A ranar 29/01/2024 an buɗe zaure a kafar WhatsApp domin tattauna muhimman batutuwa da tura muhimman saƙonni game da wannan taron ƙara wa juna sani na ƙasa-da-ƙasa. Malamai da manazarta da dama sun bayar da gudummawar ilimi sosai a cikin zauren. Daga ƙarshe an ɗauko wasu daga cikin bayanan, an kundace su wuri ɗaya domin ajiye tarihi da yaɗa ilimi.
[6:48am,
31/01/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Waƙoƙin Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Abubakar Garba. Ya yi sarauta daga
shekarar 1952 zuwa shekarar 1960 lokacin da aka cire shi.
[6:50am,
31/01/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Akwai
Waƙoƙin Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo Abubakar III wanda daga baya ya zama Sarkin Musulmi
a cikin watan Afrilun 1996.
[6:54am,
31/01/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Waƙoƙin Marigayi Galadiman Kano, Alhaji Ahmad Tijjani
Hashim tun yana Turakin Kano da Waƙar Ɗan Alin Birnin Magaji, Jihar Zamfara Alhaji Muhammad Mode Usman wanda
ya yi Sarauta daga shekarar 1945 zuwa rasuwarsa a shekarar 2005 da Waƙar Tudun Falale/Sarkin Tudun Falale, Muhammadu Ɗan Sarkin Mafaran Gummi Muhammadu Maidabo.
[6:54am,
31/01/2024] Malam Dahiru Abdulkadir:
Na ga ƙoƙarin gabatar da aiki mai muhimmanci da aka yi niyya. Allah
sa mu dace.
[7:05am,
31/01/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Waƙar Sardaunan Sakkwato Sir
Ahmadu Bello GCON, KBE, Firimiyan Jihar Arewa ɗan Sarkin Raɓah Ibrahimu ɗan
Sarkin Musulmi Abubakar II/Abubakar Mai Raɓah ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ☝️
[7:06am,
31/01/2024] Dr Rabiu Ba shir KASU:
Allah ya gafarta wa Muhammadu Maccido, ya gafarta wa Saidu Faru.
Sarkin
Kudu ya waƙu gaya, da Allah ya sa Malamin kiɗa na da rai ya zama Sarkin Muslim Lallai kuwa ba mu
san me zai gaya wa Sarki ba a waƙe.
[7:32am,
31/01/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Waƙoƙin Sakataren Di'on Ƙaura Namoda, Hassan Anka da S/Kano Alhaji Ado Bayero
da Turakin Kano, Alhaji Ahmad Tijjani Hashim da Alhaji Bello Koko Di'on
Sakkwato da Ɗanmadamin
Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo
Bunguɗu da Ɗanmalikin Gidan Goga, Alhaji Ummaru da Sarkin Yaƙin Banga, Sale Abubakar da Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji
Muhammadu Macciɗo Abubakar III da Sarkin Sudan Na Wurno, Alhaji Shehu
Malami da Sarkin Bauran Dange, Alhaji Ummaru Faruku da Sarkin Yaƙin Binji, Alhaji Usman Abdulwahab da Kekun Gada, Alhaji
Muhammadu Ɗantabawa
da Sarkin Kiyawan Ƙaura
Namoda, Alhaji Ahmad Muhammad Asha.
[10:35am,
31/01/2024] Alh. A. Nakawada: Sa'idu
Faru is known for creating "traditional Hausa royal music. "
Therefore, "traditional Hausa royal music" best describes the type of
songs made by Sa'idu Faru instead of "Royal Song"
Small
karambani👏 👆
[10:36am,
31/01/2024] Alh. A. Nakawada: Additionally,
in general terms, a "song" typically refers to a musical composition
with lyrics that are sung, while "music" is a broader term that
encompasses any organized sound or combination of sounds. Music can include
instrumental compositions, whereas a song specifically involves vocals with
lyrics.
[10:42am,
31/01/2024] www.amsoshi.com: Thank
you this submission.
The
LOC are following and monitoring all the chats in this group.
Your
contributions are always welcome.
[10:49am,
31/01/2024] www.amsoshi.com: The
popular adopted term for the category is Hausa singers and drummers.
[10:49am,
31/01/2024] www.amsoshi.com: Singer:
Singers typically focus on melody, lyrics, and vocal delivery. They may or may
not accompany themselves with instruments.
Musician:
Musicians focus on playing instruments, understanding musical theory, and
creating harmonies, melodies, or rhythms. They may or may not sing.
[10:50am,
31/01/2024] www.amsoshi.com: Singer:
Vocal training is crucial for singers to enhance their vocal range, control, and
overall performance. They often learn techniques for breath control, pitch, and
expression.
Musician:
Musicians receive training in playing their chosen instruments, learning music
theory, and understanding the principles of harmony, rhythm, and composition.
[10:50am,
31/01/2024] www.amsoshi.com: Singer:
In a band, the singer often takes on the role of the lead vocalist, fronting
the performance and delivering the lyrics. However, some singers may also play
instruments.
Musician:
Musicians in a band include those playing instruments such as guitarists, bassists,
drummers, keyboardists, etc. They contribute to the overall musical arrangement.
[10:52am,
31/01/2024] www.amsoshi.com: In the
native English sense, while all singers are musicians, not all musicians are
singers. Singers primarily use their voices as instruments, whereas musicians
encompass a broader category involving individuals who play various musical
instruments.
[10:55am,
31/01/2024] www.amsoshi.com: In light
of the distinctions outlined above, particularly in the context of native
English terminology, it is more appropriate to refer to Sa'idu Faru as a singer
rather than a musician. This classification is fitting given that his talents
predominantly lie in his vocal abilities and creative expression. His
proficiency and artistry in singing, rather than instrumental performance, are
what predominantly define his contributions to the musical domain.
[10:56am,
31/01/2024] www.amsoshi.com: This is
still debatable anyways.
[10:59am,
31/01/2024] Malam Umar Iro: Sir, kindly
help us with examples of those musicians that use their voices as instruments
[11:01am,
31/01/2024] www.amsoshi.com: An
instrument here does not refer to the conventional meaning of musical
instruments. In Hausa for instance, you may say *muryarsa ce makaminsa. Muryarsa
ce garkuwarsa. Muryarsa ce jarinsa. Maganarsa ce jarinsa. "
[11:03am,
31/01/2024] www.amsoshi.com: However,
I know of teams known as "vocals" across the world that uses their
articulatory organs as musical instruments.
A
YouTube search will be great (Vocals).
[11:08am,
31/01/2024] Malam Umar Iro: Thanks so
much sir I appreciate your explanation
[3:59pm,
31/01/2024] Prof. A.B. Yahya: Hon. sir.
Ina son gabatar da muƙala a kan
Bakandamiyar nan
[5:44pm,
31/01/2024] Prof. A.B. Yahya: Wadda
ta ƙunshi iskewar da Faru ya yi ma
suda da burtu da Labarawan bakin bahar maliya.
[5:35pm, 02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Ni
dai bari in zaka inganai,
Y/Amshi: Usumanu
na Shamaki wan maza,
Jagora: Ni
dai bari in zaka in ganai,
Y/Amshi:
Usumanu na Shamaki wan maza,
Biyash Shehu dut tahi bin rangama,
Waɗan ga Sarakunan
zamani,
Yayin Gimbiya masu guntun naɗi,
Icce da kogo ina za a kyautak kirki?
Gindin Waƙa: Mai raba
riguna na Muhamman Bello,
Jikan
Hassan ɗan Moyi.
Ɗiyan Waƙa ne ☝️☝️☝️ daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Talata Mafara, Alhaji Shehu
Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan
Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.
Ya
yi Sarauta a Talata Mafara daga shekarar 1958 zuwa rasuwarsa a shekarar 1969. Allah
ya kyauta makwanci, amin.
[5:37pm,
02/02/2024] www.amsoshi.com: Don
Allah, ko Makaɗa Sa'idu Faru ya yi waƙoƙin siyasa? Shin ana iya ba mu misalansu idan akwai?
[5:44pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Makaɗa Sa'idu Faru ya yi Waƙoƙin Siyasa, musamman a Jamhuriya ta biyu. Farko ya goyi bayan Jam'iyyar
NPN daga baya ya koma goyon bayan Jam'iyyar UPN.
Ya
yi wa Jam'iyyar NPN Waƙoƙi, ɗaya daga ciki
ita ce mai amshi " Jam'iyyad da ba munahucci ta ɗiyan ƙwarai, jama'ag ga mu zaɓi NPN tahi
gaskiya".
Bayan
ya koma UPN ya yi wa Jam'iyyar Waƙoƙi, ciki kuwa har da mai amshi "Ku zaɓi UPN Arewa, taimakon jama'a take yi, maguɗi ab bata ƙamna".
Ba
ni da waɗan nan Waƙoƙin, kuma a halin yanzu ban san a inda za a same su ba.
[5:51pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Zama
Giwa ta fito kiyo tai miƙa ta zo ta
sha ruwa,
Y/Amshi: Kuji
Ɗan Zomo na hwaɗin hwaɗama su Tsari, Tsara
mu tai gida
Daji ya ɓaci
kaa a take mutum baƙi aa'
akwai ciki,
Jagora/Y/Amshi:
Daji ya ɓaci kaa a take mutum baƙi aa' akwai ciki,
Jagora: Gurnanin
Damisa ka sa mahwarauta sun ɗora ɗemuwa,
Y/Amshi: Ga
wani ya yi Kokuwa da wan ƙarfi nai,
Ya hwaɗi ya kare,
Tun ba a tantance ba shi na nishi ya lanƙwanshe tsara,
Jagora/Y/Amshi:
Tun dai ba a tantance ba shi na nishi ya lanƙwanshe tsara,
Jagora: Ko
jiya na iske Gamdayaƙi da Tuji
sun iske Jinjimi,
To sun ko murɗa
gardama,
Sun iske su Bubuƙuwa ruwa,
Y/Amshi: Dan
naan niko ina gaton gaɓa,
Sai nik kwaɗa
gaisuwa,
Su ko sun daƙile ni dud,
Niko niƙ ƙara gaisuwa,
Dan nan Kulmen da ac cikin gurbi ya amsa gaisuwa,
Jagora: Dan
nan sai Jinjimi da yad darzaza ya suntule shi dud,
Y/Amshi: Shi
ko Tuji da ad da girman baki yak kwashe Jinjimi,
Dan nan Bubuƙuwa da tar rura tag gangame su dut,
Jagora/Y/Amshi:
Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani,
Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani,
Y/Amshi: Gwabron
Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo
Ginshimi,
Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi,
Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi,
Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi,
Daga
cikin Waƙar
Marigayi Mai Girma Dagacin Banga, Masarautar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar (wanda ya yi Sarauta daga shekarar
1934 zuwa wafatinsa a shekarar 1963), Ta Makaɗa Sa'idu Faru mai taken "Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi. Rubutawar
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin
Birnin Magaji, Jihar Zamfara.
Talata,
21/11/2023.
[5:56pm,
02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi:
Assalamu alaikum
Don
Allah zan iya samun audio na Bakandamiyar Sa'idu Faru?
[5:56pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.
Wace
Waƙar ce Bakandamiyarsa?
[6:03pm,
02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi:
Duk wadda ku masana wakokin kuka dauka a matsayin Bakandamiya. Ina so ne in
kwatanta da na wasu mawaƙan tare da
dora ta a wani mizanin.
[6:04pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Allah ya gafarta Malam, wa ne mu, yaji a gefen ƙosai!
[6:06pm,
02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: Watakila:
-wadda
ta fi fice
-wadda
ta fi fito da shi
-
wadda ake ganin ya fi so/sha'awa
..........
[6:08pm,
02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi: Duk
da yake ba dalibin Waƙa nake ba,
ina ganin kamar waƙar da ya
yi wa Maccido za ta iya zama......
[6:10pm,
02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Don
Allah ku gyara sunan sarautar Hon. Alhaji Ibrahim. Ina jin tutsun kwamfuta ne
don ba ta son ta iya Hausa!
[6:16pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Allah ya gafarta Malam akwai bayanai masu karo da juna a tattaunawar da aka yi
dashi kafin wafatinsa, a kafafen yaɗa
labarai daban daban akan Bakandamiyarsa.
Halifansa
Alhaji Ibrahim a wata tattaunawa da na yi dashi ya kawo Waƙoƙi guda biyu yana cewa Mahaifin nasa ya fi son ɗaya daga cikin su, a gefe ɗaya kuma akasarin jama'a sun fi son ɗayar.
Sa'idu
Faru ya fi son ta Marigayi Mai girma Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Ƙaura Namoda, Sarkin Kiyawa Abubakar Garba wanda ya yi
Sarauta daga shekarar 1952 zuwa shekarar 1960 da aka cire shi mai amshi
"Gwabron Giwa na Shamaki baba uban Gandu, Abu gogarman Magaji mai
kansakalin daga".
Jama'a
kuma a cewar Alhaji Ibrahim Sa'idu Faru sun fi shauƙin ta Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello Macciɗo Abubakar III
mai amshi "Kana shire Baban Yan Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo". Allahu Wa'alam!
[6:28pm,
02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Shugabannin
wannan dandali da ku fa nike! Yadda kwamfuta ta rubuta sarautar Hon. Alhaji
Ibrahim ba daidai ba. Ta yi tutsu!! "Ɗanmadami" ne!!! Ta cire "ma"
[6:34pm,
02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi:
To madalla! Bayani ya fara fitowa. Don Allah a turo mini duk biyun. Na gode
[6:36pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: In
Shaa Allah Allah ya gafarta Malam.
[6:39pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
@ Farfesa Ibrahim Sarkin Sudan. Ta farko ce Waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Abubakar Garba ☝️
[6:39pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Kana shire Baban Yan Ruwa ☝️
[6:43pm,
02/02/2024] Prof. A. M. Bunza:
Danyaro Ƙaramar ɗamba Koko- Besse Local Government.
Ga mai kiɗi
da baki
Ba ki da kalangu ba
In da akwai kalangu
Da an tattausa min
Kunga! Kun! Regidi
Regekai!
Kunga kun!
Haka
kuma akwai wani a ƙasar Haɗa LG mai kiɗin
Wanakiri Don Kwanya
[7:02pm,
02/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Bakandamiyar waƙa ko
tsakanin mawaƙa akan
samu saɓani. Wani mawaƙi kan ɗauki ɗaya daga cikin waƙoƙinsa a matsayin bakandamiyarsa saboda wasu dalilai kamar ta yadda yake
ji idan yana rera ta, ko saboda ya fi samun kyauta idan yana rera ta, ko kuma
ya yanke hukuncin cewa ita jama'a suka fi so.
Ta
bangaren jama'a kuwa yana yiwuwa saboda dukan wadancan dalilai da na ambata ko
saboda wasu dalilai na dabam. Idan aka tambaye ni wace waƙa cikin waƙoƙin Sa'idu Faru nake ganin ita ce Bakandamiya sai in ce "Kana Shire
Baban 'yan ruwa" mai farawa da/Gardaye zo kai man iso/ saboda dalilai
kamar haka:
-Tun
ina matashi nake jin daɗinta kuma har yanzu a ganina duk ta fi daɗi da tsaruwa.
-Ranar
da aka naɗa Muhammadu Macciɗo
ita ce Rima rediyo ya saka ana ambatar shi ne Sarkin Musulmi a masallacin
Muhammadu Bello. Ina saurare sai da hawaye suka zubo mini saboda jin daɗi da tausayi.
[7:27pm,
02/02/2024] +234 812 462 9009: An
nuna ma'anar meronymy kamar shi ne sashen wani abu ko a part of something. Wato
akwai abinda ake kira holonym ko cikakken abu. To part of holonym shi ne
meronym. Mango tree shi ne holonym ɗan
mangwaro shi ne meronym na mango tree.
[7:58pm,
02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Hon duk
da ban son in yi sarauta amma da yake akwai jininta cikina, idan ina sauraren
"Kana Shire" sai in nasarta cewa da ni aka yi wa ita da na ba Sa'idu
Faru Zamfara kaf!😂😂😂
[8:35pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Sarkin Musulmin wata ran kake,
Da imani da mu'ujiza na nan ga Malam Macciɗo,
Tun ga Alu mai saje nij jiya.
Ka kai kamab Bello swasswakiya,
Da
kyauta da mulki da ban gaskiya,
[9:27pm,
02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Hon. da
dai ce min ka yi:
/Ka kai kam Nana gulbin sani/
/Bajinin Giɗaɗo hab Buhari/
/Baban
Macciɗo wan Junaidu/,
da
kuwa na ba ka FUG duka har da su Abu-Ubaidah 😂!
[10:03pm,
02/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Allah ya gafarta Malam, ina
mamakin yadda 'yan galadimomi kan rikirkici idan makada sun sa su gaba!
[10:05pm,
02/02/2024] Mal. H.U. Maikwari Ban
dai sani ba ko abin a kayan kiɗan yake.
Ba
'yan Galadimomi ba, hatta' yan dambe da kokawa da ma 'yan rawa da duk wani da
aka buga wa kayan kiɗa.
[10:06pm,
02/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Wata kyautar sai daga baya
mutun ya koma cizon yatsa!
[10:47pm,
02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Tasirin
waƙa ne. Galibi ba cikin
hayyacinsu suke yin abubuwan da suke yi ba. Waƙa kamar giya take ga hankalin ɗan Adam saboda ta fi yin tasiri ga zuciya bisa ga
maganar yau da kullum ko sauran ɓangarorin
adabi. Kwatanta da yadda mata ke kasancewa idan suna gaban mawaƙa masu yi musu kiɗa
da waƙa
[10:39pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Sarkin
Tudun Falale gogarman Magaji Ummaru,
Y/Amshi: Ba
yau ba ko mazan jiya sun san kana da martaba,
Ya riƙa da gaskiya Muhammadun Muhammadu,
Dangalin gidan mai saje
shirin ka ya yi kyau
Jagora: Mai
fada Ɗan Iya
Y/Amshi: Ga
Sarkin Kiɗinku ya zaka,
Na zo a bani doki
Wani sansame abun suka,
Ya riƙa da gaskiya
Muhammadun Muhammadu,
Dangalin
gidan mai saje shirin ka ya yi kyau,
Wasu
ɗiyan Waƙa ne daga cikin Waƙar Dagacin wani gari da ake kira Falale a gundumar
Gummi ta Jihar Sakkwato (a wancan lokaci) yanzu kuma Falale hedikwatar gundumar
Falale ce a Masarauta mai daraja ta ɗaya
ta Gummi dake Jihar Zamfara.
Laƙabin Sarautar yana nan bai canja/canza daga
Tudun Falale ba. Sunan wanda aka yi wa wannan Waƙar shi ne Muhammadu ɗan Sarkin Gummi (laƙabin Sarautar Gummi shi ne Sarkin Mafaran Gummi da ya samo asali daga
wanda ya ƙirƙiri gidan Sarautar na yau tun a cikin ƙarni na 18, Malam Muhammadu Waru ɗan Sarkin Bukkuyum/Sarkin Dankon Bukkuyum Ali
Bazamfare ko Ali Jan Masari da ya fito daga gidan Sarautar Mafara/Talata
Mafara).
[10:47pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: Allahu
Akbar! Alƙali Malam
Haliru Wurno ya zauna Ƙauyenmu a
cikin 1970s/80s har ma ya auri Cousin tawa, duk da yake ba su haihu ba
suka rabu. Shekaranjiya ma ɗiyar Cousin ɗin tawa da ta aure shi ta zo ganin mu daga inda take
aure a Kano.
[10:54pm,
02/02/2024] +234 812 462 9009: Ni ko
mun yi karantarwa da Alkali Haliru Wurno a GSS Wurno daga 1989 zuwa 1990
lokacin da na bar Wurno. A lokacin ya bar alkalanci. Sha'iri sosai. Da waƙe yake karantar da yara addinin Musulunci. Kuma yana
yi wa waɗanda suka taba shi zambo a waƙoƙin sa. Allah Ya gafarta masa Ya sa aljanna firdausi ce makomar sa.
[10:56pm,
02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi:
Ni kuma mun fara haduwa da Birnin Magaji a rana 5/12/2022 a wani taro a Kaduna.
Yadda na ji yana bayani 'yan dambe da makadan dambe to ko Dan'anace iyakar abin
ke nan.
Zan
so a ce ya karasa rayuwarsa a aji. Za a amfana sosai. Allah ya ƙara lafiya da basira.
[11:02pm,
02/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Dogon sarki yana da ban shawa,
Ran da an ka zo taro,
Ya yi kyau da riguna,
Duk wanda ag gajere,
A aje shi gun rabon dawo,
Shi kai ma wanga dunƙule,
Shi kai ma wanga dunƙule,
In wurin da mata ciki,
Har
tuman gada shi kai.
[11:02pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Alhaji
Ɗan Ali ci fansa,
Y/Amshi: Abun
biya kake ɗan Shehu,
Alhaji Ɗan Ali ci fansa
Jagora: Ɗaukan ni ka goya ɗan
Korau,
Y/Amshi: Kada
kabab baƙauye ya
wahalsan,
Abun biya kake ɗan
Shehu,
Alhaji
Ɗan Ali ci fansa
Wasu
ɗiyan Waƙa ne daga cikin Waƙar Dagacin Birnin Magaji a Jihar Sakkwato ta wancan
lokaci (Sokoto, Kebbi, Zamfara) yanzu garin ya zamo hedikwatar Masarautar
Birnin Magaji mai daraja ta biyu a Jihar Zamfara, wato/watau Marigayi Ɗan Alin Birnin Magaji, Alhaji Muhammad Mode Usman
wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1945 zuwa rasuwarsa a shekarar 2005. Allah ya
kyauta makwanci, amin.
[11:04pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haƙiƙa Allah ya gafarta Malam duk da yake mun fara haɗuwa ne a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto a shekarar 2020, lokacin Taro akan
Tsohuwar Daular Zamfara da Jami'ar ta gabatar. Duk da yake Allah ya gafarta
Malam bazai tuna mun haɗu a lokacin ba.
[11:08pm,
02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi:
Jama'a a duba wadannan ko za a sami abin rubutawa a kansu:
-
Zamfarci a Wakokin Sa'idu Faru
-Fitattun
Salailai a Wakokin Sa'idu Faru
Fasahar
kulla Zaren Tunani a Wakokin Sa'idu Faru
Lafuzzan
Raha a Wakokin Sa'idu Faru
Salon
Zayyana a Wakokin Sa'idu Faru
Kambamawa
a gurbin Yabo a Wakokin Sa'idu Faru.
[11:10pm,
02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Amin Ya
Hayyu Ya Ƙayyumu. Waƙoƙin Haliru yawa ne da su kuma a fannoni dabam dabam, ga su tarshe da
hikimomi na harshe da lamarin rayuwa. Mawaƙi ne wanda ya yi kama da Shata ta fuskar saƙa waƙa nan take Ɗalibaina a wata shekara da na gayyato musu shi sun gwada shi da suka
tambaye shi yaya waƙa ke zo
masa, sai ya ce babu yadda ba ta zo masa. Suka ce masa yana iya yin waƙa nan take? Sai ya ce in sha Allahu. Matsalarsa ita ce
yana buƙatar alƙami da wurin da zai rubuta ta, wato takarda. Suka ce
to ya yi musu waƙa alhali
ranar ce kuma lokacin ne ya taɓa dafuwa da su.
Ni kuwa sai na ba shi alli, na ce ga allo nan. Haka ko aka yi. Ya yi musu waƙa mai albarka. Ɗaliban da ya yi wa waƙar na tabbata wasu suna nan da ita. Ina jin cikin
shekarun 1990 aka yi haka. Ban da tabbacin ainin shekarar
[11:11pm,
02/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A gaskiya ba taɓa taron ƙara wa juna sani mai gata irin wannan ba. Allah ya
saka da alheri, Ya sa a wanye lafiya.
[11:17pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Wa da Ƙane ne. Dogon
ne Ƙane kuma wanda ya yi wa Waƙar, gajeren ne ya zambata. Mahaifinsu ɗaya, Sarkin Mafaran Gummi Muhammadu Maidabo.
Sai
dai wanda ya zambata ɗin ne ya gadi gidan a cikin 1970s bayan an cire/yi wa
Mahaifin nasu murabus daga sarauta.
[11:18pm,
02/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu:
Ga manyan malamanmu sun hadu,
Ga manazartanmu dus sun hallara,
Suna ta begen manyan kiɗi,
Sa'idu na Faru Uban kiɗi,
Na
ji daɗin da ankai wannan hadin.
[11:27pm,
02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ina ba
shugabannin wannan Zaure shawarar su riƙa tattara irin wannan tattaunawa su tace su mayar da
ita wani kundin da za su iya sayarwa. Suna iya sa masa suna: Nazarin Waƙoƙin Hausa a Bakunan Manazarta da Masu Sha'awa Idan ko suka bar
tattaunawar ta bi iska, to kada su yi mamaki idan suka ga wani ya riga su.
[11:30pm,
02/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi:
Lallai a irin wannan tattaunawa mutane suna iya samun abin rubutawa.
[11:34pm,
02/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu:
In dai waƙa ce ta uban kiɗi,
Manyan mutanenmu suna shire,
Ga Danmadaminmu yana gaba,
Mu ga mu taronmu muna biye,
Duk kowane tasa kawa daban,
Can za mu taronmu a Zamfara,
Ga shehuna sun hadu tattare,
Muna ta waƙar Sarkin kida,
Waƙan nan da Da'umma yai nufi
[11:51pm,
02/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Jama'a
kuna lure da yadda waƙa ke
tasiri ga zukatan har da manazarta! Da tattaunawar a kan zube ko wasan
kwaikwayo take ban zaton a samu wani nan take ya gwada fasaharsa
[11:55pm,
02/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Gidan Malam Giɗaɗo Ɗan Lema mijin Kakarsa Malama Husaina/Hasana bn
Mujaddadi (Nana Asma'u) Uwar Daje muke so ya gada In Shaa Allah.
[12:12am,
03/02/2024] Prof. A. M. Bunza: To su
turakun waƙoƙin Sa'idu Faru fa? Ai su ne kan takarda.
[12:13am,
03/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Dabirtau
mai ban tsoro,
Y/Amshi: Shehu
ƙanen S/fulani Amadu,
Gwabron Giwa kana da martaba,
Usumanu
na Bunguɗu Uban Marahwan Keku na Atto mai wuyak karo,
Daga
cikin Waƙar
Marigayi Mai girma Ɗanmadamin
Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo
Bunguɗu. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[12:13am,
03/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Makada Sa'idu Faru cewa ya
yi a wata waƙar;
Karya kot tara ta yah haye,
Dawowa za ta yi ta wargaje,
Ka
ishe shi buku yana rabon ido!
[12:21am, 03/02/2024] Bilya Abubakar: Assalamu
alaikum, haƙiƙa ire-iren mu ƙananan almajirai muna biye kuma muna fa’idantuwa. Saboda
haka ina faɗa addu'ar Allah Ya ƙaro buɗi da taimako ga
abinda aka tunkara.
Bayan
haka, inda hali ina roƙon a ɗora mun waƙa "Mai babban ɗakin
ƙasar Kano Alhajiya Baba
Sa'idu" domin ina so ne in gunar da wani aiki kan waƙar. Ina fatar wannan r̃oƙo nawa zai samu karɓuwa
ga Malamaina da shuwagabannin na. Wassalam
[12:31am,
03/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Marigayiya Mai Girma Mai Babban Ɗaki, Hajiya Hasiya/Asiya Abdullahi Bayero. Matar
Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Abdullahi Bayero ɗan Sarki Abbas ɗan
Sarki Abdullahi Maje Karofi ɗan Sarki Malam
Ibrahim Dabo. Mahaifiyar Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Dr. Ado
Bayero ɗan Sarki Abdullahi Bayero. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[12:31am, 03/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Wani malaminka tun yana ɗan sakandare yake ƙuƙutawa ya halarci taro
[12:34am, 03/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Allah
Sarki! Ai kun taka muhimmiyar rawa a fagen ilmi, mu sai dai mu biyo baya!
[12:37am, 03/02/2024] Mal. H.U. Maikwari
Riƙa da gaskiya Sarkin Gobir na Bunguɗu,
Don wanga da yab baka
Yanzu ba wani gaba nai,
Jikan Nana uwad Daje na,
Kuma su aj jinin Shehu Ɗanfodiyo.
Katsinawa
sai dai su gan ka ba dai su cimma ba.
[6:28am, 03/02/2024] Mal. B.H. Tsafe:
Sarki sannunka da ƙoƙari,
Wanga aiki sai fa muzakkari,
Masana manazarta arziki
Ma su son harshen ga ya yo ciri
Ya yi gogayya da na 'yan gari
Allah
mun gode abin yabo
[7:16am, 03/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Wani dan waƙar Maituru Ubankiɗi
yakan ba ni dariya inda ya ce;
Wane ba yaro na ba,
Shekara sittin yab ba ni,
Gyara huska ka sa ana,
Ce mai danyarro.
Wanzame ukku ag garai,
Wanga guda yai da sahe,
Wanga guda yai da rana,
Wanga
guda ko yana zuwa goshin issha'i. 🤣🤣🤣🤣
[7:17am, 03/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ɗanmalikin Gabake, Ɗanmalikin Gidan Goga da Ɗanmalikin Janbaƙo duka Dagatai ne a wancan lokaci, kuma dukan su
Malamin Waƙa mai
kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ya yi masu Waƙa.
Gabake
a Gundumar Ƙaura
Namoda, Gidan Goga da Janbaƙo a Gundumar Maradun.
Laƙabin Sarautar Ɗanmaliki nada alaƙa da Cibiyar Daular Usmaniya, Sakkwato inda ake
hasashen daga nan ne ta samo asali tun bayan tabbatarwa Malam Doshiro Bn
Abdullahi Mujakka (Fulani Bororo/Bororoji ne) Sarautar Galadiman Sakkwato bayan
kafa Daula.
Galadima
ne a Daular Gobir, ya yi mubayi'a ga mujahidai. Bayan an tabbatar masa da
wannan sarauta a Cibiyar Daular Usmaniya sai ya naɗa ɗansa a matsayin
mataimakinsa da laƙabin
"Ɗanmaliki".
Ya zuwa yanzu zuriyarsa ke riƙe da wannan sarauta ta Ɗanmaliki a Masarautar Sakkwato. Marigayi Alhaji Zubairu Tela ya taɓa riƙe wannan sarauta.
A
gefe ɗaya kuma Gabake (a Masarautar Ƙaura Namoda ta yanzu) wadda ta samu ne a cikin ƙarni na 18 ta hanyar ƙirƙira daga wasu jinsin Fulani da ake kira "Alwanko" dake da
tushen su a wani wuri a cikin Jamhuriyar Nijar ta yanzu, laƙabin sarautarsu Ɗanmaliki duk da yake babu takamaiman dalili da lokacin
da suka fara amfani da wannan laƙabi.
Samuwar
Marigayi Alhaji Mu'azu a matsayin Ɗanmalikin Gabake wanda ya yi sarauta daga cikin 1940s
zuwa rasuwarsa a shekarar 1989 ya sanya wannan laƙabi na Ɗanmaliki ya yi amo sosai a mafi yawan masarautun Arewa.
Saboda
shahararsa masarautu da dama sun ɗauki
wannan laƙabin sun
ayyana sa a matsayin sarauta. Shi dai ne wanda Makaɗa da Mawaƙa suka yi wa Waƙoƙi da dama duk da yake wasu Waƙoƙin ba su yi fice ba kamar yadda ta Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun mai amshi "Jikan Musa Ɗanmaliki, gamda'aren Amadu (Baura jikan Baura, Mu'azu
Allah sa ka gama lahiya) ta yi amo ba.
Har
ila yau akwai Ɗanmalikin
Achida wanda Uban Ƙasa/Hakimi
ne a Gundumar Achida, Masarautar Sakkwato da ya fito daga tsatson Muɗagel ɗan Modibbo
Ummaru Mu'alkammu (suke sarautar Gundumar Mu'alkammu da kuma Magajin Rafin
Sakkwato).
Akwai
kuma Ɗanmalikin
Katsaura a Masarautar Ƙaura
Namoda duk da yake babu takamaiman lokacin da suka fara amfani da wannan laƙabi a matsayin Dagaci.
Gidan
Goga da Janbaƙo a halin
yanzu hedikwatocin Gunduma ne a Masarautar Maradun dake Jihar Zamfara. Ana iya
alaƙanta samuwar laƙabin Sarautarsu ta Ɗanmaliki da samuwar ta a Cibiyar Daular Usmaniya idan
aka yi la'akari da zamowar Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi a matsayin Sarki
a Maradun a cikin 1870. Koma dai me ne ne, Sa'idu Faru ya waƙe Ɗanmalikin Gabake da na Gidan Goga da na Janbaƙo.
[7:40am, 03/02/2024] Dr. H. Yelwa: Saidu
Faru na cewa;
"Mu Allah yaw wa gudummuwa da waƙa
Haw
wata ya kide wata. "
Haka
shi Danmadamin yake. Nazari da ra'ayin shi ga wakoki, wasu na ishe wasu.
[7:47am, 03/02/2024] Mal. M.M. Bello
Lalle haka. Akwai wakokin Marigayi Usmanu Dangwaggo, Danmadamin Sakkwato, Dan
Sarkin Fulanin Bungudu Usman Kure, da Kuma waƙar Marigayi Alhaji Muhammad Dan Sokoto/Hakimin Gada, Keku
Dantabawa.
[7:52am, 03/02/2024] Prof. I.S.S. Abdullahi:
A ƙara duba wadannan ko akwai abin
da za a tsinta.
1.
Kalmomin Fannu a Wakokin Sa'idu Faru
2.
Fasalin Zambo da Habaici a Wakokin Sa'idu Faru
3.
Hoton Tattalin Arzikin Hausawa a Wakokin Sa'idu Faru
4.
Tubka da Walwala a Wakokin Sa'idu Faru.
5.
Munanan Dabi'u a Mahangar Saidu Faru.
6.
Zumuntar Fasahar Saidu Faru da Wasu Makadan Kasar Hausa
7.
Koda kai a Wakokin Sa'idu Faru
8.
Waskiya a Wakokin Sa'idu Faru
9.
Hoton Rayuwar Sa'idu Faru a Cikin Wakokinsa
10.
Butulci a Mahangar Saidu Faru
11.
Alakar Sa'idu Faru da Sarakunan Kasar Hausa: Tsokaci Daga Wakokinsa
12.
Salon Yaba Kyauta a Wakokin Sa'idu Faru.
13.
Aron Hannu a Wakokin Sa'idu Faru
14.
Barkwanci a Bakin Sa'idu Faru
[7:54am, 03/02/2024] Mal. M.M. Bello
"Yan Sarkin Bungudu akwai dubu, amma manyan gidan dabam suke" 😊
A
cikin waƙar Gwabron
giwa kana da Martaba, Usmanu na Bungudu uban marahwa na Atto mai wuyar karo.
Alhaji
Attoh Bungudu, shine mahaihin Sarkin Fulanin Bungudu na yanzu, Alhaji Hassan
Attahiru.
[8:04am, 03/02/2024] Mal. M.M. Bello Wasu
daga cikin wasiyoyin Saiɗu Faru:
'Sarkin
Musulmin watan ran kake'.
Allah
Ya kaddari Muhammad Maccido da zama Sarkin Musulmi.
”Dangiwa
komai yad dade, ta tabbata yin giwa yakai inji Sarkin Maradun, Sarkin
Kaya"
Ishara
akan cewa komai tad dade, wata ran, zuri'ar Muhammad Mualleydi Dan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello zasu iya nema da yin sarautar Sarkin Musulmi.
Bayan
rasuwar Sarkin Musulmi Maccido, Sarkin Kayan Maradun na yanzu Alhaji Muhammadu
Garba Tambari yana daya daga cikin wadanda suka nemi sarautar Sarkin Musulmi.
[8:07am, 03/02/2024] Mal. M.M. Bello Ana
iya duba:
Salon
siyasa, mulki da shugabanci a masarautun Kasar Hausa daga wakokin Marigayi Saiɗu Faru.
[8:42am, 03/02/2024] Alh. A. Nakawada:
”Dangiwa komai yad dade, ta tabbata yin giwa yakai inji Sarkin Maradun, Sarkin
Kaya"
"Ishara
akan cewa komai tad dade, wata ran, zuri'ar Muhammad Mualleydi Dan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello zasu iya nema da yin sarautar Sarkin Musulmi"
👆👆
Ni
kuma abin da na fahimta da wanga baiti na Sa'idu, ba wai ishara ko hasashe ne
Sarkin Kaya ya yi a kan shi ba. Aa, hasashe ne mai kama da kirari Sarkin Ƙaya ya yi wa Sarkin Kudu Maccido
[8:59am, 03/02/2024] Mal. M.M. Yankara:
Manyan kaya
Manyan ganwo
Jakki kankambab banza garai
Wasu kaya sai bisa raƙumi
Bajini birni
Bajini dawa
Na
gaisheka da ƙoƙari.
[10:36am, 03/02/2024] Mal. M.M. Bello
Na'am. Idan na fahimceka, baitin na isar da sakon Sarkin Kaya ne zuwa ga Sarkin
Kudu Maccido na gadon Sarki Bubakar. Saboda haka, hasashen na zaman Maccido
Sarkin Musulmi ne.
[11:58am, 03/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ko dai turke/jigo; turaku/jigogi
[4:31pm, 03/02/2024] Alh. A. Nakawada:
Bere gud. Na yaba maku bisa kyakkyawan tsari da kuke tafiyar da ayyukan wannan
taro da za ayi na Makada Sa'idu Faru.
Tunda
ake irin wadannan hu66asa akan Makadan mu na gargajiya ban ga wanda ya kai
wannan tsari da azama ba. Allah Yasa ayi nasara
[7:37pm, 03/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ina ba da shawara da a ƙara wannan
cikin batutuwan da ake iya rubuta muƙala:
-Turke
da tubali a waƙoƙin Faɗa.
Na
ba da wannan shawara ne saboda ganin ba salo ba ne kurum cikin waƙoƙin fada; kuma saboda ganin ɗalibai
kan samu ruɗanin fahimta tsakanin turke/tubali da kuma salo.
A
lura: ba lalle batun da na sa ya kasance a yadda na ba da shi ba. Ana iya a yi
masa kwaskwarima don ya dace da Hausar Zauren. Haka kuma yana iya ya kasance
cikin kashin B da C.
Na
gode ƙwarai.
-
A B Yahya
[9:04pm, 03/02/2024] +2348161747863:
Assalamu alaikum, ina yi wa manyan Malumanmu da Shehunnai barka da dare. Ina
bibiyar yadda ake baje kolin ilimai a wannan zaure tun daga shigata zuwa yanzu.
Amma batun da babban Shehunmu ya kawo, ya ta6a zuciyata Kwarai da gaske., Wato
‘turke da tubali’. Da Allah zai sa Malumanmu su taimaka su 6arza mana shi, da
an samu ficewar kitse daga rogo. Abubuwa ne da suke yi mana, mu dalibai shigar
giza-gizai.
Ina
yi wa manyan Shehunanmu da Malamanmu adu’ar alheri, Allah ya ƙara lafiya da rakiya mai amfani.
Mai
rubutu:
Musa
labaran Muhammad,
Dalibi
a Jami’ar Bayero ta Kano, kuma mai Nazari a kan ayyukan Sa’idu Faru Rungumi
Dan’Umma.
[10:50pm, 03/02/2024] www.amsoshi.com:
Lallai an fara gabatar da takardu. 🙏👍😅
Wannan
taro dole ma kowa ya samu abin rubutawa. An ba mu topics an ba mu bayanai. 🥳
[11:50pm, 03/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
"... Kuma ya gama da yaron,
Da zai ja ma kinani. "
Me
kalmar ƙinani'
take nufi?
[11:51pm, 03/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Shaihunan Malamanmu na kusa In Shaa Allah zamu samu ansar wannan tambayar, ni
dai ban sani ba.
[11:58pm, 03/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
"... Baba ya bamu bandir guda dun na 'lailai'... "
"...
Hula kalabus guda goma yab ban... "
Don
Allah ko za mu samu bayanin:
a.
lailai
b.
Hula Kulabus
[12:00am, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Lailai shi ne kuke kira Alwayyo/Farin yadi.
Hula
Kalabus ita ce doguwar hullar nan ja da ake sakawa ayi rawani saman ta.
[12:13am, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Allah ya jiƙan Ɗan Umma Uban Kiɗi
mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba, Rungumi Ɗan Tumba Makaɗa
Sa'idu Faru, amin.
[12:50am, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Kila karin Hausar da Faru ya tashi da shi ne. Ni dai na san kinami. "na"
ɗin doguwar gaɓa
ce. Kinami ko ita ce fatar da ke tare da sirdin doki. Tana da lanƙwasa inda ake soka ƙarfen da ake jan (likkafar) sirdin doki. A ƙara tambayar masu hawan doki don ni ban taɓa hawan doki ba.
[1:24am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ja mai
tunani ya ce.
Abin
da hakan ke nufi wani maroki da kan tsaya tare da mawakin idan yana waƙa, wanda ke tuna masa wasu abubuwan da yake fadi a
cikin waƙar.
[1:37am, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ke
nan kuskuren rubuta abin da mawaƙin ya faɗa
aka yi ko? Ina ba da shawarar a saurari ɗiyan waƙar na
kamin da bayan layukan da kalmar ta fito. Sannan a tambai masu kiyon dawaki
musamman na bargar gidan sarki.
[6:53am, 04/02/2024] Mal. H.U. Maikwari
Ai ita ce Kakanmu Farfesa A.B. YAHYA ya ba da amsa.
A
fahimtata, ai idan doki yana da wannan kinanin da aka bayyana, da shi ɗin ma ana sarrafa dokin.
Don
haka duk kuna a kan hanya, babu kuskure.
[6:54am, 04/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Ke nan kalmar tana cikin kinin kalmomi.
[6:55am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Wato
kamar yadda shi mawakin ya nuna ya ji daɗin
yadda ubangidan yake yi masa. Bayan kyautar da yake ba shi har wani yaro yakan
hada shi da shi wanda ke jan tunaninsa ta hanyar gaya masa wasu abubuwan kamar
sunayen wasu makusantan Sarkin wadanda shi bai san su ba, sai ya ambace su a
cikin waƙar. Wannan
shi zai yiwu iyalan gidan ko aminansa ko kakanninsa da sauransu. 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
[6:55am, 04/02/2024] Mal. H.U. Maikwari
Ban da tabbaci, amma idan fasarar da Farfesa A.B. YAHYA ya yi kin fahimce ta to
lallai kalmar tana da muhalli a inda aka ɗora
ta.
[6:57am, 04/02/2024] Mal. H.U. Maikwari
Ban da tabbaci, amma idan fasarar da Farfesa A.B. YAHYA ya yi kin fahimce ta to
lallai kalmar tana da muhalli a inda aka ɗora
ta.
[7:00am, 04/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Mai yiwuwa kuma a wata rerawar yana cewa tunani, wata kuma ya ce kinani.
Kamar yadda yake cewa:
"Ban je gidan 'ɗan giya' niy yi roƙo ba,
Ko
ya raba lafiya ba ruwana. "
Amma
da jagoran zai yi takiɗi kuma sai ya ce:
"Ban
je gidan 'ɗan bita' niy yi roƙo ba.... "
[7:12am, 04/02/2024] Mal. H.U. Maikwari
Ni ma gaskiya kamar "kinani" na ji mawaƙin ya ce
[7:12am, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ai zambo/habaici ne.
[7:14am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Dukkan
ofisoshinsu ana ce masu gidan 'yan bita saboda koyaushe suna nan kuma duk inda
ya lalacce sai su gyara.
[7:22am, 04/02/2024] Mal. H.U. Maikwari
Mai yiwuwa dai wannan bayani na ki shi ne zai warware muna wannan hange.
Amma
kuma za a iya zurfafa bincike.
Ban
yi mamaki ba, domin idan mutum ya kwankwaɗi
ilmi da yawa, yakan fasara wani abu da tunaninsa, ko ya fahimce shi daidai da
tunaninsa.
Ni
da Dr. Ya ba da kalmar tunani, sai na ji kamar ita ta fi dacewa da muhallin
bayanin.
Da
na saurari waƙar kuma, sai
na ji kalmar da aka faɗa ta farko ta bayyana.
Mun
gode ƙwarai.
Allah
Ya biya ku.
[7:29am, 04/02/2024] Mal. M.A. Umar
"Ja mai tinani" ne, kasancewar da/t/ da/k/ sun yi tarayya a yanayin
furuci da matsayin maƙwallato, ma'ana,
tsayau ne marasa ziza... Sai kuma a ka samu naso, inda wasalin gaba, na sama
maras kewaye/i/ ya nashe wasalin ƙurya na sama mai kewaya/u/. Kamar yadda ake da
"buki" ya koma "biki"...
[7:29am, 04/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Da yake an gama shirya doki tsaf! Cikar kyautar ita ce a ba shi yaron da zai ja
masa ƙinani', wannan
kalmar na iya hawa, duba da yadda aka ƙulla ɗan waƙar.
Kamar
yadda kalmar 'tunani' kan iya zama saboda muhimmancin yaron ga makaɗin shi ne ya taimake shi, ya riƙa sanar da shi wasu muhimman abubuwa da zai ƙulla ƙananan saƙonnin waƙar don nuna godiya.
Amma
fa ni kunnuwa na kalmar 'Tunani' suka ji. Mai yiwuwa kuma sanyin Kano ne, ina
iya sauya ra'ayi. 😅
[7:39am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ko dai ya
take waƙa ta cika,
kuma makadin ya kai don babban bambancin cikakken makadin ke nan, wanda zai
wadatar da waƙarsa da
kalmomin da manazarta ke iya aiki a kansu. Don dabarar mutun ta fitar da shi ko
manyan masana su ƙara saita
shi.
[7:45am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Komai
cikar mawakin Hausa yana jin daɗi idan ana jan
tunaninsa na ambaton wasu kalamai a waƙarsa, shi ya sa ma sukan sami wani daga cikin
mabobinsu mai basira su aje kusa da su don wannan aikin. Wannan ne ke sa waƙar ta yi tsawo da daɗi!
[7:47am, 04/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Wato wasalin/i/ non- central vowel, kenan shi ya koma na tsakiya maras kewaya (high
central vowel unrounded)?
[8:18am, 04/02/2024] Mal. M.A. Umar A waƙar akwai abubuwa da suka shafi tsarin sauti kamar ganɗantawa da naso, misali inda ya ce "jan
damishe" daga "damisa" me ya sa sautin/s/ ya koma/sh/? Haka kuma,
"zanna", "fan talatin, fan tamanin, fam metin, fam bakwai"
"Allah
shi isam ma" da sauransu!
[8:20am, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Hwan
tamaanin da hwan talatin da hwan metin.
