Tasirin Bikin Auren Hausawa a Kan Yarabawa Mazauna Gusau

    For Citation: Haruna Umar Maikwari and Kabiru Salisu (2022). Tasirin Bukin Auren Hausawa a Kan Yarabawa Mazauna Gusau. Maƙalar da aka buga a Tauraruwa Journal of Hausa Studies (TJoHS) ISSN:2814-0222. Shafi na 224-235.

    Tasirin Bikin Auren Hausawa a Kan Yarabawa Mazauna Gusau

    Haruna Umar Maikwari

    Department of Hausa Language.
    Federal College of Education (Technical) Gusau
    maikwariharuna@gmail.Com
    (+234) 07031280554

    Da

    Kabiru Salisu

    Department of Hausa Language.
    Zamfara State College of Education, Maru
    kabirusalisu224@gmail.Com
    (+234)07067727698

    Tsakure

    Wannan maƙala za ta mayar da hankali ne wajen nazarin cuɗanya tsakanin Hausawan Gusau da Yarabawan Garin Gusau. Manufar wannan maƙala ita ce, ta fito da irin cuɗanya da ta gudana tsakanin al’ummun biyu, wato Hausawa da Yarabawa. Sannan kuma a fito da hanyoyin da aka bi wajen yin cuɗanyar da kuma sakamakon da cuɗanyar ta haifar. Hanyar da aka bi wajen aiwatar da wannan maƙalar ita ce, ta karance-karancen bugaggun littattafai da kundayen bincike da mujallu na ilmi daga makarantu daban-daban. An kuma zaɓi a ɗora wannan binciken (Maƙala) a kan ra’in Cuɗanya na Bourhis (Interraction). Wannan ra’in wani Bature ne ya assasa shi domin bayyana yadda cuɗanya take gudana tsakain al’ummu biyu. Sakamakon binciken da wannan maƙalar ta fitar shi ne, wannan cuɗanya ta haifar da zaman lafiya da fahimtar juna da auratayya tsakanin al’ummun biyu da kuma nason al’adun Hausawa a kan na Yarabawa. Maƙalar ta bayyana duk hanyoyin da ake bi wajen yin cuɗanda tare da abubuwan da suke haddasa cuɗanya kamar dai baƙunta da makamantansu.

    1.0 Gabatarwa

    Hausawa da Yarabawa al’ummu ne daban-daban, sai dai kuma sun kasance suna maƙwabtaka da junansu. Wannan ya sa al’ummun suke da kusanci har wasu sukan kasance a ƙasar wasu. Maana dai Hausawa kan je ƙasar Yarabawa su zauna su yi kasuwanci ko wata sanaa. Haka ma Yarabawa kan zo ƙasar Hausa su zauna su yi kasuwanci ko wata sanaa. Wannan ba sabon alamari ba ne idan aka yi laakari da yadda kowace alumma ta kasance a ƙasar wata.

    Kasancewar ƙasar da ake kira Nijeriya a yau ta haɗa da wani yanki na ƙasar Hausa da kuma ƙasar Yarabawa wannan ya taimaka wajen haɗuwar al’ummun biyu (Hausawa da Yarabawa). Akwai kuma sana’ar fatauci wadda tun kafin a raɗa wa Nijeriya suna ake yin ta wadda Hausawa kan je a wasu ƙasashe daga ciki har da ƙasar Yarabawa. Wannan ma ya taimaka wajen samun cuɗanya tsakanin Hausawan da Yarabawa. Dangane da Yarabawa da suke zaune a garin Gusau kuma, tarihi ya bayyana zuwan wasu Yarabawa a garin Gusau sakamakon layin dogo da aka samu a garin.

    1.1 Manufar Bincike

    Babbar manufar wannan binciken ita ce, binciko irin hulɗa da ke tsakanin Hausawan garin Gusau da Yarabawan mazauna garin Gusau. Akwai kuma wasu manufofi da suka haɗa da:

    i.                    Fito da irin cuɗanya da ta gudana tsakanin al’ummun biyu wato Hausawa da Yarabawa.

    ii.                  Sannan kuma a fito da hanyoyin da aka bi wajen yin cuɗanyar.

    iii.                Bayyana sakamakon da cuɗanyar ta haifar.

    1.2 Matsalolin Bincike

     Nazarce-nazarce sun gudana a kan abin da ya shafi tasirin aure ko wata al’ada ko wani harshe a kan wani ko ma cuɗanya tsakanin wata al’umma da wata daban wadda ke hardasa tasirin wani abu a kan wani kamar da Burgress da Locke, (19530 da Rauf, (1977) da Funtua, (2010) da Rambo, (2013) da Auta, (2014) duk sun yi magana a kan aure. Sai dai duk binciken da aka zo da shi babu wanda ya kalli cuɗanyar Hausawa da Yarabawan gari Gusau. Babu shakka waɗannan al’ummu biyu sun yi cuɗanya a tsakaninsu kuma cuɗanyar ta haifar da wani sakamako, amma manazarta hankalinsu bai kai ga wannan cuɗanyar ba. Yin wannan cuɗanyar ya haifar da tasirin bikin Hausawa a kan na Yarabawa mazauna garin Gusau.

