Rawar Da Adabi Ya Taka Wajen Koyarwa A Makarantun Allo

    Bayanin takarda: Haruna Umar Maikwari and Habibu Lawali Ƙaura, (2021). Rawar Wa Adabi Ya Taka Wajen Koyarwa A Makarantun Allo. Takardar da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani da Jami’ar An-Nahda haɗin guiwa da Kwalejin Ilimi ta jihar Jigawa da ke Gumel, Nijeriya ta shirya a ranar Laraba, 31 ga Maris zuwa 2 ga Afilu, 2021.

    Rawar Da Adabi Ya Taka Wajen Koyarwa A Makarantun Allo

    Daga

    Haruna Umar Maikwari

    Department of Hausa Language.
    Federal College of Education (Technical) Gusau
    Maikwariharuna@gmail.Com
    (+234) 07031280554

    Da

    Habibu Lawali Ƙaura2

    Department of Hausa Language.
    Federal College of Education (Technical) Gusau
    lawalikaurahabibu@gmail.Com
    (+234) 08080872142

    Tsakure

    Burin kowace al’umma da ke rayuwa a doron ƙasa shi ne ta samu nagartattun hanyoyin gudanar da rayuwa masu inganci. Nagartattun hanyoyin rayuwa kuma suna ƙunshe da addini da al’adun wannan al’umma. Hausawa sun gudanar da hulɗa tsakaninsu da Larabawa, wanda ya ba su damar aron dabarunsu na karatu da rubutu, watau abin da ya shafi haruffa. Wannan muƙala tana da manufofi da suka haɗa da: (i) Bayyana hikimar Hausawa wajen koyar da Alƙur’ani da harshen Hausa. (ii) Ƙara fito da wasu dabarun karatun Alƙur’ani Mai girma. (iii) Fito da amfani da ke tattare da koyar da Al’ƙur’ani da harshen Hausa. An ɗowa wannan maƙalar a kan ra’in kwaɗaitarwa (Motivation Theory) domin la’akari da cewa wannan ra’i yana kwaɗaitar da almajirai su tashi tsaye su nemi ilmi a cikin nishaɗi. Maƙalar za ta yi amfani da manyan hanyoyin tattara bayanai da suka haɗada da: (i) Za a ziyarci wasu makarantu don tattara bayanai da za su gina wannan bincike. (ii) Haka kuma za a karanta wasu littattafai da za su taimaka wajen gudanar da wannan maƙala. (iii) Za a tuntuɓi wasu da suke da ilmi ko masaniya dangane da karatu a makarantun allo. Daga ƙarshe za a fito da bayanin irin gudummuwar da adabi ya bayar wajen gudanar da sha’anin koyarwa a makarantun allo.

    Fitilun Kalmomi: adabi, makarantar allo/Tsangaya

    Gabatarwa

    Harshen Hausa ya samu bunƙasa a cikin gaggawa, saboda cunɗanyarsa da wasu manyan harsuna na duniya kamar Larabci da Turanci. Wannan cuɗanya ta samar wa Hausa ci gaba mai ɗimbin yawa, musamman ma ta fuskar haɓakar kalmomin Hausa. Marubuta da yawa sun tabbatar da haka. Misali, Ibrahim (1987:95) da Yunusa (1985:32) da Luke (1989) da Sarɓi (2005:59-60) da sauransu duk sun tabbatar da wannan iƙirari. Shi kuwa Yakasai (2001:2) cewa ya yi “cuɗanya tsakanin Hausawa da Larabawa da kuma karɓar musulunci da Hausawa suka yi sun taimaka wajen bunƙasar kalmomin Hausa. Domin kuwa fiye da kashi goma a cikin ɗari na kalmomin Hausa an aro su ne daga Larabci.

    Harshen Hausa ya yaɗu a duniya ta hanyar cuɗanya. Wannan cuɗanya dai wata dama ce da harshen ya samu ta cuɗanya da harsuna daban-daban na duniya. Saboda haka baya ga cuɗanya da Larabawa Hausawa sun yi hulɗa da wasu ƙabilu na nan ciki da wajen kasar Nijeriya. wasu daga cikin waɗannan kabilu kamar yadda malam Ibrahim (1987:95) ya bayyana sun haɗa da: Turawa da Nufawa da Yarbawa da Barebari da Fulani da Wangarawa da kuma Azbinawa. Ko shakka babu dangantakar Hausa da waɗannan ƙabilu da irin cuɗanyar da suka yi sun isa su taimaka wa Hausa ta bunƙasa kuma ya yaɗu zuwa sassan duniya daban-daban kamar dai yadda wasu masana suka faɗa.

    Haɗuwar Hausawa da Larabawa ya taimaka masu wajen samun hanyar karatu da rubutu. Duk da cewa Hausawa ba kai tsaye daga Larabawan suka samu addini ba. Musulunci ya shigo a ƙasar Hausa tun ƙarni na 10 zuwa na 16. An samu wasu malaman addini da suka zo da addini a ƙasar Hausa da suka haɗa da Musa Jokollo wanda daga cikin zuri’arsa ne Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya fito. Akwai kuma Malam Abdulrahman Zagaiti wanda yake Bawangare ne, ya shigo ƙasar Hausa yayin da yake a hanyarsa zuwa aikin Hajji a Makka. Waɗannan duk sun taka muhimmiyar rawa wajen shigowar addinin musulunci a ƙasar Hausa. Haka kuma akwai wani Malam Abdulkarim Almaghili wanda shi ma ya taso daga Morocco ya zo har Katsina.

    Hausawa sun samu musulunci tun a wancan lokaci, kuma sun kasance suna bin wannan addini na musulunci. Shi kuwa addinin musulunci akwai tsare-tsare da ya zo da su, kuma Hausawa sun rungumi wannan tsari. A addinin musulunci ya zama wajibi ga kowane musulmi ya koyi yadda ake yin ibada kafin ma ya fara iyin ibadar. Ba a yin ibada ba tare da an san hukuncinta a wajen Allah ba. Dukkan ibadar da za a yi a addinin musulunci sai an iya karatun Alƙur’ani Mai girma. Wannan ya ba Hausa damar duƙufa ga karatun Alƙur’ani Mai girma.

    Manufar Bincike

    Wannan muƙala tana da manufofi da suka haɗa da:

    (i)                 Bayyana hikimar Hausawa wajen koyar da Alƙur’ani da harshen Hausa.

    (ii)              Ƙara fito da wasu dabarun karatun Alƙur’ani Mai girma.

    (iii)            Fito da amfani da ke tattare da koyar da Al’ƙur’ani da harshen Hausa.

    Hanyoyin Gudanar da Bincike

    An bi muhimman hanyoyi guda uku domin tattara bayanai yayin gudanar da wannan bincike. Na farko shi ne lura (observation). Kasancewar marubutan wannan maƙala dukkan su sun halarci makarantun allo, sun kuma yi karatu a makarantun. Haka kuma akwai yara da suka sa a cikin makarantun, kuma akwai sauran malaman su a duniya. Bincike ya yi amfani da manyan hanyoyin tattara bayanai da suka haɗada da:

    i.                    Za a ziyarci wasu makarantu don tattara bayanai da za su gina wannan bincike.

    ii.                  Haka kuma za a karanta wasu littattafai da za su taimaka wajen gudanar da wannan maƙala.

    iii.               Za a tuntuɓi wasu da suke da ilmi ko masaniya dangane da karatu a makarantun allo.

    Ra’in Kwaɗaitarwa (Motivation Theory)

    An zaɓa ɗora wannan maƙala a kan ra’in kwaɗaitarwa (Motivation Theory) kalmar motivation ta samu fasara daga masana da dama, Garba, (2012:65) ya fasara kalmar motivation a matsayin zaburarwa wadda ya ce, hanya ce da ake sanya mutum ƙamin cimma wata manufa. Wannan ra’i an fi danganta samuwarsa daga MC Dougal, (1871-1838) a wani littafi nasa mai suna An Introduction to Social Psychology ya bayyana cewa zuciya da tunanin mutane na da wani halittaccen wani hali wanda ke da ƙarfin ingiza yin duk wani tunani ko aikata wani aiki.

    Ado, (2017) a maƙalarsa mai taken Sarkin Gardin Sarkin Katsina Allhaji Amadu Na Lado Gwarzon da ya yi Fice a Sana’ar Gardanci a Ƙasar Katsina wadda ta fito a littafin The Heros and Heroiness of Hausa Land, ya ce shi dai ra’in kwaɗaitarwa (Motivation Theory) ra’i ne wanda yake yin bayani kan ɗabi’a da halayyar ɗan Adam ta fannin bayar da dalilin da ke sanya ko a zaburar da ɗan Adam a lokacin da yake ƙawa ko sha’awa ta mausamman, na aikata wasu ayyuka ko wani ƙuduri ko nuna wata buƙata ta rayuwa. Don haka an ɗora wannan aiki ne a kan wannan mazhaba ta kwaɗaitarwa ga almajirai masu koyon karatu a makarantun allo.

    Tsangaya.

    Makarantar Tsangaya ta samo asalin sunanta ne daga al’ummar Barebari (Kanuri) suna kiran tsangaya da Sangaya wato makarantar allo. (Bano, Antonisis, da Ross, 2011) saboda haka Sangaya shi ne asalin sunan. Hausawa suka aro suka mayar da ita Tsangaya. A wata majiya kuma Tsangaya ta samu ne daga sunan allo. Ita dai tsangaya ko bayan wannan sunan ana kiranta da makarantar Alƙur’ani, makarantar Muhammadiyya, da makarantar Toka[1]. Babajo, (2017). Ya ce Tsangaya na nufin wani wuri ko muhalli da aka keɓe don koyar da yara karatun Alƙur’ani Maigirma, kuma yaran su kasance suna amfani da allo suna ɗaukar karatu a gaban malaminsu, galibi malami ɗaya ne babba. Abbas, (1978) ya bayyana tsangaya da cewa, “ wani muhalli ko ɗaki ko baranda ko a sarari ko ƙarƙashi bishiya ko wani wuri, da aka keɓe almajirai domin karantar da su. Imam, (2002) babban abin da ake gane tsangaya da shi shi ne karatu da allo tare ɗaga murya. Ya ƙara da cewa, tsangaya tsari ne na ilmi tsakanin almajiri da malami akwai kuma barin gari domin samo ilmin ba tare da wani shiri na musamman ba, da shiya wa wahala da fama da rashin abinci da abubuwan more rayuwa, domin samun ilmin muhammadiyya.

    Karatun Alƙur’ani Mai Girma

    Asalin kalmar Ƙur’ani a lugga “tarawa” ko “haɗawa” ko kuma “karatu”, amma daga bisani aka alamta ta a kan sunan littafin Allah Mai girma wato Alƙur’ani da ma’anar abin karatu a jimlace waje guda. Gusau, (2005:15). Alƙur’ani Mai girma littafi ne saukakke[2]. An saukar da Alƙur’ani Mai girma a cikin harshen Larabci[3]. Allah (SWA) Ya saukar wa annabi Muhammdu (SAW) ta hanyar aiko mala’ika Jibilu. An bayyana cewa sura ta farko da aka fara saukar wa ita ce “Al-Alaƙ”. An saukar wa fiyayyen halitta annabi Muhammadu (SAW) wannan surah yayin da mala’ka Jibril ya zo masa cewa ya yi karatu, har ya ce “ban iya karatu ba” Jibrilu ya ce, “ka yi karatu da sunan Allah Ubangijinka Maɗaukaki..”. Wannan yana nuna cewa, addinin musulunci sai da karatun Alƙur’ani Mai girma.

    Karatun Alƙur’ani Mai girma, shi ne ɗaukar littafin (Alƙur’ani) a bi shi daidai da yadda aka rubutu shi ana faɗar lafuzzan da ke cikinsa ta amfani da yadda sautin yake a rubuce, ko a gaban malami ko a keɓance ko a cikin taron ɗalibbai[4]. A ƙasar Hausa an jima ana koyar da karatun Alƙur’ani Mai girma. Hasali duk wanda ya tashi a ƙasar ya ga ana gudanar da karatun alƙur’ani Mai girma.

    Karatun Alƙur’ani karatu ne Allah (SWA) ya yi wa tanadin lada mai ɗinbin yawa. Inda Manzon Allah (SAW) ya yi bayanin cewa “karanta harafi ɗaya a Alƙur’ani yana da lada goma, kuma mafifici a cikin al’umma shi ne makarancin Alƙur’ani. A gobe ƙiyama kuma za a ɗaura wa iyayen makarantan Alƙur’anin kambin girma, tare da ba su damar ceto[5].

    Adabin Hausa

    Kalmar adabi an aro ta ne daga harshen Larabci, aka mayar da ita ta zama kalmar Hausa.

    Masana irin su Gusau (1986) cewa ya yi kalmar na nufin dukkan abubuwa na rayuwa da suka shafi al’adu, ɗabi’u da fasahar al’umma da harkokin rayuwar yau da kullum. Shi kuwa Ɗangambo (1985), cewa ya yi kalmar adabi tamkar wani hoto ne ko madubi na haska rayuwar al’umma wadda ta ƙunshi tunaninsu da ɗabi’unsu da fasaharsu na karantar da matasa gargajiya da sarrafa hanyoyin rayuwa.

