Nazarin Turken Koda Kai a Cikin Wasu Wakokin Sa’idu Faru

    Citation: Bungudu, H.U., Abubakar, M.S. & Saleh, M.A. (2024). Nazarin Turken Koɗa Kai a Cikin Wasu Waƙoƙin Saidu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 282-286. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.037.

    Nazarin Turken Koɗa Kai a Cikin Wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru

    Daga

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir na Bunguɗu)
    Ƙibɗau: harunaumarbungudu@gmail.com
    Lambar waya: 08065429369 

    Da

    Muhammad Shu’aibu Abubakar
    Lambar waya: 08031835262 

    Da

    Muhammad Aminu Saleh
    Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi da Ƙere-Ƙere Ta Gwamnatin Tarayya, Gusau, Jihar Zamfara.
    Lambar waya 08036166585

    Tsakure

    Wannan muƙala ta mayar da hankali ne wajen gano wuraren da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da turken koɗa kai a cikin wasu waƙoƙinsa. Manufar binciken ita ce fito da hikimomin Uban kiɗi na amfani da wannan turken a wasu waƙoƙinsa waɗanda ya riƙa yi wa jama’a daban-daban. Ra’in da aka yi amfani da shi a wannan aikin binciken shi ne ra’in Waƙar Baka Bahaushiya na Gusau (2003). Hanyoyin da aka yi amfani da su wajen tattaro bayanan wannan aikin sun haɗa da sauraren waƙoƙin Malamin waƙa wato makaɗa Sa’idu Faru tare da tattaunawa da wasu masana da masu sha’awar nazarin waƙoƙin nasa. Akwai wasu waƙoƙin da ya yi amfani da wannan tubalin ginin turken kamar yadda wannan binciken ya gano domin ba dukan waƙoƙin nasa ne ya yi hakan ba, sai dai a kalli waƙoƙin a zaƙulo irin wannan turken na koɗa kai.

    Keɓaɓɓun Kalmomi   Ma’anarsu

    Bajini     Yaya

    Ginjimi    Babba

    Kwana     Barci

    Ƙasura     Cika/Isa

    Kiɗin Barkakka da kaya  Zuwa kiɗi inda ba a gayyace ka ba

    Kamfaragi    Babba

     

    1.0 Gabatarwa

    Waƙar baka aba ce wadda take buƙatar shiryawa da tsara batutuwa a samar da gangar jikinta cikin azanci da hazaƙa da naƙaltar harshe da ake amfani da shi. Daga nan , sai a rera ta tare da amshi a kuma daɗa fito da armashinta ta amfani da sautin kiɗa. Rerawa da zaƙin murya da sauran abubuwan da suka danganci rauji abubuwa ne muhimmai a wajen samar da nagartar waƙoƙin baka. Waƙoƙin baka suna tafiya ne tare da sautin kiɗa, amma akwai wasu waƙoƙin waɗanda ba a haɗa su da wani amon kiɗa, kamar wasu waƙoƙin siyasa da ake haɗawa da tafi kurum. Misali, waƙar jamiyya mai kwando da ta jamiyyar PRP ta Auwal Isah Bunguɗu. Harshen da makaɗan baka suke amfani da shi a bisa kansa cikakke ne, yana da kamalarsa ta daban da harshen yau da gobe da ake amfani da shi wajen furuci ko rubutu. Domin kuwa, wasu sukan ce harshen waƙa taƙadiri ne saboda yakan bauɗe wa wasu ƙa’idojin nahawu. Kauce wa daidaitacciyar ƙa’ida kuwa salo ne a waƙa, amma duk da lalurar da kan sa makaɗan baka su karya ƙa’idar nahawu, waƙoƙinsu suna hawa bisa ingantaccen tsari na musamman, mai jan hankali, mai amsa-amon kari da yake daidaita layuka cikin ɗiya. Har wa yau, a waƙoƙin baka ana amfani da hanyoyin adonta harshe da sauran dabarun nuna gwaninta da burgewa. Waƙar baka tana tafiya da lokaci na aukuwar sababbin al’amura. Muddin dai makaɗi na raye, yakan so ya yi wa waƙa daɗi ta kawo wasu abubuwan da suke faruwa na rayuwa, wajen yin wannan aikin ne yake faɗawa tarkon rage wasu ɗiyan. Haka kuma a waƙar baka ba ta da tsayayyar doka ko ƙa’ida dangane da shirya layuka a ɗiyanta wato babu wata doka da ta ƙayyade yawan layukan ɗan waƙa. Makaɗan baka ba su tauye kansu wajen shirya layukan ɗiyan waƙa a kan wani ƙayyadajjen adadi, sukan numfasa, su ƙara ‘ɗa’ inda duk saƙo ƙarami ya ƙare, kuma yin haka ba zai ruguza musu tsarin karin murya ba.

    3.0 Taƙaitaccen Tarihin makaɗa Sa’idu Faru

    An haifi makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru ta cikin ƙasar Maradun, ƙaramar hukumar Maradun a shekara ta dubu ɗaya da ɗari tara da talatin da biyu (1932). Ana kuma yi masa laƙabi da Ɗan’umma wanda matar ƙanin ubansa ta sanya masa, saboda ba ya faɗin sunanta, sai dai yana kiran ta Umma. Shi ya sa ita kuma ta dinga kiran sa Ɗan’umma, amma wannan laƙabi bai shahara a tsakanin mutane ba, balle ya danne sunansa na yanka wato Sa’idu. Shi kansa Sa’idu Faru yakan yi wa kansa da kansa kirari yana cewa: Ɗan Umma Rumgumi ko Ɗan Tumba Rumgumi (Gusau, 1996:117).

    Sunan mahifin Sa’idu Faru shi ne makaɗa Abubakar ɗan Abdu, shi kuwa makaɗa Abdu, Alu Maikurya ya haife shi. A she ke nan Sa’idu Faru shi ne ɗan Abubakar ɗan Abdu da Alu mai Kurya. Sai dai mahaifiyar Sa’idu mutumiyar Banga ta cikin ƙasar Ƙaura-Namoda ce, kuma a can ne aka haife ta.

    Sa’idu Faru kamar sauran makaɗan fada ya yi gadon kiɗa ta wajen mahaifinsa. Kakansa na sama makaɗa Alu makaɗin kurya ta kiɗin yaƙi ne wadda ake yi wa kirari‚ kurya gangar mutuwa‛. Makaɗa Alu ya yi waƙoƙi da yawa a zamanin da yawa a tsawon lokaci.

    Sa’idu Faru ya yi ƙuruciyarsa ne a garin Banga ta Ƙaura- Namoda, amma kafin ya girma ƙwarai sai ya koma wurin tsohonsa makaɗa Abubakar a Faru. Makaɗa Sa’idu bai samu ilmin muhammadiyya da yawa ba, sai dai an sa shi makarantar allo inda ya yi zurfi ga karatun Alƙur’ani mai tsarki. Haka kuma ba a sa shi makarantar bako ba, domin haka bai san komai ba game da sha’anin bako. Alal haƙiƙa tun yana Yaro sha’anin kiɗa da waƙa ya ɗauke masa hankali.

    Makaɗa Sa’idu Faru ya koyi waƙa wurin mahaifinsa makaɗa Abubakar, waƙoƙinsa suka daɗa kyautatuwa ta hanyar fasaha da hikima tare da kwakwalwar da Allah ya ba shi. Tun Sa’ida Faru yana da shekara goma aka fara zuwa yawon kiɗa da shi gari-gari. Bayan da ya cimma shekaru sha shida ya soma karɓa. Baya ga tsohonsa makaɗa Abubakar Sa’idu Faru bai koyi kiɗa ga kowane makaɗi ba, dukkan salailai iri-iri da yake sakawa a waƙoƙinsa tushensu mahaifinsa da baiwar da Allah ya ba shi ta gane fasalin waƙa, ya sa himma da ƙwazo har zuwa lokacin da Allah ya karɓi ransa.

    Sa’idu Faru ya samu cin gashin kansa, ya fara da wata waƙa mai daɗin gaske ƙunshe da tarin hikimomi a shekarar 1940. Ga kaɗan daga cikinta kamar haka:

    Jagora: Bi da maza ɗan Joɗi na Rwafi,

    ‘Y/Amshi: Iro magajin Shehu da Bello.

     

    Jagora: Dawaya kora ɗimau na Wakili.

    ‘Y/Amshi: Dawaya kora na ɗimau na Wakili.

     

    Jagora: Dawaya kora na ɗimau na Wakili.

    ‘Y/Amshi: Dawaya kora ɗimau na Wakili,

    : Uban sarkin gida Bello da Yari.

     

    Jagora: Ruwa da kada,………………

     

    Wannan waƙar da ya fara yi ita ce wadda ya yi wa tsohon sarkin Yamman Faru Ibrahim. Daga nan Sa’idu Faru ya ci gaba da yi wa sarakuna da ‘ya’yan sarakuna waƙoƙi, har zuwa lokacin da ya sadu da sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar. Ya samu yi wa Sarkin Kudu Macciɗo waƙoƙi tun lokacin da yake Mafara yana riƙe da muƙamin sarkin Gabas watau uban ƙasar ita Talata Mafara wadda a yanzu ƙaramar hukumar Maradun ce.

    3.1 Iyalansa

    Makaɗa Sa’idu Faru yana da matan aure guda uku (3) tare da ‘ya’ya ishirin da shida (26) maza da mata, a cikinsu goma sha ɗaya (11) sun rasu, saura goma sha biyar (15). Yana kuma da jikoki. Sa’idu Faru ya rasu a shekarar 1987 a sanadiyyar rashin lafiya da ya yi fama da ita.

    Dabarun Gudanar Da Bincike

    Wannan bincike ya tattaro dukkananin bayanansa ne daga tushe. A cikin wannan takarda an ɗauki wasu daga cikin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru a matsayin tushen bayani domin taƙaita nazari a kansu. Haka kuma yana daga cikin dalilan wannan bincike na gano irin dabbobi da tsuntsayen da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa.

    2.0 Salo

    Malamai da masu nazarin adabi sun bayar da ma’anar salo ta hanyoyi da dama duk da yake kusan manufa ɗaya suka fuskanta, kalmomin da suka yi amfani da su kawai suka bambanta.

    Salo a waƙoƙin baka wata hanya ce wadda makaɗi ke kyautata zaren tunaninsa, ya sarrafa shi cikin azanci don ya cimma burinsa na isar da saƙo a waƙa (Gusau 2003:54).

     

    Ga abin da wannan masani ya nuna salo shi ne dabarun da mai magana ya ƙunsa a cikin zancensa da nufin isar da saƙo ta hanyar da za a fahimce shi cikin sauƙi ko da wahala, a cikin raha ko cikin ƙosawa. Duk ta hanyar da masu saurare suka ji jawabin daga hanyoyin da aka ambata, to shi ne irin turken da mai zancen ya yi amfani da shi.

    A wata ma’anar da aka bayar cewa aka yi:

    Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda aka bi domin isar da saƙo. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙar. (Yahya 1999:3).

    Wannan ma’ana ita ma kusan manufarta ɗaya da wadda ta gabace ta. Bayani yana nuni ne ga irin dabarun da mawaƙi yake amfani da su wajen isar da saƙonsa ga jama’a a cikinsa ba tare da gundura ba. Wato saƙonsa ya isa cikin birnin zuciyar masu saurare cikin nishaɗi da ban sha’awa[1].

    Shi kuma wani malamin cewa ya yi:

    Masana da manazarta suna ganin cewa salo yana da wuyar a gane shi a bisa kansa, sai dai ana iya gane wasu sigogi nasa dangane da ma’anarsa. To amma muna iya cewa salo shi ne hanyoyin isar da saƙo[2], (Ɗangambo 2007:34).