[8:25am, 04/02/2024] Mal. M.A. Umar A nan
ya ajiye Zamfarci a gefe "fan" da "fam" ya yi amfani, ba
"hwan" ko "hwam"
[10:55am, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Haƙƙan! Wasu ma da suka aje aikin
ba du je ko ina ba sai suka yi gidajensu nan cikin dajin. Na taɓa yada zango kusa da gidan irin mutanen nan.
[11:09am, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Tabbas! Manazarcin waƙa ya riƙa la'akari da cewa mawaƙan Hausa, musamman na Fada, kan sa zambo cikin
waƙokinsu amma ba su ambatar suna
sai dai ishara. Sannan wannan zambo, da yake kishiyar yabo, shi ma yabo ne mawaƙan kan yi ga ubangidansu a dunƙule domin daɗi
yake ji idan aka nakkasa ɗan hamayya, wato ɗan
sarki
Jagora: Majalisaɗ ɗunkin duniya
Majalisaɗ ɗunkin duniya
Tayi ododi ga manoma
A riƙa aiki ag gaskiya
A aje abinci ag gaskiya,
A tarda gero,
A tarda dawa,
A saida gujjiya,
A saida kaɗa,
A aje gero so nai mukai,
Babban abun Nanjeriya,
Kan dawo in yash sha nono,
Ko Bature kab ba shi
ba shi girgizawa amsa yakai,
Ko da yash sha..
Jagora/Y/Amshi:
Sai kaji ya ɗwaɗwa Ingilishi,
Kai nai ya hwashe da yat tamni tcakin dawo,
Asha hura ayi wasa,
D/Tumba shan hura ba lahani ba ne,
Jagora/Y/Amshi:
Asha hura ayi wasa,
D/Tumba shan hura ba lahani ba ne,
Farin cikin Musulmin Duniya,
Mai martaba na Abubakar,
Ci
fansa Alhaji Macciɗo
Ɗiyan Waƙa ne daga cikin Waƙar Makaɗa
Sa'idu Faru ta Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi
Muhammadu Bello Macciɗo Abubakar III mai gindi "Farin cikin Musulmin
Duniya, Mai martaba na Abubakar, Ci fansa Alhaji Macciɗo". Allah ya kyauta makwanci, amin.
[11:37am, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Shi fa mawaƙin ai
abubuwa ne yake faɗa tare da abokan burminsu, fam tamanin + riga, doki +
kayan doki + yaro mai jan likkafa....
Haka
kyautar wannan ubangida take. Ko gida zai ba ka sai ya gama (haɗa) ma da mata (wato sa-ɗaka ko kuyanga). A taƙaice cikakkar kyauta yakan yi ba rabi da rabi ba
[11:45am, 04/02/2024] www.amsoshi.com:
"Tsattsafin Tattalin Arziki a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru"
[11:46am, 04/02/2024] www.amsoshi.com:
"Gurbin Noma a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru"
[11:46am, 04/02/2024] www.amsoshi.com:
"Noma a Mahangar Makaɗa Sa'idu
Faru"
[12:11pm, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Sa'idu Faru bai kai kaiwa, gaisuwar da matafiya ko Hakimi kan kai wa basarake, ko
ma mai saukar da baƙo. Shi waƙa ya iya kuma ya san ba kowa ya iya waƙa ba, balle duk mawaƙi idan ba shi ba to shirme (ƙarya ce) ne, shi Sa'idu waƙa ya iya ita zai kai kaiwa. A farko ya ce kowa a Kano,
to amma da yake ya san sarakuna akan kai wa kaiwa, sai ya yi amfani da salon
waskiya (M B Umar ya fito da wannan salo cikin nazarin waƙa, daga kalmar "waske") ya maimaita layin ya
ce Sarkin Kano!
[1:37pm, 04/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Da wannan, na aminta da kalmar ƙinani'. Allah ya kyauta aikin Malam. 🙏
[1:50pm, 04/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Kinami
dai ko?
[1:51pm, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ki
tuntuɓi Farfesa Sa'idu Gusau don shi ne Giwa a dajin
Waƙoƙin Baka na Hausa, mu duk 'yan tsaro ne!!!
[2:04pm, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Mai yiwuwa "kinani" ɗin Faru yake faɗi don kila a karin Hausar da ya tashi da ita haka ake
faɗi. Ba ku ganin wasu su ce "faɗi/hwaɗi" wasu ko
su ce "hiɗi"; wasu su ce "can" wasu ko su ce
"in"; wasu su ce "koma" wasu su ce "dawai/dawaya".
Hausa ƙwarai take
da wadatar kalmomi da ma'anoni kamar Larabci
[2:07pm, 04/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Lallai ba karamar godiya muke ba ga Malaman mu da suke ta gogoriyo da ninkaya
wajen zakulo mana ilimummuka akan wannan fage, kuma suke shayar damu. Sannun ku
da ƙoƙari masu girma masanan mu. Allah ya tabbatar da
alkaluman ku cikin danshi a ko yaushe. Kullum ina jin daɗi yadda na yi Hausa a A-Level na kuma maida hankali
akai sosai. Gashi yanzu muna ta bi muna karuwa sannan ina ganin kamar yanzu ma
cikin aji nike. Muna biye Malaman mu. 🙏✊
[10:21pm, 04/02/2024] Dr. H. Yelwa: Wato,
Sarkin Bauran Dange Muhammadu Dangwaggo, Sarkin Musulmi Hassan dan Muazu da
Shehu baban Sarkin Musulmi Abubakar diyan Sarkin Musulmi Mu’azu gidan Bello ne.
[10:25pm, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Afuwan, Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan
Malam Usman ba ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ba ne. Jikan Sarkin Musulmi
Mu'azu ne kamar yadda Sarkin Musulmi Abubakar III ya ke, kenan Malam Usman ne
ya haifi Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo da Sarkin Musulmi Abubakar III 🙏🙏🙏
[10:30pm, 04/02/2024] Dr. H. Yelwa: Yawwa.
Saboda Sa’idu na ce ma Sarkin Gabas Shehu
"Jikan
Hassan dan Mamman"..
Hassan
a nan👆🏽Sarki Hassan dan Muazu wan Shehu baban Sarki Garba Na3.
[10:31pm, 04/02/2024] Dr. I.I. Dutsinma:
Slm. Wai don Allah ina ne Bauran Dange? Ko ita ce ake cewa Dange Shuni?
[10:40pm, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haƙiƙa! Sarkin Baura Muhammadu Ɗangwaggo ne babban ɗa
ga Malam Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu.
[10:41pm, 04/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Baura ko Sarkin Baura shi ne laƙabin sarautar Dange, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange/Shuni dake Jihar Sakkwato.
[10:45pm, 04/02/2024] Dr. I.I. Dutsinma:
Na gane. To asalin waɗnada suka asasa wannan garin Katsinawa ne daga ƙabilar Fulani mai suna Dangi. Kuma sun taso ne daga ƙasar Yantumaki ta Katsina kafin yaƙin Shehu Ɗanfodiyo
Wani
ɗa ne daga cikin 'ya'yan Dangi Yusufu. Shi ne ya kafa
Dange wadda ke kan hanyar Sokoto amma ban san tarihin Dange Shunin ba. Shi yasa
ma ya kira garin da Dangi, daga baya ya koma Dange. Akwai wani littafi da na
karanta na tarihin Fulani Dangi a jihar Katsina. Wallahu a alam
[10:58pm, 04/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Jama'a Dange/Shuni ai Ƙaramar
Hukuma ce da ta haɗa ƙasar Dange da ƙasar Shuni.
Wata rana mai yiwuwa ne a ƙirƙiro Ƙaramar Hukumar Dange, da Ƙaramar Hukumar Shuni.
Wani
ƙarin bayani ko tunatarwa, garin
Shuni nan aka haifi mawaƙin da kuka
sani mai suna Aliyu Ɗandawo
mahaifin mawaƙin nan da
kila matasan yau suka fi sani, wato Sani Aliyu Ɗandawo.
[11:02pm, 04/02/2024] Dr. I.I. Dutsinma:
Ok. To ni ba Shunin nake nufi ba Dangen dai wadda ke kan hanyar Sokoto. 'Swasswakiya'.
Don Allah me kalmar nan take nufi?
Tsakin
tama: wannan salon baubawan burmi/ salon gambiza ne Sa'idu Faru ya yi amfani da
shi domin ya kamanta Tijjani Hashim ya nuna cewa mutum ne wanda bai da daɗin gamo, ba a iya ja da shi don ba za a ji daɗi ba.
Kafin
a fahimci haka bari mu dubi kalmomin biyu: tsaki da tama.
Tsakin
da aka fi kawowa ga rai shi ne sauran dawon da bai damu ba wanda ke ƙasan ƙwarya ko kwanon fura. Tsakin nan na fura yana da daɗin tamnawa saboda nonon da ya cuɗe shi sosai. Kuma ko bai ji nono ba yana da daɗi. Saboda haka ba matsala ga wanda ya tauna shi.
Tama
kuwa dutse ne baƙi wanda ni
dai a Sokoto aka fi samu kusa da gulbi. Baƙi ne mai ƙarfi sosai kuma bai jiƙa ko ka zuba mai ruwa ko ka saka shi cikin gulbi. Ina
jin maƙera suna
amfani da shi wurin ƙira. To ka
kwatanta an samu injin ya Farfesa wannan dutse. Idan aka ba ka garin wannan
dutse aka ce ka sa ga bakinka ka tauna, yaya haƙora ka za su ji? Ko za ka ji kamar kana taunar tsakin
fura?
A
nazarin waƙa idan
mawaƙi ya haɗa kalmomi biyu wuri guda ba yadda aka saba haɗa su ba to sai a ce ya yi amfani da salon ganin
gambiza ko salon baubawan burmi. A haɗa
tsaki da tama iyakar rashin gami ke nan domin shi dai tsaki na fura aka sani ba
tama ko tsakuwa ba. Saboda haka Sa'idu Faru shi sai ya haɗa tsaki da tama domin ya samu ma'anar 'rashin jin daɗi' ko 'wuyar gamo' don ya siffanta Ahmad Tijjani
Hashim da cewa abokan hamayya ba su iya kome da shi a kokuwar mulki ko wani abu.
Kamanceceniya
da wani ta halayya, musamman halaye na gari.
Wani
malamina Bafalasdine yana koyon Hausa sai mu ɗalibansa muka gwada shi muka nuna masa riga muka ce me ake kiran wannan
da Hausa? Sai ya ce riga. Muka ce sosai haka ne. Muka nuna abubuwa da dama yana
faɗin sunayensu da Hausa. Sai kuma muka nuna masa wando, ya
tsaya ya noce kai yana tunani, can sai ya ce, "rigar ƙafa"!
A
nan ya yi gamin gambiza.
Ga
wasu misalan baubawan burmi:
Bangon
dutsi
Fitilar
sharri
Rigar
ƙaya
Wandon
ƙarfe
Tsakin
tsakuwa
Madallah
da wanga bayani, Allah ya gafarta Malam. 🙋🏽♂
Akwai
kuma:
-Rijiyar
lemu
-
Gadon ƙaya
Bari
dai in bari kada Kanawa su yi mini caa!
Allah
ya biya, Malam har da irinsu:?
Hadarin
kasa?
Azumin
jrmage?
Bakan
gizo?
Duk
irinsu ne?
Jemage
Sosai.
Ɗanƙwairo ya ce:
/Hadarin
ƙasa maganin mai kabido/.
Kabido
shi ne rigar ruwa na Bahaushe kafin zuwan Turawa.
Da
kaba ake saƙa kabido, a
yafa shi tun daga kai har zuwa guwawu. Ruwan sama ba su taɓa jikin mutum.
To
ita ce mutanen suke kwatanta da ruwa ya fito daga kasa ba daga sama ba kamar
yadda aka saba, da mutun zai jike sharkaf!
***
***
Bayan
an cire Sarki Kabiru ɗan Sule sai aka naɗa
Muhammadu Mainasara Sambo Ƙanen Sarki Sule (Mahaifinsu ɗaya
da Sarki Sule Mahaifin Sarki Kabiru) a shekarar 1976.
Sarki
Muhammadu Mainasara Sambo ya rasu a farko farkon 2000s sai aka naɗa Abubakar Atiku Muhammadu Sambo, Ƙanensu Sarki Sule da Sarki Muhammadu Mainasara (Mahaifinsu
ɗaya dasu).
An
cire Sarki Abubakar Atiku Muhammadu Sambo a cikin 2022, sai aka naɗa Muhammadu Bello ɗan
Sarki Sule Muhammadu Sambo wanda kuma yaya ne/wa ne ga Sarki Kabiru Suleiman
Muhammadu Sambo (Mahaifinsu ɗaya, Sarki
Suleiman Muhammadu Sambo). Sarki Muhammadu Bello Suleiman ke sarauta a halin
yanzu.
Eh
ɗan'uwansa ne. Da Mahaifinsa da Mahaifin Sarkin
Kudu/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo
Mahaifinsu ɗaya.
Sarkin
Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo
ne ya haifi wanda aka yi wa Waƙar, wato Sarkin Gabas na Mafara Shehu. Shi kuma Sarkin Bauran Dange
Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Modibbo Usman ne, Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ne, Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi
Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne.
Sarkin
Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar III ne, Sarkin Musulmi
Abubakar III ɗan Modibbo Usman ne, Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ne, Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi
Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne. Allah ya
kyauta makwanci, amin.
Mai
girma Sarkin Gobir Na Bunguɗu kuma Shaihin
Malaminmu Dr. Haruna Umar Bunguɗu barka da dare.
Sannu da fama ta raya muna Zaure.
Das
rayit (That is right!), haka Mai Martaba S/M Macciɗo (Allah Ya rahamce shi) ke cewa idan abin da aka faɗi ya yi masa daidai sosai.
Sarkin
Gabas Shehu ya yi Sarauta a Talata Mafara daga shekarar 1958 zuwa rasuwarsa a
shekarar 1969 sanadiyar gobara, Allah ya kyauta makwanci, amin.
Idan
kuwa ya lura da cewa akwai 'yar matsala sai ka ji ya ce, "To daidai"😂
Allah
Ya yi masa rahma da Aljannar Firdausi amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu Ya Rabbal alamina Ya Arhamar rahimina
Allah
Sarki!!! Haƙiƙa sau da yawa ina jin wannan kalmar a bakinsa. Allah
ya kyauta makwanci, amin.
Ina
iya tuna ranar da aka ba shi takardar tabbatar masa da sarautar Sarkin Musulmi
a cikin watan Afrilun 1996, a Masallacin Bello dake Ƙofar Fadar Sarkin Musulmi a Sakkwato ta hannun Alhaji
Aminu Ahmed Nahuce wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Mulkin Soja a Tsohuwar
Jihar Sakkwato (Sokoto da Zamfara). Ni kuma ina ɗaukowa Gidan Rediyon Rima na Sakkwato rahotanni daga Gidan Gwamnatin
Jihar Sakkwato a lokacin.
Ka
san Ni Bagiɗaɗe ne, saboda
haka in na je gidansa kafin ya hau sarauta, yakan ce Bagiɗade ya zo ya ci abinci. Nan na ga abin mamaki. Kwalba
cike da man shanu yake bungulewa cikin kwanon abincin!
Hakika
muna godiya ga Allah SWT da Ya nufe mu da samun wannan ilimi mai albarka daga
bakunan Malamanmu masu albarka a wannan babban zaure mai albarka.
***
***
Don
Allah ina ƙara roƙon wannan Zaure da ya gurza dukan abin da jama'a suka
saka cikinsa, tun daga rana ta farko, a mayar kundi. Na fi aminta da littafi a
kan na'urorin nan na zamani domin masu shuɗewa
ne. Kaset-kaset na rikoda sun isa misali: Ko dai su cumuimuye har su tsinke, ko
a yi ɗungum a ƙirƙiro wata na'ura da ba ta iya juyo abin da ke cikin kaset! Wa ya sani ko
nan gaba a ƙirƙiro abin da ya fi 'memory carɗ ko 'hard drive' sauƙin tu'ammuli amma kuma ba zai iya juyo abin da ke
cikinsu ba?!
***
***
Na
tambayi wani dan cikin gidan fadar sarkin Musulmi ya tabbatar man da cewa ƙumatu' jekadiya ce a gidan sarkin Musulmi. Sunanta na
yanka shi ne Halima/Halimatu. Dalilin da ya sa ake mata lakabi da Kumatu, sabo
da sunan matar sarkin Musulmi Abubakar III ke gare ta watau mahaifiya ce ga
sarkin Musulmi Muhammadu Macido.
To
amma mece ce ma'anar sunan Kumatu cikin Hausa ko wani harshe da Hausawa suke da
kusanci da shi? Misali, idan aka kira macce Tumba, to wadda aka haifa ce
sakamakon auren zumunta, wato mahaifan mata da miji 'yan'uwa ne. Haka wanda ake
wa laƙabi da Gambo
ana nufin wanda/wadda aka haifa bayan 'yan biyu. To amma Kumatu fa?
A
nan Kumatu na nufin wadda ke da manyan kumatu. Sifa ce a nahawun Hausa
Ke
nan jekadiyar mai manyan kumatu ce ba kamar yadda ka yi bayani tun farko ba ko?
An yi amfani da siffarta ne ba don tana da suna guda da mahaifiyar Sarkin
Musulmi Macciɗo ba. Da ba mai manyan kumatu ba ce da an dubi wata
siffarta an kira ta da ita. Misali, idan mai babban goshi ce watakila a kira ta
da Goshi.
...
Cikin tukar rukuɓu, tukuɗin
Tumba yai tuɓus... Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.
Sauna
da mai nagarta duh kama rika na Bubakar🤣🤣🤣
.....
Wandara Allah ya taimake ka riƙon kowa da gaskiya....
Faru
mawaki ne Mai fikra da zalaka da hikma. Allah ya jikan shi da rahama.
Sosai
kuwa, ai mashahuri ne a waƙar musamman waƙar fada. Shi
ne mawakin da muke misali da shi hankali kwance a matsayin makadin fada.
....
Sa'idu Hwaru ka Waƙam
mulki/iko, komi kaj jiya ƙarya akai...
Idan
kai ba ka yi Sarki ba, ko ka gadi sarauta, sai dai ya ambaci sunanka a cikin waƙar Sarkin ko mai niyyar zama Sarki.
Don
ya gode ma kyautad da Kay yi mai.
Ina
nufin da sarakina da 'Yangaladimomi yake yi wa Waƙa.
Ai
kamar shi ne babban dalilin yi wa wannan Taron laƙabi da "4 Decades Of Hausa Royal Songs...../Saboda
kusan kashi Casa'in a cikin kashi Ɗari na Waƙoƙinsa na masu iko/mulki ko alaƙa da mulki ko iko ne.
A
wace shekara Sa'idu Faru ya rasu?
A
shekarar 2004.
A
shekarar 1987.
An
haifi makaɗa Saɗu Faru a
shekarar 1932, a garin faru, karamar hukumar maradun.
Da
shekara 91 ya yi wafati
Anya
dai Ɗangaladima?
Duba
wannan bayani da Hon. Ɗanmadami
ya yi. -1996-9 =1987
Rankai
dade, kamar na yi karanbani.
Afuwan
🙏
Haka
nagani a sashen idon matambayi wanda suke bayar da tarihin makadan kasar hausa.
Ranka
ya daɗe barka da Jumu'a, Allah ya karɓi ibadunmu, ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau
da imani Alfarmar Sahibul Qiblataini Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin.
A
zance mafi shahara an haife shi a shekarar 1916, ya rasu a shekarar 1987. Kenan
ya yi shekara 71 a duniya.
Ƴallaɓai haka a ka
rubuta a waƙoƙin da aka turo.
"Kashi
bakwai kak kwasa,
Ƴan sarki na kallo,
Gidan
Bani,
Kai
kak kai,
Ga
irin wagga maslaha,
Ga
ka ɗan ma darijja,
Ga
ka jiƙan Usmanu,
Kurɗabi na Hodiyo,
Ga
ka sarkin nasara,
Ga
ka Alhaji Macciɗo,
Ga
jikka ta yi dubu,
Ga
ka malammi kake,
Ga
ka mummuni ka ke,
Abin
da Allah duk kai wa mutum,
Baba
yai maka".
☝️
Lissafin
7 ya fita. Amma a wata rerawa sai ya ƙara da:
"
Ga ka baka za'ida".
Yabo
iya yabo! Lalle Sa'idu Faru tuni ya share wa Sarkin Kudu Macciɗo hanyar zama sarkin musulmi.
Allah
ya gafarta musu.
Sai
kuma ga shi bayan shekaru 9 da wafatin Sa'idu Allah ya tabbatar da wannan fatar
da addu'a tasa, Muhammadu Macciɗo ya zama
Sarkin Musulmi. Allah ya kyauta makwanci, amin.
A
zance mafi shahara an haifi Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III a shekarar 1926 a garin Dange, hedikwatar
Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange/Shuni,
Jihar Sakkwato.
Ya
zo Talata Mafara a matsayin Hakimi a shekarar 1953, aka mayar dashi Sakkwato a
shekarar 1956.
Ya
zama Sarkin Musulmi a shekarar 1996, Allah SWT ya karɓi abinsa a shekarar 2006. 1926, 1956, 1996 da 2006. Allahu
Akbar! Allah ya jiƙan sa da
rahama shi da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da
imani, amin.
Gaskiya
wannan wata Makaranta ce da ya kamata a maida hankali domin kwasar garabasar
karatu. Allah ya yi muku jagora.
Daga
gidan sarautar Maradun ake tura ɗan
Sarki zuwa Faru ya yi Sarauta a matsayin Dagaci/Uban Ƙasa/Hakimi da laƙabin "Sarkin Yamma".
A
cikin wannan Waƙar za a ji
Sa'idu Faru yana cewa "Iro Magajin Shehu da Bello", yana nufin
Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio da
Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi
Shehu Usman Ɗanfodio
domin Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ne ya ƙirƙiri gidan Sarautar Maradun na yanzu, ya kuma yi sarauta daga shekarar
1870 zuwa rasuwarsa a shekarar 1874.
Shi
kuma ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne. Allah ya
kyauta makwanci, amin.
Sarkin
Yamman Faru Ibrahim ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Abubakar/Bubakar ne wanda ya yi Sarauta
daga shekarar 1939 zuwa shekarar 1960 da aka cire shi.
Shi
ma Sarkin Yamman Faru Ibrahim Abubakar an cire shi ne a farko farkon 1960s, ya
rasu a cikin 1999/2000. Allah ya kyauta makwanci, amin.
Don
Allah ina ƙara roƙon wannan Zaure da ya gurza dukan abin da jama'a suka
saka cikinsa, tun daga rana ta farko, a mayar kundi. Na fi aminta da littafi a
kan na'urorin nan na zamani domin masu shuɗewa
ne. Kaset-kaset na rikoda sun isa misali: Ko dai su cumuimuye har su tsinke, ko
a yi ɗungum a ƙirƙiro wata na'ura da ba ta iya juyo abin da ke cikin kaset! Wa ya sani ko
nan gaba a ƙirƙiro abin da ya fi 'memory carɗ ko 'hard drive' sauƙin tu'ammuli amma kuma ba zai iya juyo abin da ke
cikinsu ba?!
Tunkuda
Tunku cikin tukar rukubu..... Salam!
"Uban
Kumatu uban Isa jikan Abubakar... "
Na
tambayi wani dan cikin gidan fadar sarkin Musulmi ya tabbatar man da cewa ƙumatu' jekadiya ce a gidan sarkin Musulmi. Sunanta na
yanka shi ne Halima/Halimatu. Dalilin da ya sa ake mata lakabi da Kumatu, sabo
da sunan matar sarkin Musulmi Abubakar III ke gare ta watau mahaifiya ce ga
sarkin Musulmi Muhammadu Macido.
To
amma mece ce ma'anar sunan Kumatu cikin Hausa ko wani harshe da Hausawa suke da
kusanci da shi? Misali, idan aka kira macce Tumba, to wadda aka haifa ce
sakamakon auren zumunta, wato mahaifan mata da miji 'yan'uwa ne. Haka wanda ake
wa laƙabi da Gambo
ana nufin wanda/wadda aka haifa bayan 'yan biyu. To amma Kumatu fa?
A
nan Kumatu na nufin wadda ke da manyan kumatu. Sifa ce a nahawun Hausa
Ke
nan jekadiyar mai manyan kumatu ce ba kamar yadda ka yi bayani tun farko ba ko?
An yi amfani da siffarta ne ba don tana da suna guda da mahaifiyar Sarkin
Musulmi Macciɗo ba. Da ba mai manyan kumatu ba ce da an dubi wata
siffarta an kira ta da ita. Misali, idan mai babban goshi ce watakila a kira ta
da Goshi.
...
Cikin tukar rukuɓu, tukuɗin
Tumba yai tuɓus... Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.
Sauna
da mai nagarta duh kama rika na Bubakar🤣🤣🤣
.....
Wandara Allah ya taimake ka riƙon kowa da gaskiya....
Faru
mawaki ne Mai fikra da zalaka da hikma. Allah ya jikan shi da rahama.
Sosai
kuwa, ai mashahuri ne a waƙar musamman waƙar fada. Shi
ne mawakin da muke misali da shi hankali kwance a matsayin makadin fada.
....
Sa'idu Hwaru ka Waƙam
mulki/iko, komi kaj jiya ƙarya akai...
Idan
kai ba ka yi Sarki ba, ko ka gadi sarauta, sai dai ya ambaci sunanka a cikin waƙar Sarkin ko mai niyyar zama Sarki.
Don
ya gode ma kyautad da Kay yi mai.
Ina
nufin da sarakina da 'Yangaladimomi yake yi wa Waƙa.
Ai
kamar shi ne babban dalilin yi wa wannan Taron laƙabi da "4 Decades Of Hausa Royal Songs...../Saboda
kusan kashi Casa'in a cikin kashi Ɗari na Waƙoƙinsa na masu iko/mulki ko alaƙa da mulki ko iko ne.
A
wace shekara Sa'idu Faru ya rasu?
A
shekarar 2004.
A
shekarar 1987.
An
haifi makaɗa Saɗu Faru a
shekarar 1932, a garin faru, karamar hukumar maradun.
Da
shekara 91 ya yi wafati
Anya
dai Ɗangaladima?
Duba
wannan bayani da Hon. Ɗanmadami
ya yi. -1996-9 =1987
Rankai
dade, kamar na yi karanbani.
Afuwan
🙏
Haka
nagani a sashen idon matambayi wanda suke bayar da tarihin makadan kasar hausa.
A
zance mafi shahara an haife shi a shekarar 1916, ya rasu a shekarar 1987. Kenan
ya yi shekara 71 a duniya.
[6:05pm, 09/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A nawa ɗan gajeren nazari akan Malamin Waƙa mai kwana ɗumi
na Mamman na Balaraba na ci karo da waƙoƙinsa na faɗakarwa da na siyasa da kuma na wasu ɗaiɗaikun jama'a da
ba su alaƙanci
sarauta ko fada ba.
Daga
cikin irin waɗannan waƙoƙin na mutanen da ba su jiɓinci
sarauta ko fada ba akwai na Engineer Abubakar Sahabi Sakkwato da Engineer Tori
Aliyu.
Kafin
in san cewa Marigayi Alhaji Muhammadu Ɗandurgu Ƙaura Namoda banda zamansa Attajiri, hakimi ne na ɗora sa a cikin layin mutanen da ba su da alaƙa da sarauta ko fada da ya waƙe.
Akwai
kuma Alhaji Tumba Rawayya da nike yi wa kallon Attajirin da ya amfana daga
fasahar waƙar Sa'idu
Faru, sai daga baya na fahimci yana da alaƙa da fadar Dagacin Rawayya/Rashin Rawayya.
Duba
da rashin samun ƙarin wasu
mutane irin su Engineer Abubakar Sahabi Sakkwato da Engineer Tori Aliyu
Sakkwato masu waƙoƙi daga Malamin Waƙa ne ya sanya ni cimma matsayar kiransa da "Makaɗin Fada" kacokan.
Duk
kuwa da cewa babu mamaki ana iya samun su fiye da haka, amma idan muka duba
cewa a cikin kashi Ɗari na Waƙoƙinsa, kashi Casa'in duka na Sarauta/Sarakuna/Masu alaƙa da sarauta ne sai nike kallon kamar hujjata na iya
tsayuwa. Allahu Wa'alam!
[6:10pm, 09/02/2024] Hon. H.A. Gusau:
Allah ya ƙara lafiya
da basira da hazaƙa, Honourable.
Encyclopaedia harshen Hausa, jama'ar ta
da al'adunta.
[8:40pm, 09/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ni ma a
nan na rakube. Saboda kafin ka ji ya yi wata waƙar da ba ta fada ba wata dagar duniya ce, idan kuma ka
debi irin wadannan wakokin ka watsa a cikin sauran sai su bace bat!
[9:00pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa mutane da yawa suna kallon sa da mawaƙin fada/sarauta. Ina jin na taɓa karanta wata hira da aka yi da shi, ko kuma wani
littafi da aka ruwaito yana cewa shi sai ɗan
sarauta yake yi wa waƙa. Sai dai
gaskiya na mance da tushen wannan bayani.
[9:11pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A
lura da cewa Ƙarni na 20
ya sa mawaƙan Hausa
sassauya matsayinsu sakamakon tasirin Mulkin Mallaka da Turawa suka yi a ƙasar Hausa - kafin Ƙarni na 20 sarakuna ne manyan iyayen gidan mawaƙa, amma a na 20 ɗin
zuwa yau sai aka samu wasu rukunan jama'a sun yi ƙarfi, wasu ma fiye da sarakuna, da mawaƙan suka sauya sheƙa, wasu kuwa suka kasance da ƙafa biyu, ba su tsaya ga sarakuna ba ba su tsaya ga
wasu ba- kowa ma nasu ne kamar Sani Aliyu Ɗandawo
[9:30pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Duk da haka ba za a rasa ɗaiɗaiku ba, da
kuma wasu sabbin mawaƙa ba. Zamani
tafiya yake, mutane su zo da abubuwa na ƙwarai da miyagu, masu kyawo da munana. Ƙasar Hausa ba ta tsira ba. Muna fatar Allah Ya sa mu
dace da kyawawa mu kauce wa munana har da na cikin malamai ba masana ba kamar
yadda Haliru Wurno ke kiran wasu malamai:
/Karatu sunka yo ba dai Sani ba/
/Jawabin
saufa nan suke ba na'am ba/
[9:30pm, 09/02/2024] Mal. B. Lauwali:
Wannan zance na cewa an haifi malamin waƙa a shekarar 1916, ya rasu a shekarar 1987 Ina neman
madogara
[9:36pm, 09/02/2024] +234 806 666 5052: Allah
gafarta malam abin tambaya anan shi ne? Mawaƙan ƙarni na 20 za a iya sanya su a jemagun mawaƙa kenan ko? Kamar Sani Aliyu Ɗandawo da makamantansu
[9:47pm, 09/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Hira da ɗansa Makaɗa
Ibrahim Sa'idu Faru wanda kuma a halin yanzu shi ne Halifansa a farko farkon
shekarar 2018.
Ni
ne na yi hirar dashi. Sunana Ibrahim Muhammad Birnin Magaji.
[9:53pm, 09/02/2024] Prof. A.A. Dunfawa:
Tama dutsi ne da ake narkawa a fitar da karfe daga gare shi. Idan ka je makera
za ka ji ana ce ma wata dauda da ke fita daga jikin karfe idan ana narka shi da
suna kashin tama.
[9:56pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ina kyautata zaton idan ka duba Sa'idu Muhammad Gusau, MAKAƊA DA MAWAƘAN HAUSA NA ƊAYA za ka samu
[10:16pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A
taƙaice tama dutsi ne mai tsananin
tauri, bai fasuwa da sauƙi kamar
sauran duwatsu, sai dai a narka shi da wuta. Tsakinsa kuwa bai taunuwa.
Idan
kuwa Sa'idu Faru cewa ya yi/ƙashin tama/
To
duk salon baubawan burmi ne ya yi amfani da shi, ko ma a ce tun asali Hausawa
sun yi amfani da salon. Ƙashin rago
ko na nagge ko na kaza da makamantansu ne aka fi sanin zamansu a tare amma ba
da tama ba.
[10:19pm, 09/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ranka ya daɗe cewa ya yi "Tsakin Tama na Abashe ana shakkah
haye ma Amadu, Mai Martaba na Wambai Ɗan Hashim Ƙanen Sarkin Kano".
[10:29pm, 09/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ni dai ban son in kira su jemagu domin ga kunnuwana wannan kalma ba ta dace da
a liƙa wa masu
hikimarmu ba.
[3:38pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Yahihiya da Kunkuru, shawara guda sukai... Inji Malamin Waƙa Mai kwana Ɗumi na Mamman na Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru a cikin Waƙarsa ta Dagacin Falale dake Masarautar Gummi, Jihar Zamfara, Alhaji Muhammadu Bala mai amshi 'Ya riƙa da gaskiya Muhammadun Muhammadu, Karsanin/Dangalin gidan Mai saje shirinka ya yi kyau', Allah ya kyauta makwanci, amin.
Ya
ci gaba yana cewa da Hasbiya da Kurciya, shawara guda sukai har zuwa ƙarshen ɗan/ɗiyan Waƙar.
Wannan
shi ne Kunkuru, ko zamu samu hoton Yahihiya da kuma fashin baƙin abubuwan da ke ƙumshe a cikin wannan ɗan Waƙar/waɗannan ɗiyan Waƙar?
[3:56pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Na
san kunkuru amma ban san yahihiya ba. Idan aka sanar da ni yadda take ta fuskar
tafiya da kuma ɗabi'arta dangane da jikinta watakila zan iya fashin baƙin ɗiyan waƙar. Na dai san wata halitta mai kama da kunkuru amma
ba kunkuru ba ce. A Anka ne na sha ganin ta, kuma cikin damina na fi ganin ta, musamman
idan aka yi ruwa, a wuri mai laka-laka. Ƙumbarta sumul-sumul ba kamar ta kunkururu ba. Idan
yaro ya ga wannan halitta zai ce kunkuru ne.
[3:58pm, 10/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Kunkuru
shi ne karamin, yahihiya kuma in ya girma sosai. Kusa duka dabi'unsu iri daya
ne.
[4:02pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ashe! Kunkuru fa ko ƙarami ne
siffarsa guda da ta wanda ya girma. A dai ƙara bincike don Allah.
Mene
ne sunan wanda na yi bayani sama
[4:09pm, 10/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: To ni ma
dai abin da na yi tsammani hakan take, amma dai in akwai wani bayanin wani ya
taimaka mana.
[4:34pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Wannan da ka bayyana ƙumbarta
sumul sumul ba kamar ta Kunkuru ba ita ce Yahihiya Ranka ya daɗe.
Kamar
dai jikin Mankani da jikin Gwaza.
[4:50pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Yanzu na fahimta. Sa'idu Faru yana nuni ne da halittun da suka so su yi kama da
juna, kamar hasbiya da ƙuruciya da
makamantansu. Kusan dabi'arsu guda; sukan yi kwanci a kusan wurare iri ɗaya. Watakila Sa'idu Faru kakannin Dagacin Falale ne
yake kwatantawa da wannan; ko kuma wani ɗan
sarki ne yake yi wa zambo. Da na saurari waƙar duka da na iya sharhin sosai
[4:54pm, 10/02/2024] Dr. Kabiru Abdulkarim:
Mashaa Allah, Alhamdulillah! Allah ya sa a yi da mu!
[5:15pm, 10/02/2024] +234 812 462 9009: Yahihiya (turtle) ɗan uwan kunkuru ne amma a ruwa yake
[5:18pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Madalla da wannan gamsasshen bayani Mai Girma Babban Sakatare. Mun ƙaru sosai, Alhamdulillahi.
[5:21pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A ƙarshen ɗan waƙar/ɗiyan waƙar ya bayyana cewa "Babu wanda yat tai
haji babu mai nuhwaz zuwa".
Da
wannan nike tunanin da wasu 'yan Sarki ya ke, sune ya ke yi wa habaici/zambo. Allahu
Wa'alam!
[7:20pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ko
shakka babu! Da 'yan sarki yake. Wato babu wanda ya kama hanyar zama Dagacin
Falale, ba su kyauta ba su riƙa addini ba, kai duk wani halin abin a gode ko a yaba ga mutane ko ga
kansu ba su da.
[10:07pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A cikin ɗiyan wannan Waƙar, Malamin Waƙa ya kawo sunayen wasu Tsuntsayen da ake samu a
Ruwa/Kogi, wato/watau Gamdayaƙi da Tuji da Jinjimi da Bubuƙuwa da Kulme.
Ko
zamu samu hotunansu da bayani akan abun da ɗiyan
Waƙar da aka ambace su ke nufi
daga masananmu domin mu ƙaru?
[10:34pm, 10/02/2024] +234 812 462 9009: Ina nan
kusa Maigirma Ɗanmadamin
Birnin Magaji.
Daga
cikin abubuwan da uban kiɗi ya faɗa
akwai kulme/kullume. Shi ba tsuntsu ba ne wani nau'i ne na kifi. Wato babbar
tarwaɗa/cat fish.
[10:37pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Prof. S M Gusau da ya wallafa littafinsa MAKAƊA DA MAWAƘAN HAUSA, littafi na 1 a 1996 ya kawo wata hira da ya
yi da Sa'idu Faru da ya ce bai yi wa talaka waƙa saboda dalilin da ya bayar.
To
amma shekarar da aka haifi Sa'idu Faru wadda Gusau ya bayar ita ce
"wajajen shekara ta 1932". Wato marubucin bai tabbatar da takamammar
shekarar ba. Shafukan da marubucin ya yi cikin wannan littafi sun nuna cewa a
lokacin da yake shirya shi littafin a 1987 ne kuma Sa'idu Faru yana raye. A kan
wannan dalili ne marubucin bai rubuta shekarar rasuwar Sa'idu Faru ba. Hatta da
tarihin ƙanen
Sa'idu Faru, wato Mu'azu, da marubucin ya kawo, shi ma (Mu'azu) lokacin yana
cikin 'yan amshin Sa'idu Faru.
[10:40pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A
duba shafi na 117 zuwa na 127 na littafin Prof. Sa'idu Muhammad Gusau da na
ambata sama.
[10:41pm, 10/02/2024] +234 812 462 9009: Dan nan Kulmen da ac cikin gurbi yaa amsa gaisuwa. Mu irin wannan kifin ne mu ke kira kulme/kullume
[10:45pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Madalla da wannan ƙarin
bayani Ranka ya daɗe.
Ni
kuma a hirar da na yi dashi a farko farkon shekarar 2018, ɗansa kuma halifansa Makaɗa Ibrahim Sa'idu Faru ya sheda mani cewa an haifi mahaifin nasa a
shekarar 1916 a garin Faru, Ƙaramar Hukumar Mulkin Maradun a Jihar Zamfara ta yanzu. Ya kuma yi
wafati a cikin shekarar 1987.
Wannan
bayanin ne da kuma wasu kalaman da shi Makaɗa
Sa'idu Faru ya yi a cikin wasu hirarrakin da kafafen yaɗa labarai suka yi dashi, waɗan da na samu, na ƙumshe na kuma saka a cikin Shirinmu na Kundin Mawaƙan Hausa na Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna akan
Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa
Sa'idu Faru da muka gabatar a cikin shekarar ta 2018.
[10:59pm, 10/02/2024] Sarkin Rafin Gobir
Yayana gaskiya ne wannan shine kulme ataƙaice duk wata tarwaɗa
da ta girma itamukacema kulme, shikuma Tuji tsuntsu ne na sahara ƙato ne sosai Amman baikai agululu ba Amman yahi
Hankaka girma, Amman Gamdayaƙi da jinjimi da Bubuƙuwa sune tsuntsayen fadama sunfiyin ƙoto kusada Ruwa, maigirma Danmadami
[11:02pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Lalle shi ko Gusau da Sa'idu Faru ɗin
ya yi hira ranar 3/9/1985 da wata hira da ya kawo da wakilin GTK ya yi da
Sa'idu Faru a 1986. Duk wannan a littafin da na kawo.
Ni
dai na san lokacin S/M MACCIƊO ya rasu Sa'idu Faru ya dade da rasuwa domin a ranar naɗin kuma lokacin da gidan rediyon Rima yana kawo Muryar
naɗin ya sa waƙar nan KANA SHIRE, sai da na tuna da Faru cikin
zuciyata ina faɗin Sa'idu Faru ina ma a raye kake? Da sai Sarki ya ba
ka wasu garuruwa ba ma gari ba
[11:07pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Mu kuma muna kiran sa da ɗan ƙari, wato "kullume"
[11:12pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Madalla da wannan ƙarin bayani
Ranka ya daɗe. Kasancewar Makaɗa
Ibrahim Sa'idu Faru ɗan Malamin Waƙa mai kwana ɗumi
na Mamman na Balaraba wanda ya yi karatun zamani har ma ya yi aikin Gwamnati
irin karantarwa (inda ya kai matsayin headmaster na Primary School) da aikin Ɗan Sanda kafin daga bisani ya yi ritaya ya rungumi
wannan sabgar ta gidansu gadan-gadan wanda ya yi biyar Mahaifin nasa wajen Kiɗa da Waƙa tun yana ƙaramin yaro, sai nike gani yana iya zama madogara
wajen bayar da haƙiƙannin bayani akan Mahaifin nasa.
[11:21pm, 10/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Lalle wannan bayani haka yake. Lokacin ƙuruciyata tsakanin 1959-1965 bubuƙuwa kan zo Sakkwato, kuma ta sauka kan wani iccen a Giɗaɗawa. Wani
lokaci idan na bi ta wurin nakan ga kifi ƙarƙashin iccen wanda ya faɗo daga bakin tsuntsuwar.
Na
karanta cewa bubuƙuwa daga ƙasashe masu nisa kamar Turai takan taso lokacin wani
yanayi ta zo nan ƙasar Hausa
ta yada zango kamin ta tashi ta yi gaba ko ta koma inda ta fito. Ba a dai ganin
ta sai cikin damina zuwa ƙarshen
hunturu, kamar yadda shamuwa kan zo ƙasar Hausa ga damina ta kuma tafi abinta idan damina
ta kusa ƙarewa. Har
ma Hausawa kan ɗauka idan ka ga shamuwa to damina tana kusa; idan kuma
ka daina ganin ta to damina tana kusa da wucewa.
[11:28pm, 10/02/2024] Sarkin Rafin Gobir
Hakane Ranka yadade, Shi ma jinjimi da Gamdayaƙi anfi ganinsu lokacin Damana, musamman idan Gulbi
yazaka yabada Ruwa Hwadama duktashahe, Tafukka sunsha, Bayuyuka sunsha, ƙorammu sunsha
[11:33pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Hirar da Marigayi Alhaji Aminu Balarabe Gusau, Wakilin Gaskiya Tafi
Kwabo na Gusau ya yi da Makaɗa Sa'idu Faru
ce a shekarar 1986.
[11:50pm, 10/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Madalla Ranka ya daɗe. Ya rayu har bayan ƙirƙiro Jihar Zamfara. Mun yi aiki tare dashi a lokacin da nike
jagorancin Ƙungiyar
Yan Jaridu Ta Ƙasa Reshen
Jihar Zamfara da lokacin da na yi Daraktan Hulɗa da Yan Jaridu a Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara da
kuma lokacin da na yi Kwamishinan Yaɗa
Labarai na Jihar Zamfara.
Allah
ya jiƙan sa da
rahama tare da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da
imani, amin.
[8:11am, 11/02/2024] Dr. H. Yelwa: Ina
tuna wata waƙa ta
Sarkin Kudu Maccido mai amshin;
"Hwarin cikin musulmi
Duk kai muka takama yau
Muhammadu Muhammadu
Dan
Audu maidarajja. "
[8:45am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Salamun alaikum. Don ina tambaya:
"Gurbin
giwa sai ɗanta,
Daudu
zaman gurbi sai ɗan kada... "
Zaman
'gurbi' ko 'gulbi' sai ɗan kada?
[9:09am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Tambaya:
"Ƙarya ba magana ba ce,
Yanzu gidan Alu/Abu,
Ba kamar Macciɗon
Hausa,
Girmanka ya kai,
Muƙaminka ya kai,
Riƙon duniya,
Wada
Bubakar yak kai. "
Alu
ko Abu (short form of Abubakar)? 🙏
[9:11am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Alu mai saje ko Alu mai sango? Wanne Sa'idu Faru yake yawan danganta Macciɗo da shi?
[9:13am, 11/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A
tunanina kalma daya ce ta ruda ki a cikin jimlar. Wato "zaman" idan
Basakkwace ya ce zaman yana nufin domin/saboda. Yanzu sai ki tayar ki ji.
[9:16am, 11/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ki faɗi sunan waƙar don a ƙara saurarawa.
[9:19am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Allah ya gafarta Malam, na fahimci 'zaman' abin nufi 'muhalli'.
Gurbi
kuwa na nufin 'rami maras zurfi'.
Gulbi
shi ne 'ƙaramin
kogi'.
Duka
ma'anonin suna iya zama. Amma wacce Sa'idu Faru ya ambata?
[9:20am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
"Kana shire Baba 'Ƴanruwa...
[9:22am, 11/02/2024] +234 807 642 1242: Tama ba
dutsi ba ce. Wani nau'in ma'adani ne a karkashin kasa. Makera kan narka shi da
wuta su fitar da ruwan karfe daga cikin Tamar. Sauran birbishin tarkacen da ya
rage wanda shi ba karfe ba ne, shi Hausawa ke kira tsakin tama.
Amma
kofa a bude take domin samun karin bayani a kan wannan batu.
[9:26am, 11/02/2024] Alh. A. Nakawada:
"gurbi" ne. A cikin gulbi (river) ake samun "gurbi". Wani
mazauni ne cikin ruwa na dabbobin ruwa
[9:27am, 11/02/2024] Dr. S.S. Abdullahi:
Gurbi yake.
[9:27am, 11/02/2024] Alh. A. Nakawada: A
fahimta ta "Abu" ne. Ai kin ga a baitin ƙarshe ya bayyana "Abubakar" din.
[9:43am, 11/02/2024] Dr. H. Yelwa: Alu
Maisaje👆🏽
Alu
Maisango kuma Kano anka yi shi.
[9:46am, 11/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Haka ne. Wasu rubuce-rubuce, sun yi kuskuren rubuta Alu Maisango. Na gode.
A
fahimtata dangane da kalmar gurbi:
(1) gurbi - wuri mai zurfi cikin gulbi, manyan
namun ruwa sun fi zama ciki kuma galibi sai idan za su ci abinci suke tasowa
sama, mutumin da bai iya ruwa ba haɗari
ne gare shi ya shiga cikin gurbi.
