𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah, A kan kiraye-kirayen da ake yi a social media cewa a fito a yi zanga-zanga don neman gwamnati ta ƙara hoɓɓasa wurin gyara harkar tsaro, ko ya dace musulmi ya amsa wannan kiran?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah Wa Barakaatuh.
Da farko dai wajibi ne duk mu san
cewa: Mu musulmi ne da farkon fari kafin mu zama ’yan Najeriya, kuma dokokin
musulunci ya wajaba mu kula da su a kowane lokaci, kuma mu yi ƙoƙarin
zartar da su a cikin al’amuranmu rayuwanmu, matuƙar dai muna da hali da iko a kan yin
hakan. Da haka ne za mu amsa cikakken
sunanmu na musulmi a gaskiya.
A cikin tsari da dokokin da
Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala ya zartar a kanmu, bai yarda da ɗaukar makami don yin fito-na-fito da
shugabanni masu iko da sarauta a kanmu ba, matuƙar dai
musulmi ne, suna tsaida sallah da salati a cikinmu. Ko da ma ba musulmi ba ne
bai halatta a yi shirin sauke su ba, har sai mun tabbatar ko muna da kyakkyawan
zaton cewa muna da ƙarfi da ikon yin hakan ba tare da ya
haifar da wata fitinar da ta fi wanda jama’a suke ciki ba. Dalili kuwa shi ne:
Yawanci ba a iya kai wa ga hakan har sai an zub da jinin musulmi masu yawa,
kamar yadda tarihi ya nuna. Kuma zanga-zanga na daga cikin hanyoyin da ke
nunawa, ko kuma kai wa ga wannan fito-na-fito ɗin a fili ƙarara,
kamar yadda ake ji da gani a yau a cikin ƙasashen musulmi.
Abin da hadisai sahihai a cikin
Sahih Al-Bukhaariy da Sahih Muslim suka nuna mana dangane da shugabannin da
suka zama azzalumai macuta kuma maciya amana shi ne: Ku ba su haƙƙoƙinsu da
Allaah ya ɗora a kanku, amma ku roƙi Allaah a kan naku haƙƙoƙin da
suka danne. (Dubi: Sharhin Al-Arba’uunas Salafiyyah, shafi: 45).
Idan kuma muna da dama, to aikin
da shari’a ta koyar da mu shi ne: Yi wa shugabannin nasiha, kamar yadda Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Addini nasiha ce. Suka ce: Ga
waye? Ya ce: Ga Allaah; da Littafinsa; da Manzonsa; da shugabannin musulmi; da
sauran jama’ar musulmi.
Sai dai kuma har nasihar ma tana
kasancewa ne, a keɓe cikin hikima, kuma da lafuzza kyawawa waɗanda shugabannin suke iya amincewa su
karɓa. Amma ba da kaushi ko tsanani ko zagi ko wulaƙanci ba
a fili a gaban jama’a. Irin wannan ke sanya su ƙi yarda da mai maganar, ko da kuwa ya yi
da’awar cewa nasiha yake yi.
’Yan shi’ah ne aka sani da zanga-zanga
mai kai wa ga juyin-juya-hali don neman biyan-buƙatunsu
a wurin gwamnatin da musulmi ke jagorancinta. Da haka suke samun ɗarewa a kan karagar mulki, kamar yadda
ya faru a ƙasar Iran a shekarun baya. Sannan sai kuma masu siyasar
dimokuraɗiyya da suka shigo mana da shi, suka gyara shi da manufar wai waɗanda ake mulka su iya nuna damuwarsu ga
masu mulkinsu!
Matsalolin da muke fama da su a ƙasar
nan suna da yawa, mafi girma a cikinsu: Akwai manya daga cikin ’yan ƙasar waɗanda ba su da ƙaunar ƙasar ko
jama’arta a cikin zukatansu. Sun haɗa baki da maƙiyan ƙasar
daga ƙetare suna ta ƙoƙarin damalmala ƙasar da
janyo hatsaniya da tashin-tashina, mai kai kasar ga komawa ga sabon shirin
mulkin mallaka da turawan gabashi da yammacin duniya suke ta neman aukuwarsa.
Domin kaɗai su rufe ɓarnace- ɓarnace da ta’asar da suka tafka a shekarun baya. Su ne waɗanda ya fi kyau a kira su: ’Yan
a-fasa-kowa-ya-rasa!
A gaskiya, abin da masu wannan
shiri suke kira a fito a yi shi ne: Revolution watau: Juyin juya-hali, na kifar
da gwamnati da karfin tuwo, kamar yadda fassarar ƙamus na
kalmar ta nuna. Amma ba protest watau: Zanga-zanga ba! To, ta yaya za mu yarda
a kawar da gwamnatin da jama’ar ƙasa mafiya yawa suka yarda suka zaɓa ta hanyar kaɗa mata ƙuri’o’insu?! Watau kenan abin da suka kasa
samu ta hanyar ƙuri’a shi ne suke son samu ta hanyar juyin
mulki!! Me muke jin zai auku gare mu idan muka taimaka musu suka samu buƙatarsu
ta biya?