    Bayanin wannan malami bai tsawaita ba. Ya taƙaita abin da waɗanda aka fara ambata suka faɗa tare da ƙara bayyana wahalar bayyana ma’anar salo ta amfani da kalmomi kawai. Duk da haka ya taƙaita ya ce hanyoyin isar da saƙo su ne salo, waɗanda muke ganin su ne waɗanda waɗancan malamai da muka fara ambata suka faɗa.

    A bisa bayanan masana ana iya cewa, salo wata dabara ce ta isar da saƙo ta hanyar zaɓen kalmomin da suka dace da abin da ake zance ta yadda zuciyar mai saurare ko karatun abun za ta karɓe[3] shi, ya Allah a cikin sauƙi ko tsauri.

    3.0 Nazarin Tubalan Ginin Turken Koɗa Kai a Waƙoƙin Sa’idu Faru

    A waƙar da Uban kiɗi Alhaji Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda Abubakar Garba, wanda ya yi sarauta daga shekarar 1952 -1960 shekarar da aka cire shi daga sarauta, ya yi amfani da wannan turken na koɗa kai kamar haka:

    Jagora: Narambaɗa waƙad da yay yi ma,

    ‘Y/Amshi: Ba ta yi kamat tau ba.

     

    Jagora: Auta Daɗi waƙad da yay yi ma.

    ‘Y/Amshi: Ba ta yi kamat tau ba.

     

    Jagora: Jankiɗi waƙad da yay yi ma, ya yi ta tai daɗi.

    ‘Y/Amshi: Amma in an yi bincika,

    : Ba ta yi kamat tau ba.

     

    A waɗannan ɗiyan waƙar Ɗantumba Rungumi ya rungumo sunayen wasu makaɗan da suka yi wa ubangidan nasa waƙa kuma duk ya soke waƙoƙin nasu da cewa ba su yi kamar tasa waƙar da ya yi masa ba. Dubi manyan makaɗa irin su Narambaɗa da su Jankiɗi wai duk waƙoƙinsu ba su yi kamar tasa ba, ai ka san ya dai koɗa kansa ne kawai. Wannan shi manazarta ke ce wa koɗa kai. Dubi yadda ya rattabo su Narambaɗa waƙad da yay yi ma, Auta Daɗi waƙad da yay yi ma,

    duk ‘yan amshi na amsa mai cewa ba ta yi kamat tasa ba.

    A wata waƙar kuma makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan tubalin ginin turken koɗa kai kamar haka:

     

    Jagora: Mu ka kiɗi,

    : Mu ak kiɗi

    : Saboda mu Allah yaw wa,

    ‘Y/Amshi: Gudummuwa da waƙa,

    : Haw wata na iza wata.

    (Sa’idu Faru: waƙar Shehu Muhammadu Ɗangwaggo).

    A wannan ɗiyan waƙar makaɗa Sa’idu ya koɗa kansa da cewa su ke da kiɗi domin su Allah ya wa gudummuwa da waƙa iri-iri, kuma ba shi kaɗai Allah ya yi wa gudummuwa da waƙa ba akwai wasu makaɗan.

    Haka zalika a wata waƙar ta ɗan Hashim ƙanen sarkin Kano ya kawo wannan turken kamar haka:

    Jagora: In don kiɗin barkakka da kaya,

    : Ban zuwa ko Moriki,

    ‘Y/Amshi: Ban zuwa ko Moriki.

    (Sa’idu Faru, waƙar Ɗan Hashim Ƙanen Sarkin Kano).

    A al’ummar Hausa akan gayyaci wasu makaɗa idan ana buƙatar su wajen wani buki kamar na naɗin sarauta ko bukin suna ko aure da sauransu. Amma da yawa makaɗan da ke zuwa ba sai an gayyace su ba a wajen sha’anonin jama’ar, don su yi kiɗinsu da waƙoƙinsu su sami kyaututtukansu. To saboda Sa’idu Faru ya koɗa kansa sai ya fitar a wannan ɗan waƙar cewa shi ba ya zuwa wurin da ba a gayyace shi ba wajen kiɗi. Wato bai yin kiɗin barkakka da kaya.