    1.3 Hanyoyin Gudanar da Bincike

     Wannan maƙalar ta kammala ne ta hanyar hira da wasu mazauna unguwar garin Gusau da ma wasu Hausawa da suke zaune a garin na Gusau. An kuma tambayi wasu masu ilmi dangane da kasantuwa da cuɗanya tsakanin al’ummu biyu. Haka kuma an bi hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da kundaye da muƙalu da masana da manazarta suka gudanar. Wannan ya ba da damar tattara dukka bayanan da aka gina wannan bincike.

    1.4. Ra’in Bincike

    An zaɓi a ɗora wannan maƙalar a kan ra’in Cuɗanya Bourhis (Interraction). Bourhis ya assasa wannan ra’i, kuma ya bayyana cewa, ta fuskar hulɗa da cuɗanya tsakanin wata al’umma da wata ana samun wata al’umma ta yi tasiri a kan wata. Bourhis ya ƙara da cewa, ana samun cuɗanya ta fuskar karɓar horo, wato mutum ya samu horo kafin ya tsunduma cikin sha’anin rayuwar wasu[1]. Wannan maƙalar ta mayar da hankali ne wajen duba cuɗanya tsakanin Hausawan garin Gusau da Yarabawa mazauna gari Gusau tare da duba irin tasirin da harshen Hausa ko Hausawan suka yi a kan Yarabawa.

    2.0 Ma’anar Aure

    Aure alaƙa ce ta halaccin zama tsakanin miji da mata, ana yin sa ne domin shi aure sunna ce ta Annabi Muhammada Rasulullahi (S.A.W) domin tsarkaka zuri’a. Aure muhimmin abu ne ga al’umma saboda haka akwai hanyoyi da matakai na tabbatar da shi. Mataki na farko shi ne neman aure. Haka kuma akwai wasu matakai na wali, da dukiyar aure da sauransu.

    Rambo, (2013), ya ruwaito, Burgress da Locke, (1953) na cewa “Aure zamantakewa ce ta amincewar mutum ɗaya ko fiye da ɗaya ko mace ɗaya ko fiye da ɗaya mai dangantakar mata da miji”. Rauf, (1977:78) ya bayyana aure da: “Ƙulla yarjejeniya da za ta haifar da halaccin saduwa da mace da samun zuri’a. Kuma wani ɓangare ne na mu’amala da ibada”.

    Auren gargajiya na Hausawa ya danganci zaman tare a tsakanin namiji da mace a bisa yardar juna ko amincewar dangi ta hanyar wasu ƙa’idoji na al’ada ko na addini. Ibrahim, (1985:i). Aure muhimmin al’amari ne ba kawai a wurin al’ummar Hausawa, har ga sauran al’ummomin duniya gaba ɗaya.[2]

    A gudummuwa irin wannan za a iya cewa: “Aure na nufin haɗuwa ko ratsawar wani abu a cikin wani abu, mutum ko dabba ko tsiri da makamantansu. Domin samun albarkar da ke tattare da abubuwan da suka haɗu ko suka ratsa juna”.

    Idan kuma aka kalli ma’anar a addinance za a iya cewa, “Aure wata hanya ce ta bai wa namiji da macce damar zama tare da saduwa ta hanyar jin daɗi da mutunta junansu. Ita wannan hanya ko yarjejeniya ana gabatar da ita ne a gaban shaidu tare da yanka sadaki, kuma yadda addinin musulunci ya ƙayyade a kuma zartar da shi ta hanyar da sunnar Manzon Allah (SAW) ta tanada.

    Haka kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya ambaci aure a cikin littafinSa Mai Tsarki wato Alƙur’ani cewa, (Ku auri abin da ya fi maku daɗi daga mata biyu-biyu ko uku-uku ko huɗu-huɗu, amma idan ba za ku iya adalci ba ku auri ɗaya)[3].

    Sannan kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, (Mafi yawancin aure mai albarka shi ne, auren da yake da ƙarancin sadaki kuma babu riya a cikinsa.)[4]

    Bergery, (1934) da Roxana (1997) da Abraham (1962) dukkan su ba su bayar da ma’ana wadda za a gane aure ba. Sai dai sun yi maimaicin kalmar sun saka a cikin jimla wasu kuma sun yi fasara daga Hausa zuwa Ingilishi. A ƙamusun Jami’ar Bayero kuwa, an bayyana cewa, “Aure dangantaka ce tsakanin namiji da mace ta hanyar shari’a, ko mace da namijin tattabara, ko haɗa wani tsiro da wani don samun ingantaccen iri”. CNHN, (2006:22). “Aure wani tsari ne wanda Allah ya shirya wa mutum musulmi, wanda ya ba shi damar ya nemi matar da ta dace domin su zauna tare a matsayin miji da mata bisa wasu sharuɗɗa da Allah ya shimfiɗa masa”. Auta, (2014:279).

    Daga ma’anonin da suka gabata za a iya cewa: “Aure hanya ce ta haɗa ko ƙulla dangantaka tsakanin mace da namiji waɗanda za su zauna tare kuma a wuri guda a matsayin mata da miji, wadda kowace irin al’ada ta duniya ta amince da ita a kan dangantaka ta din-din-din domin yawaitar al’umma da kuma ci gabanta.”

    3.0 Haɗuwar Hausawa da Baƙi

     Masana da manazarta sun tabbatar da ƙasar Hausa tana da kyakkyawan yanayi da sararin noma. Noma ya zama muhimmiyar sana’a wadda take samar da nau’o’in ci da na sayarwa. Ga albarkar dabbobi da tsuntsaye na gida da na daji, sannan kuma ga ma’adanai tun daga azurfa da tagulla da tama da ƙarfe har ya zuwa kwalli da dalma da kanwa da gishiri da kuma duwatsu iri-iri da marmara da sauransu. Wannan ya sanya jama’a daga ko’ina suke sha’awar zuwa ƙasar Hausa don samun abubuwan rayuwar yau da kullum. Gusau, (1999)

     Baƙuwar al’umma wadda ta fara shigar Hausawa kuma suka cuɗanya ainun su ne al’ummar Larabawa, musamman idan zancen shigowar Bayajida a ƙasar Hausa ya tabbatar, to, yana daga cikin Larabawan na farko da suka fara haɗuwa da Hausawa, (Gusau, 2008:48-49)

     Dukkan waɗannan bayanai[5] da aka yi suna zama a matsayin dalilan da suka sadar da al’ummar Hausawa da wasu al’ummu. Kuma wannan saduwa tana haddasa cuɗanya, idan kuma aka yi cuɗanya ciki za a samu mu’amala, yayin da mu’amala da samu tsakanin al’ummu biyu mabambanta kuwa za a iya samun dangantaka da fahimtar juna wanda yana iya haifar da auratayya. Duk kuwa inda aka samu auratayya, to babu mamaki al’adu za su bayyana a cikin sha’anin kuma wasu kan iya ɗaukar na wasu daga nan kuma mu’amala da al’adu za su bazu. Bourhis, (1997)

    3.1 Dalilan da ke Haddasa Baƙunta a Al’adance

     A la’adar Hausawa abubuwa da dama sukan haddasa wa Bahaushe zama baƙo. Wasu daga cikin dalilan sananni ne ga kowace irn al’umma. Wasu kuma sun keɓanta ne ga Hausawa kawai. Babban abin da ke haddasa ƙaurar Hausawa daga mazauninsu zuwa wani wurin zama nesa da su, akwai annoba. Tun gabanin wayewar kan zamani. Idan annoba ta wanzu a ƙasa mutanenta kan sauya wurin zama a bar kangayen gidaje ba kowa. Na biyu akwai matsanancin fari na ruwan ƙasa, ko na sama, ko talafar arzikin gona, ko na lambu, duk suna haddasa ƙaurar Bahaushe zuwa wani wuri. Na uku akwai rashin mafakar yaƙi domin kariya ga abokan gaba masu kai hari da samame. Tsoron da ya zama bawa na sa abar wurin zama a ƙaura zuwa waninsa. Na huɗu aikata abin assha ko abin kunya a gari na sa wanda ya aikata ya bar garinsu bari na har abada. Bunza, (1991:2) A wannan zamani kuwa, kasuwanci da neman ilmi da yaɗa shi da sha’awar yawon buɗa ido na daga cikin musabbaban ƙaurace-ƙauracen Hausawa daga wata nahiya zuwa wata har su zama baƙi, hukuncin baƙunci ya hau kansu. Waɗannan ba su kaɗai ne dalilan da ke haddasa ƙaurar Hausawa ba. Bunza, (1991:2)

    3.1.1 Tafiye-tafiyen Buɗe Ido

     Al’ummar duniya suna tafeye-tafiyen yawo buɗe ido, don samun ƙarin hikimomi na rayuwa. A wasu lokuta yawon yakan zama buɗe ido a kan waɗansu abubuwa waɗanda suka saɓa wa zaman al’umma. A ƙasar Hausa an sami irin waɗannan tafiye-tafiye na buɗe ido daga baƙi daban-daban, amma daga cikin waɗannan ana zaton Azbinawa da Buzaye su suka fara zuwa ƙasar Hausa. Bayan sun tafi wasun su sun zauna nan sun narke suka zama Hausawa. Wasu daga cikinsu sun zauna a wurare. Misali a cikin Birnin Kano sun zauna a Agadasawa, da Fagge, da kuma Durumin Arbabi. A wajen Kano kuwa akwai yankunan da suka zauna kamar Bichi, da Kura da Birnin Kudu da Bebeji da kuma Gwarzo. (Mu’azu, 2013:37).

     Haka kuma Hausawa su ma sukan niƙi gari su tafi yawon buɗe ido, wasun su ma suna iya zama a can, kwanci tashi har su saje da al’ummar da suka samu a can. Hakazalika daga cikin yawace-yawacen buɗe ido da al’ummar Hausawa suka yi har suka samu cuɗanya da baƙin al’adu akwai:

    3.1.2 Ci-rani

    Ci-rani shi ne barin gari ko ƙauye a tafi wani gari ko maraya don ga-aiki, ko ga-sana’a, akasari daga lokacin kaka zuwa faɗuwar damina. (CNHN, 2006:77). Bincike ya tabbatar da cewa a ƙasar Hausa akan sami watanni shida babu ruwan sama, to, irin wannan yanayi ne ke ba Hausawa damar fita daga wurarensu zuwa wasu wurare don yin wasu sana’o’i da ayyuka na musamman. Irin wannan fita ce Hausawa ke ambata da ci-rani, kuma ana yin wannan fita ne don cinye tsayin rani, ta inda ba za a dawo ba sai alamun damina sun fara bayyana. Gusau, (2008:6).

    Ci-rani dai ya ƙunshi barin garin da mutum yake don samun wata sana’a da za ta taimaka masa ya samu abinci don ya kare mutuncinsa da na iyalinsa. Idan Bahaushe ya noma abinci ga damana a wancan zamanin yakan aje yana ci har wata shekara. Kwance-tashi za a zo ga wata rana da abincin zai ƙare ko kafin ya ƙare sai ya fita ya nufi inda zai samu abinci kafin wata damina da zo.

    3.1.3 Ziyarar Wuraren Tarihi

     Tarihi wani abu ne da yake fito da abubuwa na al’ummomi da suka wuce domin na baya su san su. Tarihi abu ne mai hango al’umma tare da yanayin rayuwarta, ko yanayin mazauninta, ko kamannin halittar rayuwarta. Yakan kuma duba al’umma dangane da addininsu da sarautunsu, ko abincinsu ko murna da alhininsu ko soyayya da ƙiyayyarsu, ko ilmi da jahilcinsu da dai sauran abubuwan da tarihi ne kaɗai aka tabbatar da alhakin yin haka. (Mu’azu, 2013:40)

     Al’ummar Hausawa sukan ziyarci wurare masu muhimmanci musamman wuraren da suka danganci addinin Musulunci. Misali a wancan zamani Hausawa sukan je aikin Hajji a ƙasa tun daga nan ƙasar Hausa har ƙasar Saudiyya (Makka). A kan hanyarsu sukan yada zango a wurare daban – daban. Kuma ita wannan tafiya ba tafiya ce ta ɗan lokaci kaɗan ba, suna iya yin kimanin shekara a hanya kuma suna tafiya suna neman abinci har su isa. Wasu in sun je ba su samu damar dawowa, wasu kuma sukan dawo. Waɗanda ba su samun dawowa ba dole su samu kansu a wasu ƙasashe kuma su yi kaka-gida a can (su zauna a can). Irin wannan zaman yana haddasa cuɗanya da al’ummar duk da suka zauna tare da ita. Bunza, (1991:5)

    3.1.4 Yaƙe-Yaƙe

     Al’ummar Hausawa sun buɗe ido sun ga ana yaƙi, to amma wannan bai wuce wanda ake yi tsakanin gari da gari ba. Kuma akasarin makaman da ake amfani da su ba su wuce takobi ba da wuƙaƙe da kwari da baka ba. Amma bayan Turawan mulkin mallaka sun mamaye ƙasa sai aka samu ƙarin makamai irin su bindiga da sauran manyan makamai irin su igwa. Mu’azu, (2013:41)

     Yaƙi wata musiba ce da ke aukuwa ga al’umma su tarwatse kowa ya kama gabansa. Duk wanda yaƙi ya riska ba zancen ya tsaya yin bankwana ko wani shiri don haka duk inda ya samu kansa dole ya yi ƙoƙarin sajewa da al’ummar da ya tarar ta hanyar yin cuɗanya da al’ummar da ya tarar domin samun sauƙin gudanar da mu’amula da al’ummar.

     Yaƙe-yaƙe sun kasance wasu dalilai da suka haddasa yauwar al’ummar Hausawa. Waɗannan yaƙe-yaƙe ba su rasa nasaba da zuwan Turawan mulkin mallaka, duk da cewa ko da Turawa suka zo ƙasar Hausa sun tarar Hausawa suna zuwa gari-gari su yaƙi juna su samu ganima su kama bayi. Zuwan Turawa abin ya sauya kuma ya kasance mai matuƙar tashin hankali. Wanda shi ya yi sanadiyyar tarwatsewar wasu Hausawan zuwa wasu yankuna da ba na Hausawa ba. Kuma zaman su a can yana haddasa masu cunɗanya da wasu kuma za a iya samun mu’amula a tsakani. Mu’azu, (2013:42)

    4.0 Tsokaci a Kan Al’ummar Yarabawa

     Al’ummar Yarabawa kamar sauran al’ummu da suke zaune a cikin ƙasar Afrika. Kamar yadda ya zo a ƙarni na 19, cewa al’ummar sun samu asalin sunan na su daga Hausawa, wato ‘YAR RIBA’. Wanda ya samu karɓuwa har bayan da Turawan Mulkin Mallaka da masu ‘yaɗa addinin Kirista suka sauya yadda ake furta kalmar ta koma “Yaruba” cikin sauƙi. Usman (2003:107-111). Manazarcin dai ya ƙara da cewa, wannan suna na Yoruba ya samu asali ne ga daga cibiyar Yarabawa wato Oyo. A cikin wannan ƙarni na sha tara. Babu tantama wannan ra’ayin yana da tangarɗa, musamman idan muka lura da kalmar da aka ta’allaƙa da ita a matsayin asali. Haka kuma za a iya yarda da cewa, kalmar ta samo asali ne daga su kansu Yarabawan da suke cewa, “AWA OMO YORUBA” wato (Mu ɗiyan Yoruba), wannan ya fi zama ƙwaƙƙwaran dalilin da za a iya dogaro da shi fiye da wancan. Usman (2003:107-111),

