro Magajin Shehu da Bello.

    Baya ga Sarkin Yamman Faru, Sa’idu Faru ya ci gaba da waƙoƙinsa ga sauran uwayen gidansa kamar Sarkin Yaƙin Banga Sale Abubakar da Sarkin Kiyawan Kaura Namoda Abubakar Garba da Sarkin Zamfara Zurmi Sulaiman Muhammadu Sambo, kafin haɗuwarsa da babban ubangidansa, Sarkin Kudun Sakkwato, Alh. Muhammad Macciɗo Abubakar III a Shekarar 1953, lokacin da aka kawo shi Talata Mafara a matsayin uban ƙasa. 

    Makaɗa Sa’idu Faru yana da fasaha da naƙaltar harshen da yake waƙa da shi, kuma ya iya zubin waƙa yadda za ta yi kyawo da ma’ana, fahimtarsa ga waƙa shi ya sa yake kiran kansa Malamin Waƙa. Ga abin da yake cewa a cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ta Farin cikin Musulmin duniya:

    Jagora: Sa’idu Malamin Waƙa,

    : Mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba (Maimaitawa)

    ‘Y/amshi: Ban wuce gonata da Irina ba, inda Sarkin Kudu nattsaya.

    (Gusau: 1996)

    Makaɗa Sa’idu Farubai yi wa kowa waƙa sai Sarki ko wanda ya jiɓinci Sarauta. Ya kan faɗa cewa idan zaka yi wa talaka waƙa ba ya da nasabar da zaka danganta shi da ita, musamman ta iyaye da kakanni, amma idan basarake ya ɓata maka rai, sai kayi masa habaici cikin waƙar ka, to sai ransa ya ɓace domin ba ya buƙatar abin da zai ɓata nasabarsa (Gusau, 1996:117).

    Makaɗa Sa’idu Faru ya rasu a shekarar 1987, ya bar matan aure guda biyu da “yaya goma sha biyu, maza shida da mata shida. Ya zuwa yanzu gidansa bai mutu ba a fagen kiɗa da waƙa, domin ɗansa Alh. Ibrahim Sa’idu Farushi yake jagorantar ƙungiyar kiɗa da ya bari.

    Ma’anar Habaici

    Habaici, magana ce mai ɓoyayyar manufa. Akan yi magana da niyyar nufin wani abu ga wanda aka yi maganar dominsa. To amma, shi habaici, idan ba mutum ya san kan zance ba, ba kasafai ake gane wanda aka yi habaicin dominsa ba (Ɗangambo, A. 1982). Habaici shi ne wasu maganganu da ake faɗi a fakaice domin ratayawa wani mutum ba tare da bayyana mutumin da ake nufi ba ƙuru-ƙuru. Amma shi wanda ake nufi wani lokacin da wuya ya gane abin da ake nufi da shi ake yi. (Adamu, 2008:130). Habaici kalmomi ne da ake amfani da su wajen muzantawa ko tozarta mutum a fakaice, musamman idan ana son a sa mutum a baƙin ciki ko kuma ya ji haushi, sai a dinga yin magana a kan abin da ya shafe shi ko kuma wasu ɗabi’unshi.

    Yahaya da Zariya da Gusau, da kuma ‘Yar’aduwa (1992) sun ce: “Habaici kalmomi ne da ake amfani da su a fakaice don muzanta mutum”. “Ɗangambo (1984) cewa ya yi “Habaici, wata hanya ce ta zagin mutum a fakaice”.

    Zarruk da wasu (1986:47) sun faɗi cewa, “Habaici shi ne ko gugar zana duk ana nufin abu ɗaya ne. Habaici shi ne yi da mutum a kaikaice. Habaici ya fi yawa inda kishi ko ƙyashi”.

    Habaici Magana ce da Hausawa ke amfani da ita domin isar da saƙo, a hikimance, azanci da ƙwarewa a cikin magana. Ana yin habaici saboda dalilai masu tarin yawa ga wasu daga cikin su:

    a)      Jan kunne

    b)     Ramuwar gayya

    c)      Tsokanar faɗa

    d)     Rowa

    e)      Hassada

    f)       Aikata wani muhimman aiki, da dai sauransu.

    Habaici magana ce da ake yi a dunƙule cikin duhu ba kai tsaye ake fito da maganar ba, sai dai wanda ake yi dominsa ya san da shi ake yi. Kowane ɗaya daga cikin abubuwan da aka zayyana da ma wasunsu, in suka Faru sai a yi amfani da habaici a cusa wa wanda ake magana da shi haushi.

     Makaɗan Hausa sukan yi habaici a cikin waƙoƙinsu. Musamman makaɗan fada, makaɗa Sa’idu Faru yana daga cikin makaɗan fada kuma ya yi habaice-habaice a mafi yawa daga waƙoƙinsa. Ga wasu daga cikinsu.

