Hukincin Zama A Saman Kabari

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalam alaikum. Dan Allah Menene hukuncin Zama A kan Kabari? Zaka ga waɗansu mutane idan Ana jana'iza A makabarta suna zaunawa kan Kabari. Musamman irin wanda akayi ma siminti aka zagayeshi lokacin da ake bisne Mamaci? ka huta lafiya.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

    Wajibi ne ga kowanne musulmi ya kiyaye mutunci da alfarmar kowanne ɗan Adam, musamman ma musulmi. Alokacin da yake raye ko bayan rasuwarsa. Wannan ita ce koyarwar addinin Islama.

    Zama kan Ƙabari ko tafiya bisa kanshi, ko zuba shara akansa, duk nau'i ne na wulakanci ga mamacin. Kuma Annabi (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) watarana yaga wani mutum yana taka kan Ƙabari, sai yace masa : "WALLAHI ƊAYANKU YA ZAUNA KAN GARWASHIN WUTA WANDA ZAI KONE TUFAFINSA YA CINYE FATAR JIKINSA SHI YAFI ALKHAIRI GARESHI FIYE DA ZAMANSA AKAN ƘABARI" (Sahihu Muslim hadisi na 9711, Sunanu Abi Dawud hadisi na 3,228).

    Bisa hujjar wannan ingantaccen hadisi dukkan Malaman musulunci suka dogara wajen tabbatar da cewa bai halatta mutum ya zauna kan Ƙabari ko taka kan Ƙabari ko zuba shara akansa ba.

    Duk lokacin da kaga wani ya aikata haka, yi kokari kayi nasiha gareshi cewa Annabi (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) ya hana. Kayi aiki kenan da ayar Alƙur'ani  inda Allah ke cewa "KA TUNASAR,  DOMIN TUNASARWA TANA AMFANAR DA MUMINAI NE".

    Da kuma hadithin Annabi (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam)da yace "WANDA YAGA ABIN ƘI DAGA CIKINKU, TO YA CANZASHI DA HANNUNSA. IDAN BAZAI IYA BA, TO DA HARSHENSA. IDAN BAZAI IYA BA, TO DA ZUCIYARSA".

    WALLAHU A'ALAM.

    DAGA ZAUREN FIƘHU 

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.