     Ban da waɗannan ra’ayoyi akwai ma wasu ra’ayoyi da aka samu a cikin wasu rubuce-rubucen tarihi da tarihihi. Misali mu duba wani aikin da Shaihin Malami Muhammadu B. Masani Al-katsinawi (d. 1078 A.H.-1667 A.D) ya yi da wani littafi mai taken Azharul-Ruba Fi Akhbar Bilad Yarba. Akwai wani littafi na Muhammadu Bello mai taken Infaqul Maysur. Wanda ya yi bayani a kan Yarabawa a yunƙurinsa na bayanin ƙasar Baƙaƙen fata (Tukrur). Bayansa kuma akwai wani aiki da wani limamin Kirista mai suna Rev. Samuel Johnson ya rubuta a 1897 A.D. kuma ya ƙara tabbatar da abin da Muhammadu Bello ya faɗa a cikin aikinsa game da Yarabawa.

     Su dai Yarabawa sun kasance masu yin hijira daga ainihin ƙasarsu ta haihuwa zuwa wata domin nema. Kuma sun ɗauki Ile-Ife a matsayin wata cibiya ta su. duk da cewa ba a can kaɗai suke ba. ko dai yaya lamarin yake tarihi ya bayyana cewa, babu wani musu, asalin Yarabawa daga zuri’ar KWA ta yankin Afrika suka fito. Kuma suna da dangantaka da harsuna kamar Igala, da Igbo, da Edo, da Idoma, da kuma Nupe da Makamantansu. Usman (2003:107-111),

     Akwai Yarabawan yankin Arewa maso Yamma, wato Yarabawan Oyo da Oshun, da Ibadan, da yankin Arewacin Egba. Akwai kuma na Kudu maso Gabas waɗanda suka haɗa da Ondo, da Owo, da Ikale, da Ijebu da kuma na yankin Ekiti. Kuma suna da bambancin karin harsuna a tsakaninsu. Yanzu haka wurin da suka zaune shi ne Kudu maso Yamma wanda ya haɗa da jihar Legas, da Ogun, da Ondo, da Oshun, da kuma Oyo. (Usman, 2003:107-111)

    5.0 Taƙaitaccen Tarihin Garin Gusau

     Garin Gusau, gari ne da a can baya yake a cikin tsohuwar daular Katsina, yanzu kuma ita ce babban birnin jihar Zamfara. Mafi yawan mutanen da ke zaune a wannan gari Katsinawa da Zamfarawa ne, su kuma waɗannan ƙabilu dukkansu Hausawa ne. Gusau, (2014:18) Kasancewar wannan gari (Gusau) yana a ƙasar Hausa kuma akwai albarkatun noma, ya sa ya albarkatu da yawan baƙi kamar Yarabawa da Inyamurai (Igbo) da wasu ƙabilu masu saye da sayarwa na daga kayan da ake nomawa a wannan gari da ma jihar baki ɗaya.

     Kamar yadda tarihi ya gabata an kafa garin ne a shekarar 1811, bayan tasowa daga ‘yandoto a shekarar 1806. Gusau na daga cikin manyan garuruwan tsohuwar jihar Sakkwato kafin daga bisani ya zama babban birnin jihar Zamfara a shekarar 1996. Kundin bayanin tarihi na ƙasa na 1920 ya nuna, garin yana kan titin Sakkwato zuwa Zariya ne, kilomita 179 tsakaninsa da Zariya, kolimita 210 tsakaninsa da Sakkwato. Daga gabas ya yi iyaka da ƙasar Katsina da ta Kwatarkwashi daga Arewa kuma ya yi iyaka da ƙasar Ƙaura, daga Yamma kuwa ya yi iyaka da ƙasar Bunguɗu. Ta ɓangaren Kudu kuma ya yi iyaka da ƙasar Ɗansadau da Tsafe, (Gusau, 2012:7)

     Kasancewar almajirin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo wato malam Sambo Ɗan Ashafa ya kafa Gusau, wanda yake da shi da jama’arsa ba ruwansu da bautar iskoki, ko tsafi irin wanda Hausawa ke yi kafin zuwan addinin Musulunci, wato garin Gusau ba ya da tarihin jahiliyya, haka ta sa duk al’adun Gusawa, al’adu ne irin na Musulunci, kuma shigowar wasu mutane wato baƙi a Gusau, ba ta gurɓata waɗannan kyawawan al’adu ba, domin kuwa mafi yawan baƙin da suka tahowa malamai ne na Musulunci da almajirai, Fulani da wasunsu kan taho garin don tsira da addininsu da mutuncinsu da kuma dukiyarsu.

