Shahara Da Bunkasar Tijjani Hashim Da Jihar Kano a Bakin Sa’idu Faru

    Citation: Yakasai, M.G. (2024). Shahara Da Bunƙasar Tijjani Hashim Da Jihar Kano a Bakin Saidu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 263-270. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.034.

    Shahara Da Bunƙasar Tijjani Hashim Da Jihar Kano a Bakin Sa’idu Faru

    Daga 

    Murtala Garba Yakasai Ph.D
    Department of Nigerian Languages,
    Bayero University, Kano.
    +234 08029458283
    mgyakasai.hau@buk.edu.ng

    Tsakure

    Takarda ce a kan Waƙar Baka ta Sa’idu Faru, wadda ya tsara game da shahara da bunƙasar wani Ƙasaitaccen Masarauci a fadar Kano wato Alhaji Tijjani Hashim Galadiman Kano wadda kuma ta yi naso har zuwa ga shahara da bunƙasar Jihar Kano a matsayinta na ɗaya daga cikin jihohi goma sha biyu (12) da Gwamnatin Mulkin Soja ta General Yakubu Gowon ta ƙirƙiro. An sami wannan waƙar ne a mazubin Mp3, sai aka juye ta a rubuce domin amfanuwar wannan takardar. Manufar wannan takarda ita ce domin ta bayyana yadda Tarihin masarautar Kano zai daɗe bai manta da irin shahara da bunƙasar Galadiman Kano Tijjani Hashim ba, ta mabambantan fuskokin rayuwa, wata manufar kuma ita ce domin a bayyana cewa kowace irin Jiha ko Ƙasa ko kuma Nahiya a duniya takan shahara ta bunƙasa sakamakon ƙarfin tattalin arziƙin ƙasa da bunƙsar kasuwanci. Jihar Kano ta sami tagomashin cigaba da shahara tare da bunƙasa ta hanyar ciniki da kasuwanci da kuma masa’antu, har ta kai ta kawo, a ka samu kafuwar manya - manyan Kamfanoni masu yawan gaske, hakan kuma bai kasance abin mamaki ba domin ko can dama a kan yi wa garin Kano kirari da cibiyar kasuwanci (Centre For Commerce & Industry). Ashekenan babu mamaki da Sa’idu Faru ya fito da irin martabar da wannan masarauci ya samu a cikin rayuwarsa da kuma fito da martabar Jihar Kano, inda ya dinga lissafo manyan Kamfanoni yana cewa duk suna nan a Jihar Kano. Binciken ya gano cewa shahara da bunƙasar Galadiman Kano ta samu ne sakamakon irin tallafa wa al’umma da share musu hawaye da kai musu ɗauki a ɓangarorin rayuwa iri daban - daban da ya dinga aiwatarwa ga dukkan wanda ya kai masa kuka. A ɗaya ɓangaren kuma shahara da bunƙasar Jihar Kano ta samu ne sakamakon tagomashin samun ƙasaitattun ’yan kasuwa waɗanda suka haɓaka saye da sayarwa da kuma kafa manyan Kamfanoni kamar yadda Malamin Waƙa mai kwana Ɗumi na Mamman na Balaraba ya bayyana.

    Keɓaɓɓun Kalmomi: Sa’idu Faru, Jihar Kano, Ƙanin Sarkin Kano, Injimi, Kamfanoni, Gidan Radiyo

    1.0 Gabatarwa

    An yi bayanin yadda mawaƙin ya gina tsarin waƙarsa daga dandamalin wani Bajimin masarauci wanda ya shahara a zamaninsa wato Alhaji Tijjani Hashim wato Galadiman Kano, wato ɗaya daga cikin Sakatarorin Firimiyan Jihar Arewa na farko Alhaji Sir. Ahmadu Bello K.B.E (Sardaunan Sakkwato), kuma ya kasance hamshaƙin Basarake mai faɗa a ji a fadar Kano. Alhaji Tijjani Hashim ya riƙe sarautar Ɗan Isan Kano da Ɗan’iyan Kano da Turakin Kano har zuwa Galadiman Kano, wadda a kanta ne ya rasu. Mawaƙin ya yi amfani da shahara da bunƙasar wannan Masarauci ne, har yadda sannu a hankali ya dinga fito da shahara da bunƙasar Jihar Kano cikin hikima da azanci irn nasa. An yi bayanin yadda Kano ta shahara tare da bunƙasa a fagen kasuwanci da kuma manya - manyan Kamfanoni iri daban - daban waɗanda masu hannu - da - shuni suka kafa domin ciyar da Jiharsu gaba, sai kuma yadda Jihar Kano ta haɓaka ta bunƙasa a fagen Noma da samar da wadataccen abinci, wanda ɗaukacin jihohin Arewa suke dogaro tare da alfahari da ita.