(2) gurbi- matsayi ko muƙami ko mataki ko wuri.
To
cikin wannan ɗan waƙa abin da na fahimta shi ne:
-
gurbin giwa: Jagora yana nufin babban matsayi irin wanda magabatan Macciɗo (wato Sarkin Musulmi Abubakar 3 mahaifin Macciɗo) suka kai, babu wanda ya dace da shi sai ɗan Sarkin Musulmi Abubakar 3, (Macciɗo) domin shi ne ya gado shi ta kowace fuska -
tsatsonsa ne, nagartattun halaye gare shi.
(3) gurbi wanda ɗan amshi ya faɗi: kalmar tana da ma'anoni na (1) da (2).
Duka
layukan Jagora da na 'yan amshi kalmar "gurbi" ta dibilwa ce, wato
kalmar da take da ma'ana fiye da ɗaya-
ma'anar wuri mai zurfi cikin gulbi; ma'anar matsayi ko mataki ko muƙami..
Sa'idu
Faru dai yana nufin babu wanda zai gadi S/M Abubakar na 3 sai jininsa
kuma Muhammadu Macciɗo, amma ba talakka ba ko wani ɗan sarki.
Gafarta
Malam ni hira na ji ya yi a Rima Rediyo yana iƙirarin cewa saraki kawai yake wa waƙa.
Wallahi
dai muna ta bautag godiya ga masananmu akan wannan ilimi da muke kwankwaɗa "banɗas"
kamar dai yadda Malamin Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ke cewa a cikin wata Waƙarsa mai amshi 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai', wadda/wacce ya yi wa babban
ubangidansa, Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo Abubakar III. Allah ya kyauta makwanci, amin.
Anya!
Ba 'Ramboshi' ba ne? A tambayi Dr. Musa Fadama FUGUS, ai "kulume" baƙi ne sosai.
-
Alu Maisaje - Lura da cewa Aliyu biyu suka yi sarautar Sarkin Musulmi.
-
Alu Maisango - wani ƙanen Macciɗo ne, na san shi lokacin yana ɗalibin makarantar da ake kira yanzu Nagarta College. Tare
da Sarkin Sudan na Wurno Abubakar, wanda ake yi wa laƙabi da Cika, duka sun yi wannan makaranta. Duka sun
riga mu Gidan Gaskiya, Allah Ya gafarta musu, amin
Ban
sa ran Sa'idu Faru yana nufin wani mutum da aka yi a Kano.
Allah
ya gafarta Malam tabbas ya sha faɗin
hakan a hirarrakinsa daban daban, a kafafen yaɗa labarai a lokacin da yake raye.
Ko
a cikin Waƙarsa ta
Marigayi Mai girma Turakin Kano/Galadiman Kano, Alhaji Ahmad Tijjani Hashim mai
amshi 'Tsakin tama na Abashe ana shakkah haye ma Amadu, mai darajja na Wambai ɗan Hashim ƙanen Sarkin Kano' yana cewa "Sa'idu Hwaru ka Waƙam mulki komi kaj jiya ƙarya akai".
Allah
ya kyauta makwanci, amin.
Prof.
S M Gusau ma ya ruwaito wata hira makamanciyar wadda ka ji. Duba MAKAƊA DA MAWAƘAN HAUSA na 1, shafi na 120 da ɗure na 5.
Haka
ne Ranka ya daɗe. Senator Aliyu Mai Sango Abubakar III Durumbun
Sakkwato kenan.
Sarkin
Musulmi Aliyu Babba ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da ya yi sarauta
daga shekarar 1842 zuwa 1859 da kuma Aliyu Ƙarami ɗan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi wanda ya yi Sarkin
Musulmi daga shekarar 1866 zuwa 1867. Allah ya jiƙan su da rahama su da sauran magabatanmu, ya sa mu
wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.
***
Tabbas
hakane Gurbi acikin gulbi yake hakama duk wani wuri mafi zurhi acikin Ruwa
shina mukakira Gurbi, acikin gulbi akansamu gurbi dadama kila saboda tsawon
gulbi da yawan Ruwan shi, Amman kaman acikin Tafki ko Baye da ƙorama mafiyawansu anfisamun Gurbi guda dai ne, zakaga
mafiyawan masu wanka acikin su sukan kiyaye shiga ƙurya a-inda gurbi yake musamman ga waɗanda basuiya Ruwa ba sosai, gurbi nacikin gulbi yanada
igiya gurbi nacikin Tafki ko baye da ƙorama bayada igiya saidai zurhi, too kowane daga
cikinsu idan bami yahwaɗa sai ta Allah,
Ai
Allah gafarta Malam ana samun bambancin sunan kifi daga wuri zuwa wuri. Akwai
buku wanda a wasu wurare ana kiran shi tambo wani wuri kuma ana kiran shi
gargaza. Mu dai a fadamar Kanwa da Fadamar Rima ɗan tarwaɗa babba muke kira kulme/kullume.
Wasu
kuma suna kiran buku da "karfasa"
Ka
gani ko? Ni yau ne ma na fara jin wannan sunan.
A
Abuja naji suna kiran shi da "karfasa"
***
Na
gode, wannan abin ya dade yana damu na, donn ire-iren sunayen kifayen sun yi
yawa har na fara tunanin bambance su zai yi wuya in ba ga Sarkawa ba.
Haka
ne. Amma bambamce bambancen sunayen yana faruwa ne daga wuri zuwa wani wuri.
Wannan
fa ya yi daidai, kuma ya katangance ni da wasu malaman daga rikirkita dalibanmu.
@~Idris
Garba Zagwalis, Malamin ne a fannin zane-zane... Yanzu haka ya fara aiki a kan
wasu waƙoƙin Sa'idu Faru ta amfani da kiɗa da zane... Muna maraba da wannan fasaha ta ƙarni na ashirin da ɗaya
Kififiya
mu kan kira wagga
Ka
gani ko? Mu muna cewa yahihiya ku ko kuna cewa kififiya. Hausa ke nan. Abubuwa
suna canjawa daga wuri zuwa wani wuri
Afuwan!
Don Allah Maisango yana raye ne ko?
Mu
ma a Katsina ci ƙihihiya
muke cewa
To
ita kalmar yahihiya karin harshen ina ne?
Ban
sani ba ko ya auro daga Sarkin Kabin Yabo Maishanu, amma nasan ya auro daga
gidan su Sarkin Sudan Shehu Malami. Da suka rabu da ita ta auri Marigayi
Alhaji Sahabi Dange Immigration, yanzu haka tana gidansa dake Abuja domin tayi
masa wanka.
Ban
iya tuna sunan wanda ta aura. Ko ita matar don 'yar uwa ce ga wani ɗan ajinmu na sakandaren Birnin Kabi mai suna
Umaru. Bai fi shekara da rasuwa ba. Kuma yana riƙon sarautar Torankawa ya rasu. To muna sakandare ne
matar ta rasu.
To
ita 'yar Sarkin Kabin Yabo ɗin tun cikin
shekarun 1970 ta rasu.
Ɗan'uwanta Umaru ɗan
ajina ne a G S S Birnin Kabi, shi ya faɗa
min rasuwarta kuma nurse ce. Ina jin ma a Ingila ta yi kwas ɗin
Ina
da Kaka ƴar
Chiroman Kano Abdullahi Mageli, babban ɗan
sarkin Kano Alu Maisango. Shi kuwa sarkin Kano Alu an ce mahaifiyarsa ƴa/jikar Shehu Usmanu ce, sunanta Saudatu (Goggon Dole).
Mamakina,
a tarihin Kano mun ji yadda Sarkin Kano Alu ya samu laƙanin Maisango, to Sakkwato fa? Ko kuwa nasaba ce ta sa
aka samu sunan Maisango a Sakkwato? Sai dai ban san wanda ya tasirantu da wani
ba.
Sakkwato/Kabi/Zanhwara
da wasu sassa na Arewancin Jamhuriyar Nijar.
Daga
laƙabin Sarkin Kano Alu/Aliyu Mai
Sango/Maje Lokoja ne.
Aha
Ya
yi to
Saboda
ni nazarin karin harshen ne.
Idan
naga baƙuwar kalma
gare ni ina neman sanin ta
Yes
Aiki
na na PhD da na gabatar a BUK a kan karin harshen Katsinanci da Zamfaranci ne a
kan iyakar Katsina da Zamfara.
Amma
ban taɓa ganin wannan kalmar ba
Ko
da yake daga cikin kalmomin da na nazarta ban shiga sashen kalmomin da suka
shafi tsuntsaye da namun daji ba sosai
Kaga
wannan ma ya ƙara bani
haske wajen yinƙurin yin
Post PhD research ɗi na.
Malam
a naku yankin ya kuke kiran wannan halittar?
Ƙihihiya
Kuma
idan ka lura dama duk lokacin da sautin leɓe
hanƙa na
/f/
ya zo tare da kowane wasslin Hausa, sautin na komawa sautin ɗan maƙoshi a ganɗa na
/h/.
Misali
A
daidaita ciyar Hausa a ce
fi
A
Katsinanci da sauran kare karen harsuna na yamma kuma a furta da
hi
Haƙiƙa Sarkin Kano Aliyu shi ne ya nufi Sakkwato don ya sanar game da
gurgusowa Turawan Ingila (Nasara) cikin Daular Usmaniyya. Ina jin ma (ban
tabbata ba) kamin ya isa ko ya koma ne Turawan suka isa Kano.
Ni
dai ni ma kunnuwana a bude suke su ji dalilin sunan Maisango daga masana, ba
'yan shaci-faɗi ba na wannan zamani. Allah sa mu dace, Amin.
Kamar
na taba karantawa a tarihi cewa Mahaifiyar Sarkin Kano Alu Mai Sango diya ce ga
Sarkin Musulmi Alu Babba Dan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello.
An
ruwaito cewa an rada mashi suna Alu ne saboda Kakanshi, Sarkin Musulmi Aliyu
Babba.
Allah
Ya isar wa al'umma abin da tsinannun Turawan nan suka yi a ƙasar Hausa.
Na
rantse da Allah ban ƙaunar
Nasara ko ka ɗan.
Allah
Ya gafarta Malam,
Na
taba karanta cewa shi Sarki Alu ne ya kirkiro Sango (explosive device)
domin yaki da mutanen damagaram.
Nasara
azzalumai ne makissata ne macuta ne mayaudara ne maɓarnata ne mazambata ne mahilata ne makirai ne...
***
Allah
shi gafarta, Sarki Alu Maisango/ Maje Lokoja a lokacin tafiyar shi Sokoto ne
Turawa suka shiga Kano kuma suka cita da yaki a 1903. Yazo Sokoto ne a lokacin
domin ta'aziyyar rayuwar kawun shi Sarkin Musulmi Danyen Kasko. Yana kan
hanyar komawa ne suka samu tabbacin an cinye Kano din.
Lallai
shi dan Saudatu ne diyar Sarkin Musulmi Alu, dalili kenan akayi mashi takwara
da kakan shi.
Shi
kuma wancan na Sokoton dan Garba III lallai babu shakka zai zama yaci sunan
Sarkin Kano Alu dinne. Kamar yadda a yankin Sokoto ake yawan ce ma Bello-
Maiwurno ko Buhari- Maijega ko Shehu- Malami
Madalla
da wannan ƙarin
bayani Mai Girma Dokajin Magajin garin Dikko Na Korau.
Kamar
shi ne ko kuma jama'arsa suka gwabza da Turawa a Ƙoramar Zorori/Mashigin Kwatarkwashi har ma Makaɗa Salihu Alasan Jankiɗi Rawayya ya taskace wannan gwabzawar a cikin Waƙarsa mai amshi "Ga Darajja Amadu Bello da arziki
na mazan jiya kay yi".
Fata
a Cikin Waƙar Fada
Manyan
malaman mu ban sani ba ko Malamin kiɗa Saidu
shi ma ya yi ma wani fatan zama Sarkin Musulmi, koma bayan Sultan Maccido. Misali
duk munsan Jankiɗi, in banda Sarkin Musulmi Abubakar III, mafi kusanci
dashi shine Sardauna Ahmadu. To, Jankiɗi
ya yi ma jama'a da yawa fatan su zama Sarkin Musulmi; irin su Maccido, Sarkin
Gobir Ahmadu Bawa, Sarkin Kudun Gusau Ibrahim da sauran. To, Saidu kuwa ya
rinka irin wannan fatar ga sauran yan Sarkin Musulmi, ko kawai ga Baba
Commissioner kawai ya tsayar da fatanshi?
Haka
ne Mai Girma Dokaji.
Shi
ma dai Sa'idu Faru ya yi wa masu alaƙa da sarautar Sarkin Musulmi fatar su gadi/gaji gidan,
sai dai ba kamar yadda ya fifita babban ubangidan nasa, Muhammadu Macciɗo ba.
Ya
yi wa Sardauna Ahmadu Bello da Sarkin Gobir Na Isa Amadu II, Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Tambari, Sarkin Yamman Faru
Ibrahim (Mai abu), Sarkin Yamman Faru Salihu, Sarkin Gabas Talata Mafara Shehu,
Sarkin Bauran Dange Ummaru Faruku, Sarkin Sudan Na Wurno Shehu Malami, Ciroman
Dange Ummaru Babuga Dange, Sarkin Tsabta Muhammadu Na Dange da sauran su.
Allahu
Akbar!
"Ƙoramaz Zorori wurin hwaɗa,
San
Kano ya tarbi Nasara...
Inji
Makaɗa Salihu Alasan Jankiɗi Rawayya.
MashaAllah,
Yallabai na gane. Lallai ashe shi daure bisar shi ta fata ba ga turken
Sarkin Kudu Maccido ba shi kadai.
Lallai
shi ma ya yi ma yan cikin gida waƙa sosai. To, ai Yallabai kusan ba wani Hakimin cikin
gida (Batoranke)da bayyi ma waƙa ba. Kila idan aka debe su Sarkin Gabas Goronyo, Sarkin Gobir
Gwadabawa bangaren su Sarkin Kudun Sifawa.
"Usumanu
ka hau halifag gadon Moyi,
Saura
halifag gadon Bello ɗan Shehu,
A
kira ka S/Musulmi Usumanu,
Da
mun ci ribaz zaman duniya kenan,
In
da dut an ka juya muna tare".
Yallabai
mu a karin harshen Katsinanci mu na kiransa da KIHIHIYA, amma a kamusu sun sa
KIFIFIYA, Allah ya sa mu dace
Ai
ina ganin saboda halin mu na maida 'fa' zuwa 'ha' ne ya kawo haka.
Kamar
yadda naga an yi bayani a sama. Misali mukan ce ma Funtua - Huntua (a baki
amma), Fanfarmi- Hwanhwarmi, Fartanya -Hwatanya, lafiya -lahiya dss.
Wallahi
babu na ƙwarai ga
iccen kabari. Sun fi kowa makirci da munafunci. Kada ka ba ɗayansu amana.
Dubi
yadda Dukansu suke bayan Isra'ila, amma suna kiran ƙasashen Musulmi da ƙawaye alhali suna ba Isra'ila makamai don su kashe
Musulmi. Isra'ila fa yau shekarunsu 75 suna mulkin wariya da mallakar Falasɗinu!Wai har wasu su fito suna cewa wai Falasɗinawa su suka fara tsokana, sai ka ce a Oktoba 7, 2023
rikicin ya fara.
Ahihiya
ko ihihiya a ƙasar Kabi.
Kunkuru
dabam "Ahihiya" dabam. Ahihiya har kujerar zama matan sarkawa kan yi
da ita da ranta. Yanzu haka akwai ta Gidan wani Bazabarme mai sayar da kifi a
Gidajen Tarayya na Arkilla Sakkwato.
Allah
Sarki. To shi kunkuru fa? Ba a zama a kansa?
Kihihiya
muke kiran ta, a karin harshen Katsinanci. Kihihiya ita ce macen kunkuru.
Uban
kiɗi yahihiya ya ce ba ahihiya ko kuhihiya ba. Yahihiya
ta sha bamban da kunkuru saboda bata zama tudu dangane da yanayin ƙafafuwan ta.
E
Malam ba a zama a kansa don ya yi ƙarami. Allah Masani.
A'a
Prof. Sai dai in ba ka taɓa ganin babban kunkuru ba. Ni kam na sha ganin babban
kunkuru.
[3:33am, 12/02/2024]: Kififiya/kihihiya, mu a
yankin Katsina ba' a iya zama a kanta saboda kankantarta Amma kamarsu daya da
Kunkuru saidai inka Lura akwai banbanci a halittar kofofin kokonsu daga gaba
daidai kofar kafafun da Kai na Kunkuru a hade yake na kififiya kuma akwai
tsakani kofar kafafun daban na Kai ma daban sannan ita kififiya tana kutsawa
cikin Kada mai turbaya musamman ma a karkashin shingen Gona a lokacin da ruwa
yake janyewa daga tafkin da suke chiki musamman daidai huduwar sanyin hunturu
kuma haka zataci gaba da zama karkashin kasa bata fitowa har sai damina ta fadi
sa tafito ta fada tafki,
Sannan
ita koda zata shekara nawa bata girman daya wuce girman kurtun dawadar malamin
Zaure, karka manta ita tana yatsu da farata kamar dai na Kunkurun kuma inka
Lura tana da dan wani tsigigin bindi a bayanta idan ta girma wannan ita mike
cewa Kihihiya a yankinmu na Katsina
[6:36am, 12/02/2024] Mal. H.U. Maikwari
Kullumen wajenmu bai da ƙaya sama. Muna
da kullume, akwai ramboshi.
[6:38am, 12/02/2024] Mal. H.U. Maikwari A
wajenmu (Kulwa), wannan shi ne ragon Nagwade dangin ƙaraye/ƙaraya ne
[7:48am, 12/02/2024]: Assalamu alaikum. Dangane
da shekarar da aka haifi Makada Sa’idu Faru, na dan yi karambani wajen tattara
ra’ayoyin masana a kan batun kamar haka, a Shekarar 1976 Makada Sa’idu Faru ya
ayyana shekarar da aka haife shi da cewa, an haife shi a shekara ta 1937, ya
rasu ke nan yana da shekara 50. Dutsin-Ma (1981) da Gusau (1988 da 2011) da
Furniss (1996) sun kawo cewa, an haifi Makada Sa’idu Faru a shekar 1932. Ya
rasu ke nan yana da shekara 55. A hirar da aka yi da Ibrahim Danmadami a gidan
rediyon Jihar Zamfara a shekarar 2019 da dan Makada Sa’idu Faru Malam Ibrahim
Sa’idu Faru a shekara ta 2020 da gidan jaridar leadership Hausa a shekarar 2020
duk sun ayyana cewa an haifi Makada Sa’idu Faru ne a shekara ta 1915/1916, ya
rasu ke nan yana da shekara 71/72 a duniya. Allah ya ji kan sa da rahama.
Idan
Allah ya kaddara mini yin rubutu a wannan taro, zan ƙara bibiyar wannan batu domin samar da matsaya
guda daya a takardar da za a gabatar in sha Allahu.
Dalibinku
Musa Labaran Muhammad.
[7:51am, 12/02/2024]: Hakan kuma, a wannan zaure
Honorable kuma malam Ibrahim Danmadami ya ƙara maimaita matsayarsa a kan shekarar da aka haifi
Makada Sa’idu Faru, kamar yadda ya bayyana a waccar hira da aka yi da shi.
[8:12am, 12/02/2024] Mal. B. Lauwali:
Yallai sannu da ƙoƙari, wannan dan waƙar a cikin wace waƙar Sa'idu Faru zan same shi? Na gode
[10:01am, 12/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Ƙi garaje Uban Shamaki Shehu,
Ɗan Muhamman Sarkin riƙon taro".
Wannan
☝️shi
ne amshin Waƙar da wannan
ɗan Waƙar ya fito. Waƙar Sarkin
Gabas Talata Mafara Shehu Muhammadu Ɗangwaggo ce, ya yi sarauta daga shekarar 1958 zuwa
rasuwarsa a shekarar 1969. Allah ya kyauta makwanci, amin.
@
Allah Rufa Asiri.
[10:59am, 12/02/2024]: Madallah da wannan kafa!
Muna ta kwasar ilimi a cikin dakunammu, Allah ya saka maku da alheri kuma ya ƙara sani.
Shin
wadannan dabbobi da tsuntsayen da Sarkin waƙa ya yi amfani da su a cikin wannan waƙar, zambo/habaici ne yake yi wa wasu 'yan sarki (idan
da 'yan saki yake, to suwa ne? ko yana bayanin dabi'u da halayen tsuntsayen ne.
A taimaka da Karin bayani. Muna godiya.
[11:19am, 12/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.
Malam
Bello Shehu Alkanci sannu da shigowa Zauren Taron Ƙasa da Ƙasa na Malamin Waƙa mai kwana ɗumi
na Mamman na Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru ɗan Abubakar Kusu mai Kotso ɗan Makaɗa
Alu Mai Kurya.
Allah
ya ƙara yi muna taimako, amin.
[11:25am, 12/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Dakta Sani Yahaya Mafara barka da warhaka dafatar kowa da komi lafiya. Kamar
manyan Malamammu sun ansa tambayoyinka tun shekaranjiya. Idan ka bibiyi
tattaunawar baya a wannan Zauren zaka samu amsoshin In Shaa Allah.
[5:39pm, 12/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M: "Bajinin gidan Abdullahi, Mai Martaba Zaki Na Abashe Sarkin Kano jikan Alu", inji Malamin Waƙa. Marigayi Mai Martaba San Kano, Alhaji Ado Bayero kenan riƙe da Tagwayen Masu. Allah kyauta makwanci, amin.
[5:52pm, 12/02/2024] " in sun ba ka kyauta
ka da ka amsa,
Dafi
na sun ka ba ka guba Annasara." Attahirun Ahmadu. Allah Ya gafarta masa. Don
gubar da Nasara suka feso mana tafi yawa a kan magani.
[6:13pm, 12/02/2024] Dr. H. Yelwa:
"Dan Audu sarkin manyan sarakuna kake
Kai ad da kammalallen iko Arewa
Kowa kac ce kana bida sai yazo. "
Amshi;
"Ado San Kano shirarre. "
Ina
mamakin abinda Saidu ka nuhi da ƙammalallen iko' a can. 👆🏽
[6:27pm, 12/02/2024] Dr. H. Yelwa: Saidu
na yi ma Sarkin Kudu Maccido kirari da;
"Na
Marahwa Danbaba maitura haushi
Na
Sarkin Gabas duniya hori wawa.:
[6:32pm, 12/02/2024] Dr. H. Yelwa:
Hakanan a cikin waƙag
"Gandon kasah Hausa", shi ma yana yi mai kirari da;
Na Marahwa Danbaba maihankuri
Kyautakka hat ta wuce godiya
Sai dai ace kai muna gahwara
Usumanu
sarkin rikon duniya...
[7:42pm, 12/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.
Wannan
Zauren tattaunawa ne akan Malamin Waƙa mai kwana ɗumi
na Mamman na Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru ɗan Makaɗa
Abubakar Kusu mai Kotso ɗan Makaɗa
Alu mai Kurya.
[8:10pm, 12/02/2024] Dr. H. Yelwa:
"Ban wuce gonata da irina ba
Inda
Sarkin Kudu nits tsaya. "
*
* *
Ba
mu wuce bitam mu da nazarinmu ba nanniya
Inda
Malamin waƙa munka
tsaya
[10:47pm, 12/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
"Gaba dai ka cira,
Baya na zuwa,
Wani bi,
Wata baya,
Ta
ɗara gaba".
Amshi: Toron Giwa ɗan
Abubakar,
Maifaru na Macciɗo,
Ma
ci gari.
[10:50pm, 12/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
"Kowacce maka sai ta kwana,
Kai ko ce ma shi sai tai yami,
Ya bar ce maka bai shirya ba".
Amshi: Dodo mijin maza ɗan Shehu,
Gagara ƙarya kana ban tsoro,
Alhaji
na Garba, Sarkin Rafi.
[3:51am, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya:/...
Mai da aboki baranka./
Haka
Mallamin waƙa ya ce. Ta
yaya ne mutum yake sa abokinsa ya zama baranda? Manazarta da masu sha'awar waƙa a wasa ƙwaƙwalwa don Allah!
[3:51am, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A
lura da ambaton "Gada" da Sa'idu Faru ya yi cikin wannan waƙa ba garin Gada na wajjen Illela kusa da Jumhiriyar
Nijer yake nufi ba. Wannan da Faru ke nufi da ya ce Gada, wani gari ne cikin ƙasar Bunguɗu. Na
taɓa zuwa garin har aka nuna mini wani masallaci da aka
ce Mallam Abdullahi ɗan Fodiyo ƙanen Shehu Usmanu ne ya nuna wa mutanen garin daidai
inda alƙibla take.
Ya isa garin ne lokacin da yake kan hanya zuwa aikin Hajji kafin ya isa Kano
inda jama'ar Kano suka tsayar da shi har ya rubuta wa Sarkin Kano littafinsa
mai suna Diyaul Hukkam. A nan mutanen Kano suka rarrashe shi da ya koma
Sakkwato bayan shi ma ya gano cewa abin da ya sa ya baro Sakkwato shi ne cewa
har nan Kano akwai shi, wato ɓarna, sai ya
yanke shawarar gara ya tsaya ya ci gaba da Jihadin da suka fara. Wasu sun ce
yayansa Shehu ya aika da a yi ƙoƙarin da
aka rarrashi ƙanen nasa
da ya dawo a ci gaba da jaddada Addinin Allah. Allah ne Masani.
[6:23am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
👍😁👌🙏 Sarkin Yamman Faru Ibrahim (Mai Abu) ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Abubakar/Bubakar ɗan Sarkin Rwahin Dosara Amadu Mai Dosara ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Alhaji ɗan Sarkin Ƙayan
Maradun Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi kenan. Allah ya
kyauta makwanci, amin.
[6:24am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Muna ƙara yi wa
Allah SWT godiya da ya dawo muna dakai lafiya cikin amincinsa. Allah ya ƙara yi muna kariya daga kowace irin musiba, amin.
[6:31am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
👍😁👌🙏.... Akwai Dagatai/Hakimai masu laƙabin Sarautar "Sarkin Rwahi/Sarkin Rafi guda uku
dake fittatu a yankin Sakkwato/Zamfara.
Sarkin
Rafin Dosara a Ƙasar
Maradun da Sarkin Rafin Bafarawa a Ƙasar Isa da Sarkin Rafin Kuryad Dambo a Ƙasar Shinkafi.
Wannan
Sarkin Rafin Dosara ne daga zuriyar Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da ya yi Sarautar
Maradun daga shekarar 1870 zuwa wafatinsa a shekarar 1874. Allah ya kyauta
makwanci, amin.
Tambaya
anan itace me Malamin Waƙa ke nufi
da wannan ɗan Waƙar "Kowacce maka sha ta kwana, kai ko ce mashi sai tai yami?.
[6:34am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ta hanyar karimci/kyautatawa/mutuntawa/ɗauke
nauyin lalurorin wanda/waɗan da yake tare dasu.
[6:47am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Muna ƙara godiya
sosai da ilimin da muke ta kwasa ahaha Allah ya gafarta Malam. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.
A
wannan wuri ne da ake kira Gada a Ƙasar Bunguɗu
ta Jihar Zamfara ta yanzu masu Jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular
Usmaniya daga Kano suka riski Jagororin Jihadin har ma aka naɗa Malam Sulaimanu a matsayin jagoran masu jihadin na
Kano.
Gada
wuri ne na Ribaɗi da ya yi suna sosai, daga nan ne Amirul Muminina
Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya jagoranci
jama'arsu zuwa Yaƙin Yandoto.
Laƙabin Sarautar Gada shi ne "Keku/Kekun Gada".
Kekun Gada Muhammadu Ɗantabawa
ne Malamin Waƙa ya yi wa
wannan Waƙar. Ajinsu
ɗaya da Marigayi Mai Girma Tsohon Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya, Alhaji Shehu Usman Aliyu
Shagari GCFR Turakin Sakkwato da Marigayi Mai Martaba Sarkin Yauri Alhaji
Muhammadu Tukur Abdullahi a Middle School ta Sakkwato. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau
da imani, amin.
[7:03am, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma
sha Allahu. Madallah da wannan bayani. Na ƙaru sosai. Allah Ya saka ma da mafificin alheri duniya
da Lahira Hon. amin.
Abin
da ya kai ni Gada shi ne, da ni da abokina muka tafi nemar wa wani
abokinmu mata.
[7:15am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Baban Mai Abu Faru na Mai'akwai,
Ɗangiwa komi tad daɗe ta
tabbata yin Giwa yakai,
Inji
S/Maradun S/Ƙaya"
[7:53am, 13/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A
gabaccin wannan masallacin akwai hubbaren wani Waliyi wanda har yanzu wasu ba
su daina ziyayarsa ba, sunan Waliyin shi ne Malam Dembo. An ce daidai inda
kansa yake ne wata itaciyar giginya ta fito! Kuma tana nan wurin har yanzu. Allah
ya jikan magabatanmu.
[8:01am, 13/02/2024] +234 803 397 1311: Wacce
irin ɓarna ce a Kano a lokacin ? A a adabin Ka kamar an ce
ya sami tarayyar ra'ayi da Abdussalam ne ?
[8:02am, 13/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Na sami
labarin cewa har daga wasu kasashen an yi zuwa don ziyarar hubbaren a garin
Gada, kuma ni da na taso nikan ga irin wadannan mutanen suna wucewa ta garinmu
suna zuwa Gada, ashe su ne masu zuwa Sakkwato hubbaren Shehu Usmanu Danfodiyo
suke fara ziyarar a Gada kafin su wuce.
[8:05am, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haka ne, Malam Dembo shahararre ne a Jihadin jaddada Addinin Musulunci na
Daular Usmaniya.
[8:57am, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Da
ma Mallam Abdullahi ya yi niyyar tafiya Hajji ne saboda ya ga mutane (magoya
bayan jihadin da suke yi) sun fara barin manufofin jihadi suna komawa ga
abubuwan da saboda a kawar da su ne aka ƙaddamar da da jihadin kamar tara dukiya da samun
ganima da jin daɗi. Abdullahi ya ga cewa 'yar gidan jiya ce za a koma
wa. Saboda haka ya yi niyyar guje ma haka, alhali bai san da cewa ba can
inda ya baro ba kurum wannan hali yake ba. Wannan shi nake nufi da "ɓarna". Ka kuwa san jama'ar Kano ba su zama dabam.
Domin
ƙarin bayani sai a duba littafin
Mallam Abdullahi mai suna TAZYIN AL WARAƘA. Ya yi bayani dalla-dalla
[11:36am, 13/02/2024] Prof. B.B. Usman:
Malama ko cikin waƙar nan ce
ambaci kalmar shege?
[12:38pm, 13/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Sarkin yamman Faru Salihu,
Da isowa tai ya yi lamba wan (one)
Wani ɗan sarki ya yi
lamba tu (two).
Ga wani Uban ƙasa ya ɓata
ƙawa,
Har na ga Makama
Ya yi tunzuri,
Ya ce.. su wuce da shi,
Dubi wani shegen naɗi
da yay yi,
Mahuta kunnuwa suka biya.
Maigirma
@Mal. I.M. D/Birnin Magaji a taimaka a gyara. 👆
[1:54pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Sannu da ƙoƙari Malama.
Kina
kan hanyarki daidai. 😁😅🙏
Makaman
Doka mai yan doka kenan.
Sarkin
Yamman Faru Salihu shi ya gaji/gadi Sarkin Yamma Ibrahim wanda Sa'idu Faru ya
fara Waƙarsa ta
farko a wajensa.
Dukansu
daga zuriyar Malam Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne. Sarkin Yamma Ibrahim daga gidan Sarkin Ƙaya Alhaj ɗan
Sarki Muhammadu Mu'alliyeɗi, shi kuma Sarkin Yamma Salihu daga gidan Sarkin Ƙaya Attahiru/Atto ɗan
Muhammadu Mu'alliyeɗi.
A
can baya na ɗora wannan Waƙar akan Sarkin Yamma Ibrahim Abubakar/Bubakar (Mai Abu
Faru), daga baya na ƙara
fahimtar ba tasa ba ce, ta wanda ya gaje/gade sa ce, wato Sarkin Yamma Salihu
Mahaifinsu Sarkin Yamman Faru Bello Ɗan Bello na yanzu. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[8:18pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora:
"Ya mirɗe
maza yanzu ba mai ƙara ja mai,
Y/Amshi: Kai
ab Bello kai ah Hassan,
Kai ad da kowa,
Jagora: Gazagurin
gidan Dange...
Y/Amshi: Duk
mai gaba da kai bai
bakwai bai sha kunu ba,
Ya mirɗe maza yanzu ba
mai ƙara ja mai,
Kai ab Bello kai ah Hassan,
Kai
ad da kowa,
Daga
cikin Waƙar
Marigayi Mai Girma Firimiyan Jihar Arewa na farko, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE
Sardaunan Sakkwato. Allah ya kyauta makwanci, amin.
Turken Waƙa: Ya mirɗe maza yanzu ba mai ƙara ja mai,
Kai ab Bello kai ah Hassan,
Kai
ad da kowa.
[8:19pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora:
S/shaggu ka rabka kuwa,
Kai taƙamab biri,
Kuma saki tukkuwa ta wala,
In na kiɗa
kai ko Maba
tadda gwarzon Sabongari nan dak kwana,
Kai Magajin busa ka zanki busa,
Da zamanin ana yaƙi na,
Jagora/Y/Amshi:
Maraɗi da bata kwan ukku,
In ba aljihun Abu mai saje ba,
Ginshimin S/fada ɗan
Iro na Malan,
Ubangijin
Garkuwa ɗan Muhamman mai daga.
Daga
cikin Waƙar
Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar/Hakimin
Gundumar Ƙaura
Namoda, Jihar Zamfara, Nijeriya, Abubakar Garba.
Ya
yi sarauta daga shekarar 1952 zuwa shekarar 1960 da aka cire shi. Allah ya
kyauta makwanci, amin.
Turken
Waƙa: Ginshimin Sarkin fada ɗan Iro na Malan,
Ubangijin
Garkuwa ɗan Muhamman mai daga.
[10:42pm, 13/02/2024] +234 802 687 2803: Gaskiya,
muna anfana da ilmi, Allah ya saka da mafificin alheri, ya Karo basira.
[10:44pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Sannu da ƙoƙari Malama.
Ki
turo Waƙar ko za a
samu waɗan da zasu gano muna abun da suke cewa.
[10:45pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:...
Kunnuwan Bika.../wani kalar Biri ne.
[10:46pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin, Allah ya ƙara lafiya
da nisan kwana mai albarka Allah ya gafarta Malam. Muna ta bautag godiya dai, muna
ƙaruwa sosai.
[11:07pm, 13/02/2024] Dr. H. Yelwa: Bika👉🏽Gorilla
[11:08pm, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A
fahimtata yana nufin duk halayen Sarkin Musulmi Muhammadu Bello da na S/M
Hassan duk Sardauna yana da su, saboda haka tamkar dai mulkin da Sardauna ke yi
irin nasu ne. Sa'idu Faru ya yi amfani da salon kinaya ne ya ce Sardauna shi ne
su, kamar a ce Sale zaki ne ko Amina damisa ce: ai ba ana nufin dabbobin ne ba,
sai dai halayen da Hausawa suka san waɗannan
dabbobi, zaki da damisa suna da, su ne Sale da Amina suke da > ƙarfi da sarauta; ƙin sabo da take da, da makamantan haka.
Makamancin
wannan salo na kinaya shi ne salon kamance, wanda ke cewa wane kamar wane ne. Salon
kamance bai yi cikar salon kinaya ba.
[11:09pm, 13/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
"Duk
mai gaba da kai bai bakwai,
Bai
sha kunu ba".
Wato
an yi ƙasa da
martabar kunu ke nan ko kuwa fushi/ɓacin
rai ake nufi?
[11:12pm, 13/02/2024] Dr. H. Yelwa:
Danmadami ya amsa tambayat a sama. Kunu a nan, ana nuhin ƙunun gidan yari'. Manuhwa, maigaba dashi bai kwana 7
ba a kaishi gidan yari ba.
[11:22pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:...
Ya kabre ƙawaw waɗan Gusau/Ya ɗauki
hayar ƙawar
tawagar Gusau domin ya ƙara
birgewa.
....
Makama ya tunzuri..
...
Ya ce Yan Nehu sun gama dashi.../kenan wannan taron an yi shi ne a lokacin
mulkin Sir Ahmadu Bello GCON KBE Sardaunan Sakkwato yana Firimiyan Jihar Arewa
kuma a gabansa aka yi taron/hawan kamar yadda Malamin Waƙa ya ayyana a cikin wannan Waƙar.
A
lokacin duk wanda aka ce baya goyon bayan Jam'iyyar NPC ta Sardaunan musamman
wanda ke riƙe da
madafun iko irin Dagatai da Hakimai da Sarakuna a Jihar Arewa ya shiga uku, kenan
Jam'iyyar Adawa ta NEPU ko AG (Action Group) ya ke goyawa baya.
Shi
wannan Dagaci da Makama ya yi wa tunzuri (Makaman Sakkwato, Alhaji Sani Dingyaɗi kenan. A lokacin Kansila ne babba a Majalisar Mai
Alfarma Sarkin Musulmi) har ma ya ce "Yan NEPU/Yan NEHU sun gama dashi abu
biyu ne: ko dai ya biyewa Yan NEPU dake yankinsa har ya zamo bai bi hanyar da
ta dace ba (biyar NPC) gashi har ya kasa taɓuka
wani abun kirki a irin wannan taron da Jagoran NPC ke halarta, ko kuma daga
cikin danginsa akwai masu ra'ayin NEPU da suka yi masa makaru har ya kasance
ana ganin laifinsa a hukumance daga gefen gwamnati mai ci a lokacin ta NPC. Allahu
Wa'alam!
[11:44pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Domin ya ce an yi taron ne a Giginya/Filin Wasa/Filin Sukuwa na Sakkwato da aka
alaƙanta da Giginya/Iccen
Giginyu/Giginyar da Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Attahiru I ya tarbi
Turawan Mulkin Mallaka na Ingila a Ranar 15/03/1903.
[11:53pm, 13/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Haka ne Hon.
Ni
da ina da iko da ba za a ƙara yin
sukuwa ko wata wasa cikin wannan fili ba. Ina ganin wulakanci ne Turawan Ingila
suka dasa muna, muna dirikkowa cikin filin da suka kashe kakanninmu. In
su kakannin namu sun yi bisa ga tilas, mu wace hujja muke da yanzu.
[11:58pm, 13/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ranka ya daɗe kamar ba a inda filin sukuwa/sitadiyam suke ba ne
filin dagar.
Daga
Dogondaji House zuwa Ƙoramar nan
ta Zoolane, zuwa gidan Mai Girma Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru
Ɗalhatu Bafarawa Garkuwan
Sakkwato waɗan nan itacen/bishiyoyin suke.
Kamar
Giginya Barracks da Giginya Memorial Teachers College da Giginya Hotel
suka ci wannan sunan, haka Filin Sukuwa da Stadium suka samu wannan laƙabi.
[12:23am, 14/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A
gaskiya ba haka na ji ba daga mutanen garin.
La'akari
da cewar akwai ƙorama a
wurin da ka yi magana ban zaton a shata filin daga kusa da nan. Ai inda Gidan
Gwamnati yake nan ne Turawan suka fara zama, ba su kuwa yin gida a filin da
suka ci Sakkwato domin za su yi mu'amala da Sarkin Musulmi da hakimansa, ka
kuwa san a kullum suka je gidan Rasdan ko D. O tilas su tuna da nan ne
aka karkashe musu jama'a. Sannan ka tuna da cewa a 1903, koma a shekarun 1960, filin
giginya nesa ne ƙwarai daga
Sakkwato, nan ne ake iya yin yaƙi da Dawaki, yaƙin da
kwatsam ya fara domin wasu daga cikin jama'a suna tattalin barin ƙasa ne sai kurum aka ji cewa abokan gaba sun iso, sai
aka bar batun tattalin guzurin tafiya aka koma na makamai.
Watakila
sai idan mun kawo hujja a rubuce sannan za mu iya tabbatar da ko kore wannan
hasashe. Zan duba littafin Waziri Junaidu mai suna TARIHIN FULANI la'alla in
samu haske. Akwai kuma THE SULTANS OF SOKOTO
[12:31am, 14/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Giginya Barraks da Giginya Memorial Teachers College da Giginya Hotel duk a
shekarun 1970 zuwa sama aka yi su.
Tuno
da waƙar Sarkin
Taushin Sarkin Katsina ta karɓar mulki ka ji
abin da yake cewa.
[7:52pm, 14/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji (Dr) Rilwanu Adamu a gefen hagu yake gaisawa
da Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji (Dr) Aminu Ado Bayero. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.
[7:53pm, 14/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji (Dr) Aminu Ado Bayero a gefen dama yana gaisawa
da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji (Dr) Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR. Allah
ya ƙara lafiya da nisan kwana mai
albarka, amin.
[8:00pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Ban je gidan dan giya niy yi roƙo ba
Ko
ya raba lahira ba ruwana😀
[8:05pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Na tsinci wata kamanceceniyar zance a tsakanin mawaƙa a waƙar nan. Malamin kiɗa ya ce "Ruwan
maliya sun wuce masu taru". Shi kuma Jankiɗi ya ce "an san ruwan da akan shiga ai iyo, kobbi ta maliya
ba shi gani waje"
[8:22pm, 14/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haka ne, sai dai Allah ya gafarta Malam wannan ba talla ba ce.
Hajar
Malamin Waƙa mai
kwana ɗumi na Mamman na Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru ce da ya ambata a matsayin kyautar da
Ubangidansa Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III ya yi masa.
Da
an bi ɗiyan waƙar da ke ƙarƙashin hoton da ake yi wa kallon talla ce, za a tsinci inda yake cewa
"Baba ya bamu bandur guda dun na lailai, ya bamu bandur guda dun na Yadi....
har zuwa ƙarshe, ƙila za a fahimci cewa an sako wannan ne domin a nusar
damu cewa ga irin bandur nan na Yadi da yake nufin Sarkin Kudu ya ba shi.
A
daina yanke hukunci ba tare da an bibiyi saƙonnin ba.
[8:23pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
A cikin waƙar an yi maganar
bandir na yadi, shine aka sanya don ya zama ya ƙara hasken fahimta da ƙara nishadin nazarin diyan waƙar
[8:26pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Maigirma Danmadani da sauran malamai suna yin hakan domin ya zama haske ko
dogaro wajen kawo diyan waƙa. Misali akan sanya hoton riga babba mai tsada don ayi ishara ga diyan
waƙa dake maganar kyautar kaya ko
kyankyandi da makamantan su.
[8:32pm, 14/02/2024] Prof. B.B. Usman: Ni
ina ganin bandir_bandir ɗin na fahimci amfaninsu a wajen gane saƙon cikin waƙar. Allah ya ƙara basira don tsarkin sunayensa.
[8:34pm, 14/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Ban je gidan ɗan
giya,
Niy yi riƙo ba,
Ko ya raba lahiya,
Ba ruwana
Ban
je gidan ɗan bita,
[8:35pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Allah shi gafarta Malama, ina ganin ko yana maganar "yan bita" ne. Watau
ma'aikatan Fidaburdi na da?
[8:36pm, 14/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Tooo, lahiya ce yake nufi a nan ba lahira ba. Angode da bayani Ma🙏😀
[8:43pm, 14/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Haka ne, an yi bayani kwanaki, ina zaton ranar Malam bai samu gani ba.
[9:11pm, 14/02/2024] Mal. Habibu Kaura: Assalamu
alaikum. Dangade da kalmar ɗan bita. Ina
tsammanin masu aikin godabe/titi/hanya na mota ko jirgin kasa.
[9:20pm, 14/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ina ganin an walwale wannan matsala. Ɗan giya Sa'idu Faru ki nufi. Zambo ne yake yi wa wani
da nufin mutumin ɗan giya ne, to me maroƙi kamar Sa'idu zai yi da zuwa roƙo gidan ɗan
giya tun da giya ce kurum zai ba shi, giya kuwa haramun ce ga Musulmi
[11:53pm, 15/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Mu koma Ƙaura ga ɗan Isau in aza kaya na", inji Makaɗa Sa'idu Faru a Waƙarsa ta Marigayi Mai Girma Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Abubakar Garba mai amshi ' Gwabron Giwa
na Shamaki baba Uban Gandu, Abu gogarman Magaji mai kamsakalin daga'. A wannan
wuri ne Malam Muhammadu Namoda ya kafa Bukkarsa dake nuna ƙirƙirar Garin Ƙauran
Namoda a cikin shekarar 1807. Ya zuwa yanzu a wannan wurin ne Fadar Mai Martaba
Sarkin Kiyawan Ƙauran
Namoda take. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[12:07am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Na zaka in gaka in yi mubayi'a, Masa'udun Ƙaura Amadu" inji Mai kwana ɗumi na Mamman da Balaraba, Makaɗa Sa'idu Faru a faifan da ya yi wa Marigayi Mai
Martaba Sarkin Kiyawan Ƙaura
Namoda, Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Muhammad Asha (ya yi Sarauta daga shekarar
1960 zuwa rasuwarsa a shekarar 2004) mai amshi 'Na Magaji Ƙanen Sarkin Ƙaya, Shugaban Alibawa Amadu'. Wannan shi ne Marigayi
Mai Martaba Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Alhaji Ahmad Muhammad Asha, Allah ya kyauta
makwanci, amin. 🤲🏾🤲🏾🤲🏾
[12:11am, 16/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Na taɓa zuwa Ƙaurar Maida har Fadarsa na yi gaisuwa
[12:18am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Allahu Akbar!!! Akwai Hubbaren Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ummaru Ɗan Sarkin Musulmi Aliyu Ƙarami Ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan
Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio
tagammadahullah birahamatihi a fadar Ƙaura Namoda.
Anan
Allah SWT ya yi masa wafati a shekarar 1891. Anan kuma aka naɗa wanda ya gaje/gade shi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi
Abdulrahaman da aka fi sani da Ɗanyen Kasko. Allah ya jiƙan su da rahama su da sauran magabatanmu, ya sa mu
wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
[12:20am, 16/02/2024] +234 803 639 8040: Amin ya
Hayyu ya Ƙayyum.
[12:28am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Ƙwahak
Kuturu mutuncinta takalmi, radda dub bai dasu ba ya jin sosai" inji
Malamin Waƙa a
faifansa na Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar Gundumar Talata Mafara, Sarkin Gabas Alhaji Shehu
Muhammadu Ɗangwaggo
mai amshi 'Ƙi garaje
Uban Shamaki Shehu, ɗan Muhamman Sarkin riƙon taro'. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[6:48am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Za a same ta In Shaa Allah Allah ya gafarta Malam 🙏🙏🙏
[6:49am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Ana ta tsoron ka
kai ba ka jin tsoro,
Baba
halin Abu kay yi mai Raɓah.