     Taɓangaren fada kuma duk umurnin da zai fito daga can zai kasance ne daura (kusa) da abin da Musulunci ya yarda da shi na kyawawan ɗabi’u da al’adu, musamman kuma da yake kusan duk sarakunan da aka yi a garin Gusau malamai ne na addinin Musulunci masu taƙawa da tawali’u. Da wannan shimfiɗa ce, al’adun Gusawa ke gudana daidai da koyarwar addinin musulunci da kyawawan ɗabi’u irin na Fulani da na Hausawa waɗanda ba su ci karo da shari’a ba.

     Irin wancan yanayi na kwararowar baƙi da ƙungiyoyi daban-daban musamman a zamanin Sarkin Katsinan Gusau Malam Muhammadu Modibbo (1867M/1224H – 1877M/1291H) ta sa garin ya samu bunƙasa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, (Gusau, 2012:7)

    6.0 ZuwanYarabawan Gusau

     Yarabawa sun zo Gusau rukuni-rukuni. Rukunin Yarabawan da suka zo Gusau na farko sun zo ne tun zamanin zuwan Turawan mulkin mallaka wato shekarar 1903-1960. Amma daga ƙididdigar ƙidaya da aka yi a 1952 an bayyana cewa, Gusau tana da kimanin mutane 83, 884, ciki kuwa harda Hausawa da Fulani da Igbo da Yoruba da Maguzawa. Daga cikin Yarabawa sun kai kimanin 963. Sai a shekarar 1991 aka sake ƙidaya yayin da aka samu adadin mutum 132, 390, daga ciki Yarabawa suna da 1,522. Usman, (2003:111)

     Rukunin farko na Yarabawa da suka zo a Gusau ana sa ran sun zo tun a shekarar 1910. Usman, (2003:113), ya bayyana cewa, a wata tattaunawa da ya yi da wani mai suna Mal. Raji mutumin Uyo ya bayyana masa cewa, “Yarabawan farko da suka zo sun zo ne sakamakon Turawan mulkin mallaka kuma sun zo ne domin yin aikin dafa abinci da raino da tuƙin mota. Kuma su Turawan suke yi wa wannan hidima.

     Rukuni na biyu da suka zo kuwa sun zo ne sakamakon gina hanyar jirgin ƙasa a shekarar 1917, bayan gama layin dogo a shekarar 1927 aka buɗe shi. Haka kuma an buɗe Coci a shekarar 1926 domin ma’aikata da suke kula da layin dogo.

     Sai kuma rukuni na uku da suka zo a shekarar 1965 har zuwa 1970 su kuma waɗannan sun zo ne a sakamakon aikin kamfani na masaƙu da kuma na casa da mai. Ko bayan waɗannan Yarabawan akwai waɗanda suka zo sakamakon tuƙin mota da dafa abinci da raino da masu aikin layin dogo. Akwai kuma ‘yan kasuwa, duk sun zo sun zauna a Gusau kuma sun zama ‘yan ƙasa. Yarabawa sun fi yawa a Unguwar Sabon-gari, kuma suna da sarki a unguwar. Duk da cewa ba unguwar Sabon-gari kaɗai suke ba, misali idan aka je unguwar Damɓa a Gusau za a tarar akwai Yarabawa masu yawa a can kuma suna da nasu Sarki. Yarabawan da suke a unguwar Sabon-gari sun fi Hausawa yawa, kuma sun kai kimanin kashi 95% a unguwar. Usman, (2003:111)

     Mafi yawan kayan da Yarabawa suka zo da su daga ƙasarsu ba su wuce, goro da ayaba ba. Idan suka zo nan ƙasar Hausa kuwa sai su sayi gishiri da barkono da fatar dabbobi da gyaɗa da rogo da albasa da makamantansu. Usman, (2003:111)

     Akwai rukuni na huɗu da ake sa ran sun zo a shekarar 1969 zuwa 1970 sakamakon sana’a da neman mafaka, duk da cewa ba kowane Bayarbe ne ya zo don neman mafaka ba, (Usman, 2003: 111-120).

    7.0 Haɗuwar Yarabawa da Hausawa a Gusau

     Sakamakon zuwan Yarabawa a Gusau, an samu cuɗanya wadda ta taimakawa Yarabawan koyon harshen Hausa. Kasancewar sun samu kansu a Gusau kuma sun hayayyafa a Gusau, dole su gudanar da mu’amala tsakaninsu da Hausawa. Idan kuma suka hayayyafa to akwai buƙatar su ilmantar da yaransu, kuma ilmantar da yaran yana buƙatar a samu harshen da ake amfani da shi a wannan yankin. Harshe yana taimakawa wajen gudanar da dukkan hulɗa ta zamantakewa, musamman cinikayya da yake Yarabawa sun tashi da son sana’a, su ma Hausawa sun kasance abokan sana’arsu, (Usman, 2003:187).

     Ta ɓangaren koyon harshen kuwa, lokacin da tsarin 6-3-3-4 na karatu ya samu a Nijeriya, sai aka fito da tsarin koyar da harsunan Nijeriya da suka haɗa da Hausa da Yoruba da Igbo, wannan ya ba yaran Yarabawa damar zaɓen harshen Hausa domin su samu sauƙin cuɗanya da Hausawan da suke mu’amala da su, (Usman, 2003:187).