Kuma ya kamata, ko ma a ce: Ya
wajaba mu ’yan Arewa, musamman ma Hausa/Fulani waɗanda kowane makirci da munafunci da
cutarwa aka ƙullo wa ƙasar nan a kanmu yake ƙarewa,
amma kuma duk wani alheri da za ta samu ba mu jin labarinsa sai bayan saura ɓangarorin ƙasar
sun gama morewa, mu ya wajaba mu san cewa: Ko kusa wannan ba alheri ba ne, gare
mu. Ƙarfin da muka fi su da shi a wurin zaɓe ne suke son yin amfani da wani wayo
yanzu su karɓe shi!
A yau ba sai gobe ba, menene
zanga-zanga ya janyo wa ƙasashen Larabawa a kusa da nesa da mu?!
Ta yaya aka iya ɗaiɗaita ƙasar Libya? Me ke janyo kiki-kaka a cikin ƙasar
Masar a yau? Menene ummul-haba’isin rikicin da ya ƙi ci ya ƙi
cinyewa a ƙasar Siriya? Me ya haifar da masifar da ƙasar
Sudan take ciki a yau?! Jama’a! Zanga-zanga mataki ne na haifar da masifa da bala’in da zai afkawa al’ummar ƙasa,
wanda kuma ba wanda ya san ƙarshensa ko iyakansa sai Allaah shi kaɗai. Don haka, kar mu yarda a yaudare mu.
Wani na iya cewa: Ai ana cikin
wahala da tsanani ne! Haka ne. Amma kuma ai tun ba yau ne ake cikin tsanani da
wahalhalun ba! Kuma ai ba wannan gwamnatin ce mafarin tsananin da wahalhalun
ba. Me ya hana masu tunanin yin zanga-zangar a yau su yi tunanin yin irinsa a
wancan lokacin? Ko don ba su ne abin ke shafa ba a lokacin?!
Kuma dole ne mu musulmi mu san
cewa: Mafita daga dukkan wahalhalu da tsanani da ƙuncin
rayuwa shi ne, mu koma ga koyarwar sahihin addininmu: Mu kyautata zamantakewa a
tsakaninmu da juna, mu yawaita yaɗa alheri a tsakaninmu, mu kawar da abin da muke iyawa na
sharri a cikinmu. Ta haka ne Allaah zai taimake mu, ya yi mana maganin abin da
ya fi ƙarfinmu.
Ta yaya za a riƙa yi
mana wayo, ana amfani da mu, ana ƙulla mana maƙarƙashiya
mai kai wa ga cutar da mu, da sunan ƙasa-ɗaya? In su ne a kan karaga, su cuce mu,
su danne mu, su mayar da mu saniyar-ware, su kashe mana shugabanni, kuma su ƙara
mayar da yankinmu a baya. Idan na mu ne a kan karaga su takura masa, su yi ta
janyo masa matsaloli, su hana shi yin duk abin da zai taimaka mana, ko ya
taimaka wa ƙasa. In kuma ya ƙi a ɗauki matakin hallaka shi! Ta yaya muka
rasa Tafawa Balewa? Ina Sardauna? Ina Murtala? Ina Abacha? Allaah ya gafarta
musu. Shi kansa wannan yaya aka yi da shi? In ba domin Allaah ya sa yana da
sauran shan-ruwa ba da yanzu sai dai labari ba?! Meyasa ba za mu fahimta ba?!
Don me za a riƙa haɗa kai da gwiwa da baki da mu, a riƙa cin-dunduniyar ɗan’uwanmu?! Ta yaya za mu samu cigaba da
ɗaukaka a cikin al’umma da irin wannan?!!
Jama’a! Maimakon zanga-zanga,
kamata ya yi mu yawaita yi wa ƙasa da shugabannin ƙasa
kyawawan addu’o’i, mu ƙara ƙoƙarin gyara zamantakewarmu a tsakaninmu
da juna, mu yaɗa alheri kuma mu daƙile yaɗuwar dukkan sharri a tsakaninmu, sannan
mu riƙa ɗaukar matakan maganin duk wasu ɓata-gari, masu janyo tashin-tsahina a cikinmu.
Allaah ya kare mu daga dukkan
sharri da masharranta a ko’ina su ke, ya bai wa shugabannin ƙasar
nan hikima da basira wurin ƙwato haƙƙin mai
haƙƙi daga azzalumai, da bayar da su ga waɗanda suka cancanta, da janyo duk abin da
zai amfani ƙasar da jama’arta. Kuma Allaah ya kawar mana da dukkan tsoro da
firgici da tashin hankali, ya sa a samu kyakkyawan tsaro da zaman lafiya da
kwanciyar hankali a dukkan yankunanmu da ma ƙasa
baki-ɗaya.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.