[6:49am, 16/02/2024] Dr. S.S. Abdullahi:
A taimaka min Hon! Shin ba ya Jin sosai yake ko ba ya Jin daidai?
[6:51am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ma'anar ɗaya ce, wajen zaɓen
kalmar ce ya nuna ƙwarewa.
[6:52am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Gadan-gadan kay yi uban Zagi Buba,
Usumanu ka hau halifag gadon Moyi..
[6:58am, 16/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Allah sa wani zai fito mana da wata muƙala da ke baje falsafar Hausawa cikin waƙoƙin Mallamin Waƙa Sa'idu
Faru.
[7:01am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Karen masara daɗai ba ya yin gyamro,
Yaushe talakka ka haihwa ɗan Sarki,
Bunsuru
ba ya yin layya ga Rago.
[7:05am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Ƙi garaje Uban Shamaki Shehu,
Ɗan Muhamman Sarkin riƙon taro.
[7:06am, 16/02/2024] Dr. S.S. Abdullahi:
*yaushe talakka ka haihuwar Sarki, kamar Karin waƙar ya kare, idan an ce "yaushe talakka ka
haihuwar Dan Sarki" Prof. A. B da Prof. Dunfawa ku agaza muna.
[7:06am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Sarkin Gabas Talata Mafara Shehu Muhammadu Ɗangwaggo kenan. Ɗan Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan
Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi. Ya yi sarauta
daga shekarar 1958 zuwa rasuwarsa a shekarar 1969 sanadiyar gobara.
Sarkin
Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III ya yi Hakimci a Talata Mafara kafin a
kawo Sarkin Gabas Shehu. Shi ya zo a shekarar 1953 zuwa 1956. Bayan ya tashi sai aka kawo Marafan Gada
Aliyu, ya shekara biyu 1956 zuwa 1958.
[7:11am, 16/02/2024] Alhaji Badamasi Sarkin Ƙaya Maradun.: ALHAMDULILLAH, rankai dade. Muna karfe
1:10 na dare.. ku yini lahiya mu kuma mu kwana lahiya
[7:11am, 16/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A
kullum ina tunanin cewa cikin karin magana ne Baushe ya sha adana falsarsa. Da
kuma manazarta suna mai da hankulasu a nan da sun taimaka wa ɗalibai daidaita bincikensu, ga ɗora shi kan ra'o'i marasa dangantaka da rayuwar
Hausawa, ko mu samu mu kuɓuce daga ƙangin Turawa.
[7:13am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Daga nan sai Sarkin Gabas Shehu zuwa 1969. Sai Sarkin Gabas Mu'azu Lamiɗo ɗan Sarkin
Musulmi Hassan ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio har zuwa 1975/76 lokacin da sarautar ta dawo
gidan Zamfarawa/Gidan ta na asali aka naɗa
Muhammadu Barmo ɗan Sarkin Mafara Aliyu. Bayan ya rasu a Shekarar 1996
sai aka naɗa ɗansa Alhaji
Bello Muhammad Barmo OON, Sarki mai ci yanzu.
[7:16am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Kafin zuwan Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo a
Mafara, Mahaifinsa Sarkin Musulmi Abubakar III ya yi Hakimci a Mafara na 'yan
watanni da laƙabin
Sarautarsa ta Sardaunan Sakkwato a cikin 1938 gab da ya zama Sarkin Musulmi.
[7:18am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Bayan Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo
ya zama Sarkin Musulmi a watan Afrilu na shekarar 1996 babban aikin da ya fara
aiwatarwa shi ne naɗin Sarkin Mafara, Talata Mafara Alhaji Bello Muhammad
Barmo OON da Sarkin Ɓurmin
Moriki Alhaji Sama'ila Muhammad Ari II.
[7:20am, 16/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Sannu da ƙoƙari Yallabai na fiddo tarihin da ke lunke a cikin
wakokin Malamin Kida. Lallai duk idan aka bi diyan wakokin shi to, za a dace da
samun bayanai na tarihi kamar yadda Maigirma Danmadani yake ƙoƙari ainun wajen fiddo su. Hakan shine gishirin fahimtar wakokin a yayin
nazarin su, domin an bude ma mutum su a fili an maida su kamar film yana kallon
duk yadda akayi.
[7:24am, 16/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Malam Yusufu Yunusa da kuma Dokta Hadiza Sa'idu Koko sun tattara karin
maganganu da yawa tare da bayanai masu kyawo. Ana iya zurfafa bincike a kan
wannan tunani na Falsafar Mallam Bahaushe
[7:24am, 16/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Yawancin duk garuruwan da yan Sarki ke mulkin su a Sokoto, wanda kuma kusan duk
Sa'idu ya wake su, T/Mafara ce nike ganin a mayar da ita ga ainihin wanda suka
fara mulkin ta. Ita Kuma sai ina zaton haka ya faru saboda ba da karfi aka
amshi mulkin ba. Duk da sunyi bore a wani lokaci dab da zuwan Turawa, hakan bai
sanya an dauke su ba a matsayin wanda aka sauya mulkin su ba karfin takobi.
[7:26am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Gusau ma an mayar da sarauta a gidanta na asali a shekarar 1984 lokacin da aka
naɗa Alhaji Muhammadu Kabir Ɗanbaba OFR.
[7:27am, 16/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Haka ne Yallabai, duk da daman ita ta Mallam Sambo ce kuma shi ma duk mujahidi
ne.
[7:27am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ɗansadau ta sake komawa ruwa a cikin
shekarar 2022 bayan an cire Sarkin Kudu Husaini Umar.
[7:28am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haka ne sai dai ba bani Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ba ne, ɗan
Malam Muhammadu Ashafa ne, Bafulatanin Yandoto.
[7:30am, 16/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Haka fa Yallabai. Ko Saidu ya yi ma su waƙa kuwa. Ina nufin irin su Muhammadu Maiakwai da Sarki
Kabiru. Nasan dai Jankiɗi ya yi ma Maiakwai wakoki masu daɗi, to ban san Saidu ba.
[7:34am, 16/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Sa'idu bai shiga Fadar Gusau ba, sai ya wuce zuwa Ƙaura Namoda da Zurmi da Gabake da Birnin Magaji da
Banga da Isa da Sabon Birni da Bafarawa.
[7:35am, 16/02/2024] Major A.M. Mairuwa:
Ranka ya dade lallai Saidu yana da basirar da idan aka bibiyi wakokin shi daga
janibin Falsafar Bahaushe, za a samu abubuwa da yawo. ya yi ƙoƙari sosai wajen kawo irin wadannan karin magana da yin kamanceceniya
wajen fidda bayanai masu dauke da ma'anoni. Misali a waƙar "Abubakar na Ahmadu baban Galadima.. "
inda yake maganar namun daji da kalar su da dabi'un su.
[1:17pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Ina cikin daji sai Gyado ka saƙƙwata ta....
[1:50pm, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: In an
samu waƙac can ta
Dan-Alin Birnin Magaji a turo muna.
[8:15am, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Sarkin
Sudan na Wurno Zaki,
Y/Amshi: Sarkin
Sudan na Wurno Zaki,
Gogarma Shehu na Ali
Muzakkarin Sarki ɗan
Abdu,
Abun biya Shehu na Ali
Jagora: Shehun
gidan Hassan ɗan Mu'azu,
Y/Amshi: Katakoron
Matawalle,
Jagora: Don
kasan sai an ci Talata,
Y/Amshi: San
nan Larba ka isowa
Muzakkarin Sarki ɗan
Abdu,
Abun
biya Shehu na Ali
Marigayi
Mai Girma Sarkin Sudan Na Wurno, Alhaji Shehu Malami ɗan Sarkin Sudan Na Wurno Bello ɗan Modibbo Usman ɗan
Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi. Ya zama Sarkin
Sudan Na Wurno a shekarar 1973 har zuwa shekarar 1989 da ya yi murabus na ƙashin kansa. Ya rasu a ranar 20 ga watan Disambar 2022.
Allah ya kyauta makwanci, amin.
[8:15am, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Mu'azu
kullun mahwalki ni kai sabo,
Y/Amshi: Shehu
ya ba mu doki da kaya nai,
Jagora: Daudu
kullun mahwalki ni kai sabo,
Y/Amshi: Shehu
ya bamu doki da kaya nai,
Danda hwari biyat wanda an nan haka,
Inda Liman ka bi zai Masallaci,
Koma shirin daga na Muhamman Bello,
Shehu
ɗan Shehu ganɗon ƙasah hausa,
Wannan
Dokin shi ne ake kira Danda Fari biyar domin farin da ke ƙafafunsa duka guda 4 da farin dake a goshinsa. Wani
kuma bayan fari a ƙafafunsa
ana iya samun fari a cikinsa a maimakon fari a goshinsa.
Daga
cikin Waƙar
Marigayi Mai girma Sarkin Gabas Talata Mafara Shehu Muhammadu Ɗangwaggo waɗannan
ɗiyan Waƙar suke. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[9:20am, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: A nan
Saidu Faru ya hwara da kawo tunanenai na dokin da yad dace a ba shi.
Danwaƙad da yab biyo shi, shine na rokon dokin karara, tare
da nuna cewa doki ne wanda duw wani karamin sarki bai yarda ya bayad dashi.
"Doki nika so Baban Majidadi baban kanwa na
kilisas swahe
Shi Hakimin kauye ab bai iya kyauta
In ya samai sai bargatai
Hay
yasa hannuwa yai ta shahwatai. "
Dud
dai don dokin ya hito, sai yat tunzura Sarkin da cewa;
"Manyan
kaya manyan ganwo
Sarki
shi aka roƙo doki
Kyakyautani
uban Majidadi
In
bada tsoro ga kauyenmu in nazo. "
[9:25am, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
👍😁👌🙏... Cimcintani Uban Majidadi..../kyauta asin da asin/kamalalliyar
kyauta da ba abar komai a gefe ba.
[9:35am, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: At!
'Cimcimtani'. 👆🏽😄
Hausa
ba dabo ba. Madallah da wanga gyara Onorabul.
Da
hwatab babu lauje cikin nadi ga maganatai ta Hakimin kauye bai iya kyautad doki
da kuma abinda yab biyo baya cewa a cimcimtashi ya bada tsoro ga kauyensu in
yazo.
[10:23am, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ai a cikin wani Version na Bakandamiya/Baba Uban Gandu ya yi nadamar fara roƙo a Ƙauye. Ya ma faɗi cewa ƙurciya ce ta ci su har suka ɓata lokacinsu can baya wajen roƙon Sarakunan Ƙauye, ga inda ake kyautar ƙasaita ba su gano ba sai daga baya.
[10:28am, 17/02/2024] Alh. A. Nakawada: A
waƙar Turakin dan Hashim Jikan
Dabo Bangon Dutsi, Dankwairo ya ce:
"Kowa ya kuka da arziki nai
Da ƙauye da birni dud ɗai ne
In
Allah Ya sauwaƙa ma"🤷♂️😬
[1:13pm, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: Yawwa.
Saboda, ba ga wagga waƙab ba kaɗai, Saidu ya hwa rena hakiman kauye. Ƙilan hwa da azazza. Ji nan;👇🏽
"Maibiyas sarkin kauye wawa na
Shi miyac ci bi zashi ba taro
Yak
kasatai kwatancin ta Garbadu. "
[1:16pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haka hwa yac ce Mai Girma Waziri.
A
cikin Waƙar Ɗan Alin Birnin Magaji Muhammadu Mode Usman kuma yana cewa
"Ɗaukan ni
ka goya Ɗan Korau, don
kada kabab baƙauye ya
wahalsan".
[1:17pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Ina
cikin daji sai Gyado ka saƙƙwata ta....
"Daudu
da duy yag ganan ya buɗek ke haƙori...
"Abun
biya kake ɗan Shehu,
Alhaji
Ɗan Ali ci fansa.
Shi
ne ☝️amshin
Waƙar.
Ya
zo da ita Birnin Magaji a cikin late 1970s.
[1:49pm, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: Yawwa.
Ka ga hasashen nan na azazza da hakimin kauye yana ta hitowa.
[1:50pm, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: In an
samu waƙac can ta
Dan-Alin Birnin Magaji a turo muna.
[1:54pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A keɓance Makaɗa
Ibrahim Sa'idu Faru ya sheda mani cewa dara ce ta ci gida a wannan karon.
Akwai
wani ɗan yamutsi da Malamin waƙa ya yi da maigarin nasu sai aka taskace shi a wannan
Waƙar.
[1:56pm, 17/02/2024] Alh. A. Nakawada:
Rankaidade wai me yasa bakandamiyar Sa'idu ba ta yadu sosai kamar sauran
manyan wakokin shi ba?
[2:02pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Nima na lura da hakan duk da yake na kasa sanin dalili Mai Girma Ɗanmaliki.
[2:18pm, 17/02/2024] Dr. H. Yelwa: Mhn!
Ni hwa na san 'ruwa ba su tsami banza'.
[2:27pm, 17/02/2024] Alh. A. Nakawada: Ko
ya riga yin wadancan manyan wakokin ne, kafin ya yi ta?
[2:34pm, 17/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ita ma ta daɗe domin ya yi ta tsakanin 1952 ne zuwa 1960.
[2:35pm, 17/02/2024] Alh. A. Nakawada:
Wai-wai. Lallai tsohon bugu ne.
[2:40pm, 17/02/2024] Alh. A. Nakawada: Na
samu labari ashe a cikin tawagar Sa'idu akwai wani yayan shi. Shi ba ya qarin
waƙa.
[6:16pm, 18/02/2024] +234 706 685 1000: Don
Allah Sa'idu Faru yana da Diya da Jikoki a raye? Idan akwai su, suna waƙa da kida?
[8:38pm, 18/02/2024] www.amsoshi.com:
Ire-iren waɗannan tambayoyi na da matuƙar muhimmanci. Duk masu bincike kan Makaɗa Sa'idu Faru na iya turo tambaya kan wani lamari da
ya shige musu duhu. Insha Allah malamai da dama da ke cikin wannan zaure a
shirye suke da su ci gaba da ba da gudummawa wajen ilimantar da mu.
Bannan
burinmu shi ne, kowace takarda ta zo da cikakken inganci yayin wannan taro. Wannan
gata ce gare mu.
Samun
bayanai kyauta🕺
Samun
interviewees kyauta 💃🤪
[8:39pm, 18/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
yana da ɗiya da jikoki maza da mata suna nan raye. Wasu a Faru,
wasu kuma a wasu garuruwan.
Alhaji
Ibrahim Sa'idu Faru wanda ɗansa ne mai
kimanin shekaru 65/66/67 a duniya shi ke jagorantar tawagar Kiɗa da Waƙa ta gidan Marigayi Makaɗa Sa'idu Faru.
In
Shaa Allahu zai halarci wannan Taro namu da muke tattaunawa akai.
[8:46pm, 18/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
".. Uban Tudu,
Sarkin
ɗaukar taro". In ji Sa'idu Faru.
In
Allah ya so wannan 'take' FUG za a yi wa shi. 🙏
[9:04pm, 18/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haka hwa yac ce Allah ya gafarta Malama!
Lalle
FUGUSAU ta zama "Sarkin/Sarauniyar ɗaukar
Taro😁🙏
[9:17pm, 18/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Haka ya faru ne domin, aƙalla ni
dai, a ja hankalinku masu shiryawa cewa ana iya kawo muku cikas daga waɗanda ke adawa da ƙudurinku.
[9:24pm, 18/02/2024] Dr. H. Yelwa: Akwai
wani matashi a wancan lokacin da ya kan karbi waƙa in ana yi a cikin tawagat ta Saidu Faru.
A
cikin wata waƙas Sarkin
Kudu Maccido yana cewa;
"... Wani 'andizarabul elemen' (undesirable
element) sai yas soke motat
Motan nan da za a bani
Na
barma kaba ubanka. "
Ko
shine a' Ibrahim din maijagorantat tawagat a yanzu?
[9:31pm, 18/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Shi ne fa Maigirma Waziri. A can in the background zaka ji Malamin Waƙa yana cewa "A gaishe ka Malan Ibrahim" a
cikin wasu Waƙoƙinsa inda shi Alhaji Ibrahim ke ƙari.
[9:42pm, 18/02/2024] Dr. H. Yelwa: Yawwa,
Onorabul Danmadami.
Lallai
ni kan jishi yana kawo kalmomin turanci;
".. Emiret kaunsil (Emirate Council) ta shirya
babban taro
Kuma tayi kiran 'yansarki
Su kau sun karba kiranta
Wani tandarkin bakauye
Yac
ce masu bai tahowa".
[9:46pm, 18/02/2024] Dr. H. Yelwa: 👆🏽Wasu
daga cikin tawagas Saidu Faru.
[9:47pm, 18/02/2024] Dr. H. Yelwa: Na 3
daga dama: Malamin waƙa
Na
‘2 daga dama: Muazu
[3:12pm, 19/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Harshen Hausa yana samun sauye-sauye saboda dalilai da dama. Wasu daga cikin waɗannan sauye-sauyen tubarkalla ne, wasu kuwa gara/... a
ba dillaliya/, in ji mawaƙi Alhaji
Garba Gwandu.
Daga
cikin waɗanda suke gara a ba dillaliya akwai "tawaga".
Sauyin da aka samu, musamman daga 'yan jarida, shi ne na ma'ana, watakila
saboda a yau an daina yaƙi da
dawaki. A da da ake yaƙi a kan
dawaki da takobi da masu, idan wata ƙungiyar yaƙi ta al'umma ɗaya
ta tsere wa ƙungiyar
abokan gaba saboda an fi ƙarfinta, wannan
ita ake kira "tawaga". Wato ɓangaren
rundunar yaƙi da ya
fashe. To amma yau sai ma'anar tawaga ta sauya zuwa daidai da "ƙungiya". Misali, yadda aka kira mutanen nan na
cikin hoto.
[3:58pm, 19/02/2024] Alhaji Badamasi Sarkin Ƙaya Maradun.: Akwai diyanshi da jikokinsa a garin faru
dake karamar hukumar mulki ta maradun, jihar zamfara.
Takanas
daga nan Jihar Marland na yi waya da wani dan sa..
[9:40am, 20/02/2024] Mal. Birnin Magaji Ibrahim
Muhammad: "Muhammadu Bello jan damishi ɗan
Abdu Jatau" inji Sa'idu Faru a waƙarsa mai turke 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai ' ta Marigayi Mai Alfarma Sarkin
Kudun/Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Macciɗo
Abubakar III. Muhammad Bello ne sunansa na yanka, Macciɗo alkunya/laƙabi ne, Abdu Jatau Sardaunan Sakkwato kenan kafin a naɗa Sarkin Musulmi Abubakar III wannan sarauta ta
Sardauna wacce shi kuma ya baiwa Sir Ahmadu Bello ita a shekarar 1938 da ya zama
Sarkin Musulmi. Abdu Jatau tare suka yi neman sarautar Sarkin Musulmi da
Abubakar III da Sir Ahmadu Bello da Sarkin Gobir na Isa Amadu I (Amadu
Bawa)maigidan Makada Narambada da Sarkin Kudun Sifawa Muhammadu. Abdu Jatau ya
riƙe sarautar Sarkin Gobir na
Gwadabawa bayan ya bar sarautar Sardauna. Ya fito ne daga gidan Sarkin Musulmi
Abubakar I (Abubakar Atiku/Mai Katuru) ɗan
Mujaddadi Shehu Usman Danfodio.
[9:44am, 20/02/2024] Mal. Birnin Magaji Ibrahim
Muhammad: *Sarkin Musulmi Abubakar III ya fito daga gidan Sarkin Musulmi Mu'azu
ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio ne. Sir Ahmadu Bello
ya fito daga gidan Sarkin Musulmi Abubakar II (Abubakar Mai Raɓah) ɗan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio.
Sarkin
Gobir na Isa Amadu I/Amadu Bawa ya fito ne daga gidan Sarkin Musulmi Aliyu ƙarami ɗan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio. Shi kuma Sarkin
Kudun Sifawa Muhammadu ya fito ne daga gidan Malam Muhammadu Buhari ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodio. Allah ya kyauta
makwancinsu su da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da
imani, amin.
[10:24am, 20/02/2024] +234 706 685 1000: Ko
Sa'idu Faru ya yi zurfi a cikin ilimin boko dana muhammadiya?
[10:32am, 20/02/2024] Mal. Birnin Magaji Ibrahim
Muhammad: Bai yi karatun boko ba, karatun muhammadiya kuma ya yi gwargwadon
hali.
[11:11am, 20/02/2024] Mal. Birnin Magaji Ibrahim
Muhammad: *Ya faɗa a wata hira da Malam Hamza Sanusi Funtua ya yi dashi
a wani shiri mai suna "Daga bakin mai ita" a gidan rediyon gwamnatin
Jihar Kaduna (KSMC na yanzu), ranar 15/8/1970 cewa tun bai fara saka
bante/bance ba mahaifinsa ya fara fita dashi zuwa sabgar kiɗa da waƙa.
Ya
ce ya kan aza shi akan dokinsa idan zasu fita wajen wannan sabgar. Wasu lokutan
yana amshin waƙa yana gyangyaɗi sai mahaifin nasa ya ɗan dangware shi sai ya farka ya ci gaba. Allah ya
kyauta makwanci, amin.
[8:37pm, 21/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Assalamu Alaikum Warahamatullah Wabarakatuhu. Yan Uwa barkanmu da warhaka, don
Allah ko ya sunan wannan Dokin?
[8:46pm, 21/02/2024]: Assalamualaikum yaa ku
jama'ar wannan zaure mai albarka, Ina ƙara godiya bisa dinbin ilmoma nafede waƙaoki da kuma bayyana muna hikimomin mawaƙan Hausa.
Bayan
wannan ga wata tambaya a man fassara: minene fassarar wadannan kalmomi: 1metaphor
2 personification 3 Irony, 5Hyperbol (exerggeration)? na yi wannan
tambaya be saboda na ga suna da alaka da sharhin wakoki ko rubutattu ko na baka.
Ina sauraronku yaa ku Malamai na da sauran masana a cikin wanna zaure mai tare
da ma'ilmanta da kuma manazarta.
[8:56pm, 21/02/2024] Prof. B.B. Usman: 1.
Siffantawa/kinaya metaphor 2. Mutuntarwa personification 3. Irony......... 4
Kambamar zulaƙe
hyperbole. A yi mana gyaran fassarar.
[9:16pm, 21/02/2024] +234 803 257 6475: Ina
godiya Drs and Profs. Allah Ya karama rayuwarku albarka Mai tarin yawa.
[10:18pm, 21/02/2024] Prof. A.B. Yahya: (3)
irony > habaici/gatse.
Wadannan
kalmomi biyu su ne masana suka bayar. Sai dai ni ba da alfahari ba ne fi yarda
da kalma ta biyu, wato gatse.
A
duba Bargery, sh. 372, da sh. 1188; Muhammad, sh. 27.
Duk
fassarar da Prof. B. B. Usman ya bayar ta yi muwafaƙa da ta manyan malamai, Ɗalhatu Muhammad da ɗalibinsa
Abdulƙadir Ɗangambo a nazarin waƙa da ma adabi gaba ɗaya.
Tuni
"kambamar zulaƙe" ta
samu takwara tsakankanin manazarta, wato "kambamawa" kai tsaye.
[4:21am, 22/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Yaro in taƙamas salon
magana
kaka yi ce tsare tsara
Y/Amshi: Tahi tsantsame tsantsara ka tsantsame tsari tsab ga
tsamiya
Jagora: Yaro in taƙamas salon magana kaka yi ce tsare tsara
Jagora/Y/Amshi: Tahi tsantsame tsantsara ka tsantsame tsari tsab ga
tsamiya
Jagora: Tunkuɗa tunku cikin
tukar rukuɓu tukuɗin Tumba yai tuɓus
Y/Amshi: Tumba taho yau dake da Taɓo da Taɓus
da 'Yat Tuɓus
Gwabron
Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo
Ginshimi,
Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi
[3:50pm, 22/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Waƙar Makaɗa Sa'idu Faru ta farko bayan ya fara jagorancin Ƙungiyar Kiɗa
da waƙa ta
gidansu.
Dagacin
Ƙauyensu (Faru), Sarkin Yamman
Faru Ibrahim Abubakar ne ya yi wa ita. ☝️
[4:01pm, 22/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Alhamdulillahi wallahi na yi neman waƙar nan, har na gaji Na so ayi tsokaci, a kan salon kiɗan, don ya yi kama da bandiri/mandiri. Ya bambanta
da amon kiɗansa. Ni dai har rangaji nake yi.
[4:06pm, 22/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
"Sarkin yamma,
Inai maka hwata,
Ya Allah ya yi ma 'Tabaruka',
Don girman lawalli da risala,
Don hasken yassin da muƙama. "
Wannan
ta sa na tuna da Narambaɗa mai "Tabarukin sarki".
[4:15pm, 22/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
To amma ma'anar Tabaruka a waƙar Narambaɗa, an ce tana nufin ƙyautar tuɓe',
wato nan take sarki ya shiga ya cire tufafin dake jikinsa, ya bawa maroƙi shi kuma ya saka. Ya samu albarkar gumin sarki.
To
amma anan haka Faru yake nufi? 🙏
[5:40pm, 22/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
"... har rangaji nake yi"
Wannan
shaida ce cewa waƙar tana a
mataki na ɗaya na kyawo, aƙalla wajenki. Sa'idu Faru ya fara da ƙafar dama
[6:33pm, 22/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Salon ƙarangiya
> jejjera kalmomi ko furuci cikin waƙa da ke da wuyar faɗi, kuma
wani lokaci akwai ma'ana, wani lokaci babu ma'ana.
Manufa
dai ita ce mutum ya iya furtawa cikin sauri ba tare da kuskure ba ko ƙagewa ba.
[6:35pm, 22/02/2024] Prof. A.B. Yahya: A
lura da cewa akwai ɓangaren adabin da ake kira gagara-gwari. Shi ma akan
sanya shi cikin waƙa. Ɓangare ne na Adabin Hausa
[9:20pm, 22/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Dr
Bunguɗu ba haka ne ba. Ai kalmomin Larabci suna da yawa
cikin Harshen Hausa. Sai kuwa in cire su za mu yi sai mu koma ga Hausa tsintsa.
To kuma ka lura da cewa akwai kalmomin Ingilishi da Yarbanci da ma na
wasu da ban faɗi ba da dama cikin Hausa.
Idan
kuwa har muka yi haka nan to Harshen Hausa zai mutu. Mafita ita ce a yi aiki da
hankali da natsuwa.
[11:30pm, 22/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Haka ne
Malam, ai na dauka saboda asalin nazarin rubutacciyar waƙar Hausa an yi amfani da salo ko hanyoyin Larabawa ne
don haka tun na wakokin baka namu ne sai aka samar mana wata hanyar daban, a ciki
har da yunkurin a samar mana da sunayen kamar baiti zuwa da ko baitoci zuwa
diya. Amma yanzu na fahimta cewa ba hakan take ba, na karu da wannan ina godiya,
Allah ya ƙara hasken
makaranta.
[7:00am, 23/02/2024]: Haka ne Allah gafarta
Malam, Fannin nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa su ke6anta da kalmar ɓaiti’.
Haka kuma, hanyar nazarin waƙoƙin baka su
ke6anta da kalmar ‘ ɗa ’.
Makaxan
baka na Hausa ne suka fara ba da haske a kan kiran gun-gun saɗaru ko layuka a woƙoƙinsu a matsayin ɗa. Alal misali, Makaɗa Sa’idu Faru yana faɗa a cikin wani ɗan waƙa a waƙar
Muhammad Tukur Sarkin Yawuri, inda yake cewa:
Jagora: Ga
waƙa nan wadda nay
: yi maka,
‘Y/Amshi: ɗa
Tara ta mun bar
: takwas
gida,
: Sai in kai
murnar zakkuwanmu,
: In aika ko
yanzu su taho,
: Mu ka kiɗi mu ak kiɗi
sabod mu,
: Allah yay yi wa gudummawa,
: Da waƙa ga wata na ije wata.
[7:48am, 23/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
@~MUSA KANO❤️❤️❤️ daga ɗan waƙar da ka kawo:
"Ga waƙa nan,
Wadda niy yi ma,
Guda Tara ta,
Mun
bat takwas gida... "
Ta
nuna waƙa makaɗin yake magana ba ɗan
waƙa ba. Kenan kalmar 'ɗa' a nan ba ta wakiltar saɗara ko layukan waƙa. Shi ne abin da Prof. yake so a dandaƙe. 🙏
[8:54am, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Madalla Malam Musa, sannu da ƙoƙari. Allah
ya saka da alheri, amin.
Kamar
Malamin waƙa yana nufin
waƙoƙi ne ya yi wa Marigayi mai martaba Sarkin
Yawuri, Alhaji Muhammadu Tukur Abdullahi har guda tara, ya taho masa da guda ɗaya (wannan kenan inda aka ɗebo waɗan nan ɗiyan waƙar da aka bayar da wannan misali ☝️). Ya baro guda
takwas (daga cikin waƙoƙin guda tara da ya ce ya yi masa a gida) idan ya ji daɗin yadda aka yi masa ta hanyar kyautatawa kuma aka yi
murna da zuwan nasa sai ya aika gida sauran guda takwas ɗin su same shi a Yawuri ya zube masa su duka.
Abin
lura anan shi ne hikimarsa ce a fagen Kiɗa
da waƙa ya ke so
ya bayyanawa al'umma. Saboda hikimar da Allah ya yi masa yana iya yin Waƙa/Waƙoƙi masu
yawan gaske a kowane lokaci ya ga damar yin haka muddin akwai yanayi mai kyau
da zai sanya yin hakan. Allahu Wa'alam!
[9:08am, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Malam Idris Garba Zaria muna godiya, a wayata wannan Waƙar ba ta yi.
Waƙar Alhaji Umaru ɗan
Sarkin Ƙayan
Maradun Muhammadu Tambari ce da aka fi sani da suna Bala/Balarabe. A lokacin
bikin auren Bala/Balaraben ne aka yi wannan Waƙar.
Alhaji
Umaru Bala/Balarabe shi ne Babban Uban Ƙasar/Babban Hakimin/Senior District Head na Masarautar
Maradun dake Jihar Zamfara. Laƙabin sarautarsa shi ne Sarkin Arewa/Sarkin Arewan Maradun. Ƙane ya ke ga Mai martaba Sarkin Ƙayan Maradun, Alhaji Garba Muhammad Tambari MFR na
yanzu, Mahaifinsu ɗaya, Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Tambari ɗan Amadu ɗan
Sarki ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Attahiru/Atto ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.
Dalilin
samuwar laƙabin
Sarautar Sarkin Arewa a Masarautar Maradun shi ne kafin zuwan Malam Muhammadu
Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio a wannan yanki na Maradun har ya zamo Sarki a
shekarar 1870 zuwa wafatinsa a shekarar 1874, ya zauni wani yanki a cikin Ƙasar Azbin (a Jamhuriyar Nijar ta yau), ya yi sarauta
a yankin da laƙabin
Sarkin Arewa.
Bayan
zuwansa wannan yanki na Ƙaya/Maradun
ne zuriyarsa suka ga muhimmancin taskace tarihin wancan mulki da ya yi a yankin
Azbin ta hanyar farfaɗo da wannan sarauta tasa ta Sarkin Arewa da ya riƙa a can. Allahu Wa'alam!
[9:23am, 23/02/2024] +2348161747863: Ba
ina nufin kai tsaye da Sa’idu Faru yana nufin turke ba a wannan ɗan waƙa nasa, wannan ya sa na ce, makadan baka ne suka fara ba da haske. Ma’ana,
Gusau ne ya kawo kalmar turke maimaikon jigo, kamar yadda Shehin Malaminmu ya
fada. Gusau yakan yi amfani da wasu kalmomin da makada suke amfani da su ya
kuma samar da wata ma’ana a fannin waƙar baka. Alal misali, idan aka duba Ma’anar waƙar baka da Gusau ya kawo (2003), za a ga daga kalmomin
Musa Dankwairo ya curo su ya kuma samar da ma’anar waƙar baka da su. A nan, Dankwairo ne ya ba da haske ta
ma’anar waƙar baka, shi
kuma Gusau ya yi amfani da ilimi wajen samar da ma’anar. Allah ya sa Malama ta
fahimci bayani.
[10:35am, 23/02/2024] Malama. S.S. Labbo:
Assalamu alaikum iyayena Ina muku fatan alheri. Don Allah Ina da tambaya, a
cikin wakokin Sa'idu Faru akwai in da yake magana akan Mata? Ina godiya da
fatan alheri ga shehunnan malamai, Allah ya ƙara muku basira da daukaka. Amin
[11:04am, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin Alaiki Salam Warahamatullah Wabarakatuhu Malama Shafaatu Salihu labbo. Madalla
da wannan tambaya mai muhimmanci.
Wace
irin magana kike nufi?
[3:08pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Lalle kam. Don na san da yake mawaƙin sarauta ne sarakuna mata babu su lokacinsa da ma
yanzu. Sai dai in ta kama mawaƙin bai rasa ambaton su kamar ya yaba matar sarki ko jakadiyarsa ko ya
yi wa wani ɗan sarki zambo da wani hali ko ɗabi'a ta mata
Amma
dai Hon Ɗanmadamin
Birnin Magaji shi ya fi cancanta da amsa tambayar domin ga shi nan har
ya fara
[3:10pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ranka ya daɗe a wajen bindiga wa ne kestu!
[3:13pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ai
kuwa akan samu garwashi a masaƙa a rasa a maƙera in ji
Aliyu Ɗndawo, Hon
[3:28pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A iya nawa ɗan gajeren nazari akan Malamin Waƙa mai kwana ɗumi
na Mamman na Balaraba na samu mace ɗaya
wadda ya yi wa waƙa mai
zaman kanta. Ita ce Marigayiya mai girma mai babban ɗakin Kano, mahaifiyar Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano,
Alhaji Dr. Ado Bayero, Hajiya Hasiya/Asiya Bayero, Allah ya jiƙan su da rahama, amin.
Amma
fa ba na ce babu wasu matan da ya yi wa Waƙa/Waƙoƙi ba ne, ni
dai anan allo na ya tsaya.
Ya
ambaci mata a Waƙoƙinsa daban daban domin alheri/kyautatawa zuwa gareshi,
wasu kuma saboda dangantakarsu da uwayen gidansa.
A
cikin Waƙarsa ta
Marigayi Sarkin Kiyawan Ƙaura
Namoda, Abubakar Garba mai amshi " Ubangijin Garkuwa ɗan Muhamman mai daga.... yana cewa " Ikka/Gwamma
da kar riƙe Uban
Luba.../duk da yake ban san yadda dangantakar ta take da Sarkin Kiyawa
Abubakar Garba ba, anan dai ga sunan mace ya bayyana a cikin wannan Waƙar.
...
Na gode Uwargida Dije/Maishanu kyautad da tayyi man../ da kuma abokiyar zaman
ta (bani iya kawo sunan ta a halin yanzu) wadda ta ba shi atamhwa/atamfa mai
kyawo yar rabka lulluɓi, a cikin Waƙar Dagacin Banga, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar mai amshi "Gwabron Giwa Uban
Galadima Ɗan Sambo
Ginshimi, Gamshiƙan Amadu
Na Maigandi Kai aa Uban Zagi '. Misalai ne da nike iya tunawa inda ya ambaci
mata a cikin Waƙoƙinsa.
[3:30pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Za a samu Waƙar Mai
Girma Marigayiya Mai Babban Ɗakin Ƙasar Kano,
Hajiya Hasiya/Asiya Bayero. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[5:30pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A cikin wata Waƙar da ya
yi wa Marigayi maigirma Ɗan Alin
Birnin Magaji, Alhaji Muhammad Mode Usman yana ambatar uwargida Hajiya Goshi. Duk
da yake ba ita ce uwargidan ba, amma dai sunan mace ya fito.
[6:51pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Uban Kumatu Uban Isa jikan Abubakar....
Mai
Sangon daga gamda'aren babba Kwamishina....
A
cikin Waƙar babban
ubangidansa, Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo
mai amshi " Ya yi Sarki daidai wada mai yanzu yar riƙa, Alhaji Macciɗo
jikan Mamman mai dubun bara ". Kumatu mace ce.
[7:05pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
*Gwamma/Ikka da kar riƙa Uban
Luba/Uban Liba....
[7:22pm, 23/02/2024] Malama. S.S. Labbo:
Allah ya taimaki shehin Malama na ga ka bani abin da na ke buƙata, dama na ga shi makadan fada ne to shi ne
nake tsammanin kamar ba ya ambaton mata a cikin waƙarsa, to amma Alhamdulillah ina godiya da wannan amsar.
Allah ya ƙara basira.
Amin
[7:38pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Hon. ai mutane ke ganin malami ya kai mlami har su ba shi suna. Malaman zamani
kurum kan liƙa ma kansu
suna!
Imam
Abu Hamid Muhammad al - Ghazzali bai taɓa
liƙa ma kansa wani laƙabin shahara ba. Mutane suka ga ya cancanta suka kira
shi Hujjat al - Islam.
Haka
shi Shehu Usmanu ɗan Fodiyo bai taɓa
kiran kansa Shehu ba. Ƙana'a
tarbiyyarmu ce Musulmai
[8:52pm, 23/02/2024] Dr. H. Yelwa: "...
Saratu ta ban atanhwa maikyawo
Nir
rabka lullubi. "
[9:02pm, 23/02/2024] Dr. H. Yelwa:
Maibabban daki, ta dade tana jin daɗin waƙad da Saidu Faru yay yi ma Sarkin Kudu Maccido wadda
yaka bayanin tahiyatai haz zuwa bakin Bahar Maliya da kammalac cewa sai ya'
iske larabawa wurin.
Wata
rana Saidu ya tai Kano, sai matan hwada sunka burgutamai haka.
Yaji
daɗin abin shi ma, sai yay yi mata waƙa a matsayinta na maisarauta a hwadak Kano.
[9:02pm, 23/02/2024] Dr. H. Yelwa:
Onorabul, "Barka da hayewa maliya. "
[9:07pm, 23/02/2024] Dr. H. Yelwa:
"Manya sun ishe manya
Inji
mutanen Jidda
Suna
ziyartaj juna.. " 😄
Allah
yasa an yi karbabbiya.
[9:24pm, 23/02/2024] Dr. H. Yelwa: A
cikin ambaton mata da Saidu yay yi, akwai Nana Uwardaje a wurare da yawa.
A waƙaw Wakilin Tsafta Mamman Nadange;👇🏽
"Kowa
ya san Nana uwad Daje
Ya
kau san jikanta na Gusau. "
"Jikan
Bello na Hodiyo
Jikan
Nana uwad Daje
Bawan
Allah jikan bawan Allah na Alu... "
A
cikin waƙas Sarkin
Kudu Maccido.
[9:26pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haƙiƙa!!! Sarkin Tsabta Malam Muhammadu Na Dange daga gidan
Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.
[9:35pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa Nadange jinin ɗan Fodiyo ne, amma daga gefen Nana Asma'u Uwar Daje
matar Usmanu Giɗaɗo ɗan Lema ya fito. Bagiɗaɗe ne, Allah Ya yi mai rahma, amin. 'Ya'yansa na iya
zama wazirran Sarkin Musulmi
[9:38pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Madalla da wannan ƙarin
bayani Ranka ya daɗe.
Ya
daɗe Gusau.
[9:56pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Sosai. Ɗan'uwana
ne. Kakannimmu ɗaya
[9:59pm, 23/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Yaya ne gare ni, 'ya'yansa 'ya'ya ne gare ni
[10:14pm, 23/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Na san shi saboda Mai garinmu, Ɗan Alin Birnin Magaji Muhammadu Mode Usman. Abokin shi ne sosai.
[5:10pm, 24/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Dakta Isma'il Aliyu Waziri barka da hwama, godiya mai dama da wanga aiki. Allah
dai ya hi mu yabawa, amin.
[5:45pm, 24/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Yan Ruwa laƙabin
sarauta ce ta fada a yankin Sakkwato (Sokoto, Kebbi, Zamfara).
Akwai
ta a fadar Anka da Talata Mafara da Bunguɗu. A
Moriki ta fara a fada, a halin yanzu kuma an ɗaukaka ta zuwa ta hakimci/uban ƙasa dake da gunduma mai Unguwanni/ƙauyuka da kuma jama'a.
Ga
kuma ta fadar Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III tun yana Sarkin Kudun Sakkwato.
[5:52pm, 24/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:...
Sai Sarkin Zazzau nig gani yac ce man Muhamman ya tai haji...
Domin
nuna faɗin mulkin masu iko na Cibiyar Daular Usmaniya, Malamin
Waƙa ya nuna daga Mai Martaba
Sarkin Zazzau (ɗaya daga cikin Tutocin Daular Usmaniya) ne ya samu
labarin tafiyar Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo
zuwa aikin Hajji bayan ya biyo shi daga Sakkwato.
[6:31pm, 24/02/2024] +234 806 524 0341: Salaam.....
Akwai
wadanda ba su san wadannan Tsuntsaye ba, har dani ciki, "Suda
da Burtu da Jinjimi da Beguwa da Bubukuwa, a taimako da hotunansu domin mu ƙara ilimi.
[7:30pm, 24/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Na
dai san Burtu: wani tsuntsu ne wanda ya kusan girman talotalo ga jiki amma ya
fi talotalon tsayi, bakinsa yana da ɗan
tsayi amma bai kai tsawon na bubuƙuwa ba, ƙafafunsa sun ɗan
cira. Da kansa har zuwa baƙi ne mafarauta kan samu sai su liƙa wani zare ko igiya ga kan ta yadda za su iya ɗaura shi ga kai kamar yadda sukan ɗaura fitilarsu in suna cikin daji da dare don su riƙa ganin gabansu. To idan mafarauta suka shiga dajin da
suka san akwai burtu ciki sai su ɗaura
wannan kai na burtu, su duƙa kamar mai yin noma, da hannuwa da ƙafafu za su riƙa tafiya, suna yi suna tokarar ƙasa da bakin burtu, wato kamar yadda burtu tsuntsu
yake yin kiyo. Za su yi ta yin wannan tafiya suna yin kamar burtu ne ke kiyo
har su kai kusa da burtu ko taron burtu na ƙwarai da ke kiyo. Ta haka mafarauci yake ruɗin burtu mai rai ya ɗauka cewa mafaraucin irinsa ne tsuntsu. Can sai mafarauci ya yi wuf ya
cafke burtu!
Na taɓa ganin burtu cikin dajin da ke tsakanin Ɗansadau da Ɗangulbi. Tsuntsu ne mai nama
[7:39pm, 24/02/2024] Malama H.M. Kurawa: "Ba ai wa biri burtu", Wannan na nufin ba a iya ruɗar biri ta wannan siga?
[7:45pm, 24/02/2024] Dr. H. Yelwa: Burtu👆🏽
[7:45pm, 24/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Tabbas na ga burtu. Ai saboda da kansa ne mafarauta kan ɗaura ga kansu su ruɗi
tsuntsu su kama shi, akan ce shigar burtu. Idan mutum ya yi shigar burtu ana
nufin ya ruɗu mutane ko ya yi sojan gona.
[7:49pm, 24/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Duk girmansa yana iya hawa kan reshe?
[7:50pm, 24/02/2024] Dr. H. Yelwa: Suda
uwar surutu👆🏽
[7:52pm, 24/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
'Suda sarkin labari', ɓaba Suda'.
Ita kuma yaya lamarinta yake!🙏
[8:00pm, 24/02/2024] Dr. H. Yelwa: Jinjimi👆🏽
[8:11pm, 24/02/2024] Dr. Aliyu Sambo Uny Dutse:
Mai girma Dangaladima barka da sirdi. Alla ya amsa ya inganta niyya. Ni ko ko
don in laqanci wakokin Malamin Waƙa, Makada Sa'idu Faru, Ina bara a bude min ajin koyon
Hausar kasar Hausa. Makada Yana zuba Hausa Mai dubun hikima, ni Kuma babu Hausa.
Allah ka rika mana.
[8:12pm, 24/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Barka kade Maigirma Waziri, muna ta bautag godiya dai da wanga aiki na
ilmantarwa da akai muna kullun. Allah shi ƙara hasken Makaranta, amin.
[8:15pm, 24/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Malam Aliyu Sambo ɗan mutun Bauchin Yakubu barka da dare. Sannu a hankali
zaka fahimci Hausah Hausa In Shaa Allahu in dai kana cikin irin waɗan ga Zaurukan da Shaihunan Mallammu kai muna zubak
Kurna ta ilimi.
[8:29pm, 24/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ni
sai cikin maganganun Hausawa na san suda. Misali idan yaro ya cika surutu akan
kira shi suda sarkin surutu/ ɗumi; idan mace
ce sai a ce uwar ɗumi/ surutu
[8:33pm, 24/02/2024] Mal. M.A. Umar Akwai
wani tsoho da ake kira "Jinjimi mai ƙololo" watakila sunan na da alaƙa da wannan tsuntsun!
[9:32pm, 24/02/2024] Dr. H. Yelwa: Tuji👆🏽
[9:34pm, 24/02/2024] Prof Nazir I. Abbas:
Madallah da wannan ƙoƙarin kawo muna hotunan tsuntsayen
[10:56pm, 24/02/2024] Malama H.M. Kurawa:
Shi ko Tuji,
Da ad da girman baki,
Ya lanƙwasa tsara'
Ran nan nas san,
Duniyag ga komi na ne,
Wani mayar wani".
Gwabron giwa,
Uban
Galadima,
[11:04pm, 24/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Lalle ita ake ƙira beguwa
ko kayar makaya
[11:06pm, 24/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Wani
mayen wani wato wani ya fi wani ko Hausawa su ce "gaba da gabanta"
[11:09pm, 24/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Lalle ita ake kira beguwa ƙayar maƙaya
[11:10pm, 24/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu:
"Kullun Sarki ya sai dawo,
Ita
kau ba ta san za'ida ba,
Ko
nono sai dai ta bungulo".
[11:34pm, 24/02/2024] Dr. Sakina: Salam
Malamaina, Magabata da Abokan karatuna.
Barkanmu
da dare.
Sunana
Sakina Adamu Ahmad manazarciya fannin kwari.
Ina
biye da wannan zauren mai ilmantarwa, kuma ina ta sauraren ko zan samu abin da
zan ɗauka don gina fannin nazarina.
Amma
sai na ga ana ta baje koli da ɓarin hikima a
fannin "tsuntsaye", ko canza sheƙa in dawo inda na ga an tara mini amsa?
[12:38am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
To Dr. Sakina da yake wannan zaure a kan mawaƙi Sa'idu Faru da waƙoƙinsa aka buɗe shi, za ki iya lura da cewa wannan ɓarin ne masana da manazarta da masu sha'awa suke tofa
albarkacin bakinsu. Idan kika ga ana magana a kan tsuntsaye to saboda shi mawaƙin ya ambace su ne. Idan kuma kika ga ana magana a kan
dabbobi to lalle su ma ambaton su yana cikin waƙoƙinsa ne. Da yake fannin ƙwari ne fagen nazarinki kada ki ɗebe ɗammaha. Watakila
wani ya kawo mana wata waƙa ko waƙoƙi da Sa'idu Faru ya ambace su. Me zai hana ki tambayi wani
masani (da na roƙi masu
gudanar da wannan Zaure da su ba jami'arsu shawara da ta naɗa shi Rumbun Waƙoƙin Baka na Zamfara) da ya dubo miki ko akwai waƙa ko waƙoƙin Sa'idu Faru da suka ambaci ƙwari kamar sauro da cinnaka da tarmani da zuma da
rakkuwa da makamantansu. Wannan masani shi ne Hon. Ɗanmadamin Birnin Magaji. Kila ma yana nan yana burkuto
irin waɗannan waƙoƙi in har akwai su. Allah Ya taimaka amin.
[12:55am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Na dai san akwai waƙar da
Sa'idu Faru yake cewa wani abu kamar/kowal kasa zuma bai koma batun maɗi/. Hon. Sir gare ka don Allah
[5:01am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Allah ya ƙara lafiya
da nisan kwana mai albarka Ranka ya daɗe.
Malamin
Waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ya ambaci ƙwari kamar Zuma da Zirnaƙo da Galla a cikin wasu Waƙoƙinsa.
A
Waƙar Marigayi Maigirma Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu
mai amshi 'Gwabron Giwa kana da martaba, Usumanu na Bunguɗu Uban Marafan Keku na Atto mai wuyak karo' yana cewa
"Zirnaƙo ƙaryaf faɗa
ya kai, kowa ka biɗaf faɗa ya ja zuma, sai
ya biɗi mai raba su ya rasa".
Haka
a cikin Waƙar Ɗan Uwanka, Marigayi Maigirma Wakilin Tsabta Malam
Muhammadu Na Dange yana cewa "Shaye - Shayen da aka yi ma Galla, ba a yi
ma Zuma shi" (duk da yake ba na rubuta daidai abun da ya faɗa ba ne).
Ban
taɓa ganin Galla ba a matsayin ƙwaro, amma ba na ce babu ƙwaron da ake kira Galla ba, amma tawa fahimta ita ce
"Galla" kamar wasu ruwa ne/darɓa
dake sauka daga sama/ko kuma aikin wasu ƙwarin ne dake haifar da wannan ruwan/darɓar akan tsirrai.
Wannan
ruwan/darɓar na da zaƙi, kuma saboda rashin samuwar ƙwaron/Gallar dake haifar dashi sai Bahaushe na ganin ɗibar sa a sha ba wuya, amma zuma da yake sai an yi
ganinta kafin a samu a sha ta a sauƙaƙe sai Malamin Waƙa ya bayar
da wannan misali. Allahu Wa'alam!
[5:42am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya: To
Sa'idu Faru bai faɗi wani abu ba kamar wanda na ambata >/kowal lasa
ruwan zuma bai koma batun maɗi/?
[5:56am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ranka ya daɗe ya faɗi
hakan a cikin Waƙar da ya
yi wa Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo mai amshi 'Farin cikin musulmin duniya, mai martaba
na Abubakar, ci fansa Alhaji Macciɗo'.
Sai
dai Maɗi ba ƙwaro ba ne. Wata cimaka/abun sha ne da ake yi daga wasu ɗiyan itace kamar su kaiwa/kanya da makamantansu.
[6:43am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya: Ai
ni dama zumar nake son in ji. Maɗi
kuma kamar wada ka ce daga rake ake yin sa. Zumar da Sa'idu ke magana kuwa ai
ruwan zuma ne na ƙwaron da
ake kira zuma. Ko kuwa?
[6:45am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Madallah.
Wai
ka dawo daga Umrah? Na ga wani a Zaure yana yi ma barka da zuwa
[7:10am, 25/02/2024] Dr. S.S. Abdullahi:
Watakila Hon bai yi kiwo ba, akwai kwaro da ake ce wa Galla, ana samunsa ga
itacen doruwa a lokacin da yake bututun Samar da 'ya'ya, ai wannan zakin da ke
darba a jikin bututun doruwa yana da alaka da kwarin gallar. Kwaron Galla ko
sauro bai fi shi damuwa ba, kana korar sa yana ƙoƙarin fada ma a ido.
[7:31am, 25/02/2024] Fugus Ba shir Abdullahi:
".... Maccido jikan Mu'azu makaye".
Assalamu
Alaikum!
Iyayena
da Malamai da sauran 'Yan uwana da Abokan Aikina da na Karatu duk ina yi maku
fatan alkhairi, da fatan an an tashi lafiya.
Ina
da tambaya ne dangane da ma'anar kalmar nan ta makaye. 👌🙏🙏
[7:59am, 25/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Sosai
kuwa Dr. Ai Galla in ta fara bin Idon mutun sai ya damu don korar da yake yi
mata.
[9:36am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Gaskiya akwai buƙatar samun
hotunan waɗannan ƙwarin irin su Zuma, Galla, Zirnaƙo, Rina da sauran su domin mu ƙaru.
[11:03am, 25/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Hon sir, kana da gaskiya. Ina ba ka shawara da kada ka sha kunu ga azumi da
sugar. Sai dai da zuma! Na leƙo inda ake kiyon zuma, babu nisa. Baitocin da ka tono muna yau kada
ka bari su je haka nan!
[11:14am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ƙarin wasu Tsuntsaye da Malamin
waƙa ya ambata a cikin wasu waƙoƙinsa.
Kaza,
a cikin waƙarsa ta
Sarkin Kiyawan Ƙaura
Namoda, Abubakar Garba mai amshi 'Gwabron Giwa Garba Uban Yari maci maza..
Dale
a cikin faifan Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo
mai Turke 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai' inda yake cewa "Na ishe Dale
tai ƙawa ga
jama'at ta ba ƙawa...
Angulu/Ungulu/Kolo...
A cikin waƙar Ɗanmadamin Sakkwato Usman Ɗangwaggo Bunguɗu
mai amshi ɓajini birni bajini dawa na dai gaishe ka da ƙoƙari, ɗan mai daga na Abubakar Usman kai nik zaka in gani.
A
waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Ahmadu Muhammadu Asha mai amshi 'Sarki yai
Sarki cigari ya gyado rinjaye Alu... yana cewa "Sa babba sata nig gani, tsohon
ɗan Sarki Angulu... (Sa babba sata wani kalar Wake ne
mai girma/ruɗu - ruɗu dake sanya
mutum sha'awar ya duƙa ya cire
shi a gonar da ba tashi ba).
[11:18am, 25/02/2024] Dr. Sakina: Barka
Prof. Ai tun kwanakin baya na fara tuntubarsa. Kuma ya agaza da wasu bayanai. Abin
da ya burgeni, yadda naga ana ambato sunayen tsuntsayen tare da hotunansu. Wanda
da yawan matasanmu ba su san tsuntsayen ba.
[11:19am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Da ba zai zama abun ya yi yawa ba, da na turo wasu Tsuntsayen domin a ƙara muna ilimi akai.
[11:20am, 25/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Na'am!
A
cikin Keɓɓe Local Government akwai Raha
Akwai
Raha a Kebbi can idan aka bi hanyar Bunza
Haka
ne Maigirma Babban Sakatare. Ta Tambuwal babu "n " a karshen sunan, Maradu
ne ba Maradun kamar yadda ta Jihar Zamfara take ba.
Su
kuma akwai irinsu da ke da bambance -bambance kadan irinsu Kauran Namoda ta
Zamfara da Kauran Wali ta Kaduna, akwai Bungudu garinmu da wani garin Bungudawa,
akwai alaka sosai a tsakanin wadannan sunayen.
Ba
za a rasa alaka tsakanin garuruwan ba idan aka yi binciken. Na san akwai Kuryar
Madaro da Kuryan Dembo a Zamfara. A Sakkwato akwai Kurya (ta Gandi) haka ma
akwai Kurya a Kebbi.
Mai turu yana cewa a wata waƙarsa;
"Abin da yas sa ban hau doki ba,
Na
Bungudawa shi nika son hawa.
A
nan mutanen Bungudu yake nufi ba waccan Bungudawar ba. Ina zaton shi bai ma san
da wancan garin ba.
Haka
ne Dangaladiman Shaihin Malaminmu.
Kuryar
Madaro ta Kaura Namoda kirkirar wasu Fulani ce da ake kiran jinsinsu da suna
"Jallawa" domin sun fito ne daga Dutsin Jalla a cikin Jamhuriyar
Nijar ta yau. Su da Rawayya wa ne da ƙane. Madaro ne ƙane kuma shi ne ya kirkiri Kuryar Madaro, Muhammadu Ɗan Na Ɓore ne ya kirkiri Rawayya.
Kuryar
Dambo dake cikin Masarautar Shinkafi a Jihar Zamfara kuma Mal. Makauru ne ya
kirkire ta, ƙane ya ke
ga Gatari wanda ya kirkiri garin Kware/ Kwaren Isa dake Masarautar Shinkafin
Jihar Zamfara. Su kuma Fulani Alibawa ne.
Makada
Narambada yana cewa "Ai Kurya ta Dambo ta Makauru an nan, Zanhwara babu
Bagare kama tai" a cikin waƙarsa ta Sarkin Rafin Kuryar Dambo Ibrahim mai amshi
'Masu gari mazan gabas tsayayye, Sarkin Rwahi ya wuce a rammai '.
Kuryar
Gandi kuma kirkirar masu jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya
ce. Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan
Mujaddadi Shehu Usman Danfodio ne ke kirkirar ta, amma bata haɓaka ba sai a lokacin mulkin Sarkin Musulmi Abubakar
I/Abubakar Atiku/Mai Katuru ɗan Mujaddadi
Shehu Usman Danfodio, ƙanen
Sarkin Musulmi Muhammadu Bello wanda kuma shi ne ya gaje/gade shi.
Makada
Muhammadu Dodo Mai Taushi ya tashi daga garinsu, Bakura ya koma Kurya da zama
tun a farko farkon ƙarni na 21.
Daga can ne zuriyarsa suka watsu zuwa garuruwan Wurno da Sakkwato da Shuni inda
suke a halin yanzu.
Shi
ne ya haifi Kakan Makada Amadu Mai Launi Bakura, wato/watau wanda ya haifi
mahaifiyarsa inda ta nan ne za a iya cewa ya gaji/gadi kiɗa da waƙa.
Haka
ne. Kusan abu ɗaya ne. Sau da yawa a cikin waƙoƙin Makaɗa Kurna kana jin yana cewa Maradu a maimakon Maradun. Ina
ganin da Maradun da Maradu duk abu ɗaya
ne.
Madalla
da wannan ƙarin
bayani.
Ko
a Kaura Namoda akwai garin da ake kira Sakajiki, laƙabin sarautarsu shi ne Maradu.
Rakkuwa
ke yin Danko tayi Zuma Mai Zaki da Dan tsami kadan
Gallace
Mai yin Zaki ruwa-ruwa, mafi yawa a jiki bishiya ko ganyen bishiya. Ta kan Yi
Zuma a kogon icce. Akan samu da yawa kama cikin garwar manja na dauri Wanda Yan
garuwa ke yin doso dasua.
Akwai
Birnin Yero da Badarawa a yankin Shinkafi ta jihar Zamfara, haka Kuma akwai
Birnin Yero da Badarawa a jihar Kaduna.
Da
akwai Yoro a jahar taraba babangari ne na mumuyawa l/g HQt, ce, kodayake
mumuyawa sunce asalin su kanawa ne, kumanaga haryazu sunayin staga gajeruwa
irin takanawa
Tsaga
Shaga*
Badarawak
Kaduna ainihi ba sunan unguwa ne ba. Sunan babban titin da yar ratsa cikin
unguwat ne, wato Badarawa Road. Daga nan sai anka miƙe da cewa Badarawa, Badarawa, ha' abin yaz zama sunan
shiyat.
"Ko
can hasken hwarin wata bai dushe rana ba" inji Makaɗa Alhaji Sa'idu Faru a Waƙarsa ta Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar Garba (Gwabron Giwa na Shamaki
baba Uban Gandu, Abu gogarman Magaji mai kamsakalin daga).
"Toron
Giwa yana abun da ya kai ya shigo dawa, 'yan namu suna ta gaisai sun ba da
gaskiya... Inji Ɗan Umma
Uban Kiɗi a faifansa na Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo Abubakar III mai amshi ' Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai... Allah ya kyauta makwanci, amin.
"Zomo
ya taho ya biya ya gaida Toro, shi ya yarda Allah kawa kowa nagarta", inji
Makaɗa Sa'idu Faru a Waƙarsa ta Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo mai amshi 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai.. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau
da imani, amin.
"Ina
banga - banganga mai 'yar mahuta, Alade wurin shan giya kah hi suna" inji
Makaɗa Sa'idu Faru a cikin wata Waƙarsa ta Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III. Allah ya kyauta makwanci, amin.
Zomo ya ce tsaya✋🏽shege lallashinta kay yi
In karhi gaskiya ne koma ebo gabana
Saidu na yawan ambaton giwa;
Giwa
ta sha ruwa tai mika ta taushe gurbi...
Ga
Wangara a Gezawa a ƙasar Kano.
Sannan akwai Wangara a kasar Katsina.
Wangara
kuwa watakila ƙabilar da
ta zo ne daga Senegal > Wangarawa
Abin
mamakin warwatsuwar al'umma shi ne a lokacin da babu abubuwan hawa na zamani
sosai amma sai mu yi ta samun bayanan na wannan kasar a wata kasa ko na wata
kasar a wannan kasar.
Migration
and state formation in Hausaland by Abdullahi Smith has dealt with it Dr.
Haka
ne, amma ina ganin ƙoƙarin mutanen wancan lokacin ne.
(1) Dole ba ta rasa ɗakin kwana.
(2) Hanyoyin da mutanen da suka bi suka kai
wasu wurare ratse ne bisa ga hanyoyin zamanin yau.
(3) Mutanen da ba sauri sukan yi ba. Sukan
kwana yada zango ne don su tara guzuri sannan su ci gaba har su kai inda suka
yi niyya.
(4) Wasu kuwa yaƙi ko fatauci ko neman ilmi ko yawon buɗa ido ne ya kai su amma daga baya suka zauna ba su
koma gida ba.
A
lokacin ana zaune lafiya, babu tashin hankali kamar yanzu.
"Sai
Bil'amu/Bil'amo uban dubara shi ɗai
yaz zo ga Giwa, yac ce albarkacinki ni zaka in samu ruwan da nish sha, Giwa ta ba
shi hili ya sha kuma ya ba ɗiyanai, ya tai
ya wa dangi kirari yac ce ya ƙwato da ƙarhi, Zomo
ya ce tsaya shege lallashinta kay yi, in ƙarhi gaskiya ne koma ƙwato gaba na ", inji Makaɗa Sa'idu Faru a Waƙarsa ta Sarkin Zamfaran Zurmi Suleimanu Muhammadu
Sambo mai amshi ' Babban bajinin gidan Sambo shirin ka daban, jikan
Mamudu Sarkin nasara baban Baraya'.
[3:31pm, 28/02/2024] Prof. A.B. Yahya:
Canza maganar mawaƙi ko ma
kowane marubuci kasada ce domin ma'ana ko furuci ko kari na iya canzawa. Idan
kari ya canza sai waƙa ta ƙare. Misali, a Sakkwatanci "ilmi" ake cewa
alhali a Kananci da Zazzaganci "ilimi" ake cewa > gaɓa biyu dogaye a Sakkwatanci, gaɓa uku a Kananci da Zazzaganci, biyu na farko gajejjeru,
ta karshe doguwa
[3:40pm, 28/02/2024] Mal. A.R. Mayana:
Salihu Jankiɗi yana cewa a wata rerawa ta wata waƙa:
An ka da Kumama ya faɗi,
Ya shaƙe ciki da tuwon wake,
Ya kumbura kullum sa tusa.
Nan
take kuma sai ya maimaita ɗan ya ce:
.........................
Ya
kumbura kullum sai rihi.
Me
za ka ce a nan?
[3:43pm, 28/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Ko
alama! Ba haka ilimin yake ba. Su mawaƙan ne ai da kansu, suke canza kalmomin; wani lokaci ma
nan take.
Rerawa
da ƙa'idojinta babi ne mai zaman
kansa a ilimin nazarin waƙar baka.
A
koma ga ayyukan Farfesa Gusau don ƙarin bayani.
[3:43pm, 28/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ikon Allah!!! To saboda iyawa kana iya sauya masa waɗan nan kalaman ya zuwa naka tunanin/hasashen?
[3:47pm, 28/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Dama shi ne fahimtata kuma nike ƙoƙarin jawo hankali a kai.
[3:47pm, 28/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Babu buƙatar
wannan dogon tawilin domin ba sharhi ko fassara nike nema ba.
[3:48pm, 28/02/2024] Mal. A.R. Mayana:
Mawaƙan baka
kan yi ƙare-ƙare da rage-rage da canje-canje a waƙoƙinsu saboda canzawar lokani da wurin rerawa da sadar da waƙa.
[3:53pm, 28/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ikon Allah!!! Waɗan nan ƙare ƙaren na iya canzuwa ga manazarci ko mai sharhi akan Waƙoƙin nasu?
[4:29pm, 28/02/2024] Mal. A.R. Mayana: Ai
aikin mai nazari da sharhi shi ne fara bayyana 'yadda aka yi' kafin 'yadda za a
yi. '
[10:16am, 29/02/2024] Mal. A.R. Mayana:
Malam Yusuf gajeriyar mallaka ana haɗe
ta da suna ne: Malumanmu ba maluman mu ba.
[1:28pm, 29/02/2024]: "Ina banga - banganga
mai 'yar mahuta, Alade wurin shan giya kah hi suna" inji Makaɗa Sa'idu Faru a cikin wata Waƙarsa ta Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[1:33pm, 29/02/2024]: Salaam.... Malamaina don
Allah a cikin Wakokin Sarkin kudu Maccido na Sa'idu Faru wace waƙa ce ya ambaci 👆Alade, a taimaka da gindin waƙar.
[1:44pm, 29/02/2024] Mal. A.R. Mayana:
Ina sa ran:
Bajinin
gidan Bello Manman na Yari,
Sarkin
kudu Maccido ci maraya.
[4:34pm, 29/02/2024]: Masha Allah, kyaun dattijo
magana biyu. Ya ce e, in aka sami gyara ya ce a'a.
[4:39pm, 29/02/2024] Mal. A.R. Mayana:
Kyan dattijo magana uku: í, áâ, éh!
[5:13pm, 29/02/2024] Dr. S.S. Abdullahi:
Wane Karin harshen? I & eh duk guda ne.
[5:28pm, 29/02/2024] +234 706 685 1000: Tau hwa!
Fage na manyan masana. Allah ya ƙara basira.
Tambaya.
Ko
Sa'idu Faru ya taba jira baitoci biyu zuwa uku a cikin wakokinsa, da kalmomin
ingilishi?
[5:41pm, 29/02/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Da wuya a
samu hakan, musamman ga mawaƙan da ba 'yanboko ba. Shi yana cikin irinsu.
[6:20pm, 29/02/2024] Mal. A.R. Mayana:
Inda ko Larabci ne.
[6:43pm, 29/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A ɗan nawa gajeren nazarin akan Makaɗa Sa'idu Faru ban san in da a cikin waƙoƙinsa ya jero ɗan waƙa guda uku na Ingilishi ba.
A
wata waƙar da ya
yi wa Marigayi Mai martaba Ɗan Alin Birnin Magaji, Alhaji Muhammad Mode Usman mai amshi 'Mai ɗamara Ɗan Ali, Ɗan Shehu
sadaukin Sarki' akwai inda ya kawo wani zance a cikin Ingilishi inda ya ke nuna
ya je wajen wani da Kiɗa da waƙa sai ya juye baki yana yi masa turanci/ingilishi, shi
kuma ya sanar dashi Kiɗi da waƙa su ya iya shi bai iya turanci ba.
A
hakan ne ya ke cewa "I no Ingilishi ni ban iya turanci ba".
Akwai
caffiya da ɗan amshinsa Malam Ibrahim (Ibrahim Sa'idu Faru, halinfansa
na yau) ya yi da kalmomin turanci a cikin Waƙar Marigayi Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo Abubakar III mai amshi 'Farin cikin musulmi duk kai
mu ka taƙama yau, Muhammadun
Muhammadu ɗan Abdu mai darajja', yana faɗin " wani undesirable element..
A
cikin wata waƙarsa ta
Marigayi Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III mai amshi 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai.. sun kawo wata kalma mai kama da
ta turanci inda suke cewa " Kuma ya samu yardi ga ob Lamiɗo babba.
A
Waƙarsa mai amshi 'Farin cikin
musulmin duniya ta Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III yana cewa "Farin cikin mu mutanen
nozan/northern riƙon da kay
yi Alhaji Macciɗo". Na san ba za a rasa ire -iren waɗan nan ba.
Allahu
Wa'alam!.
[7:07pm, 29/02/2024] Mal. A.R. Mayana:
Rumbun nazarin waƙar baka ya
samu ƙarin
kalma: 'caffiya' wadda take daidai da 'rakiya'.
[7:10pm, 29/02/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:...
Abdu wakilin local asorati/ Local Authority... Kamar yadda ya kira Ƙanen Marigayi Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu
da ake kira Alhaji Abdu Mafara a cikin Waƙar shi Ɗangwaggo Bunguɗun
mai amshi 'Gwabron Giwa kana da martaba, Usumanu na Bunguɗu Uban Marafan Keku na Atto mai wuyak karo'.
Afuwan,
Alhaji Bello ne ba Alhaji Abdu Mafara ba. 🙏🙏🙏
"Ana ta tsoron kai ba ka jin tsoro!
Baba halin Alu kai yi mai Raba".
Ƙi garaje uban Shamaki.........
Maigirma
Sarkin Gobir Na Bunguɗu anya Alu mai Raɓah
ne?
Saboda
wanzuwar Sarkin Musulmi Abubakar II da aka fi sani da Abubakar mai Raɓah ɗan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi sai ina ganin
kamar an fi tafiya akan cewa shi ne yake danganta wanda ya yi wa waƙar dashi.
Abu
na biyu kuma shi ne wanda aka yi wa waƙar yana da dangantaka ta jini da Sarkin Musulmi
Abubakar II/Abubakar mai Raɓah ɗin da nike cewa kamar shi ne Makaɗa Sa'idu Faru ke ambata a cikin wannan ɗan waƙar.
Shi
wanda aka yi wa waƙar, Sarkin
Gabas Talata Mafara Alhaji Shehu ɗan
Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ne, Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan
Modibbo Usman ne, Modibbo Usman ɗan
Sarkin Musulmi Mu'azu ne, Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne.
Da
Sarkin Musulmi Abubakar II/Abubakar mai Raɓah
da Sarkin Musulmi Mu'azu duka ɗiyan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ne. Wannan ya ƙara mani ƙwarin gwiwar cewa shi ne Malamin Waƙa ke ambata/nufi. Amma a sake sauraren wannan ɗan waƙar domin tantance abun da ke daidai.
Godiya
mai yawa tarin yawa Maigirma Danmadami. Ina jin daɗin wannan dan waƙar ne.
Assalamu
Alaikum
Ko
Makada Saidu Faru yayiwa Sarakunan Zazzau Waƙa?
Allah
ya saka wa Shehunmu da alheri. Ya ƙara lafiya da nisan kwana.
Amin
Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.
Ya
yi wa Marigayi mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr. Shehu Idris Waƙa.
Jagora: Shi
ad da halin ga na Bubakar
Y/Amshi: Ba
da doki garai ba komi ba na,
Jagora: Shi
ad da halin ga na Bubakar
Y/Amshi: Ba
da moto garai ba komi ba na
Jagora: Macciɗo roƙon mota niz zaka
Y/Amshi: Kai
bari katce iyakag gargare
Jagora: Macciɗo roƙon mota niz zaka
Y/Amshi: Kai
bari katce iyakag gargare,
Mai roƙon doki don suka,
In a ba shi mato amsa ya kai,
Mai roƙon riga kwakwata in an ba shi shabka amsa ya kai,
Mai roƙon riga yar diga in an ba shi kore amsa ya kai,
Kana
shire Baban Yan Ruwa...
1.
"Kai bari katce iyakag gargare"/me ne ne gargare?2. " Kwakwata
da Shabka da Yar diga da Kore duk nau'in sutura ne/riguna ne na alfarma. Ko
zamu samu sharhin da zai ƙara fito
muna da surar waɗan nan riguna/kayan ado na alfarma ƙara - ƙara?
Ina
manoma? A ɗan sanina "gargare" shi ne wurin da aka ba
mutum ya nome cikin gona. Saboda haka gargare bai kai yawan gona ba.
Don
Allah kada a dogara da wannan bayani saboda ni sanina da gona shi ne zuwa yin
shuka gonar mallamina na zaure, kuma yadda ma ake shuka a lokacin ban iya ba😂
Ranka
ya daɗe barka da asuba. Haka ne, gargare ba a wajen noma ba
ne kawai ake samun sa ba, a kowane irin al'amari da ake yi a gona ana samun sa
tun daga sassabe zuwa huɗa da shuka da zuba taki da noma da cirar shuka
da girbi da ma cire kayan gonar.
Gargare
na nufin iyakar inda aka tsaya da wani aiki a gona ko dai domin an gaji a tsaya
a huta ko kuma saboda daidaita aiki ya tafi kamar yadda ake buƙatar sa.
Yaran
Malamin Waƙa suna
ankarad dashi cewa a wajen babban ubangidansa Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ya daina iyakance roƙo saboda komai yana iya samu daga wajen sa har ma abun
da bai roƙa ba ko
abun da ya fi gaban wanda ya roƙa.
Muna
godiya sosai Ranka ya daɗe da buɗa
muna fage da wannan bayani.
Ai
gargare ana nufin tsawon kuyyar da mai noma kan datsa a lokacin da yake noman. Wato
kamar a ce tsawo kuyyen ya kai kimanin rabin "kilometer" to sai ya
rika datsawa kamar guuntu shida ko fiye da hakan idan ya gama wannan ya dora
wannan har ya kammmala. Ko mutun daya ko fiye na yin gargare wajen noma, haka
kuma zabi ne ga mai gona ko 'yan kwadago.
Da
kyau Maigirma Sarkin Gobir Na Bunguɗu
kuma Shaihin Malaminmu Dr Haruna Umar Bunguɗu. Godiya
sosai da wannan ƙarin
bayani.
Rankaidade
barka da ka tashi lafiya? Ya ibada? Allah ya ƙara maka. Kwarin guiwar wanzar da ibada, Ya kuma karbi
dukan ayyukkan da ka yi da addu'o'in da ka yi mana da kasarmu. Amin Ya Hayyu Ya
Qayyum.
Haƙiƙa tun daga bayanin da ka yi na kalmar ba fahimci abin da Faru ke nufi
cikin waƙar tasa. Shi
dai gargare ba duk gona ba ne. Na gode ƙwarai Hon sir
Dalili
da sanin haka na fara bayanina da "Ina manoma".
Dr.
Haruna barka juna. Ina fatar duk iyali na lafiya amin Ya Arhamar rahimina.
Muna
godiya sosai da ƙaruwar da
mu ke yi Ranka ya daɗe. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.
...
Waƙa ɗai mukai kamar an aza gargare...
A
kai a kama zan kyawo in don kwaramniya ba fasali ba ta...
A
sha hura ayi wasa Ɗan Tumba
shan hura ba lahani ba ne....
Madallah
Danmadami da Sarkin Gobir na BUG da bayanin gargare.
Ba
kamay yadda maitambaya yac ce ba "gargare shine wurin da aka ba mutum ya
nome cikin gona". Karin bayani nanniya shine, shi wanga wurin, da aka diba
cikin gona aba wani ya noma, shi aka cema GAMANA.
Sai
dai a bayaninsa kamar ba yana nufin an baiwa mutum wani wuri ba ne a cikin
gonar ya noma, a'a an ba shi wurin ne domin ya nome.
Dalili
ke nan da na fara bayanina da "Ina manoma?". Na kuma ce kada a dogara
da bayanin. Alhamdulillahi! Yanzu ga manoma nan suna ba mu ilmi.
Haƙiƙa. Haka nake nufi. Ka san bami ne ni ga harkar noma! Ban ma kai ga
bamin ba
*Noma/Nome....
Ya
noma na nufin ya mallaki wurin na wani lokaci akan wani sharaɗi/wasu sharuɗɗa.
Da wannan sai a ce an ba shi Gamana.
Ya
nome na nufin an nuna masa wani wuri a cikin gona aka ce ya nome daga wannan
wajen ya zuwa wancan wajen, an samu gargare kenan.
I!
Yallabai, na ga ka bidi manoma.
Asalin
kalmag gargare ta malamman zaure ce. Daga larabci.
Misali
nassinga 👉🏽Allah yana karbar tuban bawanai 'ma- lam -yu GARGIR'.
Sai
malammai sunka hausance kalmat suna cewa GARGARA, ma'ana IYAKA.
Gargara👉🏽gargare.
To
kuwa akwai yar tambaya ga bayaninka na farko cewa gargare daga Larabci take. Don
Allah tuntuɓi masana ilmin harshe
"Lallai
Amale a waƙar Isah
Maikware ya ce ".... ya sha gargara.... "
Tabbas
kalmar Latabci ce, mallakar malaman zaure. Manufarta kuma ita ce ƙarshen abu.
Gargare
kama a gona katsa shi ake yi ko datsawa ko iyakancewa.
Wannan
ma'ana ce kuma Makaɗa Sa'idu Faru ya yi luguden ta a waƙar.
Babu
shakka duk mai harkar hatshen Hausa yana da buƙata da masaniya da harshen Larabci.
Wannan
ba gargare yake nufi ba, gangara ce kamar ka hau tudu ka gangaro.
Amma
dai akwai waƙar Garba
da ya yi "Ba ka san wuyag gargare ba"
Ni
abin da na fahimta a nan ita ce. Gargara daban gargare daban. Sannan za a ce
Hausawa ba su da kalmar gargare sai da suka haɗu da Larabawa?
A
misalin da ya kawo na waƙar Amali
ne na ce mashi gangara ne ba gargara ko kargare ba.
A
Larabce غرغر kalima ce
mai tafiya da ma'anarta wato homophone a Turance. A ma'ana ta hatshe kuma tana
nufin irin sautin ruwa idan an kurkura shi a maƙoshi. A ma'ana ta fannu kuma tana nufin rayuwa ta zo ƙarshe idan ta iso a maƙoshi ta fara bayar da irin wannan sauti.
"
Ga Garba can zamu
jiɗa/sabka,
Namijin
da noma kawa
haske.
Jagora: Sannu
da jeha kalme ga yashi....
Y/Amshi: Sannu
da.... mummuƙen laka,
Bai san wuyag gargare ba,
Ga Garba can za ni shiɗa/sabka,
Namijin da noma kawa haske
Kuma
Hausawa sun fi Larabawa zama manoma.
Amma
kuma Dr. Ƙaura takan
ɗauro Hausawa su daina amfani da kalmarsu su ɗauki ta baƙi. Misali a Zariya nakan ji Zagezagi na cewa
"wundo" madadin taga
Shin
Sa'idu "Faru yake ko Hwaru"?
Haka
fa yac ce. Wato idan an aza gargare haka za a dinga kama kuyyai ana ta noma. Da
an kai ƙarshe a
sake kama wasu a juyo ba a zamnawa sai an kai inda za a tsayawa a sha hura a
huta a ci gaba da aiki. Ka ga a nan uban kiɗa a
bayar da yadda a ke gudanar da noma cikin ƴan ɗiya kaɗan masu hikima.
Hwaru
yake amma, Malamanmu Faru suke rubutawa.
Ga
faɗa Hwaru akan faɗa. Amma
ga "Daidaitacciyar Hausa" Faru ake rubutawa ko faɗa
Ai
a ilmance gafarta Malam, tsakanin Balarabe da Bahaushe, dole ne ɗayansu ne ya ari kalmar daga ɗaya.
Shi
kuwa aro na komai yana da ƙa'ida kamar yadda masana irin su Ibn Khaldun suka tabbatar.
Idan
kuwa babu aro, sai koma ga zancen مصادفة kamar yadda wasu manazarta harshe suka
tabbatar.
In
dai a bakin Saɗu Faru ne to, gargare ya ce ba gangare ba.
Ana
maganar Amale ne.
Wani
abu da zai ba ka sha'awa kuma gafarta Malam shi ne, asalin kalmar nan a wurin
Balarabe da Bahaushe duka ɗaya ne wato: غرغر. Ya'un ɗin
nan ta farko ta lamiri ce.
Haka
a Hausa daiwar kalmar wato lexeme a Turance ita ce: gargar. Wasalin e ko a kuma
morpheme ne, kamar dai yadda ka sani.
Ka
kuwa san a ilmance ba za ta yiwu ba Larabci ya zama shi ne ya ari wannan kalma
daga Hausa.
Wani
abu da zai ba ka sha'awa kuma gafarta Malam shi ne, asalin kalmar nan a wurin
Balarabe da Bahaushe duka ɗaya ne wato: غرغر. Ya'un ɗin
nan ta farko ta lamiri ce.
Haka
a Hausa saiwar kalmar wato lexeme a Turance ita ce: gargar. Wasalin e ko a kuma
morpheme ne, kamar dai yadda ka sani.
Ka
kuwa san a ilmance ba za ta yiwu ba Larabci ya zama shi ne ya ari wannan kalma
daga Hausa.
Wani
abu da zai ba ka sha'awa kuma gafarta Malam shi ne, asalin kalmar nan a wurin
Balarabe da Bahaushe duka ɗaya ne wato: غرغر. Ya'un ɗin
nan ta farko ta lamiri ce.
Haka
a Hausa saiwar kalmar wato lexeme a Turance ita ce: gargar. Wasalin e ko a kuma
morpheme ne, kamar dai yadda ka sani.
Ka
kuwa san a ilmance ba za ta yiwu ba Larabci ya zama shi ne ya ari wannan kalma
daga Hausa.
Amin.
[12:02pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Ai gafarta Malam, duk abin da Bahaushe yake tinƙaho da shi yau na aro ne.
Malanmu
magabata a wannan fage sun daɗe da tabbatar
wa duniya da cewa Hausa harshe ce ba jini ba. Duk wanda ka daduga a ƙasar Hausa kuma zai gaya maka asalinsa.
Waɗanda ke kiran kansu Hausawan asalin ma, masana a
wannan fanni sun bayyana yadda suka samu.
[12:03pm, 02/03/2024]: Wato ni a ko yaushe na ga
ana ƙoƙarin mayar da kalmomin Hausa zuwa ga asalin na aro
daga Larabci ina mamakin shin ko an san Hausa tsohon Harshe ne wanda ke da alaƙa da Larabci da Ibraniyanci da amharic da Sumerian tun
fil azal? Ni ba masani ne game da Larabci ko Hausa ba amma dai na san akwai alaƙa sosai tsakanin Hausa da Larabci tun farko. A tsarin
da Greenberg ya yi na Harsunan Afrika ya sanya Hausa cikin babban zauren da ya
kira Afro-Asiatic wato harsunan da ke Afrika kuma suna da alaƙa da Asiya. A nan cikin Afirka kuma ya haɗa shi da Kare Kare, Bolewa, Margi, Buduma, Angas da
Sauran su waɗanda ya kira Chadic group of Languages. A sani Larabci
ba Harshen Afirka ne ba. Hausa ce da Misiranci da Habashanci suke na Afrika. Kalmomin
da suka shafi addini da yawa Hausa ta aro daga Larabci amma irin gargare da ya
shafi noma da Bahaushe ke yi tun lokacin da mutum ya zauna cikin garuruwa ya
kuma sami fasahar noma da kiwo da ƙira yaya za a yi a ce an aro kalmar daga Larabawa waɗanda ko irin noman mu ba su yi?
[12:07pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Allah ya gafarta Malam. Akwai ƙanshin gaskiya a cikin batunka. Amma, ba kalmomin addini kawai Hausa ta
ara daga Larabci ba, akwai na harshe da na ala'ada da kuma adabi.
[12:19pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
To fa! Masana Ilmin Harshe sun shigo! Ni dai a ganina noma ga Bahaushe "Na
duƙe tsohon ciniki, kowa zo duniya
kai ya tarar" ne. Ta fuskar Adabi da Falsafa, in ganin zan fi yarda da
cewa babu wanda ya san takamaimen lokacin da Bahaushe ya fara noma, sau dai
hasashe
[12:23pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:....
Ko wa zo duniya kai ya tarar.
Shi
ya sa muka ce Balarabe ya riga Bahaushe noma, domin ya riga shi samuwa a duniya.
[12:24pm, 02/03/2024] +234 812 462 9009: Me ya
ke nufi da su ne Hausawan asali? Ai duk Bahaushe na asali ne idan ba na
mu'amala ba ne.
[12:25pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Wai duk wanda ba su ba a harshen, ɗan
rakiya ne.
[12:25pm, 02/03/2024] +234 812 462 9009: Babu
wata shaidar cewa Balarabe ya riga Bahaushe a duniya. Hasali ma Gidan ɗaya ne.
[12:32pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Wallahi ya kamata mu mai da hankali ga waƙokin Sa'idu Faru. Tattaunawa kan ilmin harshe kan ɗauke hankali, a samu wani Zaure ba wannan ba. Shawara
ce kurum na bayar
[12:53pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Afuwan! Ban taɓa sha'awar Ilmin Harshe ba. Ko a jami'ar da na yi sai
da aka tursasa min sannan na ɗauki
kwasakwasansa. A lokacin ba a lura da an yi kuskure ga rubuta ƙa'idojin zaɓen
kwasakwasai ba.
[12:59pm, 02/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Shi ya sa
Malam ka gagara a kan inda ka sa gaba, Kuma sai ka kai mutun ga bango idan bai
ankara ba! 🤣🤣
[1:07pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Wallahi Dr. Haruna Ilmin Harshe ne nake ganin kamar na lissafi yake, ni kuma na
tsani lissafi don ban iya shi ba, har ma wani mallamina Bafalasɗine ya taɓa
rubutu a kan takardar jarabawata ta lissafi wai don Allah kar na sake rubuta
masa waƙa!!!
[1:30pm, 02/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Haka ne
Malam, ai duk mai tsayawa kaifi guda yakan shahara a manufofinsa muddin bai zan
raggo ba.
[1:40pm, 02/03/2024] Mal. M.A. Umar Ƙwarai kuwa prof. Musamman fannin kamanta sauti
"Acoustic phonetics". A irin ci gaban fasahar sadarwa ta ƙarni na 21, ana iya samar da manhaja wadda za a koya
mata siffofin kamannin waƙoƙin Makaɗa
Sa'idu Faru, daga bisani sai ta ci gaba da samar da wasu ɗiyan waƙa tamkar na Sa'idu Faru....
[1:49pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Assha! Watarana kuma maƙiya
Musulmi su ƙirƙiro abubuwan da za su yaudari wawayen Musulmi su ce
hadissai ne! Allah Ya yi muna kariya amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu Ya Rabbal alamina Ya Arhamar rahimina
[1:53pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ka
san akwai waɗanda suka taɓa
ayoyin Alƙur'ani?
Suka kira shi al- Furqan. Ba su san da cewa Allah Ya yi alkawalin kiyaye abinSa
ba
[2:01pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Malam Arabi wannan aiki zai yi kyau. Kuma kamata ya yi a ɗora gaba ɗaya
Waƙoƙin baka na Hausa a kai.
Ta
wannan hanya za a iya Samar da abin da masana suka daɗe suna hasashe, wato ƙirya a Waƙoƙin baka na Hausa.
[2:14pm, 02/03/2024] Dr. I.I. Dutsinma:
Anya dai dai ne a cire ilimin harshe a kan duk wani abu da za a furta ko a
rubuta?
Waƙa furuci ne fa. Furuci kuma ilimi ne na harshe.
Gaɓoɓin kalmomin da
za a samar don gina kalma, kalma ta gina jimla, jinla kuma ta gina dogon
bayani. Ta yaya za a cire ilimin harshe to?
Daga
cikin maudu'ai da za a yi nazarin waƙoƙin wannan Bawan Allah kuma akwai ɓangaren
harshe.
Ina
da rubuce rubuce a kan harshe da Adabi
da
harshe da Al'ada. Wasu kuma harshe da Waƙoƙin Baka.
Idan
dai za a furta ko a rubuta harshe na da haƙƙi. Kada a cire harshe.
[2:22pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau ya fara wannan aiki shekaru arba'in da suka
gabata. Daga bisani nazari mai suna 'gidan dara' ya rinjaya.
[2:46pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Wallahi ba ni da ja ko ƙalilan. Abin
da nake nufi shi ne mu daina gardandami a kan ko kalmar Hausa kaza daga harshe
kaza take, har mu kai ga ƙabila kaza
ta riga wata duniya, da makamancin haka. Wasu suna ganin fa'idar yin haka amma
ni gare ni waɗannan ba su ƙara muna kome ga fahimtar abin da wannan Zaure ya sa
gaba
[2:52pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Na
taɓa gani a social media inda aka ce an nemi AI da ya yi
makamancin Alƙur'ani
amma ya kasa. Hadissai ne ban gani ko ji ba.
[2:54pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Tattaunawa dai ba gardandami ba.
[3:05pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Amma ai kalmar da ake magana a kanta, an cirato ta ne daga bakin Makaɗa Sa'idu Faru.
[3:37pm, 02/03/2024] Dr. I.I. Dutsinma:
Wai kare ya mutu a saura.
Haka
ne. Ai ba za a kaucewa bambance-bambancen kalmomi ba saboda tazarar ma'ana
tsakanin kare-karen harsunan Hausa da muke da su.
Ni
Bafillatanin Katsina ne, don haka baki na na Katsinanci ne. Na ga kalmomi da
yawa waɗanda ban san su ba amma akwai su a Zamfaranci da
Sakkwatanci a wannan zauren.
Allah
Ya sa mu dace.
[6:06pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Nazari ya nuna cewa, wasu Makaɗa waƙa suke fara samarwa kafin kiɗa. A yayin da wasu kuwa kida' suka fara samarwa kafin
waƙa.
Wane
ɓangare ne Makaɗa
Sa'idu Faru ya faɗa a cikin waɗanan
rukuna biyu?
[6:46pm, 02/03/2024] Mal. B. Lauwali:
Irin wannan mahawara da Malammu su ne tabbakawa akwai darasin dauka ga kananan
dalibai irina. Su na mutunta junansu wajen yin raddi, tare da kalamai na nuna
son a gudu tare a tsira tare. Allah Ya ba mu iKon koyi da irin wannan hali nasu.
[8:01pm, 02/03/2024] Malama H.A. Mayana: Tau mu
kananan dalibbai ne Allah ya gafarta mlm zanso inji kiɗa ko waƙa wanene ya fara dashi domin in ƙara da abunda nike da shi a hannuna ni da yan uwana
dalibbai abunda nasani game da makada saidu faru shine makada saidu faru ya
koyi waƙa wurin
mahaifin shi makada Abubakar wakokinsa, suka dada kyautatuwa ta hanyar fasaha
da hikima tare da kwakwalwar da Allah ya ba shi. Tun saidu faru yana da
shekaru goma aka fara zuwa yawon kiɗa gari
gari dashi. bayan da ya cimma shekaru shashidda sai ya "soma karbi"a
wannan lokaci ne kuma aka hadasu tare da kanensa muazu wanda shine
Dangaladimansa. Baya ga tsohonsa makada Abubakar Saidu faru bai kiɗa ga kowane makadi ba dukkan salailai iri iri da yake
sakawa a wakokinsa tushensu mahaifinsa da baiwar da Allah ya ba shi ta gane
fasalin waƙa. da
tsohon saidu faru ya rassu sai ya dauki gabatar waƙa. ya sa himma da kwazo yana tayi. da saidu faru ya samu
cin gashin kansa ya fara da wata waƙa mai daɗin
gaske kunshe da tarin hikimomi ga kadan daga cikinta:Tushe Bi da
maza dan jodi na iro iro magajin shehu da Bello. Hasken hitila ba dai da wata ba,. Tauraro
haskenka subahin,. Dawa ya kora
dimau na wakili,. Uban sarkin zagi Bello na yari. Ruwa da kada dibgau na magaji,. Sai tsohon
wawa ka shigarsu. Wannan waƙar da ya fara yi ita yayiwa tsohon sarkin yamman faru Ibrahim
[8:17pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ya
salam. Allah ya ƙara sani
gafarta Malama.
Abin
da ake nufi shi ne lokacin ƙulla waƙa. An lura
Jankiɗi kiɗa yake fara
samarwa. Shi ya sa a ƙungiyarsa
ake da ƙiryoyi
gadaddi.
Amma,
Maidaji Sabon Birni waƙa yake
fara samarwa. Shi ya sa waƙoƙinsa suka
yi kama da na 'yanmata.
To,
shi ne muke neman a kallar mana Faru a gano nasa rukuni.
[8:26pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ƙulla waƙa babban ginshiƙi ne a fagen nazari. ☝️
[8:38pm, 02/03/2024] +234 703 928 3077: Salam, haka
ne, don ko a Kamus na Hausa ma'anar kowacce kalma daban, gargara magagin mutuwa,
gargare kuma kadada, wato ratsin datse da ake yi wa kunya a gona.
[9:04pm, 02/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Jamil.
Ratsin
datse ɗin shi ne gargare a Ƙamusancen, ba farfajiyar kadadar ba. Abin da yake nufi
kuma shi ne iyakar kadada ko ƙarshenta.
Ka
ga sun haɗa ma'ana da magagin mutuwa, wanda yake nufin ƙarshen rayuwa ko iyakarta.
Wallahu
A'alam.
[9:25pm, 02/03/2024] Prof. B.B. Usman: Ni
na lura cewa idan zai fara sabuwar waƙa ne yake jagorancin irin amon sautin da za a aza waƙar a kansa ne zai buɗe da kiɗa, amma idan tsohuwar waƙar da yaran sun san ta, sai ya fara da kalaman waƙar.
[11:36pm, 02/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Wato dai waƙa da kiɗanta take zuwa. Kiɗan
kuwa bai tsaya ga kayan kiɗan da akan
rataya ko busa ba. Hannu, da ƙafa da motsin wata gaɓar jiki, da
bugun zuciya duk waƙa na sanya
musu irin kiɗan da ta ƙunsa.
[9:02am, 03/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Allah gafarta Malam.
Kamar
yadda kuka karantar da mu, wannan ƙulli ne na lokacin sadarwa.
Amma,
ƙulli na lokacin shiryawa wanda
makaɗi kan yi a gida. A nan gizo yake saƙar.
An
lura da wannan yanayi ne kuam sakamakon yadda za ka iya fita wata waƙa ka shiga wata, na makaɗi, ko ta wani makaɗi daban, ba
tare da ka tantance ba.
'Ya'ya
da jikokin wasu makaɗan sai suka hutar da kansu neman sabuwar ƙirya ko sabon rauji tunda ga na gado, sai kawai su hau.
Misali:
Waƙa nikai ita ni iya,
Ita
za ni wa Sarkin Kano. (S. Faru)
Da
kuma:
Sarkin
Musulmi Bubakar,
Dattijo
Baban Macciɗo. (M. Shata)
Da
kuma:
Ga
Sarki nan an naɗa,
Kuma
ga masoya sun zaka. (S. Kakadawa)
A
hannu ɗaya kuma akwai:
Dangalin
Hausa Ubangijin su Wambai Sarki,
Mai
halin Atto na Bello ɗan Hasan ci fansa. (S. Jankiɗi)
Da
kama:
Hanƙuri yay yi Jitau muna yaba ma girma,
ɗauki
mulki kai Jallah yan naɗa ba su ba. (B. Tambaya)
Wallahu
A'alam.
[2:50pm, 03/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Kakan wani ba shi da yaƙi,
Ko can ɗandaudu
na shi,
Inda dai shahwa kwalli na,
Da
kakanai ka suna. "
[3:06pm, 03/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Waƙag ga da
nam maka Mammadu,
Na
ji daɗinta Mamman Sarkin Kudu. "
[4:57pm, 03/03/2024] +2348161747863:
Allah gafarta, barka da wannan lokaci. Makada Sa’idu Faru makadin Shiri ne. Furniss
(1996:177). Haka kuma, a hannu guda yakan shirya waƙa nan take. Makada Sa’idu Faru yakan samu baiwa daga
Allah maɗaukakin Sarki yayin shirya waƙa ko tunanin samar da ita, ko kuma ya samu bunƙasar tunani a dalilin tasirin wasu abubuwa da suke
kewaye da a muhallinsa. Tun a ƙwaƙwalwa yake
fara tsara ta, ta hanyar tunanin kalmomin da za su dace da waƙar da zai samar. Daga bisani kuma, sai ya samar da
gangar jikin waƙar ta bin
wasu matakai irin na samar da rauji da ga6ar farko ta kalma, sannan kiɗa da kalma (kalmomi) da saɗara da gindin waƙa da ɗan waƙa da kuma ɗiyan
waƙar. Wato, matakan ƙulla waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru suna iya kasancewa kamar haka:
+tunani+jagora+ƙungiya+rauji+kiɗa+kalma+saɗara+G/Waƙa+ɗa+ɗiya.
[6:08pm, 03/03/2024] +2348161747863:
Wannan yasa Gusau (2014) ya bayyana halayyar makaɗan baka na shiri ta kallon yanayin yadda suke shirya waƙoƙin nasu. Yana cewa, “ waƙoƙi na shiri su ne waƙoƙin baka waɗanda ake tsayawa a ke6e, kuma natse a tsattsara su ta
yadda za a za6o musu kalmomi da jumloli a ka ko a rubuce, a samar da murya bisa
rauji mai nagarta, sannan a ɗora musu kiɗa a kuma bi ta da rerawa”. A bayanin Malam, ya nuna
cewa, yawancin waƙoƙin shiri ana fara samar da waƙa ne kafin kiɗa. Allah
ne Masani.
[5:50am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Akwai a cikin Waƙarsa ta Yaƙin Basasar Nijeriya (1967-70) inda ya ke ƙarawa Sojojin Federal ƙwarin gwiwa.
"Jahag Gabas wada duk
kun
ka shira ta watce..
[6:38am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Akwai a cikin Waƙarsa ta
Marigayi Maigirma Ɗanmadamin
Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo
Bunguɗu.
" Kwaɗɗo
na can na kiran ruwa,
Ya
kakkace kiran su ɗai ya kai....
[6:42am, 04/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Akuɗubɗun Akuɗunɗun,
ɗan Sarki da wuyan gora،
Zauna
mu ji labarin Ƙayad da
kakai Soto. "
[6:42am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Akwai a cikin Waƙarsa ta
Marigayi Maigirma Dagacin Banga, Sarkin Yaƙin Banga Sale Abubakar.
"
Kai ni bana sai nayi
lalaben
Kwaɗɗo na kai gaban wuta.
[6:46am, 04/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Gwauron giwa Uban Galadima,
ɗan
Sambo Rungumi,
Gamsheƙa Amadu na mai Gamji,
Kai
a Uban Zagi. "
[6:50am, 04/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Amma Gamsheƙa ya ce ba
Gamshiƙan ba.
[6:51am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Shi Sarkin Yaƙi Sale
Gamshiƙan Sarkin
Kiyawa Amadu ne.
[6:52am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Sunansa Sale ba Amadu saboda haka ba zai ce masa Gamsheƙa Amadu ba.
[6:52am, 04/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Mene ne Gamshiƙan?
[6:53am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Daga kalar Maciji ne.
[6:53am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Me ne ne Gamsheƙa?
[6:53am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Maciji Gamshiƙa
[6:54am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Dabbantarwa ce.
[6:54am, 04/03/2024] Mal. A.R. Mayana: To
Gamsheƙa yake a
daidaitacciyar Hausa. A ƙara
bincikawa.
[6:57am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Gamshiƙa ne karin
harshen da Makaɗin ya faɗi. Daidaitacciyar
Hausa kuma ta na nan a wurinta.
[7:01am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ban da kai ban taɓa jin wani Ɗan Gusau da ke kiran Maciji Gamshiƙa da sunan Gamsheƙa ba.
[7:01am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Na zo Gusau tun 1978.
[7:04am, 04/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
September, 1978 ya zuwa yau ban da kai ban taɓa jin wani a Gusau yana ambatar Maciji Gamshiƙa da Gamsheƙa ba.
Amma
fa tun da ita ce daidaitacciyar Hausa ba ni da ja, sai dai kuma na riƙe wannan tawa fahimtar a matsayin madogara.
[7:57am, 04/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Haka ne
Rankaidade ai wallahi ni tsoro nike ji idan ban san mai lamba ba don kar in yi
mai wani abin da bai dace ba.
[8:00am, 04/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ilminka ya amfane ka Dr. Haruna. Allah Ya ƙara yi ma Jagora, amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu
[8:13am, 04/03/2024] Dr. H. Yelwa:
Janzakara ya yi kikiriki
Ya
tare garkag gidan ubanai
Ya
bak KWADDO yana cikin rame
Ya
mirgide tsara
[8:13am, 04/03/2024] +234 803 637 4958: Allah ya
saka da alheri. Misalin homophones a Turanci shine kamar: sort/sought, red/read
(past tense), key/quay, check/cheque, principle/principal etc. Akwai kuma
homonyms, misali: bank (financial)/bank (of a river), sound (loudness)/sound (good
quality as in sound education). In fatar ban saki layi ba.
[8:34am, 04/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Amfani kuma da 'homonym' a waƙa shi na kira salon dibilwa. Misali, Mu'azu Haɗeja a wata waƙa ya ce:
/Allah kai ka isa da isarka kai ne mai isa/ Ka isar da
masu isa isa in sun isa/
Shi kuma Kassu Zurmi ya ce:
/Ku ba shi in kuna ba shi/
/Shayi dai ɗa
na/
/Ba haka munka so ba ɗan yaro/
/Ai
mun san ɗa na tun da anka haiho shi/.
Dibilwa
a Ingilishi shi ake kira "pun"
[8:50am, 04/03/2024] Mal. B. Lauwali: Ina
rokon wannan zaure mai albarka ya taimaka min da bayanin wadannan. Bajimi da
amale da Kuma toron giwa. Na gode
[9:00am, 04/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Bajimi ko bajini> namijin nagge kosasshe ake kira bajini amma ga waƙa ko maganar yau da kullum in ana son a yaba mutum
akan kira shi bajini, wato ya ƙasura ko kuma na hannun dama, misali Bajinin Bubakar, wato na hannun
daman ko ɗan gaban goshin Bubakar
[9:02am, 04/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Amale> raƙumin da ya
ƙosa. A waƙa ko maganar yau da kullum ana nufin mutumin da ya ƙasura cinjim
[9:02am, 04/03/2024] +234 803 257 6475: To ai ko
da za 'a yi amfani da daidaitacciyar hausa, su masana harshe sun me ake
nufi da Karin harshe, Kuma dole be akwai wanna bambancin. Don haka Kamar yadda
ka fada my mum tsayu ga abinda makadin ya fada"Gamshika".
Kuma
a duk inda masanin harshe yake ban taba jin ya kyamaci wanna bambancin ba.
[9:04am, 04/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Toron Giwa> namijin giwa ke nan. A waƙa ko maganar yau da kullum ana nufin wanda ya ƙasura kamar bayanin amale/amali a sama
[6:40am, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Ina cikin daji sai Gyado ka saƙƙwata ta, Daudu da duy yag ganan ya buɗek ke haƙori.. Inji Mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba a faifansa na Marigayi Mai Martaba Ɗan Alin Birnin Magaji, Alhaji Muhammad Mode Usman mai
amshi 'Alhaji Ɗan Ali ci
fansa, abun biya ka ke ɗan Shehu'.
[12:17pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Assalamu alaikum!
Ga
mu dai cikin ikon Allah mun sake dawowa wannan zaure mai albarka.
Muna
bayar da haƙuri ga duk
wanda muka sosa wa rai. Duk wanda ya sosa namu kuma, mun yafe.
Allah
shi yafe mana baki ɗaya, amin.
Malamin
waƙa ya ce:
"Albarkar Abubakar,
Na bat shan hurad da ba nono,
Ba ni cin tuwo in ba tsokoki,
A ba ni gumi wanda adda kyau,
In
gasa yatsuna. "
Gwabron
Giwa na shamaki..............
[1:01pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu.
Madalla,
amin ya rabbal alamin 🤲🏾🤲🏾🤲🏾🙏🙏.
...
A ɓarje gumi wanda da ad da kyau in gasa/in luma yatsu na....
[3:53pm, 06/03/2024] Malama H.M. Kurawa:
"Kowas samu so ga sarki,
Ba tambaya akai ba,
Sai a gani ga riguna nai".
Bajinin
gidan...
[3:57pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
👍
... Shiryayye Uban Magaji
Garba ruwan kashin fari/hwari,
Baban
Amadu gizago
[4:07pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A halin yanzu garin Torawa na cikin Masarautar Birnin Magaji.
[4:10pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ɗan Isa da Ƙawari kuma suna nan a Masarautar Ƙaura Namoda. Ƙasar Ɗan Isa ke da hedikwata a garin Dogon Kaɗe da laƙabin
Sarautar "Sarkin Fulani".
[5:21pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Jama'a shin don Allah ko Makaɗa Sa'idu Hwaru
ya yi wa Sardaunan Sakkwato Amadu waƙa?
[6:08pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Mu ka kiɗi mu ak kiɗi,
Saboda mu Allah yaw wa,
Gudunmawa da waƙa,
Haw
wata na kiɗe/ije wata. "
[6:46pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: " Ya mirɗe maza yanzu
ba mai ƙara ja mai,
Y/Amshi: Kai
ab Bello kai ah Hassan,
Kai ad da kowa,
Jagora: Gazagurin
gidan Dange...
Y/Amshi: Duk
mai gaba da kai bai
bakwai bai sha kunu ba,
Ya mirɗe maza yanzu ba
mai ƙara ja mai,
Kai ab Bello kai ah Hassan,
Kai
ad da kowa,
Daga
cikin Waƙar
Marigayi Mai Girma Firimiyan Jihar Arewa na farko, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE
Sardaunan Sakkwato. Allah ya kyauta makwanci, amin.
Turken
Waƙa: Ya mirɗe maza yanzu ba
mai ƙara ja mai,
Kai
ab Bello kai ah Hassan,
Kai
ad da kowa.
[9:03pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Malamin Waƙa ya ce:
"Wane ba yaro ne ba,
Shekara sittin yab ba ni,
Gyaran fuska ka sa,
Ana ce mai ɗan
yaro. "
Wazame ukku ya aje don gyaran fuska,
Wanga ya zo da safe,
Wanga ya zo da rana,
Wanga guda ko yana zuwa goahon Isha'i. "
Amshi:
Sai na zo in yi mai kiɗi.......................
[9:05pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Malamin Waƙa ya ce:
"Wane ba yaro ne ba,
Shekara sittin yab ba ni,
Gyaran fuska ka sa,
Ana ce mai ɗan
yaro. "
Wanzame ukku ya aje don gyaran fuska,
Wanga ya zo da safe,
Wanga ya zo da rana,
Wanga guda ko yana zuwa goahon Isha'i. "
Amshi: Sai na zo in yi mai kiɗi.......................
1984.
[9:10pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
👍😁👌✊
Karin
Waƙar Marigayi Sarkin Kudun
Sakkwato/Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo
Abubakar III ce ya mai amshi 'Sai nazo in yi mai Kiɗi in ƙaro ilmi, Mamman bajinin Magaji mai takakkay yaƙi' ya yi amfani da shi a wannan Waƙar ta Marigayi Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji
Muhammad Kabir Ɗanbaba OFR
a shekarar 1984. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[9:15pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Tabbas Maigirma ɗanmadami.
A
ciki yake cewa:
"Lafiya Manyan Hausa,
Korau mai ɗamarad
daga,
Da gaskiya yaka komi na duniya,
Bai
san ƙarya ba. "
[9:24pm, 06/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Ina ganin wannan kamar wani salo ne da za a iya dangantawa ga Makaɗa Sa'idu Faru. kalli amshin waɗannan waƙoƙi nasa biyu mabanbanta:
Koma
shirin yaƙi,
Jandamishin
gidan Kure Abdu.
Da:
Koma
shirin yaƙi,
Jandamishin
gidan Abdullahi.
[9:44pm, 06/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haka ne Maigirma Ɗanmasani. Sai
dai kamar kusan Makaɗan Baka na da wannan ɗabi'ar.
Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi irin wannan salon a Waƙoƙinsa na Marigayi Mai Martaba Sarkin Misau Muhammadu Manga da Marigayi
Sardaunan Dutsi, Senator Bello Maitama Yusuf.
Amshin
Waƙar Sarkin Misau shi ne "Ci
da ƙarfi Mamman Manga ya bi da arna,
ƙi sake mazan daga".
A
faifan Bello Maitama Yusuf kuma yana cewa "Ci da ƙarfi Mamman Bello ya bi da arna, ƙi sake mazan daga".
Makaɗa Ibrahim Narambaɗa
Tubali a faifansa na Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III (duk da
yake ba rerawarsa ba ce, rerawar Halifansa Ummaru Mai Sa'a ce) yana cewa "
Tattaki maza ɗan Shehu na Gatau, Abubakar Uban Sarakuna".
Sai
kuma a cikin wata Waƙar tasa ta
Dagacin garinsu (Tubali) Magaji Shadawa yana cewa "Tattaki maza ɗan Shehu na Babba, gamda'aren Salau mazan ƙwarai".
Ba
batun Dr. Mamman Shata Katsina ake yi ba, shi da yana iya yi wa mutum 100 Waƙa da amshin Waƙa guda ɗaya,
musamman amshin da ya ke cewa "Sadauki Shehu Magajin Mamman"
da kuma "Haka nan ne Mamman Ƙanen Idi wan Yelwa". Allah ya kyauta makwanci, amin.
[6:30am, 07/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ko alama Maigirma Ɗanmasani. Ta
Sarkin Kudun Sakkwato ta riga ta Sarkin Katsinan Gusau domin ko a shekarar 1981
da Malamin waƙa ya je
Birnin Magaji wajen Ɗan Alin
Birnin Magaji Muhammadu Mode Usman ya rera ta a matsayin Waƙar Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo a gabanmu. Ta Sarkin Katsinan Gusau kuma ya yi ta ne
a wajen naɗinsa a shekarar 1984.
[7:31am, 07/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Malamin Waƙa ya ƙara da cewa:
"Sarkin
Katcinan Gusau na yau jikan Modibbo,
Allah
yab ba ka duniya,
Kyauta
sai Allah. "
Amshi:
Sai
na zo in yi mai kiɗi................
[7:42am, 07/03/2024] Fugus Isa Sarkin Fada:
Allah Ya ƙara sani. Mu
daliban ilimi muna fa'idantuwa kwarai.
[8:40am, 07/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Tabbas!
Manyan
Malanmu a wannan fage sun daɗe da lura da
wannan yanayi.
Gusau
(2014) ya dunƙule
yanayin ya zana masa duna ɗani a Waƙoƙin Baka na Hausa. Ƙarshe kuma ya karkasa shi rukunna.
✊✊✊😃
[9:14am, 07/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Sir! Na tuna wani ɗa:
"Ka
ba ni gida kuma ka ba ni gona,
Kai
mani Sarkin kiɗin Gusau,
Don
in dawo nan,
In
da ko kai hakan ga da,
Korau
ka kyauta.
Amshi:
Sai
na zo in yi mai kiɗi...........
[9:55am, 07/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Aikin rinjaya yay yi
makaye,
Ya
kwan da shirin maza,
S/Kabi
gamda'aren
Kilodi".
[10:23am, 07/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin Maigirma Ɗanmasani.
Waƙar Marigayi Maigirma Sarkin Kabin Keɓɓe, Jihar Sakkwato Alhaji Labbo ce.
Kilodin
da yake ambata laƙabin
Sarautar wani Ƙauye ne da
ake kira Margai a cikin Gundumar Keɓɓe ɗin. Daga gidan sarautar Keɓɓe ake tura wanda ke yin Dagaci a Margai. Shi kansa
wanda aka yi wa wannan Waƙar ya taɓa zama Kilodin Margai kafin ya ci sarautar Keɓɓe. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[2:12pm, 07/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haƙiƙa Allah ya gafarta Malam. A Margai ne aka haifi
Honorable Alhaji Lawali Labbo, shi ne dalilin da ya sa ake kiransa da sunan
Margai ɗin a cikin sunansa.
Ya
taɓa zama ɗan
Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato a lokacin mulkin Malam Yahaya Abdulkarim Mni
Sarkin Rafin Sakkwato na NRC kafin ya sake dawowa Majalisar har ma ya zama
Speaker ko a lokacin mulkin Garkuwan Sakkwato, Alhaji Attahiru Ɗalhatu Bafarawa ne (?).
[9:39pm, 07/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Tun da muna tattaunawa ne akan Makaɗin
Sarakai da Sarakai da Sarauta ne, ga wata ɗabi'a
nan ta cire Alkyabba idan wani Saraki ya haɗu
da wani Sarakin.
A
wannan bidiyon☝️☝️☝️Mai Girma Galadiman Kano ne, Alhaji Abbas Sanusi aka cire wa Alkyabba
yayin da suka haɗu da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad
Abubakar III CFR. Ko wane sharhi zamu samu akan wannan ɗabi'ar daga masananmu? ☝️☝️☝️
[10:09pm, 07/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Lalle irin wannan ɗa'a akwai ta. Haka nan wurin gaisawa da juna. Sarakunan
suna sane da waɗanda ke tsaye ƙiƙam da masu duƙawa. Misali,
idan Sarkin Kano zai gaisa da Sarkin Musulmi to shi ne zai ɗan durƙusa idan a tsaye suke musabaha, shi kuwa Sarkin Musulmi ya kasance a
tsaye ba tare da durƙusawa ba.
Tsakanin
talakkawa kuwa gaisuwa kan banbanta daga nahiya zuwa nahiya. A Kano ko da babba
ya miƙa hannunsa
ga na ƙasa da shi
domin su yi musabaha, to ƙaramin ba
zai kama hannun babba ba, saɓanin yadda abin
yake a Sakkwato. Na kasa canzawa da nake karatu a BUK. Idan malamaina suka ba
ni hannu sai in kama, abokaina Kanawa su kuwa sai na ga duk sun kauce. Wani abokina
har da ce min ya yi ai ba a karɓar hannun babba
a yi musabaha amma wallahi na kasa yi
[10:12pm, 07/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ka lura sosai musamman Kano da Zariya. Ban Sam ma Katsina ba
[10:16pm, 07/03/2024] +234 802 663 3308: Mafi
yawanci an fi ɗabbaka wannan al'ada ta girmamawa, a tsakanin Sarki da
sauran masu riƙe da
sarautu.
Yana
daga cikin girmamawa, idan Basarake ya zo gaida Sarki dole ne ya cire alkyabba,
koda kuwa a kan Doki ne za a yi gaisuwar.
[10:57pm, 07/03/2024] +234 812 462 9009: Wato ɗabi'a ko al'adar saukar da alkyabba idan wani Sarki ya
haɗu da Sarkin Musulmi tana faruwa tsakanin Sarkin
Musulmi da Sarakunan da aka bai wa tuta daga Shehu Usmanu ko Muhammadu Bello ne.
Da na san wannan abun ya kan faru duk lokacin da ɗaya daga cikin waɗannan sarakuna suka ziyarci Sarkin Musulmi a Sakkwato
kawai ba a ko'ina suka haɗu ba. Wannan yana nuna cewa da yake shi ne matsayin
wanda ya ba su tuta to a lokacin haɗuwar
shi kaɗai ne Sarki. Amma da ya buga ya saukar da alkyabbar
sai kuma ya mayar.
[11:00pm, 07/03/2024] Malama H.M. Kurawa:
Akwai wani kakana hakimi a masarautar Kano, kunne 2 yake yi. Watarana mun taho
Kano da shi, daf da za mu shigo, sai na ga ya lanƙwashe kunnuwan rawaninsa sun koma ciki.
[9:34am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ko da aka yi Jihar Zamfara Shinkafi da Birnin Magaji ne ba Ƙananan Hukumomi ba daga cikin Ƙananan Hukumomin Jihar 14.
[9:35am, 09/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Tabbas Maigirma ɗanmadami. Allah ya ƙara girman daraja.
Babban
abin cewa dai shi ne, wannan aiki na Gusau ba zai wadatar ba a wannan taro, domin
Fwaru ya rayu na tsawon wani lokaci bayansa da, abubuwa da dama sun faru a
rayuwarsa.
Lalle
ne a yi wa aikin kashin ƙanfa a
yanzu.
[9:37am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Anka da Gummi da Bukkuyum da Bakura da Talata Mafara da Maradun da Maru da
Bunguɗu da Gusau da Tsafe da Ƙaura Namoda da Zurmi ne Ƙananan Hukumomi 12 da ke yankin Zamfara a lokacin da
aka ƙirƙiro ta watan Oktoban shekarar 1996.
[9:40am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haka ne, yana ɗaya daga cikin aikin da wannan babban taro zai yi In
Shaa Allah. Nasan Masananmu da Manazarta suna akan bincike domin ƙwaddamu.
[9:41am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Daga Kamfani 47 dake Tsohon Lardin Sakkwato, 15 ne ke yankin Zamfara a lokacin
da aka ƙirƙiro Jihar Zamfara a shekarar 1996.
[9:42am, 09/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A lokacin
muna makaranta kuma hankalinmu bai yi karfi ba!
[9:43am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Kamfanonan kuma sune:- Anka da Gummi da Bukkuyum da Bakura da Talata Mafara da
Maradun da Maru da Bunguɗu da Gusau da Ɗansadau da Kwatarkwashi da Tsafe da Ƙaura Namoda da Zurmi da Moriki.
[9:44am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Daga baya aka yi kamfanin Birnin Magaji da Shinkafi.
[9:44am, 09/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: "Ga
kamfani ya buda ya kasa ku diba ku tahi! Inji Sani Sabulu Kanoma.
[9:46am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Kamfanin Moriki da Kwatarkwashi da Ɗansadau ba su yi sa'ar zamani ba, sai ba su zamo
hedikwatocin Ƙananan
Hukumomi ba kamar yadda sauran yan uwansu 12 suke tun gabanin samun Jihar
Zamfara.
[9:49am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Madalla. Makaɗa Abu Ɗan Kurma Maru zuriyar su Makaɗa
Ibrahim Gurso Sarkin Makaɗan Talata Mafara kenan. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[9:49am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A shekarar 1987. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[9:51am, 09/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Madallah Hon. Sir. Haƙiƙa Gusau ya kwatanta ga yin adalci saboda ko bayan nuna
shekarar da aka buga wannan littafi, ya kuma nuna shekarar da ya shirya shi.
Kada
a manta a 1987 akwai ƙarancin ƙwararrun masu buga littaffai a Arewa, sannan kuma
akwai ɓata lokaci kafin a buga ta fuskar kamfanoni da fuskar
mawallafa. A halin yanzu ga yadda na san Farfesa S M Gusau a matsayin mawallafi
kamar shanshani kuma da ake da kamfanoni masu buga aiki ya fito da kyawo kamar
yadda yake buƙata, ina
kyautata zaton cewa tsawon lokacin da yake ɗauka ya buga littafinsa bai wuce watanni shidda da yardar Allah
[9:51am, 09/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Amin Ya
Hayyu Ya Qayyum. Ka makadan dauri, shi har makarantar allo yake da ita a
gidansa inda yake karantar da yara.
[9:55am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Sai dai waɗan nan Kamfanonan na nufin Gundumar Uban Ƙasa/Hakimi.
Wasu
tun kafin 1903 lokacin da Turawan Mulkin Mallaka na Ingila suka ƙwace mulkin a hannun magabatanmu suke da wannan
matsayin, misali Gusau da Kaura Namoda da Zurmi da Anka da Tsafe da Bunguɗu sun daɗe
da irin wannan matsayin. Ɗansadau ta
zama hedikwatar gunduma ne a cikin shekarar 1939, lokacin da Turawan Mulkin
Mallaka suka haɗo garuruwan Kuyambana da Ƙasar Daraga (Ɗankurmi) da Ɗangulbi suka yi Gundumar Ɗansadau da hedikwata a garin Ɗansadau.
[9:57am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Kamfanin da Makaɗa Abu Ɗan Kurma Maru ke magana na Furojet/Waldibankin duniya kuma na nufin
Service Center/Gidan Gona/Gidajen gona inda Malamin Taki da Malamin gona ke
zama domin hulɗa da manoma.
[10:01am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Madalla da wannan ƙarin
bayani Ranka ya daɗe. Haƙiƙa Farfesa
Sa'idu Muhammad Gusau zaƙaƙuri ne, samuwarsa a wannan bagire ba ƙaramin arziki ba ne zuwa garemu. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.
[10:11am, 09/03/2024] Prof. A.B. Yahya: A
shekarar da muke karatun M. A. (Hausa) mu biyar, shekara guda ake iya yin sa a
BUK, amma mu biyu, da shi da ni, ne Allah Ya ba ikon kammalawa cikin shekarar
guda
[10:19am, 09/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ranka ya daɗe akwai wasu abubuwa da kuke yi kai dashi dake burgeni
sosai.
Kun
zamar muna fitila mai haskaka muna domin fita daga cikin duhun jahilci. Ba ku
rowar ilimin da Allah ya baku, ba kamar wasu takwarorinku da ke ɓoyon ilimi ba. Allah ya ƙara maku lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.
[10:23am, 09/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Gusau saurin wallafa ne da shi, malamin da ya duba shi naci da sauri ne da shi.
An gamu an dace ke nan. Ni kuwa kamar kunkuru nike amma mallamin da ya duba ni
mai naci ne da sauri. Ka ga ni kamar tursasa ni aka yi😂
[11:26am, 09/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Yakan fi haka gafarta Malam. A ɗan matsatina na
ƙaramin ɗalibin turakarsa ta karatu na san bayan baiwar da
Allah ya yi masa a fagen wallafa, yakan ɗauki
lokaci sosai yana bauta wa rubutu. Da yawa a raina nake kwatanta shi da Zuhairu
Ibn Abi Sulmah.
[3:01pm, 09/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Wallahi Maigirma ɗanmadani.
Shekaru
fiye da 30, duk lokacin da Gusau yake kan wata wallafa muna ganewa:
1)
Sau da yawa sai dai abincinsa na dare ya iske na rana kan tebur. ƙatshe kuma ko ɗaya
ba zai ci ba dai bayan sallar Isha'i.
2)
Idan kuma ya fito ban-iska gad da Magriba, za mu ga jininsa ya tafasa sosai, ba
ya son magana da kowa.
Haka
zai koma bayan ɗaki ya zauna shi kaɗai
abinsa.
To,
da mun ga haka mun dan akwai sabon aiki tafe.
Sai
dai ina ba wa Malam Gusau haƙuri. In a yi ta kama yi ake yi. Idan baba ta jiƙa kuwa sai rini. 🤣🤣🤣🤣🙏🙏🙏
[9:04pm, 09/03/2024] Dr. A.R. Bakura:
Idan an ce gyara, wato an yi kuskure ke nan. Sai dai a ce akwai ƙarin bayani. Saboda a daidai wannan lokacin Maradun da
Bakura duk sunan cikin ƙaramar
Hukumar Talata Mafara ne, tamkar yadda Bungudu ke cikin Gusau, Maru ta kasance
a Anka. Da fatan an fahimta.
Shi
ya sa muke cewa, Gobir bata cikin Hausa Bakwai. Turawan Mulkin Mallaka ne suka
tunkuɗe Zamfara suka kawo Gobir domin su sami gindin zama.
[12:08am, 10/03/2024] Dr. A.R. Bakura: Idan
ana maganar sauran Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau, zan Iya cewa babu na biyunsa.
Tun sanina da shi, na san shi mutun ne marar kasala kuma haziki marar ƙeta ga aiki tukuru kamar injin.
Ina
tunawa, muna ɗalibta a A. T. C. Maru, shi ne Shugaban Sashen Hausa, kuma
ya koyar da masu share fagen fara karatun EN, SI, I, kuma ga EN, SI,
I, 1&2. A ajinmu mun Kai kusan 50, idan ya tara aikin jingar da ya bayar
yau gobe cikin ikon Allah zai mayar muku da ita bayan ya gyara kura-kurai. Hasali
ma ya ƙayyade ƙarancin shafukan da za a gabatar masa wadanda ba su
kasa 10 ba.
Shi
ne malamin da na ga ya ba ɗalibansa
handout mai shafi 212, kyauta a daidai lokacin sai da ya yi amfani da keken
rubutu aka tafa a sitansil kana aka gurza. Ya yi wa aikin suna: Nazarin
Za6a66un Waƙoƙin Baka Na Hausa. An kammala tafa aikin cikin watan
Agustan 1984.
Nawa
na nan, har an yi mini tadarishinsa.
Farfesa
Gusau halayensa na gado ne. Ya taso babban gida na ilimi da malanta tare da yi
wa al'umma hidima domin gina su.
Shi
ne wanda ya Soma aza ni kan tafarkin bincike da wallafe-wallafen littafin. Har
kullum da mun haɗu sai ya tambaye ni sabuwar wallafar da na aiwatar. Muna
daɗa rokon Allah ya ƙara masa lafiya da yawan rayuwa mai albarka. Ya Kuma
jiƙan iyaye da kakanni. Ya haskaka
kaburburansu. Ya arzutta shi da cikawa da Imani. Amin.
[11:55am, 10/03/2024] +234 803 852 9952: Lallai
Farfesa S. M. Gusau kam bai yi rowar ilimi ba. Hannayensa masu albarka sun bai
wa alkalaminsa dama ya rattabo mana tarin ilimin da yake kimshe cikin
kwakwalwarsa wadda zuciyarsa ta hararo a fagen adabi da kuma tarihi. Allah
Ta'ala ya ƙara mana
irin su. Allah Ta'ala ya sanya mu a danshinsu.
[12:02pm, 10/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Na'am. Sirrin shi ne Gusau ya wadatu ne, da baiwar da Allah ya yi masa, ya kuma
gode. Ya tsaya inda Allah ya aje shi, ya kuma miƙa wuya ga hukuncinsa.
Duk
kuwa wanda ya ɗauki irin wannan tafarki, Allah ba zai tozarta sa ba.
[2:02pm, 10/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Ikon Allah. Maigirma ɗanmadami. To, lalle ni ne ban ji daidai ba.
Yadda
ka jiya ɗin nan shi ne daidai.
Ba
mujamala ce na yi ba. Ka fi ni nutsa cikin wannan sha'ani. Allah ya ƙara sani.
[9:32pm, 10/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma
sha Allahu. Wani abu da na lura da shi shi ne irin wannan bayani naka Hon yana
da matuƙar amfani.
Dalilina shi ne yadda muke saka sunayen 'ya'yanmu ta amfani da sunayen magabata,
domin neman lada da kuma tuna baya. Idan zamani ya yi tsawo sai ruɗani ya kutso, shin wanen nan shi ne wane? Idan babu
bayanai irin waɗanda kake yi sai a kasa ganewa. Misali, mutane da yawa
sun ɗauka cewa Nana Uwar Daje ita ce Nana Asma'u 'yar Shehu
Usmanu, alhali wadda ake kira Nana Uwar Daje sunanta Maryam kuma wasu masana
sun ce ita ma 'yar Shehu Usmanu ce kamar Asma'u matar Waziri Giɗaɗo.
[9:37am, 11/03/2024] masters dtj: Gaskiya ni ma
na sami waraka daga wannan bayani. Domin a da na yi zaton cewa Nana Uwar Daje
ita ce Nana Asma'u. Wallah saboda tsananin ƙauna da nake yi wa wannan baiwar Allah yanzu haka ina
da 'yata mai sunan Nana Asma'u. Allah ya gafarta wa magabatanmu.
[2:44pm, 12/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Kashi bakwai kak kwasa,
'Yan Sarki na kallo,
Gidan Bani kai kak kai,
Ga
irin wagga martaba. "☝️☝️
[4:57am, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Kashi bakwai kak kwasa
yan Sarki na kallo,
Gidan bani kai kak kai
ga irin wagga maslaha,
Dud gidan bani kai kak
kai ga irin wagga maslaha,
Ga ka ɗan mai daraja,
Ga ka jikan Usumanu
kurɗabi na fodiyo,
Ga ka Sarkin nasara,
Ga ka Alhaji Macciɗo,
Ga jikka ta yi dubu,
Ga ka mallami ka ke,
Ga ka mummuni ka ke,
Abin da Allah duk kai
ma
mutun Baba yai maka".
[5:31am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa Hon sir. A binciken da na yi na gano ce wannan Nana Uwar Daje sunanta
na yanka Maryam, ta kuma haifi ɗiya da aka sa
mata suna Maryam. Don haka ita maifiyar aka yi mata laƙabi da Nana Uwar Daje. Nana kuwa laƙabin girmamawa ne kamar Modibbo da ke nufin Malama. Nana
kuwa watakila na nufin "shugaba". Wasu wurare ba lalle sai mai suna
Maryam ake wa laƙabi da
Nana ba. Maryam dai da muke magana a nan 'yar Shehu Usmanu ce
[5:35am, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Madalla da wannan ƙarin
bayani Ranka ya daɗe.
Ita
Nana Asma'u matar Malam Usman Giɗaɗo Ɗan Lema tagwaye/tawaye ne, ita da Hassan ɗin ta. Ina kyautata zaton Hassan ɗinta
ne mahaifin Malam Halilu Sardaunan Sakkwato na farko wanda Amirul Muminina
Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya fara naɗawa a matsayin Sardauna ya kuma kai shi garin Marnona
a matsayin Sarki/Hakimi.
[5:39am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma
sha Allahu. Hassan ɗinta ya riga ta rasuwa da nisa
[6:08am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Ana iya tabbatar da wannan idan an koma ga littafin: "Collected Works of
Nana Asma'u.... " Na J. Boyd da Mark.
[6:11am, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
J. Boyd ta yi wani aiki akan Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi
Muhammadu Bello Macciɗo Abubakar III da ke nuna an haife shi a shekarar 1926,
ba kamar yadda mafi yawan manazarta/masu sharhi suka tafi akan cewa an haife
shi a shekarar 1928 ba.
[6:19am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Sir! Kamar yadda kuka karantar da mu, wannan ɗabi'ar marubuta ce, musamman tarihi.
Farfesa
Gusau a ayyukansa akwai wurare da dama da ya nuna an haifi Mujaddadi Shehu
Usmanu a 1745. A wasu wuraren kuma ya nuna 1754.
Wasu
marubuta sukan buga lissafi ne da shekarar Hijiriyyah, a yayin da wasu kuma suke
bugawa da Miladiyyah.
Wasu
kuma ajizanci ne irin na 'yan adamtaka.
Wallahu
a'alam.
[6:22am, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haƙiƙa Maigirma Ɗanmasani kuma hikimar da ke cikin irin wannan
lamarin shi ne ke bayyanar da ajizancin da ka ambata, Allah ya datar damu, amin.
[6:26am, 13/03/2024] Malama H.M. Kurawa:
Na taɓa ganin irin wannan, sai na yi zaton musayar gurbi ne:
45/54 daga wajen ɗaɓi.
[6:31am, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Malama wani lokaci akan samu hakan ta fuskar ɗaɓi tabbas.
[6:38am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Dangane da alƙaluman da
Gusau ya bayar a nan ina kyautata zaton cewa rikicin na'ura ne, musamman
kwamfuta. Sau da yawa wasu kalmomi masu ƙarewa da "i", ga misali, na'ura kan mayar
"i" ɗin da yake karami zuwa babba, "I". Inda
Gusau ya shigo a nan bai wuce rashin lura wanda duk marubuci bai tsira gare shi.
[6:42am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa. Rikicin na'ura ne. A wayata da kwamfuta nakan samu haka muddin ban
taskace ba
[6:49am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Allah gafarta Mal. Ai wasu daga cikin waɗannan
ayyuka nasa, an yi su ne tun kafin fasahar Kwamfyuita ta zo mana.
Amma,
ina da yaƙini har ga
Allah cewa, akwai wani dalili ko wata hujja da ya dogara a kansu.
Sau
da yawa jigon wallafa kan haifar da irin haka.
Wallahu
a'alam.
[6:55am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Sake tambayar sa. Gusau mai nazari ne, ba sai ga littaffan Shehu Usmanu zai
samu shekarar haihuwarsa ba.
[7:01am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ko
mai bugun tafureta kan yi irin wannan tuntuɓe
[7:04am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Akan samu tuntuɓe har a harshe, a rubuta kalmar Ingilishi alhali
harshen da ake rubutu da shi wani ne daban
[7:15am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Tabbas! Shi ya sa nake cewa, duk abin da ka ga Gusau ya rubuta, yana da hujja
kuma mai ƙarfi.
[7:18am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Tabbas. Ni ban ɗauka abin da Gusau ya rubuta kuskure ne ba. Ban kuma
ce ba ya kuskure ba. Amma, ina cewa ne, yana da hujja a kai, domin ba ya ƙwai sai da zakara.
[7:42am, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Waye ni? Ni ɗin me? Me aka yi aka yi ni? Ana babbakar giwa ai ba za
a ji ƙaurin kusu
ba.
[10:15am, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ƙauna ƙarfi ne da ita. Sai ta hana masoyi ganin laifin masoyinsa ko da rana
tsaka, kai ko da wasu na ƙoƙarin su kare masoyin daga abin da ke kusa da shi ba da
yinsa ba sai masoyin ya tsammaci liƙa masa za a yi..
[12:22pm, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Na taɓa rubuta wata jinga da wani malamina ya ba ni. To
da yake Bature ne don haka cikin Ingilishi na rubuta aikin. Sai bayan ya gama
gyara ya zo aji da takardata. Kamin ya ba ni sai ya ce in zo in yi masa bayanin
wata kalma da ya kewaye da jan biro. Shi dai ga shi Baturen Ingila amma ya kasa
ya fahimci wace kalma ce na rubuta cikin aikin da na rubuta cikin Ingilishi.
Duba
kalmar ke da wuya sai na ga ashe Hausa ce na rubuta. A takaice kalmar Ingilishi
da na yi niyyar in rubuta sai na rubuta kalmar Hausa da take ma'anar ta
Ingilishi ɗin. Wallahi ban san yadda aka yi na rubuta ta ba. Haka
ya auku ne lokacin da ina karatun digiri na biyu.
[12:48pm, 13/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Allah
Sarki, ai abin a zuuci yake. Haka ne watarana wani Malamin yana yi mana wata
public lecture sai ya yi amfani da kalmar handamise! Sai na ga mutanen kudanci
da ba su jin Hausa su fito da dictionary suna neman ma'anar kalmar.
[12:51pm, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Na taɓa jin wata kalma "Political Gigita" da ake
ta'allaƙawa zuwa
ga Shaihin Malaminmu Mahdi Adamu Ngaski, Allah ya kyauta makwanci, amin.
Ko
gaskiya ne shi ya ce hakan, ko ba shi ba ne, Allahu Wa'alam!
[12:52pm, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Shi wannan kila da sani ya yi amfani da kalmar. Amma ni ba da sani ba. Ina jin
ma kalmar "wanda" ce na rubuta a madadin "which" da yake
aikin cikin Ingilishi ne na rubuta ba Hausa ba
[1:22pm, 13/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ni
ma na taɓa ji daga bakin wani Dr. Educationist a Buk, ya ce:....
Handamization.
Amma
wannan ba kuskure ba ne tsananin gwaninta ne a harshe. Malamin yana sane ya yi
wa dawonsa miya.
[1:38pm, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Idan kana so ka tambai Prof S M Gusau a keɓe, Malam
mene ne salon hauhawa? Kuma mene ne asalinsa? Da kyar idan bai sa tambayar mala
ba, ko ya ce ka tambai wanda ya turo ka 😂😂
[1:39pm, 13/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ba
zai faɗa ma ba saboda ladabi. Ko ni ma haka sai kaɗan. Cikin aji ne asalin kalmar
[2:58pm, 13/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ai ya
sade kalmar ko ina yana iya amfani da ita, na san a lokacin mulkin Sani Abacha
ne, sai ya "under your regime Muhammad Sani people are allowed handamising
government property?"
[4:04pm, 13/03/2024] +2348161747863: A
kodayaushe Malam Gusau yakan koɗa tare da ɗaga darajar abokin karatunsa. Da nuna wa ɗalibai irin baiwa da Allah ya yi masa ta ilimi. Wannan
yasa kusan idan ka zauna da Malam Gusau a aji ko a gida, sai ya ba ka labarin
wannan aboki nasa mai albarka. Har yakan bada labarin lokacin da suke ajin Baba
ɗangambo, a cikin hanyoyin nazarin salo akwai ‘sauka’
da Baba ɗangambo ya kawo, a nan take wannan aboki na Malam
Gusau shi ma ya ƙirƙiro sabon salo da ya kira da ‘HAUHAWA’.
Muna
addu’a Allah ya ƙara muku
lafiya, ya kuma albarkace mu da ilimin da Allah ya ba ku.
[7:58pm, 13/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Shi Sarkin Yaƙin Banga
Sale Abubakar/Sale Ɗan Abu/Salihu
Abubakar ya yi Sarauta a cikin 1930s zuwa cikin 1960s. Saboda haka ya shaidi
mulkin mallaka na Turawa dake yin D. O/District Officer da a lokacin Jami'in
mulki ne a matakin yanki kamar Ƙaura Namoda inda can ne Dagacin ke biya a hukumance.
Kenan
an yi lokacin da D. 0n dake duba yankin Ƙaura Namoda Baturen Ingila (Jan D. O) ne. To
shi ne fa Malamin Waƙa mai
kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ke tabbatar ma Sarkin Yaƙi cewa ko kusa kada ya razana ko da kuwa zasu yi
arangama da D. O ko da Bature ne ballanta lokacin da aka samu mulkin kai, aka
kawo D. O ɗan Ƙasa saboda Ƙasar ai
asali tasu Sarkin Yaƙin ce, kowa
ya shigo ya shigo cin arziki ne.
[8:50am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
👍👍👍
"Su
Boƙoboƙo ana zanne ana kumburin wuya,
An
kashe kunya an bakka kana zanne gungume".
[8:51am, 14/03/2024] Alhaji Badamasi Sarkin Ƙaya Maradun.: Gaka sarkin NASARA..
Gaka
MALAMI kake..
Gaka
MUMMUNI kake..
ƘURƊABI na HODIYO..
[8:52am, 14/03/2024] Alhaji Badamasi Sarkin Ƙaya Maradun.: Shin Wai dan Allah mi maƙaɗa ka nuhi da
"GUNGUME"
Ko
irin itacen nan da ake ɗaure mahaukata ?
[8:53am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Kashi bakwai kak kwasa yan Sarki na kallo,
Gidan bani kai kak kai ga irin wagga maslaha,
Dud gidan bani kai kak kai ga irin wagga maslaha,
Ga ka ɗan mai daraja,
Ga ka jikan Usumanu kurɗabi na fodiyo,
Ga ka Sarkin nasara,
Ga ka Alhaji Macciɗo,
Ga jikka ta yi dubu,
Ga ka mallami ka ke,
Ga
ka mummuni kake,
Abin
da Allah duk kai ma mutun Baba yai maka".
[8:57am, 14/03/2024] Alhaji Badamasi Sarkin Ƙaya Maradun.: Yallaɓai
ai "GUNGUME" ko daukuwa baiyi ko? 😆
[8:59am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Sai dai mirgina kenan Ɗangaladima.
Kaga dai rashin amfani ya sake bayyana.
[9:01am, 14/03/2024] Sarkin Rafin Gobir
Kuɗabi
Shin
Yana kwatanta shi ne da Littafin kurɗabi
yu dari zuhudu kaƙi Duniya ɗan malan,
[9:04am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ƙwarai kuwa Maigirma Sarkin
Rafin Gobir domin hanyar Kakansa Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da yake akai.
[9:07am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Kowab bi Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo a
cewar Malamin Waƙa zai
tsira duniya da ƙiyama
saboda kau horo shi kai akan ayi daidai a kuma daina abun da ba daidai ba
tamkar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi na nan a raye.
[9:34am, 14/03/2024] Sarkin Rafin Gobir
Maigirma Danmadami Birnin magaji, niko na yi zaton yana kwatanta muhammadu
maccido ne da Littafin kurɗabi saboda
tarihin Wanda ya Rubuta shi, kasan abukanai ne guda biyu asalan suna-atare
akodayaushe bayanda sukasamu wani dogon lokaci basuhadu ba, da ɗayan yasamu labarin bayan rabuwarsu ɗayan ya yi Arziki sosai duniya tasamu sai shi ɗayan yashiryo Mai tahiya takanas tare da tsara wannan
waƙen Wanda idan ka kalura da
waken ko littafin gabaɗai yana hani ne da kwaɗayin Duniya da sha'awa abinda acikinta, shine dalilin da Almajirai
kayima littafin kirari da zuhudu kaƙi Duniya ɗan
malan
[9:37am, 14/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Babu mamaki Maigirma Sarkin Rafin Gobir, dama wannan abun da na gabatar tawa
fahimta ce la'akari da abubuwan da aka jero a cikin ɗiyan Waƙar har ya zuwa ƙarshe.