    A gudummuwa irin wannan za mu iya cewa, “Adabi na nufin wata hanya ta musamman wadda bil-adama (ɗan adam) yake bi don sadar da abubuwan da suka shafi rayuwarsa da ta ‘yan uwansa. Abubuwa da yakan sadar ɗin kuwa, mafi yawansu abubuwa ne da suke daɗaɗa masa rai watau annushuwa, ko suka munana masa zuciya don nuna baƙin cikinsa da ƙin abin; watau a taƙaice dai adabi madubi ne na rayuwar ɗan adam dukkaninta”.

     An kasa adabi gida biyu watau, adabin baka/gargajiya/ka da adabin zamani/rubutaccen adabi. Kuma kowanensu ya kasu gida uku wato labari da waƙa da wasa a adabin gargajiya, a na zamani kuwa zube, rubutacciyar waƙa da wasan kwaikwayo. A wannan maƙala waƙa ce ke a gabanmu don haka ga ma’anar waƙar domin sanin inda muka dosa.

    Ma’anar Waƙa.

     Masana da yawa sun ba da gudunmuwa wajen samar da ma’anar waƙa. Yahya ya ba da tasa ma’anar waƙa da cewa: “Magana ce da ake shisshirya kalmominta cikin azanci, ta yadda wajen furta su ana iya amfani da kayan kiɗa”. Yahya (1997). A cewa Gusau, “Waƙar baka fage ce wadda ake shirya maganganu na hikima, da ake aiwatarwa a rere cikin rauji tsararre, waɗanda za su zaburar da al’umma tare da kuma hankaltar da su dangane da dabarun tafiyar da rayuwa da za su ba da damar a cim ma ganga mai inganci. Waƙa bisa jimla, takan zama fitila wadda take haskaka rayuwar jama’a kuma take kare rayuwar al’umma daga sallacewa” Gusau (2011). Bunguɗu (2014) kuma ya bayar da ma’anar waƙa kamar haka: “Waƙa ta ƙunshi wasu jerin hikimomi ne da a kan tsara domin su daɗaɗa zukatan masu saurare, inda a kan yi amfani da wata zaɓaɓɓiyar murya don rerawa, ana kuma yin amfani da zaɓaɓɓun kalmomi domin fizgar hankalin jama’a ya dawo gare su da zimmar bin diddigin ma’anoni da manufofinsu.

    Gudummuwar Adabi a Makarantun Allo

    Gudummuwar adabi ga al’umma ta fi mayar da hankali ne ga rawar da adabi yake takawa a hali na zamantakewa. Kuma tana duba yadda adabi yake tafiya da al’adu da fasahohi na al’umma da suke daɗa inganta rukunonin rayuwa. Gusau, (2008:13)

    Adabi ya kasu kashi biyu, na gargajiya da na zamani, haka kuma kowane ya kasu kashi uku, watau, labari, waƙa da wasa a adabin gargajiya, a na zamani kuwa, akwai rubutaccen zube, da rubutacciyar waƙa da wasan kwaikwayo. A makarantun allo waƙa ce ta fi taka rawa daga cikinsu wajen koyarwa a cikin raha da nishaɗi. Waƙa na ɗaya daga cikin muhimman rukunnan adabin al’umma da ke da matuƙar tasiri ga rayuwarsu. Bahaushe ya ɗora waƙa a wani matsayi mai girma inda yake amfani da ita a kusan dukkanin ɓangarorin rayuwarsa. Wannan kuwa ya haɗa da tattalin ariziki (inda ake da mawaƙan sana’o’i daban-daban), da zamantakewa (inda ake da mawaƙan jama’a, da mawaƙan fada, da makamantansu). Ɗangambo, (2007:6) ya bayyana waƙa da cewa, waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya), da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”. Bayan samuwar ilimin karatu da rubutu ga Bahaushe, ya duƙufa kan rubuta waƙoƙi bisa jigogi daban-daban.[6] A cikin irin waɗannan waƙoƙi, akan ci karo da hoton rayuwar Bahaushe da tsarin zamantakewarsa. Da ma dai adabi dukansa madubi ne na hango hoton rayuwar al’umma. Baya ga haka, “Muhallin marubuci na da matuƙar tasiri a kan abin da yake rubutawa ko abin da ya ke rerawa ko faɗa.”. Gobir da Sani, (2018: 3). A taƙaice dai waƙoƙi wani ɓangare ne na adabi da ke mamaye da al’adun Bahaushe.

