Shin Ya Halatta A Bayyana Wata Niyya A Wani Aiki A Musulunci

Assalamu alaikum warahmatullah

Allah ya taimaki malam abinda kamanta baka fadi ba yadda zatayiniyya wato abin da zata karanta kafin ta fara wankan janaba dana hailah yadda ake fada aniyar wankan ina so kafada musu domin mutane da dama basusan yadda ake

niyar ba., da kuma abinda ake karantawa sannan afara wankan fatan kafahimce ni na gode.

AMSAH

ALHAMDULILLAH

yar'uwa Allah ya saka miki da alkhairi, saboda koqarin ki na son al'umma su fahimci addinin allah.

yar'uwa haka yake ban gayi yarda ake cewa ba kafin a fara wankan, kuma ba mantawa niyi ba, Naqi gaya ne  saboda hakan bai tabbata daga annabi Muhammad  (s.a.w) ko wani sahabi daga cikin sahabban sa a bayyana niyyar yin wani aiki a yayin da za a aikiata shi, shi dai ya ce: dukkan aiyuka ba sa yuwuwa sai da niyya. ya fadi haka cikin hadisin amirul mu'uminin umar dan qaddab (r.d) ruwayar bukhari da muslim.

kuma malaman musulunci sunyi ijma'i (wato kansu ya hadu) akan cewa qirqirarran abu ne kuma bid'ace ayi furuci da niyya yayin da za a yi wani aiki na shari'a

Kuma malamai magabata sun ce ita niyya muhallinta shine  zuciya (wato azuciya ake nufatar ta  ba'a furtata ba)

kamar yadda aka tambayi sheakh bn uthaimin a kace shin ya halatta ayi furuci da niyya ko bai halatta ba

sai ya ba da amsah da ce wa: yin furuci da niyya ba'a shar'anta shi ba  a shari'a, yin hakan ma bad'a ne (wato abune da aka qirqiru shi), idan mutum yai niyyar zaiyi salla kada ya ce: nayi niyyar yin salla kaza da kaza, kuma ka da ya ce nayi niyyar yin dawafi ko sa'ayi, ita  niyya mahallin ta shine zuciya, hakama a wajan yin alwala ka da yace: na yi niyya zan yi alwala, ko na yi niyya zan yi  wankan, niyya mahallin ta shine zuciya, dukkan aiyuka sai da niyya, niyya muhallinta shine zuciya, niyya ita ce nufin yin wani abu, nufata ta zuciya, ba a shar'anta furuci da ita ba. (wato niyyar)

Kuma abun da wasu daga cikin malaman fiqihu suka ce na furuci da niyya babu wani dalili akan shi, kai hakan ma kurkore ne, abun da aka shar'anta mutum yayi niyya da zuciyar sa, idan mutum ya mike zaiyi alwala yayi niyar da zuciyar sa, idan ya ta shi zaiyi salla yayi niyyar wannar sallar da zai yi azuciyar sa, idan ya nufaci ka'aba domin yin dawafi sai yayi niyyar hakan (a zuciyar sa), idan ya fuskanci wajan yin sa'ayi domin yin sa'ayi sai shima yayi niyyar yin hakan a zuciyar sa, kada ya ce nayi niyyar zan aikata kaza.

[ya fadi hakan ne afatawar sa nurun alad darbi].

ina fatan kin fahimta, domin a shari'ar muslinci ba'ayin furuci da niyya,  kawai idan kika sa a ranki zakiyi wanka domin daukewar jinin haila ko nifasi to shi kenan niyyar  ki tayi, hakama kowani aiki a musulunci, ba a yin furuci da niyar sa, domin allah ya fimu sanin abun da yake a cikin zuciyoyin mu.

WALLAHU A'ALAM

amsawa [abu abdullah]

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments