Sanarwa Daga Zauren Tambayoyi Da Amsoshi Game Da Gyaran Ibada

    Assalamu alaikum, warahmatullahi wabarakatuhu

    Muna yiwa yan uwa da iyayenmu dake cikin wannan zaure na TAMBAYA DA AMSA fatan kuna lafiya

    Ya aka ji da ibtila'in jarabawar rayuwa - to Allaah ya bamu ikon Nasara akan kowacce jarabawa da Allaah ya tsara mana

    Bayan haka !

    Saqonnin ku dayawa sun riske ni, inda wasu suke tambaya a game da group na musamman wanda zasu gyara ibada don bautawa Allaah kamar yanda Annabi Rahama Sallallahu alaihi wasallam ya koyar damu wasu kuma sun bada shawarar a bude wani group din da za'a saka littafin koyarda Sallah kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyarda sahabbansa

    Ina son duk wanda yake karanta wannan saqon, yayiwa kan sa tambaya

    "SHIN SALLAR DA NAKE YI A KULLUM SAU 5 IRIN TA CE ANNABI YA KOYAR A ADDINANCE KO KUMA INA YI NE KAMAR YANDA NA TASO NAGA ANA YI A AL'ADANCE

    Ka maimaita tambayar kanka kamar sau 3. Anan take zaka ji hankalin ka ya dawo jikin ka sannan zaka fara kwokwanto akan anya sallar tawa ma an amshe ta kuwa ?

    Tunda ga dai Hadisin Abu Hurairah nan a cikin Sahihul Bukhari da Muslim wanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: Sallu kama ra'ayta Muni usalli" Bi ma'ana: "Kuyi sallah kamar yanda kuka gani Ina yi" Kadai sake tambayar kanka: Anya irin sallar Manzon Rahama nake yi

    To kada ka samu damuwa domin kuwa ga wata dama ta samu cikin sauqi da zaka gyara ibadarka idan har kana da niyyar gyarawa din

    Da akwai littafin: SIFATU SALATIN NABY - MINAT TAKBIRI ILAT TASLIM - KA'ANNAKA TARAHA" Ma'ana: "SIFFAR YANDA ANNABI YA KE SALLAH - TUN DAGA TAKBIR (ALLAHU AKBAR) HAR ZUWA TASLIM (ASSALAMU ALAIKUM) - KAMAR KANA GANIN ANNABI DIN YANA SALLAH A GABANKA"

    Wanda ya wallafa littafin shine: Allamatish Shaikh Muhaddith Mujaddid Muhammad Nasiriddin Ibn Nuhu Al-Albaany (Rahimahullah - ya rasu a 1999 a kasar Jordan) wanda malaman duniya suke kiransa da likitan ilimin Hadisi. Malamai irinsu: Shaikh Abdulaziz Bin Baaz (shugaban committee na Fatawa Lajnah ad-Da'imah dake a kasar Saudiyya kafin ya rasu a shekarar 1999), Shaikh Saleh al-Uthaymeen da Shaikh Ali Shaikh da Shaikh Saleh Al-Fawzaan duk sun sallamawa Shaikh Al-Albaany indai magana ake ta ilimin Hadisai

    Na karanta littafin Kuma na fahimce sa ba sau 1 ko 2 ba amman duk da haka ji nake da akwai gyararraki a cikin sallata to ina kuma ga wanda bai karanta littafin ba ko Kuma wani littafin makamancinsa na koyon sallah

    Dalilin da yasa na aminta da fara karatun littafin a cikin sabon group din da zamu bude shine

    1️Domin na qara gyara Sallah ta yanda zanyi koyi da irin Sallar Annabi Sallallahu alaihi wasallam kamar yanda yayi umarni

    2️Domin dubunnan musulmi da suke a group dinnan su dinga koyi da Sallah irin ta Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam - Wanda a yanzu haka Zan iya zayyano kura-kurai sama da guda 100 da masu Sallah suke yi

    3️ Domin mu samu ladan koyi da Sunnar Annabin Rahama Sallallahu alaihi wasallam

    Idan har muna son mu zamo muminai da Allaah Azzawajallah ya saukar da Surah musamman mai sunan Suratu Muminuun to fa sai mun saka Tawadu'u wato Khushu'i (Tsoron Allaah) a cikin sallar mu, kamar yanda Allaah Subhanahu wata'ala yace

    ( قَدْ أَفْلَحَ الْمُؤْمِنُونَ )

    المؤمنون (1) Al-Muminoon

    Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ.

    ( الَّذِينَ هُمْ فِي صَلَاتِهِمْ خَاشِعُونَ )

    المؤمنون (2) Al-Muminoon

    Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne.

    To ta yaya zamu samu Khushu'i a cikin sallar mu indai har bamuyi koyi da fiyayyen halitta ba

    Mu sani cewar Sallah itace Ibadar da za'a fara tambayar mu a ranar Alqiyama, kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya faɗa: idan tayi komai zaiyi kyau ammanfa idan ka tozar ta to sauran ayyukan naka ma ba'a magana. Domin kuwa ka ga ita musamman Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya je ya karbo ta a can saman 7, ba kamar Azumi, Hajji da Zakkah da Mala'ika Jibril Alaihis salam aka aiko ba

    Dan Haka duk Wanda yake da ra'ayi da Kuma niyya: Namiji ko Mace, Tsoho ko Tsohuwa, Miji ko Mata, Babba ko Yaro sai ya yi min magana ta private yaji tsare tsaren da ake bi daganan sai a sakashi a group din: "USMANNOOR ACADEMY"

    Zamu fara karatun littafin: SIFATU SALATIN NABY din duk ranar Asabar da Lahadi da daddare, (daga Asabar/Lahadi ta sama) in Sha Allaah

    A tura saqon sanarwan zuwa ga sauran yan uwa da abokan arziki da basa wannan zauren. Wanda yake buqata yayimin magana ta private idan so samu ne a kirani ta WhatsApp call ta Yanda Zan saurin ganewa saboda yawan saqonnin da ake turowa

    Ya Allaah ka bamu ikon bauta maka yanda ka umarci a bauta maka ba yanda muka taso muka ga ana bauta maka ba

    Ya Allaah kamar yanda muka hadu a wannan zaure na TAMBAYA DA AMSA, Allaah ka sada fuskokinmu a ALJANNATIL FIRDOUS

    ( اتْلُ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِنَ الْكِتَابِ وَأَقِمِ الصَّلَاةَ ۖ إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَىٰ عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنكَرِ ۗ وَلَذِكْرُ اللَّهِ أَكْبَرُ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا تَصْنَعُونَ )

    العنكبوت (45) Al-Ankaboot

    Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littãfi, kuma ka tsayar da salla. Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abni ƙyãma, kuma lalle ambaton Allah ya fi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa.

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    SANARWA

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.