    A wani wurin ya ambaci wasu dabbobin da cewa:

    Jagora: Sa’idu Faru ka waƙam mulki,

    ‘Y/Amshi: Komi kaj jiya ƙarya akai.

     

    Jagora: Sa’idu Faru ka waƙar iko,

    ‘Y/Amshi: Komi kaj jiya ƙarya akai.

     

    --------------------------------------

    Jagora: Sa’idu Faru ka waƙar yaƙi,

    ‘Y/Amshi: Komi kaj jiya ƙarya akai.

     

    Jagora: Sa’idu Faru ka waƙar ilmi,

    ‘Y/Amshi: Komi kaj jiya ƙarya akai.

     (Sa’idu Faru, waƙar Turakin Kano)

    A nan makaɗa Sa’idu Faru ya koɗa kansa da nuna cewa babu wani mai waƙar mulki ko iko in ba shi ba. Har yana ganin kowa aka kira mai waƙar mulki ko iko in ba shi ba ne ƙarya akai. Ba a nan ya tsaya ba, a can gaba ya ƙara da cewa shi kaɗai ne ke waƙar yaƙi da waƙar ilmi kuma duk wanda aka ce yana yin waɗannan waƙoƙin ƙarya ce.

    4.0 Sakamakon Bincike

    Wannan aikin binciken ya gano wasu tubalan ginin turke ne da mawaƙin ya yi amfani da shi a wasu waƙoƙinsa inda yake koɗa kansa yana nuna ya fi wasu makaɗan musamman wajen waƙa. An dubi wasu tubalan da ya yi amfani da su a wasu waƙoƙin nasa, amma dai an mayar da hankali ne a turken koɗa kai a cikin waƙoƙin nasa har ma an zaƙulo misalai da dama a wasu waƙoƙin domin a ɗaure akuya a gindin magarya.

    5.0 Kammalawa

    Godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki wanda ya nufe mu da kammala wannan binciken wanda ya kalli yadda makaɗa Sa’idu Faru yake amfani da tubalan ginin turken koɗa kai a cikin waƙoƙinsa. Mun sami nasarar zaƙulo ire-iren waɗannan wuraren da ya yi hakan mun fito da su tare da sharhantawa don su amfanar da jama’a musamman manazarta waƙoƙin Hausa. Allah ya sa abin amfani ne.

    Manazarta

    Bunza, A.M (2006). Gadon Feɗe Al'ada. Lagos: Tuwal publishers Limited.

    C.N.H.N. (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity press.

    Damgambo, A. (2007), Daurayar Gadon Feɗe Waƙa, (Sabon tsari), Kano: Amana Publishers Limited.

    Gusau, S.M. (2003), Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark publishers Limited.

    Gusau, S.M. (1996), Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kaduna: Fisbas Media Services.

    Muhammad, (2006). Gudunmuwar waƙoƙin baka na yara wajen adana al’adar Hausawa, Kundin digiri na biyu, Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya: Jami’ar Bayero.

    Muhammad, D. (1978). Waƙa Bahaushiya: Studies in Hausa Language, Literature And Culture. Bayero University, Kano.

    Sarɓi S. A. (2007), Nazarin Waƙar Hausa, Samarib Publishers.

    Yahaya, I. (2010). Waƙoƙin Addini Na Siyasa: Nazarin Waƙoƙin Emmanuel Wise Mai Molo. Kundin digiri na biyu, Zaria: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello.

    Yahaya, I.Y (2002), Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-rubucen Cikin Hausa. NNPC.

    Yahya, A. B. (1997). Turken Nazarin Waƙa, Fisbas media service.

    Yahya, A. B. (1996). Salo Asirin Waƙa, Fisbas media service.

    Yahya, A. B. Da Dumfawa, A. A. (2010). Waƙar Motar Siyasa: Saƙon Talakawa Zuwa Ga ‘Yan  Siyasar Zamani.

    NNPC (1966), Ikon Allah. Zaria: Amana Printing Ltd.



    [1] Wa]anda kan sa mutane su yi dariya.

    [2] Abin da ake son nuna wa ga jama’a.

    [3] Yarda da shi.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.