    Malaman makarantar allo sun jima suna amfani da dabaru musmman na jan hankalin almajirai. Malami yakan yi amfani da fahimtar ɗalibai sai ya koyar da su daidai fahimtarsu. A ƙasar Hausa dukkan makarantun allo sukan yi ƙidan baƙi, kuma a tsarin makarantun duk wanda zai yi almajiranci a makarantun dole sai da allo, wannan allon kuma shi ne malami ke yi wa almajiri rubutu kafin almajirin ya iya. Idan kuma za a karanta masa ƙidan baƙi akan yi masa dukkan harufa (Huruf) watau daga alifun zuwa ya’un. (ا-ى)

    Wannan dabara ta ƙidan baƙi, akwai sunayen harufan da aka ba su suna da Hausa daidai da fahimtar malaman (Hausawa). A tasu dabara shi ne su samar da sunayen harufan daidai da sifofin waɗannan harufa. Misali:

    Furucin Hausa   Furucin Larabci Yadda Ake Rubutawa Da Larabci

    Alu     Alif    ا 

    Alu-baƙi   alif   

    Ta-guje   taa’un    ث

    Nunguda   nuu-nun   ن

    Lodi    dwaadun   ض

    Sodi    swaadu    ص

    Ƙam-mai-ruwa  Ƙaafun    ق

    Fii-faa-iya   Faa’un    ف

    Haakuri   haa’un    ه

    Haaƙarami-mai-ruwa  Kha’un    خ

    Haaƙarami   hhaa’un   ح

    Jin-ƙarami   jiimun    ج

    Dal    Daalun    د

    Shim-mairuwa   Shiinun    ش

    Sin ƙeƙasassa   Siinun    س

    Baguje    baa’un    ب

    Lan    laamun    ل

    Taguje    taa’un    ت

    Min    miimun   م

    Kaulasan   kaa’un    ك

    Ɗaamasu-hannu  Ɗwaa’un   ط

    Yaa’ara   yaa’un    ئ

    Hanza    ainun    ء

    Raa    raa’un    ر

    Lamali    lam’ailf   لا

    Takuri    Twaa’un   ة

    Wau    waawun   و

    Zaira    zaa’un    ز

    Ɗaamasu-hannu-mairuwa Ɗwaa’un   ظ

    Zal    zwalun    ذ

    A wancan lokaci kafin yaro ya fara buɗa littafi (Alƙur’ani) sai ya fara da allo, kuma a allon za a riƙa yi masu rubutu tun daga haruffa. Bayan ya kammala ƙidan baƙi za a rubuta masa Alhandu (suratul Fatiha) tun daga farko har ƙarshe ya biya ta da ƙidan baƙi, bayan ya gama za a shiga Ƙula’uzzai (Falaƙi da Nasi) har a kai Alantarakaifa (Suratul Fil). Duk waɗannan almajiri (ɗalibi/mai koyon karatu) zai koye su ne da ƙidan baƙi. Haka kuma idan ya iya za a kuma dawo da shi baya a koya masa yadda ake karanta su. Wannan tsarin koyarwa da malaman makarantar allo ke yi yana taimaka wa almajirai wajen gane abu da fahimtarsa da kamannun baƙi ta yadda ba zai ɓace masu ba a ko’ina suka ci karo da shi a cikin Alƙur’ani.

    Akwai wasu harufa da suka haɗu suka bayar da ayoyi da ake koyarwa da ƙidan baƙi waɗanda idan aka faɗe su sai a ji kamar suna da wani rauji da zai ba da damar fasara su. Sau tari domin nishaɗi almajirai sukan bayyana hoton rayuwarsu da abubuwan da suke a cikin ransu a cikin waɗannan ayoyi. Wannan ba ya nufin sun yi fasara, sai dai sun saka nishaɗi da zai sa su ji sha’awar wannan karatu. Misali. A wasu harufa da suke gina wani ɓangare ko sashe na wata aya ko wasu ayoyi kamar:

    Bismillahir rahmanir rahim   بسم الله الرحمن الر حيم

    Ba, sin, mi’ara, ali, lallan, hakuri, ali, lan, ra, haa ƙarami, min, alijja, nu’ara, ali, lan, raa, haa ƙarani, yaa, mi’ara.     ب س م ا ل ل ه ا ل ر ح م ن ا ل ر ح ي م

    Wannan Basmala ce har ƙarshe aka yi da tsari ƙidan baƙi. Duk wani rubutu da za fara shi a kan allo to ya zama wajebi a yi basmala. Don haka duk lokacin da wani (almajiri) ya zo zai karanta to sai ya fara da wannan basmala.

    Maaliki Yaumid diin      ملك يوم الدين

    Min, lan, kaulasan, raa, wau, mi’ara.     م ل ك ي و م

    Da bilbili da jemage sun bi ruwa sun tafi

    Amajirai suna bi kari (raujin) waɗannan baƙaƙe suna maye su da wani sauti. Irin wannan yana hardasa nishaɗi a cikin karatu. Yin irin wannan yana ƙara masu shauƙin dagewa da naƙaltar wannan karatu da suke yi. Faɗin da bilbili da jemage sun bi ruwa sun tafi ba shi ne fasarar wannan baƙaƙe da suka bi tsarin karinsu wajen karatu ba.

    A wasu baƙaƙen ma irin wannan lamari yana aukuwa, wannan ya bambanta daga makaranta zuwa wata makaranta. Har wa yau ga wasu baƙaƙe da aka yi wa irin hikima:

    Nunguda, a’ilikkafa, baa, dal.   Na’abudu   نعبد

    Mariya na can na tuyar ƙosai       ن ع ب د

    Almajirai kan ɗora karin sauti faɗar ƙida baƙi na kowane sauti (harafi) a mizanin hawa da saukar murya yayin faɗarsa. Don haka wannan ma sun tanadar masa da wata jimla da za ta hau daidai wannan kari na baƙaƙen (harufa). A lokacin faɗin wannan sukan nishaɗantu, hakan, kan ja hankalinsu da su matsa ƙaimi wajen koyon waɗannan baƙaƙe (harufa).

    A wani sashen ƙidan baƙin suna cewa:

     Wa’iyyaka       وإياك    Wau, Ali, yaa, ali baƙa, kaulasan.    و إ ي ا ك

     Maalam yaa kamata a tasshe mu

    Da wannan suke maye gurbin karin ƙidan baƙin “Wau, Ali, yaa, ali baƙa, kaulasan.” A lokacin da muna a makarantar allo, na san duk lokacin tashi ya gabato idan har malam da sauran manyan almajirai masu kama wa malami koyarwa ba su kula ba, sai ka ji sauran almajiran sun ɗauki wannan karatu don su yi wa malami ishara cewa lokacin tashi ya yi.

    A ƙidan baƙi na gaba ma almajirai sukan bijiro da hoton aukuwar wani abu wanda ba lallai ne ya auku ba. Misali:

    suuratu       سورة

     Sin, wau, ra, takuri.     س و ر ة

     Kare yaa jaa tsohuwa,

    Da sin da wau da raa da takuri, idan aka haɗe su, za su ba da suuratu to su kuma almajirai sai su bi karin (raujin) faɗar waɗannan baƙaƙe su maye su da wannan lafazi (Kare yaa jaa tsohuwa) wasu ma sukan ƙara da cewa, tana dahuwar langaɓu. Wannan yana fito da hoton aukuwar wani abu wanda ba lallai ne sun taɓa ganin faruwarsa ba. Amma don nishaɗi sai ka ji suna rera abin su.

    Alhamdu         الحمد

    Ali, lan, haa-saɓe, min, dal.       ا ل ح م د

    Halan dai kai laifi zo dai

    Makarantar allo sai da horo. Duk inda ake koyarwa dole ne ya zamana akwai hani da horo. Akwai dabaru daban-daban da ake bi wajen yin horo, amma dai a makarantun allo akan haɗa da yin bulala don a saita yara (almajirai). Wannan yana daga cikin farfajiyar tunaninsu. Hasali ma idan malami ba ya bugu ana raina shi, wasu iyaye ma ba sa kai yaransu a makarantar duk da ba a bugu. Wannan ya sa sukan zo da lafazin gargaɗi ko yunƙurin hukunta duk wanda ya yi laifi da ƙidan baƙin farkon Faatiha (Alhamdu) wato ali, lan, ha-saɓe, min dal.

    LillaHi, Rabbi,        لله رب

    Lallan, hakuri, raa, baguje.       ل ل ه ر ب

    Kwannan tsohuwa sun wargaje (yamutse)

    A wannan sautin na ƙidan baƙi suke bi su gwama nasu sauti wanda yakan hau daidai da raujin sautin faɗar bakinsu. Almajirai sukan zo da abin da yake a cikin zuciyarsu ko su ɗauko hoton aukuwar wani abu da suka san jera waɗannan kalmomi yakan yi daidai da karin waɗannan baƙaƙe.