    Ginidin waƙar: Ba jinin gidan Mamman na yari,

    : Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.

    Jogora: Shi wane girma shi kai bai da wayo,

    Y/Amshi: ya togu daidai shina nan bani na,

    : ya bar azumi da kono da sunnah,

    : sai ya ji goge shi ɗauko kujera,

    : a shisshirya benci matsata su zanna,

    : a aika a ɗauko kwalabe a buɗe,

    : da ka gane ka koma ma Allah,

    : ko da inyamuri yab bi Allah,

    : shi ad da shi babu mai tsarguwatai.

     

    Wannan habaici ne, da makaɗa Sa’idu Faru ya yi a cikin waƙar da ya yi wa ubangidansa Sarkin Kudu Macciɗo. Inda ya yi wa abokin adawarsa habaici, inda ya bayyana shi a matsayin wanda ba ya azumi da kono, da Sunnah. Ga al’adar Bahaushe idan aka ce mutum ba ya ɗaya daga cikin shikashikan Musulunci to ana yi mashi kallon mutumin banza, duk girmansa duk asalinsa. Balle ga shi ya lissafa ɗabi’un banza ga mutumin. Waɗannan kalmomi da ya rataya wa abokin adawar ubangidansa, suna da muni sosai ga rayuwar Bahaushe, sannan kuma suna da nauyi a zukatan masu saurare. Suna kuma da tasiri da sosa rai ga wanda aka yi masu. Haka, ya ƙara kwatanta shi da wanda ba ya farilla, balle ya yi nafila, wato ba ya yin ibadar dole balle ya yi wadda ba dole ba, wato azumin da kono da ya ce.

    Haka, dai ya ƙara fito da habaici a wata waƙa da ya yi wa Sarkin Yawuri Muhammad Tukur. Ga abin da yake cewa:

     Gindin Waƙa: Koma shirin daga na Bubakar

    Jagora: Amma shi ko har da dama-dama,

    ‘Y/Amshi: Ga wani Sarki na ta kumburi,

    : Da yara nai sun sha mashi hura.

    Jagora: Ga wani Samɓolon uban ƙasa,

    ‘Y/Amshi: Da yara nai wajjen guda huɗu,

    : Ba ko mai Suturar kwabo huɗu,

    : Ya shiga mota ya yi tagumi,

    : Da kwandon ɗunya yay yi guzuri.

    (Gusau, S.M (2009:171)

     

    Idan muka dubi waɗannan ɗiyan waƙar da kyau, za mu ga cewa habaici ne da makaɗa Sa’idu ya yi ga wani Sarki, da wani ubanƙasa, inda ya kwatanta Sarkin da kumburi wato ya sha toka, yana fushi, sakamakon ganin ubangidansa.

    Wannan shaguɓe ne ya yi ga wani Sarki da yake adawa da ubangidansa. Kumburi kalma ce da ke nuni da ɓata fuska, sakamakon rashin jin daɗin rayuwa, bisa ga wani abu da ka ji, ko ka gani. Haka kuma ya yi habaici ga wani ubangidansa da yake adawa da ubangidansa ko kuma ya ɓata masa rai. Wato ya kwatanta shi da samɓolo, a al’adar Hausawa samɓolo yana nufin samna ko sakarai wanda bai san ciwon kansa ba. Don haka, duk wanda yake da waɗannan halayen ba zai iya zama sarki ba, don ko kansa ba zai iya riƙewa ba balle al’umma. Haka dai makaɗa Sa’idu Faru ya ƙara yin habaici a cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo inda ya ce:

    Gindin Waƙa: koma shirin daga na Bubakar,

    : Gamɗarin Alƙali wan maza.

    Jagora: Ga wani Sarki ba shi da zagi,

    : To kuma sannan bai da guzuri,

    : Garin rogo ɗai suka ta ci da guru,

    : Kowane na aza ruwa.

     