[9:41am, 14/03/2024] Sarkin Rafin Gobir
Duk daine fahimta mu, abin nuhi sakon makada yakai ga maigidansa da Kuma
Al'umma sugane cewa mutun ne Mai tawaliu da kaucema kuɗayin Duniya s/m maccido Allah yajikan shi da Rahama
[3:17pm, 14/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Jama'a, adabi fa ba wahayi ba ne. Muddin manazarcin adabi yana iya kafa hujja
ga iƙrarinsa
daga adabin da yake nazari, to ya kamata a mutunta ra'ayinsa. Ƙololuwar abin da wani mai nazari ke iya yi shi ne ya
kawo wani ra'ayi ba tare da ya soke ra'ayin wani ba. Ta haka ne ilmin adabi ke
ginuwa.
[6:21pm, 14/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Gabas ga
Sakkwato,
Ni
Sule mai Zurmi nis sani,
Ban
san kowa ba.
[12:11am, 15/03/2024] Dr. A.R. Bakura:
Wannan zancen fari ne fes ba wani surki. Musamman idan aka yi la'akari da yadda
duniya ta zama kusa sakamakon cigaban zamani.
Bai
dace ba a soke wani aikin da magabatanmu suka aiwatar a can baya, ko da mutun
yana da kwakkwarar hujja. Abin da ya dace, a fagen ladabi shi ne, sai a nuna
cewa, Allah ne bai nufi hannayensu da dafa wannan fage da shi ya kafa hujja da
shi ba.
Wannan
shi ne cikakken ladabi a fagen nazari.
[10:45am, 15/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A rana mai kamar ta yau, 15/03/amma fa a shekarar 1903 ne Turawan Mulkin
Mallaka na Ingila suka ci Cibiyar Daular Usmaniya wato Sakkwato da yaƙi wanda aka yi a Giginya. Haka ma dai a wannan ranar
ce a shekarar 1903 a garin Dange hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange/Shunin Jihar Sakkwato ta
yanzu aka haifi Malam Abubakar ɗan Malam Usman ɗan Malam Mu'azu ɗan
Malam Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi wanda ya zama
Sarkin Musulmi a ranar 20/06/1938 da laƙabin Sarkin Musulmi Abubakar III.
Allah
ya jiƙan
magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
[11:47am, 15/03/2024] Dr. I.I. Dutsinma:
Slm
Amma
kuma wasu littafan tarihin na nuni da 1908 aka ci daukar Usmaniyya da yaƙi
1903
idan zan iya tunawa an haifi Sarkin Musulmi Abubakar ne a 1903. But i stand to
be corrected.
[11:49am, 15/03/2024] +234 703 232 2222: Wannan
maganar ai Babu jayayya a ciki na cin Daular Hodiyawa a alif 15/03/1903
Babu
ko jayayya a ciki
Akramakallahu
[11:56am, 15/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu. Allah ya gafarta Malam zance
mafi shahara dai shi ne an ci Sakkwato a ranar 15/03/1903 kuma a ranar ne aka
haifi Sarkin Musulmi Abubakar III.
[12:13pm, 15/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Sun tarad da Sarkin Musulmi Muhammadu Attahiru I ɗan Sarkin Musulmi Ahmadu (Zaruƙu) ɗan Sarkin
Musulmi Abubakar I/Abubakar Atiku/Mai Katuru ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ke mulki. Ya ci
sarauta ranar 13/10/1902 ya zuwa wannan rana ta 15/03/1903 lokacin da ya fita
daga Sakkwato zuwa Ɓormi dake Ƙaramar Hukumar Mulkin Funakayen Jihar Gombe ta yau
inda a can ne suka bishi suka kashe shi a watan Yulin shekarar (1903).
Bayan
fitarsa daga Sakkwato ne suka naɗa
Muhammadu Attahiru II ɗan Aliyu Babba ɗan
Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio a matsayin sabon Sarkin Musulmi a ranar
21/03/1903, ya kuma yi mulki har zuwa shekarar 1915.
Saboda
haka idan ance an ci Sakkwato a shekarar 1908, to kenan a lokacin mulkin Sarkin
Musulmi Attahiru II ɗan Aliyu Babba ɗan
Bello ɗan Shehu ake nufi wanda ba haka abun ya ke ba.
[12:23pm, 15/03/2024] +234 812 462 9009: Ai
yadda maganar take shi ne da yake akwai Sakkwato ita ce helkwatartar Daular
Usmaniyya kuma an ci ta da yaƙi ranar 12/05/1903 har ma Sarkin Musulmi Attahiru I ya yi hijira ya bar
gari an naɗa wani daga ranar nan ne za ya ɗauka an ci Sakkwato ko da ko ba ci sauran sassan ta ba
sai daga baya.
[8:40am, 18/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Assalamu
don Allah a turo man waƙar Malamin
Waƙa ta.. inda yake cewa
Gamshikan
Amadu na mai Gandi.
Can
gaba ya ce
Shi
ko tuji da ad da girman baki....
Dan
nan bubukuwa da tar tura
[10:16am, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Zama
Giwa ta fito kiyo tai miƙa ta zo ta
sha ruwa,
Y/Amshi: Kuji
Ɗan Zomo na hwaɗin hwaɗama su Tsari, Tsara
mu tai gida
Daji ya ɓaci
kaa a take mutum baƙi aa'
akwai ciki,
Jagora/Y/Amshi:
Daji ya ɓaci kaa a take mutum baƙi aa' akwai ciki,
Jagora: Gurnanin
Damisa ka sa mahwarauta sun ɗora ɗemuwa,
Y/Amshi: Ga
wani ya yi Kokuwa da wan ƙarfi nai,
Ya hwaɗi ya kare,
Tun ba a tantance ba shi na nishi ya lanƙwanshe tsara,
Jagora/Y/Amshi:
Tun dai ba a tantance ba shi na nishi ya lanƙwanshe tsara,
Jagora: Ko
jiya na iske Gamdayaƙi da Tuji
sun iske Jinjimi,
To sun ko murɗa
gardama,
Sun iske su Bubuƙuwa ruwa,
Y/Amshi: Dan
naan niko ina gaton gaɓa,
Sai nik kwaɗa
gaisuwa,
Su ko sun daƙile ni dud,
Niko niƙ ƙara gaisuwa,
Dan nan Kulmen da ac cikin gurbi ya amsa gaisuwa,
Jagora: Dan
nan sai Jinjimi da yad darzaza ya suntule shi dud,
Y/Amshi: Shi
ko Tuji da ad da girman baki yak kwashe Jinjimi,
Dan nan Bubuƙuwa da tar rura tag gangame su dut,
Jagora/Y/Amshi:
Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani,
Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani,
Y/Amshi: Gwabron
Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo
Ginshimi,
Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi,
Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi,
Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi,
Daga
cikin Waƙar
Marigayi Mai Girma Dagacin Banga, Masarautar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar (wanda ya yi Sarauta daga shekarar
1934 zuwa wafatinsa a shekarar 1963), Ta Makaɗa Sa'idu Faru mai taken "Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, Gamshiƙan Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi. Rubutawar
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin
Birnin Magaji, Jihar Zamfara.
Talata,
21/11/2023.
[2:46pm, 18/03/2024] Malama Maimuna Sulaiman:
Assalamu Alaikum Ina yi wa kowa fatar alhairi, Allah ya karbi ibadunmu. Muna ta
ƙara godiya ga iyayenmu da
Malamanmu bisa wannan namijin ƙoƙari da
suke yi. Allah ya saka da aljannah.
Don
Allah Ina neman alfarma idan akwai Mai hotunan tsuntsayen nan, da Makada Sa'idu
Faru ya lissafo a waƙan nan ya
turo muna. Nagode.
[3:00pm, 18/03/2024] +234 703 232 2222: Hmmm
Ai
Wagga Magana Bata ko Karin bita akan abunda kahhwadi
Sai
dai Kawai a samu Karin Aiki a group
Tunda
Kowa ya yi Laushi Kamak Karen da yassha Rana 🐶........ 😅
Maigirma
Danmadamin Birnin Magaji
Ho
da hwamag giginya....... 🙈
[3:06pm, 18/03/2024] +234 703 232 2222: Kabi, Kaabi
Kawuce Ba garin Zama ba ta Kanta
Makiyin
Ku Wanda yab bauce Ku....... 😅😁😅😁
[3:07pm, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin Alaiki Salam Warahamatullah Wabarakatuhu, amin.
Za a turo waɗan da ke akwai, a kuma turo sauran da ƙila ba a samun su a wannan yankin namu a halin yanzu sai masana su taimaka muna da sunayensu.
[3:28pm, 18/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Beguwa. Na taɓa jin ana kiran ta, ƙayam maƙaya. Idan aka rutse ta sai ta sako ƙayar da ke jikinta. Kariyar da Allah Mahalicci Ya yi
mata ke nan.
Ita
kuwa bushiya dunƙulewa take
yi idan aka rutse ta, duk wanda ya taɓa
ya soke kansa. Kada ma komi yunwar da yake ji, sau guda zai taɓa ta bisa rashin sani, ba zai ƙara ba. Na ga haka a TV da ke nuna halittu
[8:48pm, 18/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Lafiya jikan Usumanu×2
Mujaddadi
na daɗa, Babu kokwanto,
Farilla
ba nafila ta ba. "
Hattara
Sarkin Kudun Hausa.
[10:41pm, 18/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Tsuntsun da zai kama kifin kamar zalɓe
[10:41pm, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Malam me ne ne Karfasa?
[10:43pm, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Mai kasada Zalɓe/Zalɓi...
[10:44pm, 18/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Jan tsuntsun nan kuma sunansa Dale.
Muna
yara idan muka je korar tsuntsaye da ke cin gero har waƙa muke yi wa wannan tsuntsun.
Misali:
"Dale
na ba ni shawa,
Ba
irin buwa ta ba,
Kafin
in jefa bindo,
Ga
dame goma ta ci. "
[10:45pm, 18/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Zalɓe tsuntsu ne mai dogon wuya kuma ya fi yin farautarsa
a bakin ruwa inda yake kama kifi
[10:45pm, 18/03/2024] Mal. M.A. Umar
Kifin da tsuntsun ya kamo, ana kiransa gargaza.
[10:47pm, 18/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Daga cikin hotunan nan akwai:
Dale
Buwa
Shaho
Mujiya
Kwala
Balbela
Botaro
Tcaddi
Waiwaya
[10:48pm, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
😁😅🙏... Shi kuma Malamin Waƙa mai kwana ɗumi
na Mamman na Balaraba yana cewa "Na ishe Dale tai ƙawa ga jama'at ta ba ƙawa", a cikin faifansa na Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin
Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III mai amshi 'Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai'.
[10:56pm, 18/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ya kan tura ƙafarsa a
cikin rame/ramin da ya tabbatar akwai Maciji a ciki. Ya kan gume yatsun ƙafar da ya jefa a cikin ramen/ramin idan Maciji ya haɗiye ta sai ya buɗe
yatsun a cikin bakin Maciji ya fito dashi waje abun kalaci ya samu kenan.
Wannan
ɗabi'ar ce ta sanya Bahaushe ke yi wa Zalɓe/Zalɓi kirari
"Mai Kasada", har ma wasu daga cikin Mawaƙan Baka Na Hausa su ka saka wannan batu a cikin wasu
Waƙoƙinsu.
Dr.
Mamman Shata Katsina a Waƙarsa ta
Sarkin Sulluɓawan Katsina/Hakimin Kaita Suleiman Usman Nagwaggo (Sule
Jikan Korau) ya ke ce masa "Mai kasada Zalɓe/Zalɓi..../ amshin Waƙar shi ne " Na gode Sule jikan Korau".
[5:38am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Dale
[5:39am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Mujiya
[5:41am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Shaho
[5:42am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Tcaddi/tcalli/shaboli
[5:46am, 19/03/2024] Prof. A.B. Yahya: To
me ya sa kuma ake kiran wannan tsuntsu da 'yas sha-boli ko 'yatc-tcaddi?
[6:02am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari A
ɗan bayani da na samu shi ne wai tana shan boli (fitsari).
Tcaddi kuwa wannan tuma da take yi, domin ba fafiya take yi da ƙafa ba kamar sauran tsuntsaye
[6:09am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Botaro
[6:11am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Buwa
[6:14am, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Goto
[11:55am, 19/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Kakan wani ba shi da yaƙi,
Ko can ɗandaudu
na shi,
Inda dai shafa kwalli ne,
Da kaka nai ka suna.
Da madubi nai da hoda,
Da farar riga da kore,
Da gani nai ka ga ?????
Geme
cinjim da shuni. "
[2:24pm, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Katsinawa na da wata rawa da ake yi mai suna "moli" kuma ga dukkan
alamu a wajen wannan tsuntsun aka samu wannan rawar
[2:35pm, 19/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Mu
ma Gusau 'yar moli muke cewa da ita.
[2:44pm, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Ban yi mamaki ba domin Gusau wani yanki ne daga cikin ƙasar Katsina
[9:20pm, 19/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Wata ƙil kamar
flamingo kenan, rawar da wasu jajayen fata suka kwaikwaya daga tsuntsu mai
wannan suna.
[11:26pm, 19/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Salaam. Ina cigiyar wata waƙa da ake cewa:
"Da kare, da biri da baƙar mussa,
Suna gardamar dogon bindi,
Sai tsari yaz zaka yaw wulga,
Yac ce na fi ku tsawon bindi,
Tunda ni ka koro maza daji,
Su bar iri wajen shuka,
Fakkara tac ce da mun tone,
Jaka tac ce da mun huta,
Akuya tac ce ba ku huta ba kam,
Don saishe mu akai a sawo damma,
A aza miki dole ki kawo su,
Jaka tac ce ba dole ba kam,
Don tuma nikai in yasshe su,
In sheƙa dole a kamo ni. "
Don Allah wa ya yi wannan waƙar?
Ina za a same ta?
Ina kamun ƙafa ga ma'abuta ilimi na wannan zaure.
Na gode
Naku
Haruna Umar Maikwari.
[1:33am, 20/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Akwai dai hikima ta fuskar yadda Bahaushe yake ganin waɗannan dabbobi; da kuma dangantakar rayuwarsu da ta
Bahaushe; idan aka natsa za a fahimci cewa mawaƙin ya wakilta wasu rukunan mutane masu halaye daban
dabam, da waɗannan halittu
[3:49am, 20/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Jama'a
kowai yi tuwon gishiri,
Da
mi yaka kayan miya?
[5:40am, 20/03/2024] Malama H.M. Kurawa:
Malam da ina karantawa sai na ji raujin kamar ba irin na Sa'idu Faru ba. Allah
ya sa a dace, mu ji.
[8:26am, 20/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ba
waƙar baka ce ba. Wasu
gutsattsarin kalmomi ne a cikin sigar waƙa. Ina tunawa an koya mana su muna Firamare:
Da kare da biri da baƙar mussa,
Ana rigimar dogon bindi,
Sai tsari yaz za ka yar ratsa,
Yac ce ku tsaya duk na fi ku,
Ni ne mai koro maza daji,
Su baro tsabarsu wurin shuka,
.....................
[9:37am, 20/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Haba! Ni
fa na kasa tunawa sai waƙar siyasar
NPN ta Dankwairo inda yake cewa;
Da
kare da biti da bam mussa,
Bannar
da kukai an gane!
[10:08am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Jitam mai Ƙaura,
Garba
amanaɗ
Ɗanmaliki".
[10:24am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Duhun buda...
Baya
ɓad da Giwa
ƙarya a kai".
[10:45am, 20/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Radda kay yi shukka tah hito da mi kaka noman shukat?
Amsa
muna tambayar, mu amsa maka taka.
[11:05am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Da ku masu bakandama
Da ku masu jalalaini..
Y/Amshi: Ku
tabbata danƙo Mu'azu
ya yi ishiriniya
Jagora: Ni
mai ishiriniya ta waƙa
Danƙo ƙanen Gyaɗa
mai kwana Kiɗi
Y/Amshi: Domin
ni dai in ana bamu
ba gajiya nikai ba ramtsat turu nikai,
In turu yam mace,
Mu ja attafiyatu azzakiyatu mu sallame,
Mu ɗauko tabbayyada
abilahabi watabbama,
Mu jawo yash shamsu walluhaha,
Waƙa muyi ta ɗori sai tai wata guda sai zaƙi takai,
Cakwai zad daɗin
bugu,
Gwabron Giwa,
Jirayi
gaba ɗan Amadu..
[1:33am, 20/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Akwai dai hikima ta fuskar yadda Bahaushe yake ganin waɗannan dabbobi; da kuma dangantakar rayuwarsu da ta
Bahaushe; idan aka natsa za a fahimci cewa mawaƙin ya wakilta wasu rukunan mutane masu halaye daban
dabam, da waɗannan halittu
[3:49am, 20/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Jama'a
kowai yi tuwon gishiri,
Da
mi yaka kayan miya?
[5:40am, 20/03/2024] Malama H.M. Kurawa:
Malam da ina karantawa sai na ji raujin kamar ba irin na Sa'idu Faru ba. Allah
ya sa a dace, mu ji.
[8:26am, 20/03/2024] Mal. A.R. Mayana: Ba
waƙar baka ce ba. Wasu
gutsattsarin kalmomi ne a cikin sigar waƙa. Ina tunawa an koya mana su muna Firamare:
Da kare da biri da baƙar mussa,
Ana rigimar dogon bindi,
Sai tsari yaz za ka yar ratsa,
Yac ce ku tsaya duk na fi ku,
Ni ne mai koro maza daji,
Su baro tsabarsu wurin shuka,
.....................
[9:37am, 20/03/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Haba! Ni
fa na kasa tunawa sai waƙar siyasar
NPN ta Dankwairo inda yake cewa;
Da
kare da biti da bam mussa,
Bannar
da kukai an gane!
[10:08am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Jitam mai Ƙaura,
Garba
amanaɗ Ɗanmaliki".
[10:24am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Duhun buda...
Baya
ɓad da Giwa ƙarya a kai".
[10:45am, 20/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Radda kay yi shukka tah hito da mi kaka noman shukat?
Amsa
muna tambayar, mu amsa maka taka.
[11:05am, 20/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Da
ku masu bakandama
Da ku masu jalalaini..
Y/Amshi: Ku
tabbata danƙo Mu'azu
ya yi ishiriniya
Jagora: Ni
mai ishiriniya ta waƙa
Danƙo ƙanen Gyaɗa mai kwana Kiɗi
Y/Amshi: Domin
ni dai in ana bamu
ba gajiya nikai ba ramtsat turu nikai,
In turu yam mace,
Mu ja attafiyatu azzakiyatu mu sallame,
Mu ɗauko tabbayyada
abilahabi watabbama,
Mu jawo yash shamsu walluhaha,
Waƙa muyi ta ɗori sai tai wata guda sai zaƙi takai,
Cakwai zad daɗin
bugu,
Gwabron Giwa,
Jirayi
gaba ɗan Amadu..
[6:42pm, 23/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Gardaye zo ka yi man iso,
Fwaɗa mashi murna
niz zaka,
ɗan Sardauna jikan Hasan,
Babban
ɗa ga Baura Sarkin Kudu. "
[10:49pm, 23/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ɗan Sardauna jikan Hassan...
Ɗan Sir Ahmadu Bello GCON, KBE Sardaunan Sakkwato, Firimiyan
Jihar Arewa na farko kuma na ƙarshe.
Jikan
Hassan....
Jikan
Sarkin Musulmi Hassan ɗan Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.
Babban
ɗa ga Baura...
Sarkin
Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan Modibbo Usman ɗan
Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi.
[5:15am, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Modibbo Usman ɗin nan shi ne mahaifin Abubakar III. Mahaifin Usman da
Hassan guda ne, wato Sarkin Musulmi Mu'azu. Hassan shi ya riƙa Abubakar III kuma kamar yadda al'adun kasar Hausa
suka tanada, mutum yana dubin ɗan'uwan mahaifi
a matsayin mahaifi. Don haka Abubakar ya kasance mai tsananin riƙon Hassan a matsayin mahaifi kuma Hausawa sun fi ɗaukar mutum a matsayin ɗa ga ɗan'uwan mahaifinsa, dalili ke nan da mawaƙa ke ambaton Abubakar III da ɗan Hassan.
[6:12am, 24/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haƙiƙa Ranka ya daɗe!
Shi
kuma Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan
Modibbo Usman ne, kenan Mahaifinsu ɗaya
da Sarkin Musulmi Abubakar III.
Dalilin
hakan ne Ɗan Tumba
Rungumi ya kwatanta Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar III da "Babban Ɗa" ga Baura. Allah ya jaddada masu rahama, amin.
[6:21am, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa! Ya kamata a yi wani bincike ta nazarin waƙoƙin baka na tsofaffin mawaƙa, ba na yau ba, da nufin a fito da al'adun Hausawa da
m'anoninsu kan shiga duhu ga manazarta da baƙi. Wannan zai iya farfaɗo da wasu kyawawan al'adu da matasa a yau ko dai suka yi watsi da su ko
kuma ba su san su ba.
[6:32am, 24/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haƙiƙa Ranka ya daɗe
wannan abun so ne ko da lamurran da muke ciki na gushewar kawaici da mutunci na
samun kwaskwarima.
Ina
iya tunawa a watan Afrilun shekarar 1996 bayan an ayyana Sarkin Kudu Muhammadu
Macciɗo Abubakar III a matsayin sabon Sarkin Musulmi, ni da
sauran abokan aikina da ke ɗauko rahoto
daga Fadar Gwamnatin Jihar Sakkwato muka tarbi Sarkin Sudan Na Wurno Shehu
Malami domin muji ta bakinsa akan lamarin.
A
cikin tambayoyin da muka yi masa akwai wadda muka ce masa mun yi tsammanin shi
ne zai kasance sabon Sarkin Musulmi bayan cire Sarki Ibrahim Dasuƙi. Amsarsa ta bamu mamaki matuƙa, domin ya sanar damu cewa "muddin ɗiyan Sarkin Musulmi Abubakar III suna buƙatar wani abu, to ni kuma na ba wannan abun baya har
abada, kuma zan yi iyakar yi na domin ganin sun mallaki wannan abun, saboda ban
san daɗin Mahaifina ba kamar yadda nasan daɗin Mahaifinsu". Allahu Akbar!!! Allah ya jaddada
masu rahama, amin.
[7:04am, 24/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin Maigirma Ɗanmasani.
Ko
an san dalilin kiran Shehu Malami Sarkin Sudan da laƙabin "Na'aɗɗa
kuwa?
[7:17am, 24/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Daga wata hadimar gidansu ce da ake kira "Aɗɗa" wadda ita ce ta yi hidima dashi tun bai wuce ɗan shekara biyu zuwa uku ba.
Mahaifiyarsa
ta rasu ne wajen haihuwar ƙanwarsa dake bi masa, saboda haka ita "Aɗɗa" ce aka damƙawa alhakin kula dashi. Wannan ne dalilin shaƙuwarsu har ya kasance ana kiransa da nata, wato
"Na'aɗɗa".
A
wata tattaunawa da na yi da ita ta nuna mani jin daɗinta na ganin akwai sunanta a cikin sunan Sarkin Sudan
Shehu Malami da ya sanya sunan nata ya shiga duniya. Ta kuma bayyana godiyarta
zuwa ga Sarkin Sudan Shehu na yadda ya riƙe ta da amana da mutunci da kyautatawa.
[7:33am, 24/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Sunan Maton Sarkin Sudan alferi ya hi mugunta".
[7:34am, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Aikin Bunza manazarta da dama sun yi irinsa kamin sa. Abin da nake nufi a karaɗe waƙoƙin mawaƙa da dama da nufin zaƙulo tarin al'adun Hausawa da ke neman su shige duhu. Misali,
a kan wace al'ada ce Hausawa ba su cika ambaton sunan mahaifa ba? A wani taro
da na taɓa halarta a kan waƙar Najeriya ta Shehu Shagari kuma shi ma yana wurin a
matsayin baƙo na
musamman, an gabatar da shi da sunan, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari. Lokacin
da zai yi jawabi sai ya fara da cewa sunansa Shehu Shagari.
Haka
za ka yi ta gani ga magabata, kuma akwai ƙalilan cikin matasan yau, suna yin haka. Akwai Ibrahim
Gusau da Abdu Sakkwato da Yahaya Gusau da Abubakar Imam da Sa'adu Zungur da
Mu'azu Haɗeja da Yusufu Kanta da mafi yawan sarakunanmu. Babu
sunayen mahaifa liƙe ga
sunayensu. Na ga Prof. Ibrahim Muhammad Malumfashi yakan rubuta Ibrahim
Malumfashi kwanan nan.
[7:35am, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Sosai! Musamman kafin Hausawa su iya karatu da rubutu
[7:48am, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Su
kansu mawaƙan abin ya
shafe su: Salihu Jankiɗi da Musa Ɗanƙwairo da Ibrahim Narambaɗa
da Aliyu Ɗandawo da
Barmani Coge da dai sauransu
[12:01pm, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Masu yin ma Hausawan ne. Mai da ruwa rijiya ba ɓanna ba
[12:03pm, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Haka ne. Waƙar ma na
cikin al'ada. Ta cika ta batse ne saboda haka ta zama mai cin gashin kanta!
[12:05pm, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Mamman Gawo Bahaushe ne da ya iya karatu da rubutu.
[12:25pm, 24/03/2024] +234 806 409 4889: Na zaka
in yi ziyara,
Ganin Muhammadu ni daɗi yaka yi min,
Inda duk giwa tat tashi tay yi girgiza,
Tai mika tar rufe wuri,
Sai ka ga yan namu suna gudu suna kwanto wasu na kare
wasu.
Karyar banza rijiya takai,
Ruwa na gulbi na garainiyya.
Kamfarakin Sarkin Kiyawa ginshikin alkali,
Baba gwarzon Galadima zaure mijin gida.
Ga waƙa nan wadda nay yi ma,
Da, tara ta mun bar takwas gida,
Sai in kai murnan zakkuwarmu,
In aika ko yanzu su taho,
Mu ka kiɗi, mu
ak kiɗi saboda mu,
Allah yay yi wa gudummuwa,
Da waƙa ha wata na ije wata.
Taron bara da munka zo Kaduna,
Ka ciri lamba naj jiya kwarai,
Sarkin Yawuri dai aka fadi,
Uban tafiya lardin wadanga duk,
Sarkin nan ya kammala kwarai da kyawo,
In ji wadan Rigachikun,
Sa'ad da Bature yay yi dariya,
Da yag ga mutane Yawuri,
Suna da haske ga wasu na ta wagara.
Ga wani sarki ba shi da zagi,
To kuma sannan bai da guzuri,
Garin rogo dai suka ta ci da guru,
Kowane na aza ruwa.
Taho da shirin daga,
Ginshikin Galadima namijin jiran maza,
Amma shi ko har da dama dama,
Ga wani sarki na ta kumburi,
Da yaranai sun sha mashi fura.
Ga wani kambolon uban kasa,
Da yara nai wajjen guda hudu,
Ba ko mai suturar kwabo hudu,
Ya shiga mota ya yi tagumi,
Da kwandon dunya yay yi guzuri.
Na zaka in ziyara,
Ganin Muhammadu ni daɗi shi ka yi min.
Allah bar min Mamman na Audu,
Mu kuma Allah bar mashi muwa.
________
Barkan mu da hutun karshen mako
Allah ya karbi ibadan mu
Mu
sha ruwa lafiya.
[9:25pm, 24/03/2024] Alh. A. Nakawada:
Congratulations to the organisers in advance.
Allah
Yasa wanga taro ya gano muna 6oyayyun wakokin Sa'idu Faru, wadanda ga alama
wasun su sun salwanta. Wasu kuma zasu salwanta idan ba ayi himma aka taskace su.
Misali,
akwai waƙar nan da
nake ta jan hankali akan ta, mai amshin: "na zaka in yi ziyara wurin
Galadiman Birnin Kano
Arna
tsoro nai su kai". Ita wannan waƙar wasu bayanai masu qarfi sun nuna Galadiman Kano
wanda Tijjani Hashim ya gada, aka yi wa ita. Ance kuma mutumin Sa'idu Faru. Na
tabbatar kuwa a zaman shi da shi ya yi mashi waƙa fiye da ɗaya.
Akwai ire-iren wadannan wakokin da ya kamata mu yunqura mu zaqulo domin
taskacewa.
[9:38pm, 24/03/2024] +2348161747863:
Assalamu alaikum. Allah gafarta malam barka da war haka. Makada Sa’idu Faru
wace waƙa kuwa ya
yi ta karshe a rayuwarsa kuma wa ya yi wa ita?
[10:04pm, 24/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Lalle kam! Ashe haƙata ta
kusa cimma ruwa: Taron nan na Sa'idu Faru da Waƙoƙinsa ya roƙi Jami'ar
Tarayya ta Gusau ta naɗa Hon Ɗanmadami a matsayin Rumbunan Waƙoƙin Hausa na Baka!
[1:37am, 25/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ko
waɗanne waƙoƙi suna da wannan matsala ta salwanta. Na baka kan salwanta saboda a ka
suke ba a rubuce ba; su kuwa rubutattu mafi yawan mawallafansu ba su cika
damuwa da baza su ba, musamman masu ilmin Addini. Ba wai ba su sha'awar su ba, a'a
taƙwa da tsufa kan yi tasiri ga
haka. Amma waɗanda suke ganin waƙoƙinsu wa'azi ko nasiha ne ƙwarai sukan so su taskace su su baza su.
Misali, Wazirin Gwandu Alhaji (Dr.) Umaru Nassarawa Birnin Kabi da Ɗangaladinan Wazirin Sakkwato Alƙali (Dr.) Bello Giɗaɗawa ƙwarai suka so ganin an taskace waƙoƙinsu a diwanoni. (B. B. Usman yayin bincikensa kan waƙoƙin Wazirin Gwandu, A.B. Yahya yayin nasa bincike kan waƙoƙin Dangaladima da kuma tattara diwanin mawallafin, duk sun tabbatar da
haka.)
[1:44pm, 26/03/2024] Mal. M.A. Umar
Assalamu alaikum...
Ko
ana samun ɓurɓushin Hadisi a
wasu daga cikin waƙoƙin Makaɗa
Sa'idu Faru? Idan ana samu, ina miƙa ƙoƙon bara.
[1:51pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Amin Alaika Salam Warahamatullah Wabarakatuhu. Daga cikin Waƙar Sarkin Kudun Sakkwato/Sarkin Musulmi Muhammadu
Macciɗo Abubakar III mai amshi "Kana shire Baban Yan
Ruwa, Na Bello Jikan Ɗanfodiyo"
aka samu waɗan nan ɗiyan
Waƙar 👇. Me za a kira
wannan kenan?
Jagora: Alhamdulillahi
shukurni
Y/Amshi: Rabbil
alamina ni nau nuhi,
Jagora/Y/Amshi:
Ka san Kiɗi ba karatu ba na,
Mui
astangafari in mun gama,
[1:53pm, 26/03/2024] Mal. M.A. Umar A
tura mana ire-irensu, za su taimaka wajen fito da abin da ake hasashe insha
Allah!
[1:56pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Malam suna yi ke nan?
[2:05pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A duba wasu daga kalaman "Jagora" a cikin waɗan nan ɗiyan
Waƙar ƙila a dace da ɓurɓushin abun da ake nema Malam. ☝️
[2:33pm, 26/03/2024] Prof. A.B. Yahya: To
Dr. Muhammad Arabi Umar, ya kamata ka yi muna tsokaci kana danganta waɗannan hadissai da ɗiyan
waƙar. Zan yi mamaki in ƙaru ƙwarai kuma in sake tunanina kan zurfin ilmin Sa'idu Faru.
[2:44pm, 26/03/2024] Dr. S.S. Abdullahi:
Salam, wani dalibi kuwa yana farautar "Karin Magana a Farfajiyar Tafashen
Sa'idu Faru" wadanne daga cikin wakokinsa ake samun wadannan diyan Waƙa? Hon Danmadamin BMJ Bismillah!
[2:57pm, 26/03/2024] Prof. A.B. Yahya: A
hasashena kusan duk inda ka ji Faru ya kawo maganar dabbobi ko tsuntsaye ko
zambo to to ba za a rasa karin magana ko tatsuniya ciki ba.
[3:52pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Mai kabrak Kiɗi zo ka sha Waƙam mu kyauta/banɗas
Y/Amshi: Kuma in baka kuɗɗin
Kiɗi Dogo da wayo...
[3:55pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Na ishe Dale tai ƙawa ga jama'at ta ba ƙawa...
[4:00pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Duka al'amarin duniyag ga ko mi na ne,
Wani
mayen wani...
[4:02pm, 26/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Salaam. Ko me Sa'idu Faru ya ce game da gine-ginenmu?
[4:12pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:....
Kuma ka bani Rihenin da zamu ci tare da barwai na.... A cikin Waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar Garba mai amshi 'Gwabron Giwa na
Shamaki baba Uban Gandu, Abu gogarman Magaji mai kamsakalin daga'.
[4:23pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:...
Zama kai ag ginshiƙi, kana
tsaye bango baya razana ko da an shekare ruwa.../Ga bangon Shigafa nan. Ya yi
wannan kalamin ne a cikin Waƙar Sarkin Yaƙin Banga
Sale Abubakar mai amshi "Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, Gamshiƙan Amadu Na Maigandi Kai aa Uban Zagi '.
[5:08pm, 26/03/2024] Mal. H.U. Maikwari
Lallai akwai abin da ya dace a tsinta a wannan ƙaulin.
Mun
godiya Maigirma Hon (Dr) Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji. Ɗanmasanin Waƙar Baka.
Bajinin
Adabin Baka.
[5:40pm, 26/03/2024] +234 803 443 2042:
"Zama ɗaki
ko yana ruwa,
Muazu ai ya dara wuri,
Koda Sarkin yaƙi na yi man rowa,
Na
bar biyar wani"
[6:54pm, 26/03/2024] +234 705 558 5055: Allah Ya
ƙara sani Dr. ko a kwai in da
Sa'idu Faru ya kawo baitoci masu dauke da sifofin launi
[7:21pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: Kakan
wani ba shi da yaƙi ko can Ɗan Daudu na shi
Y/Amshi: In
da dai shahwa kwalli na da Kaka nai ka suna,
Da madubi nai da hoda,
Da hwarar riga da kore,
Da gani nai ka ga Kure,
Geme
cinjim da shuni
A
cikin Waƙarsa ta
Marigayi Maigirma Sarkin Zamfaran Zurmi Suleimanu Muhammadu Sambo mai amshi
"Babban Bajinin Gidan Sambo shirinka daban da raggo, jikan Mamudu Sarkin
nasara Baban Baraya".
An
samu kalar fari da shuni/Ɗanyen haki
a cikin waɗan nan ɗiyan
Waƙar.
Kore
da ya ambata anan ba na launi ba ne, na nau'in sutura/riga ne.
[7:37pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Kamar haka na ce Malam Imrana. Barkammu da shan ruwa dafatar Allah ya karɓi ibadunmu, amin.
[7:41pm, 26/03/2024] +234 803 443 2042: Barkan
mu juna ranka ya daɗe. Sai naga kamar kore
[7:43pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Akwai Koren akwai Kuren a cikin ɗiyan
Waƙar.
[7:53pm, 26/03/2024] +234 803 443 2042: Koren na
launi da kure na Sarkin fawa
[7:56pm, 26/03/2024] Alh. A. Nakawada:
Toh. Ai na aza kure na hyena 🤔
[7:57pm, 26/03/2024] +234 803 443 2042: Halayyar
su guda, duka biyu.
[7:57pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A'a, Kore ba na launi ba ne a wannan bagiren. Kalar Riga ce da ake kira Kore. Ya
ambaci riguna guda biyu, farar riga da kuma kore, kenan farar rigar na iya
kasancewa Kwakwata ko girken Nupe ko girken Zazzau sai kuma gashi da wata rigar
nau'in/siffar da ake kira Kore, gemen nashi kuma cinjim da kalar Shuni. Shi
kuma ya zama Kure/Sarkin Fawa/Mahauci/Barundaye/Barunje/Barunji/Runji.
[7:59pm, 26/03/2024] +234 803 443 2042: Lalle
akwai riga kore
[8:00pm, 26/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Siffar shigar Sarkin Fawa ce ya kamanta.
[9:17pm, 26/03/2024] +2348161747863:
Makada Sa’idu Faru bai fiya baddala nassin hadisi ba a cikin wakokinsa sai dai
ya yi ishara ga nassin ko ya furta wasu kalmomi wadanda za a iya karfafar su da
nassin hadisi. Amma bai fiya kawo hadisi kai tsaye ba ko a baddale.
[10:40pm, 26/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ashe? Kore ai rigar ta samu sunan ne daga launin kore, wato tsana (launin
shuka)
[6:14am, 27/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ikon Allah! Ranka ya daɗe ashe riga kore sai mai kalar shuka/launin kore?
[6:24am, 27/03/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ganin na yi kuna maganar launi na ga kamar ba ku gane Sa'idu Faru yana maganar
riga mai launin kore yake nufi ba. Kore kuwa tsanwa ake nufi, akwai sutura kore
kuma ga da kore abin ƙawa ne (kila
har ga yau). Ko ka lura da wani rawani sa Sardauna yake naɗawa?
[6:28am, 27/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ƙwarai kuwa na san wannan
rawanin na Marigayi Maigirma Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello GCON, KBE.
[6:54am, 27/03/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma
sha Allahu. Amma ko ni ne ban fahimci Sa'idu Faru ba Hon. ? Don Allah faɗa mini don kada in zauna cikin duhu
[7:08am, 27/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A'a Ranka ya daɗe ƙila taka fahimtar kai da Malam Imrana Mukhatar Mafara ce daidai bisa ga
tawa.
[12:00pm, 27/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
Kore a ma'ana ta harshe na nufin kalar tsanwa.
Amma
a ma'ana ta fannu kamar yadda Makaɗa
Sa'idu faru yake nufi wata nau'in riga ce da aka rina sosai da baba har tana
walƙiya.
Wasu
Hausawa kai tsaye suna ce wa wannan riga baƙa.
Dubi
abin da Dr. Mamman Shata ya ce:
"Kyawon
dattijo ya sha shuni,
Tsoho
ko yai fara da baƙa. "
Rawanin
da aka yi masali da shi irin wanda Sardauna ke naɗawa shi ma irin wannan rini ne ake yi masa. Amma, sunansa 'ɗankura'
Tabbas,
riga fara da kore/baƙa da
rawani ɗankura kayan ado ne na ƙasaitattun rundawa. Amma, an wayi gari duk wanda ya ji
gishiri, na iya caɓawa.
Barkarmu
da Asuba.
[9:46pm, 27/03/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Fwarin maciji cizonka ba dahi,
A
yi gumba a sha a samu lafiya,
Gumba
ko ba cizon ƙwaro
taimako takai. "
[3:22pm, 29/03/2024] Malama H.M. Kurawa:
"... Ka kai kamab Bello ka gadi Moyi,
Saura
ka kai,
Inda
Maihausa yak kai".
Bajinin
gidan Bello,
Mamman
na Yari,
Sarkin
Kudu Macciɗo,
Ci
maraya.
1.
Wane ne Bello kuma wane ne Moyi? Yaya nasabarsu take da Macciɗo?
2.
'Maihausa', wa yake nufi, menene cikakken sunansa?
Na
gode 🙏
[3:40pm, 29/03/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
1. Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan
Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio
tagammadahullah birahamatihi kenan. Mahaifin Baban Kakansa, Sarkin Musulmi
Mu'azu ne. Domin Sarkin Musulmi Mu'azu ne ya haifi Modibbo Usman wanda ya haifi
Sarkin Musulmi Abubakar III wanda ya haifi Muhammadu Macciɗo. Shi kuma Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne.
1
(b). Muhammadu Moyin biyu ne ko uku. Ɗaya shi ne Muhammadu Moyi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio wanda ya taɓa
riƙe muƙamin Sarkin Kabin Silame a lokacin Ribaɗi. Silame hedikwatar gunduma ce a Ƙaramar Hukumar Mulkin Silame dake Jihar Sakkwato a
halin yanzu. Bayan tashin/fitar Kabawa daga hedikwatarsu da ake kira Surame
wadda Sarki Muhammadu Kanta ya girka a cikin ƙarni na 16 (a halin yanzu kufai/kangon Surame na nan a
cikin Ƙasar
Silame ta yau). Babu mamaki daga Tsohuwar Surame ce Silame ta samo wannan suna
nata, Allahu Wa'alam!
Akwai
Muhammadu Moyi daga zuriyar Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio wanda ya taɓa
riƙe muƙamin Sarkin Bauran Dange. Akwai kuma Muhammadu Moyi da
ya fito daga zuriyar Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio. Shi ne Kakan Marigayi Mai Martaba Sarkin
Kayan Maradun Ibrahim Maigandi II wanda Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi wa waƙar nan mai amshi " Jikan Moyi Iro ɗan Mamman tura haushi, ja gaba tsayayye". Ya yi
Sarkin Ƙayan
Maradun daga shekarar 1923 zuwa 1929. Shi ne Mahaifin Malam Fadama Nuhu wanda
ya haifi Marigayi Sarkin Ƙayan
Maradun Ibrahim Maigandi II da muka ambata a sama.
Saboda
kasancewar dukan Moyin guda uku sun fito ne daga Zauren Sarkin Musulmi
Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi duk wanda aka aza
a wannan gurbin yana iya shiga domin shi ma Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III daga wannan Zauren ne ya fito. Allahu
Wa'alam!
2.
Mai Hausa a wannan ambaton shi ne Mahaifin Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu
Macciɗo, wato Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III domin
shi ne jagoran Tutocin Shehu Mujaddadi a lokacin da aka yi wannan Waƙar. Yammawa kuma suna kiran Sakkwato a matsayin Hausa
tun bayan kammala Jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya. Allahu
Wa'alam!!!
Danganta
shi da ya yi da Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio cewa "ka kai kamab Bello... ina ganin
fata ce na ya kasance Sarkin Musulmi.
Inda
kuma ya ke cewa "Ka gadi Moyi.... Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Abubakar III ya yi hakimci a Talata Mafara daga
shekarar 1953 zuwa 1956 da aka ɗauke shi. Kenan
da Muhammadu Moyi ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello wanda ya yi Sarkin
Kabin Silame da Muhammadu Moyi dake gidan Sarkin Musulmi Mu'azu wanda ya yi
Sarkin Bauran Dange da Muhammadu Moyi ɗan
Sarkin Ƙayan
Maradun Attahiru/Atto ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello wanda shi ma ya yi Sarkin Ƙayan Maradun duka dai sun yi hakimci ko sarauta kamar
yadda Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo
Abubakar III ya taho daga bayansu ya yi.
[10:04am, 06/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Alibawa kuna ganin hwansak ku wurin Sule babu dama, Giwa ta sha ruwa tai
miƙa ta taushe gurbi.... Inji Ɗan Umma Uban Kiɗi a
faifansa na Marigayi Maigirma Sarkin Zamfaran Zurmi, Suleimanu Muhammadu Sambo
mai amshi ɓabban Bajinin gidan Sambo shirinka daban da raggo, jikan
Mamuda Sarkin nasara Baban Baraya'. Allah ya kyauta makwanci, amin. A wannan
hoton ga Giwa nan ta sha ruwa ta na neman ta taushen gurbin.
[10:17am, 06/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Daudu kullun mahwalki nikai sabo, Shehu ya bamu doki da kaya nai, Danda
hwari biyat wanda an nan haka, inda Liman ka bi zai Masallaci", cewar Ɗan Tumba Rungumi a Waƙarsa ta Marigayi Maigirma Sarkin Gabas Talata Mafara
Shehu Muhammadu Ɗangwaggo
mai amshi 'Shehu Ɗan Shehu
ganɗon ƙasah Hausa'. Wannan shi ne Dokin da ake kira Danda fari biyar domin
duka ƙafafunsa
na da kalar fari da kuma fari a goshinsa.
[11:11am, 09/04/2024] +234 803 852 9952: Abubuwa
da dama suka haifar da haka. 1. Mutanenmu sun saba yin abu a kirarren lokaci. 2.
Halin yau: galibi mutane sun rage sha'awa ga harkar bincike sosai, sai dai a yi
ta shiga aji kawai. Shi din ma a daburce. Amma wannan gwamnati ta jawo. 3. Galibin
Malamai suna halarta irin wadannan tarurruka ne domin fafutukar neman
"promotion". Da zarar an haye, shike nan. 4. Sha'anin tattalin arziki
da tsadar rayuwa da kuma halin firgici da ake ciki na rashin tsaro a kasar da
kuma yankin. Kila wadannan abubuwa ne suka jawo jinkirin. Amma kar a fitar da
rai. "Gate crushers" suna nan tafe.
[7:25pm, 11/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
@ Malam Murtala Isa. Muna maka maraba da shigowarka wannan Zaure da wannan Waƙar ☝️wadda ita ce Waƙar Makaɗa
Sa'idu Faru ta farko bayan ya fara jagorancin Ƙungiyar Kiɗa
ta gidansu daga Mahaifinsu, Makaɗa
Abubakar Aliyu Mai Kotso/Abubakar Kusu a cikin 1940s/1950s. Waƙar Dagacin Ƙauyensu (Faru) ce, watau Sarkin Yamman Faru Ibrahim
Abubakar/Mai Abu Faru ɗan Sarkin Ƙayan Maradun Bubakar/Abubakar ☝️
[7:14pm, 16/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Ko
alama. Daga gare ni ne. N kasa naƙaltar sahihiyar hanyar rubuta kalimar har yanzu.
[12:48am, 14/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Dukanku ku biyu bisa hanya kuke. Abin la'akari shi ne da baiti da ɗa ra'ayi ne, babu wanda yake wahayi. Kowa ya yi
rawarsa tare da hujja ko hujjoji.
[6:38am, 14/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Maigirma Ɗanmasani
barka da kwana da fatar munyi Sallah lafiya. Allah ya karɓi ibadunmu ya jiƙan magabatanmu, ya shirya muna zuriyarmu, ya sa mu
wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
Ina
goyon bayan Ranka ya daɗe akan wannan batu domin abun duka ƙirƙira ne kamar theories da masana ke kawowa su kuma tsayu akan su ta
hanyar kafa hujjojin da mabiyansu ko ɗalibansu
zasu dogara dasu wajen watsa su domin al'umma su aminta dasu.
To
tunda abun kamar mashaba/mashabobi ne kenan kowa na iya ɗaukar abun da ya sauƙaƙa a wajensa.