     Don haka wannan tsari ya yi daidai da ra’in Bourhis da ya ce ana samun cuɗanya ta fuskar karɓar horo, wato mutum ya samu horo kafin ya tsunduma cikin sha’anin rayuwar wasu.

     Mafi yawan Yarabawan da suka samu kansu a wasu biranen Hausa, harshe ne babban abu mai muhimmanci a wajensu. Kuma shi wannan harshen yana samuwa ne ta hanyar koyo. Ba baƙon abu ba ne Hausawa su nashe wani harshe, saboda kusan dukkan ƙabilar da take kusa da Hausawa tana fuskantar barazanar salwantar wasu kalmomi sakamakon cuɗanya da Hausawa. Don haka, ba wani abin mamaki ba ne harshen Hausa ya mamaye Yarabawa musamman waɗanda suke zaune a garin Gusau.Yarabawan da ke Sabon-gari da Bakin Kasuwa da Sabon-Fegi da Damɓa duk sun yada wasu kalmomi nasu. Usman, (2003:114)

     Haka kuma taɓangaren al’adu kuwa, Yarabawan da suka samu kansu a Gusau sun samu sauyin al’adu musamman waɗanda suka jima a Gusau, wato waɗanda aka zo da su suna ƙanana (second generation) da waɗanda aka haifa a Gusau ɗin (letter generation) sun ɗauki mafi yawan al’adun Hausawa na Gusau, saboda cuɗanya ta auratayya da wasu bukukuwa na gargajiya da na addini kamar bikin salla da maulidi da saukar saukar Alƙur’ani Mai girma. Al’adun sun fi yin tasiri ta fannin auratayya, saboda Hausawan sun kasance suna auren Yarabawa, musamman waɗanda suke tare da su a gari ɗaya. Irin wannan alaƙa ta haddasa yin al’adun Hausawa na aure, kuma Yarabawan sun ɗauki waɗannan al’adu. Sha’anin auratayya ya samu tun a shakarar 1970 an samu cuɗanya ta auratayya tsakanin ‘yar Yarabawa da ɗan Hausawa[6]. Wannan auren ya kawo haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummun guda biyu.

     Haka kuma wata cuɗanya tsakanin Hausawa da Yarabawa a Gusau ita ce ta zuwa kallon wasu al’adu kamar dambe da sharo, wanda dukkan al’ummun biyu sukan haɗu a waje ɗaya su kalli wasan. Ko bayan kallon dambe da sharo akwai haɗuwa a masallaci ga Yarabawan da suka Musulunta a yi salla tare a kuma saurari wa’azi ko tafsir a lokacin Azumi.

     Wannan haɗuwa da Yarabawa suke yi da Hausawa ya sa an samu wasu Yarabawa sun shiga sana’ar dambe inda akwai wani ɗan dambe a Gusau mai suna Bade ainihin sunansa Badaru kuma a Sabon-gari nan Gusau yake. Akwai kuma wani mai suna Soja wanda ainihin sunansa Abdulganiyu[7]. Auratayya kuma an samu wasu Hausawa sun auri matan Yarabawa kamar yadda Usman, (2003:111) ya bayyana a kundinsa na digiri na uku. Haka kuma an samu wasu matan Hausawa da suka auri Yarabawa.

     Tsare-tsaren auren Hausawa yana da bambanci da na Yarabawa. Kama daga lehe, da bikin aure kamar sa lalle, walima, ƙauyawa day, ɗaukar amarya da makamantansu. Da ma tambayi Boda Radiyo a Sabon-gari ya bayyana mani cewa saboda yaran sun tashi a nan sun fi son tsarin da ake yi a Gusau, ba su san nasu al’adun na aure ba. Sai dai kuma ya bayyana cewa dangane da ajo da su suka saba a al’adunsu sukan shigo da wannan duk lokacin da aka tashi yin hidimar aure.[8]

     Kamar yadda aka sani Hausawa suna da hali na karamci kuma ga son tarbon baƙi, haka al’ummar Gusau suke wanda shi ya ba da damar ƙabilar Yarabawa suka yawaita a garin.

    8.0 Kammalawa

     Wannan maƙala ta duba lamarin cuɗanya tsakanin Hausawa da Yarabawa. Sakamakon wannan cuɗanya ya haddasa tasirin wasu al’adu da kuma harshen Hausa a kan na Yarabawa. Maƙalar ta gano cewa har alaƙa ta auratayya ta shiga tsakanin al’ummun biyu. Wasu Yarabawan in aka dube su in ba an faɗa maka cewa su Yarabawa ba ne, ba a ma iya ganewa. Wasu al’adun Yarabawa sun samu sauyi ko garwaya da na Hausawa kamar al’adun aure da haihuwa da mutuwa, biki, sana’o’i, gaisuwa, wasanni da makamantansu. Wannan maƙala ta taɓo wasu muhimman bayanai da suka haɗa da cuɗanya tsakanin Hausawa da Yarabawa, inda aka bayyana an yi cuɗanyar har an samu tasirin harshe da al’adu. Haka kuma ta zo da taƙaitaccen tarihin garin Gusau, wadda aka ce almajirin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ne ya kafa garin, kuma Hausawa su suka fi rinjayi a cikin garin. An kuma bayyana zuwan Yarabawa a garin Gusau tun daga na farko har zuwa na baya-bayan nan.

