Sallah A Cikin Najasa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mara lafiya ne ba ya iya komai da kansa sai an taimaka mi shi. Ba ya riƙe najasa, a kullum alwalarsa ya karye ta ke. Sallar ma sai an ce masa ya isa, sannan yake yin sallama. To ko zai iya yin sallah duk da yana cikin najasa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    Asali a wannan babin dai shi ne maganar Allaah Maɗaukakin Sarki cewa:

    فَاتَّقُوا اللَّهَ مَا اسْتَطَعْتُمْ

    Ku kiyaye dokokin Allaah da gwargwadon iyawarku. (Surah At-Taghaabun: 16).

    Kenan wanda yake iya yin sallah da cikakken tsarki na hadasi (alwala ko wanka) da na khabasi (jiki da tufafi da wuri) haka ɗin zai yi. Wanda kuma ba zai iya ba saboda larura, sai ya yi gwargwadon ikonsa. Sallarsa ta yi, kuma ba shi da laifi, in shaa’al Laah.

    Don haka, idan lokacin sallah ya yi, sai a taimaka ma wannan mara lafiyan, a gyara shi ta fuskar wanke ƙazantarsa da yi masa alwala ko wanka, da sabunta masa tufafi da wuri mai tsarki. Sannan a taimaka masa har ya iya bayar da wannan farillar, ko a tsaye ko a zaune ko kuma a kwance da gwargwadon yadda yake iyawa.

    Idan kuma an lura cewa, akwai wahala ko takurawa wurin yin sallarsa kowacce a lokacinta, ana iya rage lokutan zuwa uku, ta hanyar ya haɗa Azahar da La’asar ya yi su a lokaci guda. Haka ma Maghriba da Isha’i a lokaci guda. Asubah ma a lokaci guda. Kamar dai yadda nassi ya zo a kan mai larurar istihaala.

    Sannan ko da yana sallar kuma najasar tana cigaba da zuba, wannan ba zai ɓata masa sallar ba, saboda larura ce a gare shi. Kamar dai yadda nassoshi suka tabbata a kan haka game da mai istihala.

    Muna roƙon Allaah ya ba shi lafiya tare da dukkan marasa lafiyarmu a koina su ke. Ya sa jinya ta zama kaffara a gare su.

    Masu kula da majinyata kuma a duk inda su ke, Allaah ya ba su lada, ya sa su yi ƙoƙari domin neman yardar Allaah da hakan, kuma ya saka musu da alkhairi. Kuma ya haɗa mu gaba ɗaya a Gidan Aljannah.

    Wal Laahu A’lam.

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    +2348021117734

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.