    2.0 Wane ne Sa’idu Faru ‘Malamin Waƙa na Mamman na Balaraba?

    Bincike ya tabbatar da cewa an haifi Sa’idu Faru a garin Faru ta cikin ƙasar Maradun, Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara a wajejen shekara ta 1932. Ana kuma yi masa laƙabi da Ɗan’umma wadda matar ƙanin Ubansa ta sanya masa, saboda ba ya faɗin sunanta, sai dai yana kiran ta Umma, amma wannan laƙabi bai shahara a tsakanin mutane ba, balle ya danne sunansa na yanka watau Sa’idu. Shi kansa Sa’idu Faru yakan yi wa kansa da kansa kirari cewa:

    Ɗan’umma Rungumi,

    Ɗan Tumba Rungumi.

     

    Sannan mahaifin Sa’idu Faru shi ne Makaɗa Abubakar ɗan Abdu, shi kuwa Makaɗa Abdu, Alu Maikurya ya haife shi. Ashe ke nan Sa’idu Faru shi ne ɗan Abubakar ɗan Abdu da Alu Maikurya, dukkan waɗannan makaɗa an yi su ne a garin Faru, sai dai mahaifiyar Sa’idu mutuniyar Banga ta cikin ƙasar Ƙauran Namoda ce, kuma a can ne aka haife ta.

     

    Gadon Kiɗa

     

    Sa’idu Faru kamar sauran makaɗan Fada ya yi gadon kiɗa ta wajen mahaifinsa, Kakansa na sama makaɗa Alu makaɗin kurya ta kiɗin yaƙi ne wadda ake yi wa kirari, “Kurya gangar Mutuwa”. Makaɗa Alu ya yi waƙoƙi da yawa a zamanin yaƙi, sai dai ba za a iya kawo su a yanzu ba saboda tsawon lokaci.

     

    Ƙuruciyar Sa’idu Faru

     

    Yawancin ƙuruciyar Sa’idu Faru ya yi ta a garin Banga ta Ƙauran Namoda, inda aka haifi uwarsa, amma kafin ya girma ƙwarai sai ya koma wurin tsohonsa makaɗa Abubakar a Faru. Makaɗa Sa’idu bai sami ilimin Muhammadiyya da yawa ba, sai dai an sa shi makarantar allo inda ya yi zurfi ga karatun Alkur’ani mai tsarki. Haka kuma ba a sa shi makarantar boko ba, domin haka bai san komai ba game da sha’anin boko. Alalhaƙiƙa tun yana yaro sha’anin kiɗa da waƙa ya ɗauke masa hankali.

     

    Sa’idu Faru a Fagen Waƙa

     

    Makaɗa Sa’idu Faru ya koyi waƙa a wajen mahaifinsa makaɗa Abubakar, waƙoƙinsa suka daɗa kyautatuwa ta hanyar fasaha da hikima tare da ƙwaƙwalwar da Allah ya ba shi. Tun Sa’idu Faru yana da shekara goma aka fara zuwa yawon kiɗa da shi gari - gari. Bayan da ya cimma shekara goma sha shida ya soma karɓi, a wannan lokaci ne kuma aka haɗa su tare da ƙanensa Mu’azu wanda shi ne Ɗangaladimansa a halin yanzu.

     

    Taƙaitaccen Tarihin Jihar Kano da Cigaba ta Fuskar Masana’antu

     

    Jihar Kano tana ɗaya daga cikin jihohi goma sha biyu da Gwamnatin Nijeriya ta Sojoji ta kafa a watan Mayu, 1967. Girman jihar yana da murabba’in mil dubu goma sha shida da ɗari shida da hamsin (16,650 Square miles). A ƙidayar mutanen da aka yi a 1973 an samu akwai mutane kusan miliyan goma sha ɗaya a cikin jihar Kano. Yawancin mutanen da ke Kano Hausawa ne kuma Musulmai.

    Kasancewar Kano a matsayin jiha tana gabatar da mulkinta ƙarƙashin kulawar Gwamna, wanda yake gabatar da Gwamnatinsa da taimakon Kwamishinoni, waɗanda suke riƙe da ma’aikatu daban - daban (wato Ministries), waɗanda Gwamnati ta kakkafa saboda su taimaka mata sauƙin tafiyar da aikace - aikacenta na yau - da - kullum.

    A ƙarƙashin Gwamnati kuma akwai ƙananan hukumomi waɗanda suke taimakon Gwamnati wajen tafiyar da aikace - aikacen mulki. Waɗannan ƙananan hukumomi Gwamnati ce ta kafa su, domin a samu sauƙin tafiyar da mulki. A lokacin da aka kafa Jihar Kano cikin 1967 akwai manyan masana’antu guda hamsin da uku (53). Waɗanda jarinsu ya kai Naira Miliyan ɗari da sittin ( 160,000,000:00K), kuma suna da kimanin maaikata guda dubu takwas, sannu a hankali kullum yawan waɗannan masa’antu ƙaruwa suke yi, haka kuma yawan ma’aikatan yana daɗa bunƙasa. Kodayake yawancin waɗannan masana’antun na ’yan kasuwa ne, amma Gwamnati ta kafa wasu daga cikinsu da ƙarfin kanta ko kuma da haɗin kan wasu mutanen waje da kuma wasu ’yan ƙasa ga misalin wasu daga cikinsu.

    a.      Kano State Oil and Allied Products Limited - - Man gyaɗa

    b.      Northern Nigeria Flour Mill - Fulawa

    c.       Textiles Commodities - - Saƙa

    d.     Kano Dyeing & Printing Factory - Kujeru da Gadaje

    e.      Nigerian Bottling Company Limited - Lemon Kwalba

    f.        Kano Citizens Trading Company Limited - Tufafi

    g.      Nigerian Suiting Man. Co. Limited - Tufafi

    h.      Kano Transport Corporation - Sufuri da Motoci

    i.        Kano Mid - West Timber Limited - Katako

    j.        Kano State Ginnery - Gurzar Auduga

    Bayan waɗanan Kamfanonin mallakar Jihar Kano, wasu daga cikin manyan ’yan kasuwa na jihar Kano sun yi hoɓɓasa wajen buɗe kamfanoni mallakin kansu kaɗan daga cikinsu sun haɗa da:

    a.      Nigerian Industrial Group (Na Sunusi Ɗantata) - Gidan Ƙusa

    b.      Bagauda Textile Mill Ltd. (Alh. Isyaku Rabi’u) - Tufafi

    c.       Kano Citizen Trading Co. Ltd. (Alh. Baba Ɗanbappa)— - Tufafi

    d.     Federal Industries Limited (Alh. Inuwa Wada) - - Ashana

    e.      Fertile Acres Limited (Alh. Audi Howeidy) - Gidan Kaji

    f.        Moon Confectionary Ltd. (Alh. Nababa Badamasi) - Alewa

    g.      Mai Nasara and Son’s Ltd. (Nasiru Ahali) - Bulo da ɗab’i

    h.      Fedco Foam (Nig) Limited (Alh. Ibrahim Musa Gashash)—Katifun Roba

    i.        Alh. Uba Ringim & Co. Nig. Ltd. (Alh. Uba Ringim) - Man gyaɗa.

    j.        Nigerian Manufacturers & Distribution Co. Ltd. (Alh. Ibrahim Musa Gashash) - Man Gyaɗa

    Babu shakka jihar Kano ta amsa kirarin da ake yi mata na Cibiyar Ciniki domin waɗannan Kamfanoni mallakar Gwamnati da kuma na ’yan kasuwa sun sanya jihar ta shahara da bunƙasa da kuma haɓaka ƙwarai a ɓangarori daban - daban. A wancan lokacin har kuma zuwa yanzu haka akwai masa’antu waɗanda suke yin abubuwa iri - iri kamar tufa da man - gyaɗa da alewa da takalma da naman gwangwani da dai sauransu. Da can wajen 1948 an fara kafa masana’antu a tsohuwar Bompai, watau wajen Haɗeja Road zuwa Maganda Road, zuwa hanyar filin jirgin sama da gidan Mishan. Bayan nan ya cika sai aka sake keɓe filin Bompai inda yawancin masana’antun Kano suke a yanzu. Daga wajen 1968 ita ma Bompai ta cika da masana’antu, filaye suka ƙare, saboda ganin yadda sababbin masana’antu suke ƙaruwa a Kano sai Gwamnatin Jihar Kano ta sake keɓe wani filin a can Sharaɗa da Challawa, wato kudu da tsakanin ƙofar Ɗan’agundi da ƙofar Na’isa domin bai wa masu neman fili damar kafa masana’antu.

    Tabbas irin wannan haɓaka da jihar Kano ta samu a fagen kasuwanci da Kamfanoni da saye da sayarwa da ƙere - ƙere da cigaban zamani su ne suka yi tasiri ƙwarai a zuciyar Sa’idu Faru Malamin waƙa mijin Talatu da Balaraba, har aka wayi gari ya fito da irin wannan shahara da bunƙasa ta Birnin Kano a wasu ɗan waƙa da ya rera wa Galadiman Kano Marigayi Alhaji Tijjani Hashim. Waƙar da ya kira ta da sunan “Komai kaj jiya ƙarya a kai.”

