Ranar 26 ga watan Agusta na kowace shekara ce ake bukukuwan Ranar Hausa ta Duniya.
Wannan ranar dai ta samo asali ne a shekarar 2015 inda ma'aikacin Sashen Hausa na BBC, Abdulbaki Aliyu Jari da wasu abokansa na shafukan sada zumunta suka ayyana ranar a matsayin ranar da masu magana da harshen Hausa za su hadu su tattauna ci gaba da kalubalen da harshen ke fuskanta a karni na 21.
A kowace shekara idan ranar ta zagayo ma'abota shafukan sada zumunta na yin amfani da tambarin #RanarHausa domin tattaunawa da yin muhawara. Daga bisani kuma a shekarar 2018 aka fara gudanar da bukuwa na zahiri a gidan ɗan Hausa da wasu ƙasashe a fadin duniya kamar Ghana. (BBC Hausa).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.