Romantic Words Tsakanin Saurayi Da Budurwa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Malam saurayina ne wanda zan aura idan ya zo zance saiyana son riƙe hannuna wai yana son fingers ɗina, ko kuma ya riƙa min irin maganganun romantic words dai innayi masa magana sai yace min wai ba haramun bane, wai we have to be romantic tunda ba aikata wani abun banza zaiyi dani ba kuma wallahi bashida wani mugun niya a zuciyan shi akaina, Malam to dan Allah menene gaskiyan hakan shin ba laifi bane hakan yana cikin soyayya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    Allah maɗaukakin sarki idan ya haramta wani abu yakan haramta dukkan wata hanya komai kankantarta da zata kai zuwa ga aikata wannan abun. Saninmu irin wannan maganganu na romance ko taɓa jikin mace babbar hanya ce wadda ke motsar da sha’awa zuwa ga aikata zina.

    Duk macen da ta bada kanta wa wani dan iska mayaudari wanda baya sonta baya son rayuwarta da tarihinta da sunan wai yana sonki ko kuma kunyi alkawarin aure wallahi duk yaudara ce, duk wanda zaki masa haka kina tunanin zai aminta cewa idan wani ya zo gunki ba zaki bashi irin damar da kika bashi ba? Kiyi tunani da kyau yake ‘yar uwa! ba wani sonki da yake kawai wani abu ya keso ya cimma akanki na mummunan aiki ya ɓata ki dajin kunyar duniya da ta lahira. Ki sani da zarar ya cimma mugun burinsa akanki shine zaifi kowa kyamarki da gudunki.

    Kiyi masa nasiha akan yadaina yayi haƙuri idan akayi Aure daga nan kinzama mallakinsa amma yanzu bayada ikon komi akanki, idan bai dainaba toki faɗawa manyanku, su nema miki ɗan arziƙi.

    .

    Daga lokacin da saurayi yaga wadda yakeso yaganta sau ɗaya aka fahimci juna to ko shakka babu kada wani abu yaƙara shiga tsakaninsu saidai Aure, Halal abayyane take hakama haramun itama abayyane take.

    Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Abu Hurayrah (Allah ya yarda dashi) Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Yace: ”Allah yana rubutawa ɗan Adam kasonsa na zina, zai riski wannan kason babu makawa, zinar ido itace kallo, zinar kunne saurara, zinar harshe zance, zinar kafa tafiya, zuciya tayi buri tayi sha’awa, farji shi zai yarda ko ya karyata”.

    Hadisi ya tabbata wanda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace: Abuga Narkakkiyar kusar wuta ta bakin karfe akan ɗayanku shi yafi masa alkhairi akan ya shafi jikin macen da bata hallata agareshi ba. Albany yace hadisine ingantacce acikin sahihul jamiul kabeer (5045).

    Waɗannan hadisan kaɗai ya isa ya zama tsawa da firgitarwa ga samari da kuma ‘yan matan da ake yaudara da sunan ana sonku, ya isa kuji tsoron Allah ku tuba tun kafin lokaci ya kure muku, ku lazumci yiwa Allah biyayya cikin abunda ya haramta na dokokinsa, na daga abunda shafar mace yake haifarwa wanda yake kaiwa zuwa ga fitintunu da alfasha kala-kala.

    Lallai tsantsar soyayyah tana cikin bin tafarkin Allah da kuma bin Annabinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Allah yasa mudace.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.