    4.0 Fito da Tumbatsar Alhaji Tijjani Hashim da Jihar Kano a Ɗan Waƙar

    A wannan ɗiyan na waƙar Malamin waƙa na Mamman na Balaraba mai kwana Ɗumi ya taɓo azanci da hikima irin waɗanda ya shahara a kansu domin kuwa waƙa ce wadda ya gina ta domin fito da ƙima da martaba ta wani hamshaƙin ɗan Sarki wadda tarihin masarauta da garin Kano ba za su taɓa mantawa da irin gagarumar gudunmawar da wannan masarauci ya bayar ba musamman ta fuskar mulki da cigaban kasuwanci, da uwa - uba taimakon gajiyayyu da marassa ƙarfi da kuma ƙoƙarin yayyafa wa dukkannin wata wutar rikici da ta kunno kai ruwan sanyi. Wannan kuwa ba wani ba ne illa Alhaji Tijjani Hashim (Galadiman Kano), amma da waƙa ta yi waƙa sai yabon shahara da bunƙasar Jihar Kano ya mamaye waƙar.

    A ɗiyan waƙar na farko - farko ga abin da Makaɗa Sa’idu Faru yake cewa:

    Jagora : Mai ɗamara na Abashe ana shakkar haye ma Ahmadu.

    ’Yan amshi : Mai daraja na Wambai ɗan Hashim ƙanin Sarkin Kano.

    Jagora : Toron Giwa ƙi fasawa ƙi fasawa,

    ’Yan Amshi :Ɗan Hashim ƙanin Sarkin Kano Keta maza ba fasawa.

    Jagora : Toron Giwa ba togewa ɗan Hashim ƙanin Sarkin Kano x2

    ’Yan Amshi :Keta maza na Abashe ana shakkar haye ma Ahmadu.

    Jagora : Ga ka da kyawu zamne da kyawu,

    ’Yan Amshi : Ahmadu kamfaragen Sarkin Fada,

    : Sansanin Galadiman Kano,

    : Kurum kake mai ban tsoro,

    : Ɗan Hashim ƙanin Sarkin Kano.

    Jagora : Baba kware kake ba faɗawa,

    ’Yan Amshi : Ɗan Hashim ƙanin Sarkin Kano,

    Jagora : Sa’idu Faru ka waƙar ka waƙar iko,

    ’Yan Amshi : Komai kaj jiya ƙarya a kai.

    Jagora : Sa’idu Faru ka waƙar mulki,

    ’Yan Amshi : Komai kaj jiya ƙarya a kai,

    : Sake da maza na Abashe ana shakkar haye ma Ahmadu,

    : Mai daraja na Wambai ɗan Hashim ƙanin Sarkin Kano.

     

    Makaɗa Sa’idu Faru ya yi yabo ga Tijjani Hashim inda ya kira shi da mai ɗamara ya kuma danganta shi da kakansa wato Abashe (Sarkin Kano Abbas) wanda yake mahaifi ga Sarkin Kano Abdullahi Bayero. Shi kuma mahaifi ga Sarkin Kano na goma sha uku (13) a Daular Fulani wato Alhaji Ado Bayero CFR, LL.D, JP. Ya kuma kwarzanta shi da cewa ba a haye masa, ma’ana ko kaɗan ba ya ɗaukar raini/wargi. Sai kuma ya kira shi da mai daraja na Wambai (Wamban Kano Abubakar ɗa ga Sarkin Kano Sir Muhammadu Sanusi I), wato kakan Sarkin Kano na goma sha huɗu (14) a Daular Fulani Mai Martaba Malam Muhammadu Sanusi II CON, ya kuma yi nuni da cewa ƙani ne ga Sarkin Kano Ado Bayero. Har kuma ya yi masa kirari da cewa shi ɗin Toron Giwa ne, mai keta maza wanda ba ya fasa tunkarar inda ya sanya gaba cikin lamuransa na rayuwa. Bugu da ƙari, ya bayyana cewa yakan keta maza kuma su ɗin ma sukan ji shakkar haye masa, saboda kwarjininsa. Ya kuma yi yabo a gare shi, ta fuskar halittarsa, ya kuma ambace shi da cewa, shi mutum ne mai kawaici, kuma kamewarsa takan bai wa maza tsoro. A cigaban waƙar ya kira shi da “kware ka ke ba faɗawa” wato wata matattarar ruwa mai zurfi wadda ake shakkar afkawa cikinta kai tsaye.

    Ya bayyana ƙarara a cikin ɗan waƙar inda ya ce, “Sa’idu Faru ka waƙar ka waƙar iko” a nan yana nuni da cewa tabbas shi Sa’idu shi ne yake yi wa Alhaji Ahmadu Tijjani Hashim waƙar mulki/iko, domin kuwa ɗan sarauta ne.

    A cikin waƙar ne sai ya yi dabararsu ta makaɗan dauri ya kutso da yabon Birnin Kano inda yake cewa: -

    Jagora : Na so zuwa Birnin Kano,

    ’Yan Ashi :Sai an ka ce in za a zuwa waƙa Kano kai wa a kai.

