Shin Ko Ka San /Ke San Cewa Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III Ya Ƙarfafa Zumunci Tsakanin Masarautar Sakkwato Da Sauran Masarautun Arewa Ta Hanyar Auratayya?

Kamar yadda ya taras a gidan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi na sada zumunci da ƙarfafa dangantaka tsakanin Cibiyar Daular Usmaniya ta Sakkwato da sauran Tutocin dake ƙarƙashin Daular ta hanyar auratayya, Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III ɗan Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi a tsawon mulkinsa na shekara 50 da watanni (domin ya yi Sarauta daga watan Yunin shekarar 1938 zuwa wafatinsa a watan Nuwamban shekarar 1988) ya jaddada wannan manufar.

A lokacinsa kamar yadda ya gada daga magabatan farko, Sarkin Musulmi Abubakar III ya ƙarfafa auratayya tsakanin 'ya'yansa/ɗiyansa mata da Sarakunan Tutocin Daular har ma da na cikin gida( a Cibiyar Daular ).

WASU DAGA CIKIN SARAKUNAN DA SUKA AURI' 'YA'YA /ƊIYA MATA NA MARIGAYI MAI ALFARMA SARKIN MUSULMI ABUBAKAR III A CIKI DA WAJEN CIBIYAR DAULAR USMANIYA.

1. Marigayi Mai Martaba Sarkin Gwandu, Alh. Haruna Rasheed.

2. Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Dr. Ado Bayero.

3. Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr. Shehu Idris.

4. Marigayi Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Muhammadu Mera.

5. Mai girma Sarkin Gobir Sabon Birni, Alh. Abdulhamid Bawa.

6. Marigayi Mai girma Wazirin Sakkwato, Dr. Junaidu.

7. Marigayi Mai girma Magajin garin Sakkwato, Alhaji Aliyu Usman.

8. Marigayi Mai girma Sarkin Bod'inga, Alh. Abdulra'uf.

9. Marigayi Mai girma Dikkon Gande, Alh. Garba.

10. Marigayi Mai girma Sarkin Gobir na Isa, Alh. Ahmadu II.

 

Wannan lamarin ya daɗa ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin Cibiyar Daular Usmaniya da Tutocinta da mataimakanta. Allah jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

 

Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.

Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.

08149388452, 08027484815.

birninbagaji4040@gmail.com

Talata, 06/08 /2024.

Post a Comment

0 Comments