𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, ko ya halatta wanda ba musulmi ba ya yi aikin yin fenti (painting) a masallaci?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa
Barakaatuh.
Hadisi daga Abdu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ya
ce:
بَعَثَ النَّبِيُّ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - خَيْلًا
قِبَلَ نَجْدٍ، فَجَاءَتْ بِرَجُلٍ مِنْ بَنِي حَنِيفَةَ يُقَالُ لَهُ ثُمَامَةُ بْنُ
أُثَالٍ، فَرَبَطُوهُ بِسَارِيَةٍ مِنْ سَوَارِي المَسْجِدِ، فَخَرَجَ إِلَيْهِ النَّبِيُّ
- صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -، فَقَالَ: «مَا عِنْدَكَ يَا ثُمَامَةُ؟» فَقَالَ:
عِنْدِي خَيْرٌ يَا مُحَمَّدُ، إِنْ تَقْتُلْنِي تَقْتُلْ ذَا دَمٍ، وَإِنْ تُنْعِمْ
تُنْعِمْ عَلَى شَاكِرٍ، وَإِنْ كُنْتَ تُرِيدُ المَالَ فَسَلْ مِنْهُ مَا شِئْتَ،
فَتُرِكَ حَتَّى كَانَ الغَدُ، ثُمَّ قَالَ لَهُ: «مَا عِنْدَكَ يَا ثُمَامَةُ؟» قَالَ:
مَا قُلْتُ لَكَ: إِنْ تُنْعِمْ تُنْعِمْ عَلَى شَاكِرٍ، فَتَرَكَهُ حَتَّى كَانَ بَعْدَ
الغَدِ، فَقَالَ: «مَا عِنْدَكَ يَا ثُمَامَةُ؟» فَقَالَ: عِنْدِي مَا قُلْتُ لَكَ،
فَقَالَ: «أَطْلِقُوا ثُمَامَةَ». فَانْطَلَقَ إِلَى نَجْلٍ قَرِيبٍ مِنَ المَسْجِدِ،
فَاغْتَسَلَ ثُمَّ دَخَلَ المَسْجِدَ، فَقَالَ: أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ،
وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ.
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya
aika wata runduna ta mahaya ta jihar Najd, sai kuwa suka komo da wani mutum
daga cikin ƙabilar
Banu-Haneefah ana kiransa: Thumaamah Bn Uthaal, suka ɗaure shi a jikin wani ginshiƙi daga cikin ginshiƙan cikin masallaci. Manzon Allaah (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fito gare shi ya ce: ‘Thumaamah, yanzu me kake tsammanin zan yi maka?’ Ya ce: ‘Ina zaton
alkhairi, ya Muhammad! Idan ka kashe ni, ka kashe mai haƙƙi. Idan kuma ka yafe, to ka yafe wa mai godiya.
Idan kuma dukiya kake buƙata, ka tambayi abin da kake so.’ Sai ya ƙyale shi zuwa washegari,
ya ƙara cewa: ‘Thumaamah, me kake zaton zan yi maka?’ Ya ce: ‘Abin dai da na
gaya maka ne: Idan ka yafe, ka yafe ga mai godiya.’ Sai ya ƙara barin sa har zuwa
jibi, sai ya ce: ‘Thumaamah, me
kake tunanin zan yi ma ka?’ Ya ce: ‘Abin dai da na riga na gaya maka ne.’ Sai ya ce: ‘Ku saki
Thumaamah.’ Sai kuwa ya fita ya tafi wurin wani idon ruwa a
kusa da masallaci ya yi wanka, sannan ya shigo masallacin ya ce: ‘Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah, kuma
na shaida lallai Annabi Muhammad manzon Allaah ne.’ (Sahih Al-Bukhaariy: 4372;
Sahih Muslim: 1764).
Wannan ya nuna halaccin shigar da kafiri - kowane
iri - a cikin masallaci da izinin musulmi. Har kuma a ɗaure shi na tsawon kwanaki a cikinsa.
Idan wannan a masallacin Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ne a auku, ina kuma ga sauran masallatan da ba su
kai shi girma da daraja ba?!
Amma duk da haka,
lallai a kula kuma a sanya ido sosai a kan wannan kafirin da za a shigar
da shi a cikin masallaci, musamman a irin wɗannan zamunnan waɗanda ƙulla sharri da ta’addanci suka yi yawa a tsakanin jama’a.
Allaah ya ƙara kare mu, kuma ya yi mana maganin dukkan fitinu.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.