    Jagora :Na so zuwa Birnin Kano,

    ’Yan Amshi :Sai an ka ce in za a zuwa waƙa Kano kai wa a kai.

     

    Tirƙashi, a nan ne ya cusa dabararsa ta marari/soyayyarsa zuwa Birnin Kano, ya kuma yi nuni da cewa ‘wai idan za a zo Kano, “kai wa a kai” wato ma’ana mutum bai zuwa garin Kano hannu - rabbana ko kuma yadda masu azancin magana suke cewa hannu yana dukan cinya, wato dai duk wani talaka wanda zai zo Kano (kai wa a kai) ma’ana sai ya riƙo ɗan wani abin hasafi wanda zai gabatarwa da Sarki ko wani masarauci a matsayin girmamawa. Wato dai abin da mutanen fada suke kira da gaisuwa a yanzu kuma a ce cin - hanci ko toshiyar baki. A ɗiyan da ke biye sai ya kuma jaddada cewa shi fa ko kaɗan ko alama ba zai sayo tabarmi ko wundiya ba, domin ya kawo su a matsayin “kai wa” (gaisuwa/cin - hanci/rashawa) zuwa ga sarkin Kano ba, ga abin da yake faɗi:

     Jagora : Ni ban biya tabarmi in aika su gun Sarkin Kano,

    ’Yan Amshi : Kuma ban sayen Wundaye in aika su gun Sarkin Kano.

     

    Sai kawai ya fito da sana’arsa a fili wadda ita ce wadda ya shahara a kanta, ga abin da yake cewa:

     

    Jagora  : Waƙa ni kai ita niy iya,

    ’Yan Amshi  : Ita za ni wa kowa Kano,

    Jagora : Waƙa ni kai ita niy iya,

    ’Yan Amshi  : Ita za ni wa Sarkin Kano.

     

    Makaɗa Sa’idu Faru, ya cigaba da yi wa Tijjani Hashim kirari da yabo kamar haka:

    Jagora  : Keta maza na Abashe ana shakkar haye ma Ahmadu,

    ’Yan Amshi  :Mai daraja na Wambai ɗan Hashim ƙanin Sarkin Kano,

    : Ahmadu cika ni aza ni ka ba ni,

    : Kuɗi in tai Haji in dawo bisa marsandi in raba baƙƙan ciki,

    :In dai gidan ga da kaya ban zuwa ko Moriki.

    Jagora  : In dai kiɗin barkan ka da kaya ban zuwa ko Moriki.

    Jagora : Na keta maza na Abashe ana shakkar haye ma Ahmadu,

    ’Yan Amshi  : Mai daraja na Wambai ɗan Hashim ƙanin Sarkin Kano.

     

    A irin hikimar makaɗan fada, Makaɗa Sa’idu Faru ya yi roƙo na cika masa aljihunsa a kuma cicciɓa shi bisa, a ɗaukaka darajarsa a kai shi Ƙasa mai tsarki ya yi ibadar aikin Hajji, idan kuma ya dawo a saya masa mota marsandi domin ya dinga hawa, ko ba komai zai raba wa abokan hamayyarsa baƙƙan ciki, wato zai tunkuɗa musu haushi. Ya kuma nuna cewa idan dai har yana samun kyautuka to fa ya zo Kano kenan da zama ko kaɗan bai komawa gida garinsu, kai a taƙaice ma ba zai je ko Moriki ba, wato ya ji daɗin zaman Kano kenan.

     

    Bashakka Makaɗa Sa’idu Faru mai kwana ɗumi, malamin waƙa na Mamman na Balaraba fasihin makaɗi ne domin kuwa a cikin wannan waƙa ne sai makaɗin ya cuso dabarar yabo da shahara da kuma bunƙasar Jihar Kano wanda daman yana ɗaya daga ɓangaren taken wannan takardar (Shahara da bunƙasar Tijjani Hashim da kuma Jihar Kano ta bakin Sa’idu Faru) ga abin da ya fara da shi,

    Jagora : Za ni gidan Rediyon Kaduna,

    ’Yan Amshi :In yi yabon Jihar Birnin Kano.

     

    Jagora : Za ni gidan Rediyon Kaduna,

    ’Yan Amshi:In yi yabon Jihar Birnin Kano.

     

    Tabbas a nan ya yi babbar hikima domin kuwa ya ambato gidan Radiyo mafi ƙarfi da shahara a dukkannin faɗin Najeriya ta arewa, (wato Rediyon Tarayya na Jihar Kaduna). Ya bayyana cewa can ne zai je domin ya yi waƙar yabon Jihar Kano, wato ma’ana domin ta karaɗe dukkannin ƙasar Hausa, domin Radiyo ce wadda take da ɗimbin al’ummar Hausawa masu saurarenta. Shakka babu a wannan ɗiya da suka gabata ne wani ɓangare na sunan takardar ya bayyana.