    Manazarta

    Abraham, R. C. (1962). Dictionary of the Hausa Language. London: Hodder Sydney.

    Adamu, (2010) “The Major Landmarks in the History of Hausaland”. The Eleventh  Inaugural Lecture. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.

    Adamu, M. (1991) Hausa Factor In West African History, (Tasirin Hausawa a  Afrika ta  Yamma. Zariya: Ahmadu Bello University Press.

    Bargery, G. P. (1934). A Hausa-English Dictionary. London: Oɗford University Press.

    Burgress, and Locke, (1953). The Family, 2nd (ed): New York. American Book. Co.

    Bourhis, R. Y. (1997) Language in Ethic Interaction: A Social Psychological Approach. England: Pergamon.

    Bunza, A. M. (1991), “Ba Baƙo Ruwa ka sha Labari; (Ƙimar Baƙo da Baƙunci a Al’adar Bahaushe)”

    CNHN (2006), Cibiyar Nazarin Al’adun Nijeriya Jami’ar Bayero Kano.

    Funtua, da Gusau, (2010), Al’adu da Ɗabi’un Hausawa da Fulani El-Abbas Printers and Concepts Kaduna

    Gusau, R. A. (2014) Garin Gusau a Taƙaice Gusau: Al-Huda Ventures.

    Gusau, S. M da Gusau B. M. (2012) Gusau Ta Malam Sambo. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Ibrahim, M. S. (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci a Kan  Rayuwar  Hausawa ta Gargajiya”. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Jam’iar  Bayero.

    Madabo, M.H (1979) Ciniki da Sana’o’i a Ƙasar Hausa Annuri Printers and Publication D/Rimi.

    Mu’azu, A. (2013) Baƙin Al’adu a Ƙagaggun Littattafan Soyayya na Hausa. Zariya:  Ahmadu Bello University Press

    Rambo, R. A. (2013), “Gwagwarmayar Kamancen Neman auren Hausawa Da Na Dakarkari”. Takardar da aka gabatar a taron ƙarawa juna Sani a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

    Rauf, M. A. (1977). Islamic View On Women and Family: New York: Cambrige Press.

    Sallau, B.A. (2010) Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna:  Najiu  Professional Printers.

    Smith, M.G. (1959) “The Hausa System of Social Status” in Africa Vol. XXVII.  No. 1.

    Usman A. F. (2003) “Inter-Group Relations in Gusau: A Case Study of Yoruba and  Hausa C. 1920-1996. PhD Theses, Department of History Usmanu  Ɗanfodiyo University Sokoto.

    RATAYEN HIRARRAKI

    S/No

    Suna

    Shekaru

    Adireshi

    Matsayi

    Rana

    1

    Mal. Raji

    57

    Sabon-gari Gusau

    Mamba a ƙungiyar Yarabawan Gusau

    Litinin 10/10/2021

    Da 10:00ns

    2

    Haruna Umar Gusau

    40

    Sabon-gari Gusau

    Ma’aikacin Gwamnati sashen lafiya a Gusau

    Lahadi 8/5/2022

    Da 5:31ny

    3

    Boda Radiyo

    55

    Sabon-gari Gusau

    Mai Gyaran Radiyo

    Lahadi 8/5/2022

    Da 5:00ny



    [1] A duba Bourhis, (1997) The Interactive Acculturation Model.

    [2] Ahmad Magaji ya bayyana Aure a matsayin wata yarjejeniya ce a tsakanin namiji da mace da kuma bin wasu ƙa’idoji da dokoki da wannan al’umma ta tanada domin samun zuri’a ta gari.

     

     

    [3] Suratul Nisa’I. aya ta 4. A cikin Alƙur’ani mai girma

    [4] Hadisi na 22, a cikin Zadul Muslimat. Haka kuma akwai shi a Buguyatul Muslimin, da kuma Bulugul Maram Min Adillatul ahkam.

    [5] Bayani ya gabata cewa Larabawa sun shigo ƙasar Hausa tun zamani mai tsawo. An bayyana cewa Abu Yazid wanda ake kira da Bayajida Balarabe ne, kuma an ce ya zo a ƙasar Hausa tun kafin bayyanar Annabi Isah AS. Ko bayan shi ma wasu Larabawa da aka ce sun zo a ƙasar Hausa sakamakon cinikayya. A a bayanin Gusau (1999) da kuma Gusau (2008) duk suna a matsayin bayanai na hujja kan haɗuwar Hausawa da Larabawa.

    [6] Hira da Mal. Raji Mutumin Uyo mazauni Unguwar Sabon Garin Gusau a ranar 10 ga Octoba, 2021 da misalin ƙarfe 5:00 na Yamma a cikin shagonsa.

    [7] Hira da Haruna Umar Gusau ɗan unguwar Sabon-gari nan Gusau a ƙofar gidansa. A ranar Lahadi 8/5/2022 da misalin ƙarfe 5:31 na Yamma.

    [8] Hira da Boda Rediyo a shagonsa da ke unguwar Sabon-gari Gusau a ranar Lahadi 8/5/2022 da misalin ƙarfe 5:00 na Yamma.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.