    Sa’idu Faru ya yi habaici a wannan ɗan waƙa domin ƙara nuna martabar ubangidansa, da kuma yin shaguɓe ga abokan adawarsa, inda ya nuna ba ya da zagi. Zagi shi jami’i ne mai shiga a gaban dokin Sarki. Danganta shi da rashin zagi, tamkar zubar ƙima ce da daraja ga idon Hausawa. Ya kuma ƙara kwatanta shi da tawagarsa da rashin guzuri, wato Sarkin talaka ne da garin rogo suke guzuri. Garin rogo ba cimar Bahaushe bace asali, wahala da yunwa da rashin tabbas kesa Bahaushe cinsa da kuma yawaitar shi a kasuwanninsu, alama ce ta yunwa a kasarsu. Ya yi wannan habaicin ne, don ya nuna ƙima da darajar wanda yake yi wa waƙar, da kuma ƙasƙanta abokan adawar ubangidan nasa. Sanannen abu ne, a ƙasar Hausa Sarki mutum ne mai arziƙi da cikakken iko, don haka bayyana shi a matsayin akasin haka, tabbas zai sosa masa zuciya, dama kuwa, wannan shi ne dalilin yin habaicin: domin ya sosa zuciyar yan adawa ya kuma ƙara ɗaukaka ubangidansa. Ya kuma huce takaicin zamansa ɗan adawar, da kuma ƙoƙarin tasirantar da hakan, ga zukatan masu sauraro. Haka kuma, ya yi habaicin ne don ya cusa takaici ga zuciyar wanda ya yi wa habaicin da kuma fadawansa, ko ‘yan tawagarsa. A cikin waƙarsa ta Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Alhaji Ahmad Muhammad Asha, ya yi habaici kuma ga abun da yake cewa:

    ‘Y/amshi: Sarki yai sarki cigari,

    : ya gado rinjaye abu,

    : Toron giwa jikan isau,

    : Mashasha banwaren Alu.

    Jagora:  Kana ta harare-hararenka Daudu,

    : Ni dai ban gane kanka ba,

    : Sa babba sata nig gani,

    : Tsohon ɗan sarkin mai kwaɗai,

    : Tsohon Ɗan Sarki Angulu,

    : Kolo komi namanka na,

    : Kolo komi namanka na,

    : Komi dai kas samu ka ci.

     

    A waɗannan ɗiyan waƙar, habaici ne makaɗa Sa’idu Faru ya yi ga abokin adawar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda. Daudu shi ne Dangaladiman waƙa, ko kuma duk wani mai jiran gadon Sarauta ana kiransa da Daudu. A nan Makaɗa Sa’idu Faru yana nuni ne ga Dangaladimansa Mu’azu cewa ya lura da wani ɗan sarki yana ta harare-harare. Harara wata ɗabi’a ce da take nuna jin haushi game da wani abu da ya damu mutum. 

    A nan yana nuna cewa wancan ɗan sarkin yana jin haushin Sarkin kiyawan Kaura. Harwayau, ya ƙara kwatanta shi da kwaɗayi, kuma ga shi kwaɗayi mummunar ɗabi’a ce wadda take zubar da kima da mutumcin mai yin ta a idon mutane. Kwatanta shi da ɗan Sarki muzantawa ne gare shi, da kuma idanun masu saurare. Ɗan Umma ya ƙara yi masa habaici da cewa Angulu. Angulu dai wani tsuntsu ne, wanda yake cin komai. Wato komai ya samu zai ci har da ƙazanta. Hakan ya sa musulunci ya yi hani da cin naman angulu. Ba wanda aka yi wa habaicin ba ko wanda ya saurari habaicin zai tabbatar da cewa kalamai ne da suke nuna muzantawa ga wanda aka yi wa su. Musamman a ce ɗan sarki mai cikakkiyar nasaba. A baya an faɗi cewa, ana yin habaici ne domin huce takaici ko don mayar da martani da sauransu. Waɗannan kalamai da suka gabata suna nuna nauyin adawar da yake yi da ubangidansa da kuma huce takaici game da adawar da yake yi da ubangidansa. 

    Makaɗa Sa’idu Faru ya kara yin wani habaici a wata waƙar tasa inda yake cewa:

    Jagora: wanga yana haka gurun kolo,

    : Wanga na nan haka tandun ba’u,

    : Marag gaɓoɓi wat taba,

    : Sarki da hangaham baki ya twaɓe?

     (Waƙar Sarkin Zamfaran Zurmi Suleimanu Muhammadu)

     

    A wannan habaicin ya kwatanta abokin adawar maigidansa da gurun kolo. A zahirin kalmar gurun kolo shi ne sassan jikin kolo idan aka yayyanka aka soya. Amma a al’adance idan ake ce gurun kolo, shi ne abu wanda ba ya da wani amfani. Duk yanda ya ji suya ba za a iya cin sa ba, saboda an yi hani da cinsa a musulunci. Kenan, suyarsa ba shi da wani amfani. Bahaushe yana yi masa kirari da “gurun kolo ba ka kashin kunya’’ wato duk yadda ya soyu ba zai yiwu a tarbi baƙi da shi ba. Makaɗa Sa’idu Faru ya nuna cewa duk girmansa ba ya da wani amfani, kuma ba ya kashin kunya, wato shi sarkin da yake yi wa habaicin. Haka kuma, ya kwatantashi da tandun ba’u. Wannan wani tandu ne da ba a iya saka mashi mai domin tsiyaya yake yi saboda haka man zai zube ne ga banza. Kenan dai wannan ɗan sarkin da aka jefa da wannan kalmar ta habaici ta nuna ba shi da amfanin komai. Haka kuma ya kwatanta shi da marar gaɓoɓi, kuma mai hangaham baki kuma bakin taɓaɓɓe.