     

    Haka kuma yabon bai tsaya a nan ba, sai da ya ambaci gidan Radiyon Sakkwato inda ya ce:

     

    Jagora :Za ni gidan Radiyo na Sakkwato,

    ’Yan Amshi:In yi yabon Jihar Birnin Kano.

     

    Sai kuma ya gangara wata shiyyar wato Ikko inda ya ce:

    Jagora :Za ni gidan Rediyon Ikko,

    ’Yan Amshi : In yi yabon Jihar Birnin Kano.

     

    Ko ba komai makaɗa Sa’idu Faru ya yi hikimar bayyana cewa, al’ummar Hausawa suna can sun yi kaka - gida a Jihar Ikko (Lagos), har ga shi yana cewa zai je har can domin ya yi waƙar yabon Jihar Kano.

    Haka dai mawaƙin ya dinga lissafo wasu Jihohin kamar Barno da Badin (Ibadan) da Jamhuriyyar ƙasar Nijar, duk ya bayyana cewa zai je gidajen Radiyonsu domin ya yi waƙar yabon Birnin Kano ga abin da ya ce:

    Jagora: Za ni gidan Rediyo na Barno,

    ’Yan Amshi:In yi yabon Jihar Birnin Kano.

     

    Jagora:Za ni gidan Rediyo na Badin,

    ’Yan Amshi:In yi yabon Jihar Birnin Kano.

     

    Jagora:Za ni gidan Rediyo na Nijar,

    ’Yan Amshi:In yi yabon Jihar Birnin Kano.

     

    Bayan da Makaɗa Sa’idu Faru ya zayyano kewayen wasu Jihohin Nijeriya tare da bayyana zai kai musu ziyara domin ya yi yabon Jihar Kano, sai kuma kawai ya yi ta yanke - ta gille, inda masu azancin magana suke cewa an yi ta ƙare wai haihuwa da hanji inda ya ce:

    Jagora:Nijeriya kaf Arewa babu jiha irin Birnin Kano,

    ’Yan Amshi:Nijeriya kaf Arewa babu jiha irin Birnin Kano.

     

    Makaɗa Sa’idu Faru ya ɗebo ta da faɗi, domin ya bayyana cewa a dukkannin jihohin Nijeriya na wancan lokaci guda goma sha biyu (12), to kuwa lallai babu kamar Birnin Kano, domin ya ɗaure akuyarsa a gindin magarya, sai ya dinga kafa hujjarsa kamar haka:

     

    Jagora:Lallai shi na Birnin Kano,

    ’Yan Amshi:Yadi yana Birnin Kano.

     

    Jagora:Kyauta tana Birnin Kano,

    ’Yan Amshi:Mulki shi na Birnin Kano.

     

    A waɗannan Ɗiya na waƙa da suka gabata Malamin Waƙa ya bayyana cewa Birnin Kano ta shahara ta fuskar sayar da sutura/tufafi (yadi) sannan kuma Kanawa mutane ne masu kyauta, sannan ya yaba musu ta fuskar iya gudanar da mulki.

     

    A fagen ƙara fito da shahara da bunƙasar Jihar Kano Makaɗa Sa’idu Faru Malamin Waƙa mai Kwana Ɗumi na Mamman na Balaraba ya kwarzanta Jihar Kano inda ya dinga jero sunayen manya - manyan masa’antu da suke sarrafa abubuwan cigaban zamani ya bayyana cewa dukkannin irin waɗannan Kamfanoni suna nan a cikin Birnin Kano ga misalai daga ɗiyar waƙar tasa:

    Jagora: Injimin yin jirgin sama,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora :Injimin yin iirgin ƙasa,

    ’Yan Amshi :An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin yin motoci,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin ƙera makkammai,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin yin tasoshi,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin yin mashin hawa,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin yin motar noma,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin yin vaspan hawa,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagoara:Injimin yin motar noma,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin galmal shanu,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin ban - ruwa na lambu,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin yin takalma,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin shirya agogo,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Jagora:Injimin yin langogi,

    ’Yan Amshi:An ce shi na Birnin Kano.

     

    Malamin Waƙa mai kwana Ɗumi na Mamman na Balaraba, ya fito da matsayinsa na shahararren mawaƙin ƙasar Hausa, a wannan waƙa tasa domin kuwa ya bayyana shahara da bunƙasar Jihar Kano a ɓangarori daban - daban na cigaban zamani da fasahar ƙere - ƙere, inda ya dinga ɗaukar abubuwan more rayuwa daki - daki yana bayyana cewa dukkanninsu akwai injimin sarrafa su a jihar Kano, tun farko dai ya bijirar da kalmar Injimi (inji) wadda ita ce karɓaɓɓiyar kalmar da ake fassara kalmar (engine) wato na’ura da ita daga Ingilishi zuwa Hausa.