    A wani misali kuma a ƙidan baƙi da ake cewa;

    Haa babba, haa ƙarami, watau     ه ح

    Sai su ce:

    Baa babba, baa ƙarami

    A wannan ƙidab baƙi shi ma kamar sauran musamman idan ana rabon wani abu za ka ji an ce, “haa babba, haa, karani” wannan a makarantun tsangaya (makarantar allo ya samo asali. Don haka da wannan kalmar suke maye gurbin karin waɗannan baƙaƙe.

    Ba a karatun baƙi kaɗai irin waɗannan lafuza suka tsaya ba, sai dai ba su cika shiga a cikin ainihin karatun zurare ba. Duk da haka akan samu wasu ayoyi an ɗora masu irin waɗannan lafuza, sai dai ba shi ne fasararsu ba. Ko almajiran ka tambaya ba su cewa fasara ce suka yi. A karatun zurare (Taƙara) kuwa sukan bi wata aya da wani ɗan waƙa wanda shi ma suna bayyana abin da ke cikin zuciyarsu. Misali:

    Wassamudal laziina jaabus sahra bilwadi  وثمود الذين جابوا الصخر بالواد

    In kunu ya buwaya sai a kai shi Mungadi[7]

    Wannan aya ce sukutum. Kuma suka ɗaora ta a mizanin karin faɗar ta da masu tunani. Wasu sukan ƙara da cewa, ”Inda malam Habibu su ka gyara mai yami (Tsami)”. Da yawan almajirai sukan ji shauƙi yayin da suka samu kansu suna amfani da irin wannan raha.

    A wata ayar kuma sukan yi amfani da raujin (kari) sai su bayyana nishaɗi kamar haka:

    Fadakhulu fi ibadii, wadakhuluu Jannati   فادخلوا في عبادي، وادخلوا جنتي

    Sai su ce:

    Wani gari baabu wake, wani garii ko akwai[8].

    Almajiran sukan maye gurbin karin wannan aya da muradun zuciyarsu. Dama dai almajiri yana da buƙata ta abinci, don haja ba abin mamaki ba ne don ya zaɓi wake daga cikin nau’ukan abincin da ke cikin zuciyarsa, ya ɗora a mizanin faɗar karatunsa.

    Kammalawa

    Yara almajirai sun kasance suna gudanar da raha, suna nishaɗantar da kawunansu, musamman a lokacin da suke cikin yanayi mai kyau na ƙoshi. Adabinsu kuma ya yi tasiri a cikin sha’anoninsu da suke gudanarwa. Wannan maƙala ta gano cewa, abin nan da suke bayyanawa a cikin nishaɗinsu ta amfani da salon raujin karatunsu musamman na ƙidan baƙi, su kansu sun san cewa ba wai fasara waɗannan ayoyi ne sukai ba, sun san cewa fasara waɗannan ayoyi da wannan hasali ma laifi ne. Don haka ba su ɗauke shi fasara ba, sai dai sun ta’allaƙa niyarsu ta wannan ga nishaɗi. Nashaɗi na sa yaran su ji suna ƙaunar abu. Idan a darasi aka saka nishaɗi to zai ja hankalin masu koyo. Da wannan muke ganin cewa adabin Hausawa ya yi tasiri ga sha’anin karatun allo ta fuskar saka ma almajirai nishaɗi da zai ja hankalinsu ga mayar da hankali wajen karatu. Haka kuma ina kira ga sauran malaman makarantun allo da su duƙufa wajen fito da sababbin dabarun koyarwa kamar yadda na baya suka yi. Kuma su riƙa wayar wa mutane da kai game da illa, ko rashin illar wannan dabara ta karatu.

    Manazarta

    Alqur’an Alkarim.

    Abbas, M. J. (1978). Al-madd Al-Islami fi ifriqiyyah. Cairo: Al-Mukhtar Al-Islami.

    Babajo, H. H. (2017). The challenges of tsangaya Quranic schools in contemporary societies:  A study of Kano State Nigeria. Asian Journal of Multidisciplinary  Studies,5(6).  Retrievedfrom http://www.ajms.co.in/sites/ajms2015/index.php/ajms/article/view/2530

    Bano, M., Antonisis, M., & Ross, J. (2011). Islamiyya, Qur’anic and Tsangaya education  institutions census in Kano State (Final Draft Report). Kano, Nigeria: Education  Sector Support Programme, Kano University

    Bunguɗu H. U. Da Maikwari, H. U. (2016). Waƙa Zancen Hikima: Gusau. Nasara Printers.  Zamfara State

     Ɗangambo, A. (1981) Rikiɗar Azanci: Siddabarun salo da harshe  cikin  Tabarƙoƙo Tahamisin Aliyu Ɗan Sidi Sarkin Zazzau,  Takardar da  aka gabatar a Kano Studies.

    Ɗangambo, A. (1984) Rabe-raben Adabin Hausa da  Muhimmancinsa  ga  Rayuwar Hausawa, Kano: Triumph  Publishing Company.

    Ɗangambo, A. (2011) “Waƙa da Rawar da Take Takawa A  Rayuwar  Hausawa” (Domin tunawa da cikar shekara  Goma  sha biyu da  rasuwar Alhaji Mamman Shata yana da  shekara 76),  Kwalejin Ilimi ta  Tarayya da ke Kasina ta Shirya.

    Ɗangambo A. (2007), Ɗorayar GadonFeɗe waƙa, (Sabon Tsari) Zariya, Amana Publishers  Limited.

    Ɗangambo A. (1981) Ɗaurayar gadon feɗe waƙa, SHN BUK, Kano

    Ɗangambo A. (1984) Rabe-raben Adabin Hausa da Mahimmancinsa ga  Rayuwar Hausawa, Kano: Triumph Publishing Company.

    Gusau, S. M. (2005). Shari’a A Musulunci: Benchmark  Publishers. Kano.

    Gusau, S.M, (1993) Jagoran Nazarin Waƙar Baka:  Benchmark  Publishers. Kano.

    Gusau, S. M. (2008). Dabarun Nazarin Adabin Hausa: Benchmark  Publishers. Kano.

    Gummi (1970), “Alƙur’ani Da Tarjamarsa, Ma’anoninsa Zuwa Ga

     Harsunan Hausa”, Saudi Arebiya, King Fahad.

    Imam, Y. M. (2002). Appraisal of the historical development of traditional Qur’anic schools  in Northern Nigeria’ Kano (Unpublished PGDE Project). Federal  College of  Education, Kano University, Nigeria.

    Nasir da Wasu (1993) “Tabbataccen Bayani Na Ma’aunin Alƙur’ani,”    Mainasa Kano Nijeriya.

    Sarɓi S. A. (2007), Nazarin Waƙar Hausa, Samarib Publishers Kano.

    Yakasai (2012), Jagoran Ilmin Walwalar Harshe, Garkuwa Media Services    ltd, Sokoto Nigeria.



    [1]A duba maƙalar Ahmad Yahaya Jurnal Pendidikan Islam 4 (1) (2018) 1-14 mai taken Tsangaya: The Traditional Islamic Education System In Hausaland

     

     

    [2] An bayyana a cikin Alƙur’ani maigirma a sura ta As-Saffat, aya ta 28.

    [3] Suratush Shu’arah (26:190-199) an bayyana cewa, Alƙur’ani saukarwar Ubangijin halittu ne Allah (SWA) ga fiyayyen halittu Annabi Muhammadu (SAW) ta hanyar aiko mala’ika Jibrilu (AS).

    [4] Sanin al’umma ne cewa mutum yakan ɗauki littafi mai tsarki (Alƙur’ani Mai girma) ya karanta ko dais hi kaɗai ko ya je gaban malami ya koya masa yana faia shi ma yana amsa wa, ko kuma ya kasance cikin ɗalibai ‘yan uwansa yana karantawa.

    [5] Wata zantawa da muka yi da malam Abdulmalik Abdullahi mainasara a ranar 22, ga Maris, 2021 a cikin ofishinsa da ke FCE(T) Gusau, da misalin ƙarfe 4:30 na Yamma.

    [6]A farkon ƙarni na goma sha tara (Ƙrn 19), hasken waƙoƙin baka ya daƙushe a sakamakon tasowa da bunƙasar rubutattun waƙoƙi a ƙasar Hausa. Wannan ya faru musamman da yake a lokacin ne masu jihadi ke ta fafutukar gyaran halaye tare da kiran jama’a da su kauce wa hululu. A ɓangare guda kuwa, da yawa daga cikin waƙoƙin baka an gina su ne a kan hululu. A duba misalin wasu waƙoƙi da suka haɗa da na makaɗan karuwai da kuma makaɗan ‘yan caca da makaɗan sata.

    [7] A wata zantawa da muka yi da malam Liman Ɗan’audu na Maikwari tun da jima. Kimanin shikara biyar da suka gabata.

    [8] Tattaunawa da Malam Bashir Aliyu Tsafe a ranar 22, ga Maris 2021. A Makarantar Kwalejin Ilmi da Ƙere-Ƙere ta Jihar Zamfara dake Gusau a Ofishinsa da misalin ƙarfe 11:00 na rana.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.