    A nan Ɗan Umma yana nuna cewa ɗan sarkin ba shi da wani kuzari ko karsashin da zai iya zama sarki, kuma halittar bakinsa kaɗai ba za ta ba shi damar zama sarki ba.

    Makaɗa Sa’idu Faru ya ƙara yin wani habaicin inda yake cewa:

    Jagora: Ga shi kamar malami,

    : Ga sanda tare da mala,

    : Kabag gani nai rike da casbaha,

    : Bai iya ba sin ba”

     

    A cikin waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar Garba ne aka ciro ɗan waƙar da yake a sama. Waɗannan ɗiyan waƙar da makaɗa Sa’idu Faru ya yi, habaici ne ya jefi wani sarki da su ya siffanta shi da siffar malamai ta riƙe sanda da casbaha da mala. Mala na nufin Gafakka/jaka ta fatar dabbobi da ake saka Alqurani ko wasu littafai na addini a cikinta. Dukkan waɗannan siffofi suna nuna cewa ya yi shigar malamai, amma kuma ba malami ba ne kenan ya jefe shi da kalmar jahilci a fakaice.

    A Bashaushiyar al’ada idan aka ce wannan jahili ne, to ba shi da wata ƙima ko daraja a idon Hausawa.

    To balle a ce ko farkon fara karatun addinin musulunchi bai iya ba, kenan jahilcin nasa ya kai maƙura.

    Haka makaɗa Sa’idu yaƙara yin habaicin ya ce

    Jagora: Kakan wani ba shi da yaƙi ko can

    : Ɗan daudu na shi,

    : Kaka nai ka suna,

    : Da madubi nai da hoda,

    : Da hwarar riga da kore,

    : Da gani nai ka ga kure,

    : Geme cim jim da shuni.

     

    ‘Yan Amshi: Babban bajimin gidan Sambo,

    : Shirin ka daban da raggo,

    : Jikan Mamuda Sarkin Nasara baban Baraya.

    A cikin waƙarsa ta margayi maigirma Sarkin Zamfaran Zurmi Suleiman Muhammadu Sambo. A wannan ɗan waƙar habaici ne makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa wani ɗan sarki cewa kakansa bai iya yaƙi ba, har ya kwatanta shi da daudanci, da shafa kwalli, har da madubi da hoda. Kenan ya soki kakansa da ragwanci, har ta kai ga daudanci da rashin iya yaƙi.

    Ga al’adar Hausawa, abin takaici ne a samu namiji da kwaikwayar ɗabi’un mata. Ya kuma ƙara jifar kakan da cewa kure ne. Kure dai, shi ne namijin kura wato ya danganta shi da ɗabi’ar kure ta rashin amana da rashin sabo. Sannan kuma ya ƙara da cewa ya shafe gemu da shuni. Shuni dai wata kala ce da ake amfani da ita don yin kwalliya, wato dai shi kakan ba shi da aiki sai ɗabi’ar mata da kwaikwayar halayensu. Duk da ga shi an ce yana da kamalar maza ta gemu.

    Kammalawa

    Habaici dai ɗan’uwan zambo ne, sai dai shi habaici bai yi tsananin zambo ba. Habaici wasu kalmomi ne da ake ratayawa mutum, ba tare da kama sunansa ba kai tsaye. Waɗanda suka fi yin habaici a cikin al’ummar Hausawa su ne mata, sai kuma makaɗan fada, kamar makaɗa Sa’idu Faruda makamantansa. Muradin wannan mukala shi ne zaƙulu wasu habaice-habaice da makaƙa Sa’idu Faru ya yi a wasu waƙoƙinsa da kuma nuna nauyinsu a al’adar Hausawa, da ma bayyana ma’anar wasu daga ciki.

    Manazarta

    Ɗangambo, A. (1982) Adabin Hausa da rabe-rabensa. Zariya: NNPC

    Zarruk, R.M da Kafin Hausa A. da Bello S.Y (1986). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare. Ibadan: University Press plc.

    Gusau, S.M (2015) Mazhabobin Ra’i da tarke a adabin da al’adu na Hausawa: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau S.M (1996) makada da mawakan Hausa Usman A/amin Publishing Company Kano, Nigeria.

    Gusau S.M (2014) Diwanin waƙoƙin baka juzu’i na biyu. Kano:  Century Research and Publishing Limited.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.