    Makaɗin ya bayyana cewa injimin yin jirgin sama da injimin yin jirgin ƙasa da injimin yin motoci da injimin ƙera makammai da injimin yin tasoshi da injimin yin mashin hawa da injimin yin motar noma da injimin yin vaspan hawa da injimin yin motar noma da injimin galmal shanu da injimin ban - ruwa na lambu da injimin yin takalma da injimin shirya agogo da kuma injimin yin langogi duk ya tattare manya - manyan abubuwan more rayuwa da cigaban zamani ya bayyana cewa injimin da yake samar da ɗaukacin waɗannan abubuwan duk suna nan a Birnin Kano. Babu shakka wannan shahara da bunƙasa ta Jihar Kano ya kai matuƙa ta bakin Sa’idu Faru.

    A ɗaya ɓangaren kuma makaɗin ya nuna ƙwarewa a fagen waƙa, domin kuwa bayan ya gama bayyana shahara da bunƙasar garin Kano ta fuskar kasuwanci da ƙere - ƙeren zamani sai kuma ya ambato babban al’amari wanda shi ne yake haifar da shahara da bunƙasar gari cikin sauƙi da kwanciyar hankali wato abinci kenan ga abinda yace:

    Jagora: Babban abincin ’yan Arewa,

    ’Yan Amshi: Gero na shi na Birnin Kano.

     

    Jagora: Gero yana Birnin Kano,

    ’Yan Amshi: Dawa tana Birnin Kano.

     

    Bashakka samuwar abinci a wadace shi ne yake haifar da shahara da bunƙasa da kuma ɗorewar arziki da zaman lafiya a cikin kowace irin al’umma. A matsayin jihohin Arewa su ne suke ɗauke da mafi yawan kaso daga ɗimbin al’ummar Nijeriya, kuma babban abincin da suka dogara a kansa shi ne gero da dawa, sai Malamin Waƙa Mai kwana ɗumi ya bayyana cewa dukkannin nau’in waɗannnan cimaka suna nan da yawa a cikin Jihar Kano.

    5.0. Kammalawa

    An karkasa wannan takarda zuwa ɓangarori guda biyar (5). Bayan gabatarwa, sai aka ɓuntulo tarihin Makaɗa Sa’idu Faru tun daga haihuwarsa har zuwa fara waƙarsa, a babi na biyu kenan, sai kuma aka bibiyi taƙaitaccen tarihin Jihar Kano da ambato sunayen wasu daga cikin manya - manyan ’yan kasuwa da masu hannu - da - shuni na Jihar Kano, waɗanda suka yi amfani da arzikin da Allah ya hore musu domin kafa Kamfanonin da Jihar take taƙama da su, kuma kamfanonin ne dai Malamin Waƙa ya hau bisa doronsu domin fito da shahara da bunƙasar Jihar ta Kano, wanda shi ne babi na uku. Dangane da Babi na huɗu kuwa shi ne inda takardar ta yi bayanin waƙar tun daga kan ɗiyan da suka yi magana game da hamshaƙin masarauci Alhaji Tijjani Hashim (Galadiman Kano), wanda ya kasance fitaccen ɗan Sarki kuma Masarauci sannan hamshaƙin ɗan kasuwa, mai bayar da taimako ga gajiyayyu har ma da masu ƙarfin. Lokacin rayuwarsa kullum gidansa a cike yake da jama’a masu neman agajinsa walau na kuɗi ko kuma wasu hanyoyi na alfarma, domin kuwa a duk faɗin ƙasa Nijeriya babu inda ba shi da alfarma, waya - Allah ta nemo kwangila ko ta samarwa matasa aikin Gwamnati ko kuma ta kashe wutar wata rigima ko rikici da yake neman kunno kai. Shi ne ya mallaki kamfanin tafiye - tafiye na Trans - Air Services mai hidimar ɗaukar mahajjatan Nijeriya zuwa ƙasa mai tsarki na dukkannin jahohin Arewa da kuma wasu daga Kudancin ƙasar. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da hikima da basira a cikin ragowar ɗiyan waƙar inda suka taimaka wajen fito da ƙima da shaharar birnin Kano ta fuskar cigaban zamani. Daga bisani aka kawo kammalawa da manazarta, sai kuma rataye na hotunan Galadiman Kano Tijjani Hashim lokacin da yake ganiyar ƙuruciyarsa yana yaro da kuma lokacin da yake cikakken magidanci yana kuma riƙe da sarautar Galadiman Kano, A ɓangaren rataye na wannan takarda an kawo hotunan Alhaji Tijjani Hashim har guda biyu (2), hoto na farko tun lokacin ƙuruciyarsa ne, suna su huɗu ne tare da ’yan ’uwansa na jini, daga ɓangaren hagu zuwa dama na hoton, marigayi mai martaba Alhaji Ado Bayero ne, wadda ya zamo Sarkin Kano na goma sha huɗu a ƙarƙashin Daular Fulani, kusa da shi kuma sai Alhaji Tijjani Hashim (wadda wannan waƙar ta yi jan - geza daga waƙar da Sa’idu Faru ya shirya masa), sai kuma Alhaji Hamidu Bayero wanda shi ma ɗa ne ga Marigayi Abdullahi Bayero, dukkanninsu ukun nan sun rasu kawo zuwa lokacin rubuta wannan takarda, sai cikon na huɗunsu daga ƙarshen ɓangaren hannun dama shi ne Ambasardor Ado Sunusi shi kuma har kawo rubuta wannan takarda yana nan a raye, duk sun ɗauki wannan hoto na tarihi ne lokacin ƙuruciyarsu. Dangane da hoto na biyu kuwa hoto ne na shi Alhaji Tijjani Hashim yana zaune bisa kan doki, hoto ne na hawan sarauta lokacin yana kan sarautar Galadiman Kano, ga shi nan bisa doki yana sanye da koren rawani da farar babbar riga, wato shiga irin ta ƙasaitaccen masarauci. Ko shakka babu duk inda aka ji an ambaci wani mutum da suna Malam to lallai ya cancanta, hakan ne ya tabbatar mana da yadda Makaɗa Sa’idu Faru ya zamo Malamin waƙa musamman ta yadda ya shirya wannan waƙa tasa mai cike da armashi.

    Manazarta

    Abba, M. & Zulyadaini, B. (2000). Nazari kan waƙar baka ta Hausa. Zaria, Nigeria: Gaskiya Corporation Limited.

    Bunza, A. (2008). Gadon Feɗe al’ada. Lagos: Tiwal Publishers Nigerian Limited.

    CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University, Press.

    Ɗanmusa, M.A. (1990). Nazari a kan yadda mawaƙan baka ke aiwatar da waƙoƙinsu. Kundin digiri na ɗaya. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Furniss, G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa. Edinburgh: Edinburgh University Press Limited.

    Gusau, S.M. (1988). Waƙoƙin makaɗan fada: Sigoginsu da yanaye - yanayensu. Kundin digiri na uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Gusau, S.M. (2003). Jagoran nazarin waƙar baka: Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S.M. (2008). Waƙoƙin baka a ƙasar Hausa Yanaye - yanayensu da sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S.M. (1996). Makaɗa da mawaƙan Hausa: Kaduna Fisbas Media Services.

    Gusau, S.M. (2012). Makaɗan Hausa Jiya da yau. Takarda da aka gabatar a taron makon Hausa na 39. Kano: Ƙungiyar Hausa, Jami’ar Bayero.

    Gusau, S.M. (2014). Waƙar baka Bahaushiya: Professorial inaugural lecture on the Hausa oral songs, series No. 14. Kano: Jami’ar Bayero.

    Government, K. S. da Ministry of C..& I. (1968). Harkokin Ciniki da Sana’o’i a Jihar Kano: Kano: Government Printing Press.

     Ibrahim, M.S. (1983). Kowa ya sha Kiɗa. Ikeja: Longman Nigeria Limited.

    Sokoto, S.N.H.N.J.U.D (2013). Makaɗi a mahangar manazarta Jerin takardu da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani kan tubar Muhammadu Gambu Mai Kalangu. Kano: Gidan Dabino Publishers.

    Salisu, D.M. (1982). Rabe - raben waƙoƙin baka na Hausa da tasirinsu ga rayuwa a ƙasar Hausa. Kundin digiri na biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Umar, M.B. (1987). Dangantakar adabin baka da al’adun gargajiya. Kano: Triumph Publishing Company.

    Yahya, A.B. (1997). Jigon nazarin waƙa: Kaduna: Fisbas Media Services.

     

    Rataye Na I



    Alhaji Ado Bayero

    Daga ɓangaren hagu zuwa dama na wannan hoton, marigayi mai martaba Alhaji Ado Bayero ne, kusa da shi kuma sai Alhaji Tijjani Hashim, sai kuma Alhaji Hamidu Bayero, sai cikon na huɗunsu daga ƙarshen ɓangaren hannun dama shi ne Ambasardor Ado Sunusi duk sun ɗauki wannan hoto na tarihi ne lokacin ƙuruciyarsu.

    Rataye Na II

    Alhaji Tijjani Hashim

    Dangane da hoto na biyu kuwa hoto ne na shi Alhaji Tijjani Hashim yana zaune bisa kan doki, hoto ne na hawan sarauta lokacin yana kan sarautar Galadiman Kano.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.