[7:50am, 14/04/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Shi dai
baiti an riga an saba da shi domin shi ne tushe, da ko diyan waƙa kuwa daga bisani ne ake son su tsayu.
[8:44am, 14/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ni
matsalar da ta daɗe wurina ina ta tawan ta ita ce, "Idan aka samu
waƙar mawaƙi da rerawa da dama, watakila ya kamata manazarcin ta
ya natsu ya tsamo ɗiyan da wata rerawa ta ƙunsa amma babu ga wata rerawa ya saka. Har
nakan yi tunani cewa da yake mawaƙi guda ne ya rera dukansu, yin haka ba aibu ba ne. Yanayi,
da haliyyar mawaƙin, da
tasirin wanda aka tsara waƙar don shi a kan mawaƙin, da tasirin masu saurare kan mawaƙin (shin a gaban wanda aka tsara wa waƙar ko kuma ba a gabansa ba ne mawakin yake rera waƙar, misali a dandalin wata jami'a ne amma ba a gaban
wanda aka tsara wa waƙar ba), duk
waɗannan dalilai ne masu haifar da wata rerawa bayan ta
farko.
[11:12am, 14/04/2024] Alh. A. Nakawada:
Yalla6ai, ni na yarda "ɗan waƙa'a" ne daidai bisa ga kasancewar akasarin masana
sun amince da hakan.
Shi
yasa nace: "Na sani. Amma na fi son in yi amfani da baiti" musamman a
irin wannan informal setting.
Amma
kamar yadda nace a can farko, nafi jin daɗin
in yi amfani da baiti. Watakila saboda shi na saba dashi kuma ya fi sauqin
rubutawa, da saukin faɗa da baki, kana an fi saurin gane abin da mutum yake
nufi😬
[7:14pm, 16/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Ko
alama. Daga gare ni ne. N kasa naƙaltar sahihiyar hanyar rubuta kalimar har yanzu.
[11:41am, 14/04/2024] Mal. M.A. Umar Ni
kiɗin yaƙi niy yi ma,
Abu na Isau,
Ba ni son,
Kana zannawa banza,
Ka ɗauki takobi,
Da bindigogi da bakunkuna,
Ka sa sirdi,
Ba mu sansani,
Sai bakin Tsabre,
Kano da Katsina,
Kwantagora,
Hab Borno,
Riƙon Namoda na,
Shi na hac can,
Garba ka amshe riƙon,
Dud da Ummaru,
Ummaru yab bar ma,
Garba ka hisge riƙon,
Dud da Ummaru,
Ummaru yab bar ma.
Amshi:
Gwauron giwa na Shamaki,
Baba Uban gandu,
Abu gogarman Magaji,
Mai
kansakalin daga.
[2:26pm, 14/04/2024] +234 806 951 3160: Allah ya
gafarta Malam, daɗin daɗawa, mai nazari
ka iya dubawa ya ga ƙari ko
ragin da aka samu a rerawar a waƙar farko ce ko a ta biyu.
Misali,
idan a waƙa ta biyu
aka samu ragi, a iya hasashen matuwa, kasancewar ajisancin ɗan'adam ko kuma mawaƙin yana sane ya yi haka saboda wasu dalilai da za a
iya ji daga gare shi ko waninsa. Ko shi manazarcin ka iya tsinkayen dalilin yin
ragin. Haka ma samun ƙarin ɗiya a rerawar waƙar ta biyu.
[2:40pm, 14/04/2024] Alh. A. Nakawada:
Nima na ta6a yin irin wannan tunanin na haɗa
hancin versions na waƙa da aka
rera ta a lokuta daban-daban. Sai na fahimci abin zai yi wuya. Dalili kuwa wasu
wakokin ana maimaita su da yawan gaske. Sannan kuma banbancin lokacin da aka yi
su ana samun tazara. Sannan za a iya samun matsalar sanin inda za a dasa wasu
baitocin, saboda ita ma waƙar tana da structure da Makadi ya yi mata. Ya tsara yadda zai bude ta, ya
tsara abun da ya ce ya fada bayan ya bude ta, ya tsara daidai inda ya
kamata ya yi zambo ko ya kawo salo, ya tsara inda zai yi wata doguwar gangara
ko hira, ya tsara wurin dai zai shigo da gaisuwa da godiya ga mutanen shi ko
ambaton masoya da yanuean wanda aka yi wa waƙar da dss. Sannan wasu baitocin ba tsayayyun baitoci
na waƙar ne ba. Suna
kawo su ne saboda wasu dalilai da suka waƙana a lokacin da ake rera waƙar. Daga nan kuma sun ajiye wadannan baitocin ba za su
sake maimaita su ba.
Inda
wannan group na general Makada da Mawaƙa ne da na kawo maka misalai na abin da nake nufi.
[2:47pm, 14/04/2024] Malam Jibril Yusuf: Allah
ya ba shi lafiya.
Allah
gafarta Malam mene ne mazallako da maiso da kora? Kalmomin duk baƙi ne a wajena.
[3:16pm, 14/04/2024] Alh. A. Nakawada:
Okay, yanzu na fahimta. Wannan watakila zai iya tasiri ga wakokin da ba a buga
ko rera su da yawa ba. Kuma zai yi tasiri ga wakokin wasu Makada da Mawaƙa wadanda wakokin da su maimaita rera su ba zai wuce
sau biyu ko uku ba.
Amma
akwai wakokin wasu Makadan da za ka samu an maimaita rera su yafi sau 20, wasu
ya fi 30 zuwa sama.
[3:39pm, 14/04/2024] Alh. A. Nakawada:
Yana da kyau ayi haka din. Sai dai abun da zai iya yiyuwa shi za a yi.
Ni
ina ganin da ace a hade wakoki rerawa daban-daban a wuri guda, zai fi kyau idan
an tsakace su daban-daban, ko wace a muhallin ta, domin kaucewa creating
confusion. Sai ace rerawa ta 1, ta 2, ta 3 dss.
Abin
da yasa nace haka shine, za ka samu wata waƙa an yi ta a 1950, sai aka ta maimaita rera ta har
zuwa 1990s. A ciki za ka samu Makadi ya kawo batutuwan da suka faru a wadannan
lokuta mabanbanta da sunayen mutane da suka wanzu lokuta mabanbanta. Idan aka
ce a gwamatsa su wuri ɗaya za a iya samun confusion gaskiya. Kuma wasu
wakokin suna da tsayi. Wata waƙa za ta kai minti 15 wata 20 har zuwa 30 ko fiye
da
haka.
Kamar
yadda na faɗi da farko idan waƙa ba ta wuce rerawa biyu zuwa uku ba kuma tazarar
lokacin da aka rera su ba tsayi, zai iya yiyuwa. Amma ace waƙa an yi ta lokacin Sardauna, misali, an ambaci mutanen
gwamnati da siyasa da alummah na wannna lokacin, bayan lokuta an maimata
fiye da so ashirin, kuma a ko wace maimaitawa za a samu irin ambato na wadancan
ababe, sannan ace a hade komai a wuri guda? Zai iya kawo rudu ga manzarta da
kuma tarihi. Zai yi kyau a bar ko wace rarawa a mazauni da matsayin ta. Illa dai
ayi ƙokarin
taskace su.
[3:44pm, 14/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Haka ne amma waƙa ba
Hadisi ba ce, daɗi da fahimta da hujja ake so a nazarin adabi. Ni ma
ban aminta da cin amanar adabi ba.
Babbar
matsala mai ban tsoro a yau ita ce, "Yaya za mu yi da AI? A zauren nan
wani ya taɓa cewa ana iya tsara magana (waƙa) wadda idan aka saurara ba za a iya rarrabewa
tsakaninta da ta wani mawaƙi da aka sani ba, duk sanadiyyar AI. Watakila Dr. Abu-Ubaidah na iya ƙarin bayani a nan.
[7:38pm, 15/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haƙiƙa! Sun haɗu a
lokacin da Muhammadu Macciɗo yana riƙe da Sarautar Sarkin Kudun Sakkwato, suka yi zamaninsu
har zuwa wafatin Mawaƙin a
shekarar 1987. Shi kuma Muhammadu Macciɗo
ya zama Sarkin Musulmi a watan Afrilun shekarar 1996, Allah ya yi masa wafati a
shekarar 2006 sanadiyar hatsarin/haɗarin
Jirgin Saman ADC Airlines. Allah ya kyauta makwanci, amin.
[7:14pm, 16/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Ko
alama. Daga gare ni ne. N kasa naƙaltar sahihiyar hanyar rubuta kalimar har yanzu.
[3:26pm, 16/04/2024] Mal. B. Lauwali: Ina
rokon wannan zaure ya taimakamin da waƙar Sa'idu Faru inda yake cewa: 'Yan Sarki kui ta
biyayya da biyayya aka sarki....... In zamaninka ya zaka ba sai an yi gada-gada
ba. Na gode
[3:57pm, 16/04/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A da na
dauka na Sakkwato ne, amma yanzu sai in ce na Zamfara saboda ku ne Sakkwatawa
kun ce ba ku gane ba, amma dai duk Bazamfare ya san wadannan kalmomin, saboda a
ciki muka tashi.
[5:28pm, 16/04/2024] Mal. M.M. Yankara:
Salam
Don
Allah a taimaka min da waƙar Sa'idu
Faru wadda yake cewa:
"Na yi mahwalki nai
Sallah Makka,
Nai Ɗawafi,
Kuma na rungumo
hirami da bagaruwa da
tasbahohi/casbahohi,
An ce mani Alhaji baital
fasalin Kiɗi,
Wanga mahwalki in
Allah ya nuhwa a
shirya
shi ya zan haka..
[5:31pm, 16/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ba
wuri ko gari guda na tashi ba. Firamare kurum na yi cikin Sakkwato kuma birni, birni
kuwa bai aje Hausa gangariya, kauye ya fi shi.
[5:46pm, 16/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Wannan sai Hon. Ɗanmadami. Na
dai san wata karin magana da ke kusa da abin da ka ruwaito mai cewa:
MAI
LAYA KIYAYI MAI ZAMANI
[5:49pm, 16/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ranka ya daɗe bani da wannan Waƙar mai amshi "Hwarin cikin Musulmi duk kai muka
taƙama yau, Muhammadun Muhammadu ɗan Abdu mai darajja".
[6:04pm, 16/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Allah Sarki. Wani na gani a wanga Zaure yana tambaya. Kila ba ka lura da
tambayar ba. Ga ta:
Ina
rokon wannan zaure ya taimakamin da waƙar Sa'idu Faru inda yake cewa: 'Yan Sarki kui ta
biyayya da biyayya aka sarki....... In zamaninka ya zaka ba sai an yi gada-gada
ba. Na gode
(Allah rufa asiri ya yi tambayar)
[6:06pm, 16/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haka ne Ranka ya daɗe. Bayan kayi wannan maganar ne sai na lura da
tambayar da wancan Malamin ya yi.
Shi
ne dai nike cewa ba ni da ita, amma nasan Waƙar mai amshi "Hwarin cikin Musulmi duk kai muka
taƙama yau, Muhammadun Muhammadu ɗan Abdu mai darajja".
[6:12pm, 16/04/2024] Mal. A.R. Mayana:
Sakin Makaɗan Gusau Tambai ya wanki wannan waƙa ya yi wa Maimartaba Sarkin Katsinan Gusau Alh. Muhammad
Kabir Danbaba.
"Da mai zakkuwa da gaskiya,
Da mai zakkuwa da ƙarya,
Allah shi ka fwaɗa
mashi,
Ɗan Sambo
na ganin shi.
Muhammadun
Muhammadun ɗan Sambo mai darajja. "
[6:15pm, 16/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
In Shaa Allah idan na same ta zan turo maka Ranka ya daɗe. Ta na daga cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru guda 10 da aka samu a faifan Gidan
Rediyo.
[6:16pm, 16/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
*Ko in ce waɗan da na sani/samu a faifai.
[6:19pm, 16/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Malam Aliyu, afuwan! Na lura da kana rubuta "fw" a madadin
"hw" da na sani. Ko za ka ƙara mini bayani don Allah?
[7:14pm, 16/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Ko
alama. Daga gare ni ne. N kasa naƙaltar sahihiyar hanyar rubuta kalimar har yanzu.
[7:39pm, 16/04/2024] Mal. B. Lauwali: A
taimaka man da wannan waƙa, inda
Sa'idu Faru ke cewa: Da Allah muka takama Ba tsafi muka takama Ba
Koway yarda da Allah Ba zai yi gada-gada ba.
[7:49pm, 16/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Sakkwatanci ce, Hausar Yamma ba ta Gabas ba kamar KT da KN da kuma
"Daidaitacciyar Hausa". Wajajen Daura ne ban san yadda suke faɗin ta ba. Na dai san suna da "hy".
[10:57pm, 16/04/2024] Dr Dangulbi FUG: Ina neman
waƙar sarkin yakin Banga Salihu
wadda makada Sa'idu Faru ya yi masha. A turo ta wannan zaure
[6:42am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:....
Ba zai riƙa/riƙe Aljani ba.....
"Farin
cikin/Hwarin cikin Musulmi duk kai muka taƙama yau,
Muhammadun
Muhammadu ɗan Abdu mai darajja ".
[7:21am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:...
Ba twsahi mu ka taƙama ba...
[7:33am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
??? "twsahi"
[7:34am, 17/04/2024] Mal. A.R. Mayana:
Wace irin kalma ce kuma wannan?
[7:45am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ni
ma ita nika tambaya. Kamar tsafi, kamar tciishi, wato abki/auki. Sai an furta
watakila mu fahimta
[7:45am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Daga tsafi a Yankinmu. Domin ba tsafi mu ke cewa ba, tswahi muke cewa.
Afuwan,
na yi kuskuren rubuta ta ne a maimakon tswahi sai na rubuta twsahi. 🙏🙏🙏
[8:03am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Lalle a Anka ana faɗar haka, da mafi yawan kasar Hausar Yamma. Muna
kuma cewa tsahi.
[8:16am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haka ne Haka ne Ranka ya daɗe.
Anka
ita ce hedikwatar Zamfarawa ta ƙarshe domin Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo ne ya taso daga Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura zuwa Anka tsakanin
1815 zuwa 1824. Sun tarad da Anka a matsayin ginannen Birni daga gidan Sarauta
wanda Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau ya gina bayan masu jihadi (Malam Muhammadu
Sambo Ɗan Ashafa
da Malam Muhammadu Da'e/Daɗi wanda
zuriyarsa ke Sarautar Maru da laƙabin Banaga ya zuwa yanzu da Malam Muhammadu Bachiri
na Bunguɗu) bisa ga umurnin Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi suka kore shi
daga garinsa da ya assasa mai suna Birnin Banaga bayan ya baro gidansu watau
Mafara. Birnin Banaga a halin yanzu kango/kufai ne dake Kudu Maso yammacin Maru.
Daga
wannan shiga ta Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo (1815-1824)
ya zuwa yau anan Anka hedikwatar Zamfarawan da suka fara shigowa wannan yanki
na Kasar Hausa a cikin 1300 take.
Sun
fara zama a Dutci/Dutsi dake cikin Masarautar Zurmi ta yau, suka koma Birnin
Zamfara dake kusa da Isa ta Jihar Sakkwato inda Gobirawa suka riske su har ma
suka mamaye su, suka ƙirƙiri sabuwar hedikwatarsu (su Gobirawan) a Gandun/Alƙalin Zamfara da ake kira Alƙalawa kafin masu Jihadi su mamaye su a 1804/8.
Bayan
Birnin Zamfara Sarkin Zamfara Abarshi shi da sauran jama'arsa sun zauna a
Kiyawa da Banga da Kuryam Madaro da Tumfafiya (Mazaunin Zamfarawan Mafara kafin
su koma Talata Mafara) da Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura kafin daga bisani
Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo ya dawo Anka.
[8:39am, 17/04/2024] Dr. S.S. Abdullahi:
Tumfafiya mazaunin Zamfarawan Mafara da Gummi
[8:44am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Haƙiƙa Maigirma Kogunan Gummi kuma Shaihin Malaminmu Dr. Abdullahi
S/Gulbi.
Daga
nan ne Malam Ali Bazamfare/Ali Jan Masari ya fita ya je ya ƙirƙiri Daular Bukkuyum. Ɗansa Malam Muhammadu Waru ya je ya ƙirƙiri Masarautar Gummi. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya shirya muna zuriyarmu, ya sa mu
wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
[9:20am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Wannan ya haska min yadda Yarima Ahmad yake jini biyu, da Bakura da Anka.
A Anka ya yi sakandare, yana form 3 na je can karantarwa inda yake yaro mai
basira amma ɗan ƙyamshe ne, bai da ƙiba😂
[9:28am, 17/04/2024] +234 803 443 2042: Haka
mutanen Bakura suke yan ƙyamshe ne,
ba su da ƙiba
[9:32am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Amma ina kyautata zaton ya gama da mutanen Anka.
[9:35am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Mahaifiyarsa daga gidan Sarkin Zamfaran Anka Ahmadu ta fito.
[9:37am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma
sha Allahu. Da ni da Imran mun ƙaru. Allah Ya saka ma da mafificin alheri Hon. Sir
[9:44am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Lokacin da na zaman Anka Sarkin Zamfara na lokacin classmate ne na wani yana a
Farfaru Boarding Primary School, Sokoto. Ya rike ni da karimci sosai. Very
humble person ne. Sarkin Zamfara Anka Lauwali sunansa. Allah Ya jiƙansa da rahma amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu
[10:07am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Allah Sarki. Zamfarci ne ya yi mini ke nan. Bai san da ina iya kai tsaye in
tambai Yariman ba?
[10:17am, 17/04/2024] +234 803 443 2042: Walki
ya jefe shi. Da fuskar Baɓurme muke kallon shi ba Bazanhwaren ba
[10:22am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ai na zamna Anka tsawo shekaru huɗu
na san ƙoramarsu
da ake kira 'Yar Anka, na san Bagwai da Ɗangulbi da Dankurmi da Kwanar Maje kuma na ci hoce. Nakan
sha iska gindin wani gamji da Anka round na Yamma ya bi kusa da shi. Na san
kuma wani mawaƙi Ɗan Balɗo!
[10:27am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Kada ku yi mai Zamfarci naku😂
[10:27am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Allah Sarki! Sani Ɗan Balɗo Waramu kenan, sai dai asalinsa Baɓurme ne.
Ranka
ya daɗe ka bar biye Malam Imrana kasan akwai wasan barkwanci
tsakanin mutanen Mafara da Ɓurmawan Bakura😅✊🙏
[10:28am, 17/04/2024] +234 803 443 2042: Ɓurmanci dai zamu yimai tunda shi ya iya
[10:30am, 17/04/2024] Mal. A.R. Mayana:
Meye banbancin Zamfarci da ɓurmanci ne?
[10:32am, 17/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ni kuma ina so da kare ɗalibina domin ɗa
ne ta bakin Kassu Zurmi, amma shi Yarima ɗan
ne na kowace ma'ana, ba dibilwar Kassu ba!😂😂😂
[10:36am, 17/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jinsin jama'ar ba ɗai ba ne Maigirma Ɗanmasani. Ɓurmawa daga Tsohuwar Daular Borno suka fito, su kuma
Zamfarawan Mafara daga Rano/Kano suka fito suka tarad da Ƙayatawa (Su Malam Imrana) a Mafara.
[8:28am, 20/04/2024] Mal. A.R. Mayana:
"Kai na yarda Tukur ya dawo,
Don an ba mai tara mutane,
Ba
mai watse mutan birni ba.
[9:23am, 21/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
👍😁👌🙏..... Wada yazzo da lahiya Na Kanau kuma ya dawo da
girma, Bajinin ci fansa Amadu mai takakka ga Arna....
[9:56am, 21/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ashe ba cewa yake, "haka nan kuma.. " ba?
[10:01am, 21/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A'a Ranka ya daɗe. Na Kanau kirarin Sarakunan Zurmi da Ƙaura Namoda ne saboda Sarkin Zamfaran Zurmi Kanau da
aka yi, ya shahara sosai.
Kamar
a je Katsina ne a kira mai alaƙa da Sarautar Katsina da inkiyar Muhammadu Korau (Yanke Masheɗi Baƙon Sanau) a ce masa "Na Korau".
[10:03am, 21/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Kanau da Isau da Loci dukansu Sarakunan Zurmi ne.
[10:18am, 21/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Tooh! Ka ga jahilcina game da naƙaltar Zamfara ko?
A
kan haka a koyaushe nake dagewa lalle ɗalibaina
su riƙa rubuta
abin da mawaƙi ya ce
kuma ya rubuta, kada su bi ma ɗaidaitacciyar
Hausa'. A kullum nakan ba su misali da yadda a Kananci ake cewa 'ilimi', Sakkwatanci
kuwa a ce 'ilmi'. Idan mawaƙi Basakkwace ya faɗi kalma ko ya
rubuta ta kai kuwa don ka mayar da waƙarsa da kalmar Bakano sai karin waƙar ya sauya, watakila ma ya karye.
[10:22am, 21/04/2024] +234 803 314 6863: Kanau
da Isau na yi zaton wa ne da kane ance Babansu daya Alin Bawa kohaka labarin
yake?
[10:25am, 21/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Lallai tsatson su ɗaya duk da yake bani da takamaiman bayani akan yadda
lamarin yake.
[10:25am, 21/04/2024] Prof Nazir I. Abbas: Haka
ne Allah gafarta Malam. Mu a mahangar harshe: "ilimi" da
"ilmi" sai mu ce shafe wasali ne aka yi a nazarin tsarin sauti. Allah
ƙara amfanar da mu daga iliminku👏
[10:26am, 21/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A cikin Waƙarsa ta Marigayi
Sarkin Kiyawan Ƙaura
Namoda, Abubakar Garba Ɗan Tumba
Rungumi yana cewa "Ni Kiɗin yaƙi niyyi ma Abu Na Isau bani son kana zannawa banza....
[12:28am, 22/04/2024] +234 803 257 6475:
Assalamualaikum! 'Yan uwa masu albarka, ina tambaya musamman ga masana ilimin
kwari (biology). Mine sunan Jinjimi, bubukuwa, da turanci?
[7:49am, 22/04/2024] Dr. H. Yelwa:
Biology 👉🏽Ilimin halittu ke nan kacokam
Ilimin
kwari👉🏽Entomology.
Kilan
kace ilimin tsuntsaye👉🏽Ornithology
In
ka bibiyi tattaunawad da anka yi a baya can, zaka ga tsuntsayen da ka' ambata
tare da sunayensu da ma hotunansu.
[1:09pm, 22/04/2024] Malama. S.S. Labbo:
Assalamu alaikum warahamatullahi wa barakatuhu Shehunnan Malamai Ina maku barka
da warhaka. Don Allah Ina bidar wata alfarma, in akwai rubutacciyar waƙar Mai babban daki da shi Sa'idu Faru ya yi don Allah
a taimaka min da ita. Na gode
[8:51pm, 22/04/2024] Mal. M.A. Umar Za a
samu Waƙar Mai
Babban Ɗakin Ƙasar Kano/Mahaifiyar Marigayi Mai martaba Sarkin Kano,
Alhaji Dr. Ado Bayero (Hajiya Asiya/Hasiya Bayero) a cikin wannan faifan ☝️
[9:15pm, 22/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Allah Sarki. Wadda aka rubuta ta nema ba ta cikin faifai ba, amma kuma watakila
ko ta cikin faifai ba ta mallaka ba. An ba ta shawarar da yake akwai ta ga
faifai to ta juya da kanta, abin da ni ma ina goyon bayan haka don idan na yi
haka nan na fi samun kwanciyar hankali. Sai kuwa idan mai juyar irina ne da bai
canza waƙar zuwa
"Daidaitacciyar Hausa".
[9:35am, 23/04/2024] Mal. A.R. Mayana: Ya
kamata a wannan taro wani daga cikin Malami ya gabatar da takarda a kan
hanyoyon taskace waƙoƙin baka na Hausa. Akwai mazhanobi biyu da suka yi fice,
Mazhabar Gusau (2009) da ta Bunza shi ma (2009). A zaɓi ɗaya ko a
tabbatar da su, ko a zaƙulo wasu
ko wata.
[12:26am, 24/04/2024] Prof. A.B. Yahya: A
farkon waƙar nan na
ji Sa'idu Faru ya yi amfani da salon waskiya. Ban ji waƙar duka ba yanzu sai an jima ko gobe. Salon na waskiya
yana cikin ambaton cewa daga Kano har ƙofar Lagos, har Ingila har bakin ruwan Yamma Babban Ɗaki guda ne. Ina sauraren ya ci gaba don ya ambaci
Gabas sai bai yi ba saboda a zatona ya san kwaɓa ta zai yi saboda Gabas ga Hausawa Musulmi ba su kawo kome ga ransu in
ba Ɗakin Ka'aba ba. Wato bai
ambaci Gabas ba; ya yi amfani da salon waskiya ke nan.
[12:50am, 24/04/2024] Prof. A.B. Yahya:
Dukansu ba sabbin ba ne. Tun zamanin zamunna ake taskace waƙoƙi da hanyoyin. Na Hausa akan samu irin haka cikin DAUSAYIN SOYAYYA na
Bello Sa'id. Kundayen masana da dama kamar Ɗandatti Abdulƙar da Sa'idu Muhammad Gusau. Tun daga sunan da Sa'idu
Gusau ya ba littattafansa za a fahimci cewa hanyar sananniya ce, wato DIWANI.
[8:01am, 24/04/2024] Dr. H. Yelwa: 😀👆🏽Madallah.
Lallai
ko shi a wani wuri da yah hwadi gabas, ya hwadi inda ag gabas din.
"GABAS ƊAKIN KA'ABA shi muke dibi don haske
To,
ko Gobir akwai NaYakuba ga Jangwarzo Da imanin Shehu yai tudu Ummaru yad
dawo".
Jagora: Zama
zucci ga mai rabo
Daudu yahi zama kusa
Y/Amshi: Wata
goma buhu goma a kan bamu na marmari,
Jagora: Zama
zucci ga mai rabo
Daudu yahi zama kusa
Y/Amshi: Wata
goma buhu goma a kan bamu na marmari,
Ga zakka metin na gumi don ayi ma tuwo,
Ga kuɗɗi fan goma na
zabbi ayi romuwa,
Jagora: Hawan
Sallah Baba ɗan
Muhammadu yai kyau bana,
Y/Amshi: Ku
duba muna kaya na zuwa idi acan-acan,
Turken Waƙa:Babban
bajinin gidan Hassan Shehu na Yan Ruwa,
Ba
ai maka wargi bahago babu kahway yima.
Daga
cikin Waƙar
Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar/Hakimin
Gundumar Talata Mafara, Sarkin Gabas Alhaji Shehu ɗan Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo ɗan
Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi. Ya yi sarauta
daga shekarar 1958 zuwa rasuwarsa a shekarar 1969. Allah ya kyauta makwanci, amin.
"Babban
gambun sirrin duniya Uban Alhaji Salihu", a cewar Ɗan Tumba Rungumi a Waƙarsa ta Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo mai amshi 'Farin cikin musulmin duniya, mai martaba
na Abubakar, ci fansa Alhaji Macciɗo'.
Allah ya kyauta makwanci, amin.
[8:27am, 24/04/2024] Dr. H. Yelwa: Saidu
ya ambace ta;
1.
A cikin wace waƙace?
2.
Wa yay yi ma waƙat?
3.
A yi bitaɗ ɗan waƙat.
[8:29am, 24/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:...
Hwarah hwatsa cinki sai ga mai ƙararrin kwana, a ciki a kwan rirriƙam mutun za shi garin kewa...
A
cikin Waƙar Sarkin
Kiyawan Ƙaura
Namoda Abubakar Garba mai amshi " Gwabron Giwa na Shamaki baba Uban Gandu,
Abu gogarman Magaji mai kamsakalin daaga".
[8:36am, 24/04/2024] Dr. H. Yelwa: Haka
ne, Honorabul!👆🏽😀
Abu
baban Shamaki na Jekada
Dangalin
Gabas Na Isau dan Mudi
Kashi
tahi giggilme ƙargage
Hwarah
HWATSA cinki sai ga maikararrin kwana
A
ciki akwan rirrikam mutum za shi garin kewa
In
ana yaki na Abubakar....
Gaskiya
wuringa👆🏽Saidu ya buga Hausa.
To,
mi an na wani abu kuma ƙargage?
[8:38am, 24/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:...
In da zamanin ana yaƙi ne
Abubakar sai ya kama wanda am magudanci....
[9:07am, 24/04/2024] +234 803 443 2042:..... shi
bani sunai man noma,
Ina zamne ina gida
Ina ɗunkin turu na,
Cikin albarkar Abubakar,
Na bar shan hurar da ba nono, bani cin tuwo in ba
tsokoki,
a murje gumi wanda adda kyau,
in
dasa yatsuna"
[9:12am, 24/04/2024] Dr. H. Yelwa: 👆🏽😀Jumla bi-da-bi.
Amma,
in DASA yatsuna yaka cewa, ko in GASA yatsuna?
[9:18am, 24/04/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Ko kuma
in nasa yatsuna?
[9:22am, 24/04/2024] +234 803 443 2042: "In
dasa" yake cewa maigirma Perm Sec. Watau kamar ya ce in soka
yatsuna amma saboda lalurar waƙa, sai ya ce in dasa
[9:25am, 24/04/2024] Dr. H. Yelwa:
Madallah Mal Imrana. Hausat tashi ce sai ta ba mutum dariya, yadda yaka jerota.
[6:40pm, 26/04/2024] +234 706 259 1505: Don
Allah me ya sa, kamar yadda Sa'idu Faru ya ruwaito, Bahaushe ya ce mai ƙararren kwana duniya kurum zai ci farar fatsa? Kuma
fatsar ce kuma ake kira mamari?
[6:46pm, 26/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ranka ya daɗe saboda sai kifin da aka nufi mutuwarsa/ajalinsa ya
yi ne zai haɗiye farar fatsa. Domin da zaran ya haɗiye ta waje aka yo dashi sai cikin kwando ko gora daga
nan sai talle, ya zama kalaci/cimaka/abinci kenan.
Ba
ita ce mamari ba, mamari a zare ake jera shi da yawa sai a saka ƙoto a zuba shi a ruwa, a ɗaure shi da dutci ko iccen dake cikin ruwan da ake Suu
ɗin.
[7:30pm, 26/04/2024] +234 706 259 1505: To ma
sha Allahu. To ita fatsa launi launi ce?... akwai fara, akwai ja, akwai baƙa... ?
Godiya
nikai Hon. sir
[7:32pm, 26/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ma Shaa Allah Ranka ya daɗe. Mai jikin silver na sani Sir.
[7:33pm, 26/04/2024] +234 706 259 1505: Ka ga
tashin birni ko? Larabawa sun dade da sanin haka, don haka sukan kai 'ya'yansu ƙauye don su tashi can su iya Larabci sosai
[7:34pm, 26/04/2024] +234 706 259 1505: Ƙara haƙuri da ni don Allah, ke nan farar fatsa ta fi halaka kifi ko?
[7:39pm, 26/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Eh Ranka ya daɗe tunda ita ci maza ce, da ya ga an jefa ta cikin ruwa
naɗe da ƙoto/fara ko makamantan ta sai ya haɗiye
a matsayin abincin da ya samu a banza.
[10:52pm, 28/04/2024] Mal. A.R. Mayana:
Muna sane! Su Furnis da su paden duk sun yi. Amma, babu kamar waɗannan biyu da muka ambata.
[10:38pm, 29/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Tsakin tama na Abashe ana shakkah haye ma Amadu ☝️
[10:40pm, 29/04/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
"Sa'idu Faru ka Waƙam iko
Komi kaj jiya ƙarya akai
Sa'idu Faru ka Waƙam milki
Komi
kaj jiya ƙarya
akai".
[12:14pm, 30/04/2024] Fugus Ba shir Abdullahi:
Assalamu Alaikum.
Muna
ƙara yin tuni dangane da biyan
kuɗin rijista ga wanda zai gabatar da Maƙala kamar yadda aka sanar a sama.
Idan
an biya sai a tura rasiti ta wannan layi nawa a kan WhatsApp don zama shaida
Insha Allah.
[5:38pm, 01/05/2024] Mal. M.A. Umar Aslm.
A taimaka mana da taƙaitaccen
tarihin Hajiya Hasiya Mai Babban Ɗaki.
Muna
godiya!
[6:54pm, 01/05/2024] +234 806 921 4605:
Assalamualaikum Warahmatullah. Jama'ar wannan gida mai albarka barka da warhaka.
Dafatar duk muna lafiya.
Suna
na Samaila Yahaya Jami'in hulda da Jama'a na Kungiyar marubutan Jihar Zamfara. Ina
daya daga cikin wadanda ke bibiyar abin da ke gudana a cikin wannan gida. Bisa
ga wannan ne nake bada shawara ga masu ruwa da tsaki na wannan taron karawa
juna sani da za a fara ranar Juma'a da su duba yiyuwar aikewa da takardar
gayyata ga Kungiyar marubuta ta kasa reshen Jihar Zamfara wato (Association of
Nigerian Authors).
Dafatar
za a duba wannan kira. Allah Ya nuna mana ranar fara wannan taro a yi lafiya a
kare lafiya Amin.
[7:18pm, 01/05/2024] Fugus Ba shir Abdullahi:
Muna godiya da waɗannan shawararwari masu muhimmanci. 👍🙏
[12:32am, 07/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ruwan da aka wanke tsaba kamar geron da aka dake, aka aje domin dabbobi
su sha, kuma duk wani sauran abinci ko abin sha wanda bai cutar da dabba akan
yi haka da shi, wato ya zama ƙasari. Manufa dai akan tara shi domin a ba dabbobi kamar awaki da
tumaki da shanu.
A ƙauyuka da birane iyaye kan tura 'ya'yansu su je gida
gida domin su roƙo ƙasarin da za su ba dabbobinsu. Ba mamaki a wannan
zamani a riƙa sayar da
ƙasari. A yanzu dai a nan
Sakkwato kyauta akan bayar da ƙasari domin yin haka wata hanya ce ta rabuwa da ƙazanta saboda babu abin da magidanta za su yi da ƙasari idan ba su da dabbobi, kuma kullum ne sukan tara
shi muddin suna yin abinci ko abin sha.
Ina
fatar wannan bayani zai gamsar, amin.
[6:53am, 07/05/2024] Malam Abubakar Tijjani: Na
gode
Na
kuma gamsu, amma dukkan kasar Hausa haka ake kiransa, ko akwai bambanci a
Hausar Nahiya ko karin Harshe?
[11:29am, 07/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Na so a yi bayani kan kirarin da aka yi wa Sakkwato. Kila Hon. Birnin Magaji ne
mai iya yin fashin baƙin. Saura
kuwa irin Bawa Jan Gwarzo ta-ciki ke hana su😂
[3:39pm, 07/05/2024] Sheik Hafizu Hadi: Assalamu
alaikum. shuwagabanni Masu girma na wannan sashe, Mai kula da harsuna a wannan
jami'a Mai AL barka. Ina Taya ku murnar kammala wannan taro lafiya. Da fatar
Allah Shi Mai Mai ta Muna. Mai girma Danmadami Allah ya Saka Maka da alheri. Dan
Allah ka ƙara Rika
hannun wannan sashe na mu Mai Albarka. Allah ya Baka lafiya, yanda ka haskaka
wannan sashe na mu, Allah ya ƙara haskaka tauraruwar ka a Duk Inda ka shiga. Mai girma zanna yanda ya
sadaukar da dukiyarsa domin sama wa wannan sashe na mu girma da daukaka da a
cikin Wannan jami'a Allah ya nuna Muna lokacin da zai Shigo cikin Wannan jami'a
Yana a matsayin gwamna jahar zamfara. Ni dalibin ku ne a yi haƙuri da
kura-kuran da za a Gani. Allah Shi taimaki wannan makaranta tamu da Malamanmu.
[4:47pm, 07/05/2024] Mal. B. Lauwali:
Amin, wallahi na karu da Danmasani sosai, haƙuri da karamin dalibi irina ba kowa ke iyawa ba. Ina
da yawan tambaya ga duk abinda ya shige min duhu. Shi kuma Danmasani bai taba
gajiya da yi min bayani ba. Allah Ya saka masa da alheri. Ba shi kadai ba, har
da sauran 'yan kwamiti domin irin haƙuri sai dai a kwatanta ba zai lissahu ba. Mun gode
[5:13pm, 07/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Don Allah ko mawaƙan Hausa na baka daga wata nahiya daban da nahiyar Yamma sun halarci wannan muhimmin taro? Na yi tambayar ne saboda na yi imani da sun halarta da sun amfana ƙwarai da Hausa da hikimomin tsara waƙa daga wannan nahiya in sha Allahu.
[10:09pm, 02/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Malamin Waƙa mai
kwana ɗumi na Mamman na Balaraba.
[12:05am, 03/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Waƙar Turakin Argungu Shehu (Kangiwa),
ga alamar da ke cikinta Sa'idu Faru ya yi ta kamin 1979 lokacin da Turaki ya
zama gwamnan Sokoto. Sa'idu Faru bai ambaci Turaki a matsayin gwamna ba, saboda
haka mai yiwuwa lokacin da shi Turakin yana cikin shirin fitowa takara
ne aka yi waƙar.
Abin
da ya saka mini tunani cikin waƙar nan shi ne kyautar mota da Naira ɗari
biyar "don in aje in yi ta kwasar hetur"! Haƙiƙa a lokacin fetur bai da tsada a ƙasar nan. Har zuwa 1976 kamin mulkin OBJ na soja ya ƙara kuɗin fetur, nakan
cika tankin motata da Naira biyar kacal!!!
[8:38am, 03/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ƙwarai kuwa Maigirma HOD. Marigayi
Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa yana cikin aikin gwamnati a lokacin Masarautar
Argungu ta zaƙulo shi ta
naɗa shi Turakinta na farko.
Makaɗa da Mawaƙan Baka Na Hausa irin su Musa Ɗanƙwairo Maradun da Sani Aliyu Ɗandawo Yauri sun baje kolinsu a wajen bikin naɗin wannan sarautar.
[12:17pm, 03/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Makaɗa Ibrahim Sa'idu Faru na uku daga gefen hagu da
jama'arsa tare da Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji na uku daga gefen dama bayan
kwamitin masaukayye ya saukar da tawagar Makaɗan yayin da suka shigo Gusau babban birnin Jihar Zamfara, Ranar Juma'a
03/05/2024 domin dakon Taron Ƙasa da Ƙasa akan
Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa
Sa'idu Faru da Sashen Harsuna da Al'adu na Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau
ya ɗauki nauyin gudanarwa daga 3-6 ga watan Mayun 2024.
[9:13pm, 22/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudu/Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III. Allah ya jaddada masa rahama, amin.
[10:09pm, 22/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Makaɗa Sa'idu Faru: Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo Abubakar III/Ya yi Sarki daidai wada mai yanzu yar
riƙa ☝️
[10:13pm, 22/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Haƙiƙa da wannan kama na san Mai alfarma cikin shekarun
1970!!!
[9:02am, 24/05/2024] Malam Bello Gedawa: Allah
ya taimake ka na fahimta gaskiya. Na gode da wannan shawara. In sha Allahu zan
gwada. Koda dai Basullube ni ke yallabai😃
[9:04am, 24/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Halan Sulluɓawa ba Fulani ba ne?
[9:05am, 24/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Na
aza kamar Kanawa da Sakkwatawa ne
[9:11am, 24/05/2024] Prof Nazir I. Abbas: Salam,
Ni fa ban ganin rubuta wani abu da ya shafa Hausa cikin wani harshe a matsayin
wani abun kyama ko kuskure. Hasali ma akwai wadanda ba Hausawa ba da za su iya
sha'awar sanin wani abu game da harshen da kuma al'ummar ta hakan za a iya
sanar da su.
[9:13am, 24/05/2024] Malam Bello Gedawa: Allah
ya taimaki shugabana, malamina kuma Shaihin malami, wane ni in iya amsa wannan
tambaya a gabanku.. Wallahi ban isa ba.
[9:19am, 24/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
A'a don Allah. Na sha ganin Sulluɓawa,
kai har da Gurumaɗa, da ke Fulfulde raɗam.
[9:44am, 24/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Allah Sarki. A Zamfara musamman a Anka Sulluɓawa
suna ji
[9:46am, 24/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Kuma Sulluɓawa ai Fulani ne. Fulani sun kasu dangi-dangi
[8:34am, 26/05/2024] Mal. A.R. Mayana:
Maigirma Danmadami.
1)
Ko dukan Sarakunan nan kafin su dawo an naɗa
wasu?
2)
Cire waɗanda aka naɗa
bayansu aka yi suka dawo, ko ƙaƙa?
Allah
ya ƙara sani, amin.
[3:52pm, 26/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Na'am Maigirma Ɗanmasani
kuma Ɗangaladima
barka da warhaka. A gaskiya bani da cikakken bayani akan wannan/waɗan nan tambayoyi naka.
Abun
da kawai na sani shi ne a Kwantagora da aka cire Sarkin Sudan Ibrahim ɗan Sarkin Sudan Ummaru Nagwamatce ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I/Abubakar Atiku/Mai Katuru
ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi a shekarar 1904, Kwantagora
ta zauna babu Sarki har zuwa dawowarsa a shekarar 1906. Domin bayan Turawa sun
cire shi su ka kai shi a Lokoja inda ya zauna har tsawon shekara biyu, sun bar Ƙasar babu Sarki sai a shekarar 1906 su ɗauko shi daga Lokoja su ka dawo dashi Kwantagora ya ci
gaba da mulkinsa har zuwa wafatinsa a shekarar 1929.
A
Suleja kuma bayan walwale naɗin Malam Awwal
Ibrahim da Gwamnatin Jihar Neja ta yi an naɗa
wani ne a matsayin sabon Sarki. Malam Awwal Ibrahim kuma ya shigar da ƙara ya ƙalubalanci cire shi da aka yi inda ya samu nasarar
abun da ya nema a Kotu cewa yana son a mayar dashi domin an cire shi ba bisa ƙa'ida ba, ya kuma samu hakan sai aka rushe wancan naɗi da Gwamnatin Jihar Neja ta yi aka mayar dashi. Allahu
Wa'alam!
[4:43pm, 26/05/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma
sha Allah Hon. Yanzu fa wannan mayarwar da aka yi wa Sarkin Kano haƙiƙa 'yan siyasa dasa tuɗar da darajar
masarautar suka yi. Na kuma 'yi imanin mai hali bai barin halinai. Allah Masani.
Allah kuma Ya yi muna magani, amin Ya Hayyu Ya Ƙayyumu
[4:49pm, 26/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Wallahi Ranka ya daɗe tun lokacin da aka janye ikon gudanarwa daga
Sarakuna zuwa ga masu mulkin zamani aka dasa ɗambar wannan wulaƙanci ga
Sarakuna Masarautunmu.
Shigar
masu jinin sarauta a cikin sha'anin siyasa wai domin su ceci gidajensu ko
mutuncin sarauta/Masarautun a tawa fahimta zai ƙara dagular da lamarin ne kawai saboda kuwa ta kansu
zasu yi, ma'ana tasu biyan buƙatar zasu saka a gaba. Allahu Wa'alam!
[5:47pm, 29/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Allahu Akbar, kamar jiya ne wannan abu ya
faru!
Shaihin Malaminmu Abdullahi Bayero Yahya na Sashen Harsunan Nijeriya dake
Jami'ar Jihar Sakkwato ne a gefen hagu (mai bulan kaya) ke gaisawa da Malam
Bilyaminu Abubakar Gusau na Sashen Shirye - Shiryen Gidan Rediyon Gold City FM
mallakar Gwamnatin Jihar Zamfara dake Gusau na farko daga gefen dama (mai kaya ɗanyen haki) yayin da Alhaji Murtala Alhassan Garkuwan
Maru, Shugaban Sashen Shirye Shirye na Gidan Rediyon Jihar Zamfara (a tsakiya)
ke sambarka a lokacin da Shaihin Malamin ya gabatar da jagabar manyan Maƙaloli a Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Rayuwa da Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru da Sashen Harsuna da Al'adu na Jami'ar
Gwamnatin Tarayya dake Gusau, Jihar Zamfara ya shirya domin karammawa zuwa ga
Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III da ya gudana a Dandalin yaye Ɗalibai dake harabar Jami'ar Ranar Asabar, 04/05/2024. Allah
ya ƙara lafiya da nisan kwana mai
albarka, amin.
[6:07pm, 29/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Jagora: S/shaggu
ka rabka kuwa,
Kai taƙamab biri,
Kuma saki tukkuwa ta wala,
In na kiɗa
kai ko Maba
tadda gwarzon Sabongari nan dak kwana,
Kai Magajin busa ka zanki busa,
Da zamanin ana yaƙi na,
Jagora/Y/Amshi:
Maraɗi da bata kwan ukku,
In ba aljihun Abu mai saje ba,
Ginshimin S/fada ɗan
Iro na Malan,
Ubangijin Garkuwa ɗan
Muhamman mai daga.
Daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Nijeriya, Abubakar Garba.
Ya yi sarauta daga shekarar 1952 zuwa shekarar 1960 da
aka cire shi. Allah ya kyauta makwanci, amin.
Turken Waƙa: Ginshimin
Sarkin fada ɗan Iro na Malan,
Ubangijin
Garkuwa ɗan Muhamman mai daga.
[8:41am, 31/05/2024] +234 803 696 1436: Ina
neman sunan waƙar sarauta
ta farko da Alhaji Musa Dankwairo ya yi wa Sardaunan Sokoto Alhaji Ahmadu Bello
a 1962. A taimaka mini da sunan waƙar.
[10:27am, 31/05/2024]
Malama. H.M. Kurawa: Kada marake giwa,
Ba a haye ma Barde,
Amadu ɗan Ibrahim,
Baka
yada gudun arna ba.
[10:41am, 31/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
A gaishe da Malama. Ɗan ƙarin bayani wannan Waƙar ita ce ta farko wacce/wadda Musa Ɗanƙwairo Maradun ya fara rerawa zuwa ga Marigayi Maigirma Firimiyan Jihar
Arewa, Sir Ahmadu Bello GCON KBE Sardaunan Sakkwato.
Ya
yi masa ita ne a lokacin yana Daudun Kiɗi/Ɗan Amshi a Ƙungiyar Kiɗa
ta yayansa/wansa Makaɗa Abdu Kurna ɗan
Makaɗa Usman Ɗankwanaga ɗan
Makaɗa Kaka Allahu ya jaddada masu rahama su da sauran
magabatanmu, ya shirya muna zuriyarmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau
da imani, amin.
[10:52am, 31/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ma sha Allahu. Hon Kai fa ne Rumbunmu! Ni kuma waƙoƙi biyu nake buƙata, ɗaya ta Kurna wadda ke faɗin/ In ka ga gashi na ta tashi bisa//Gun gije yaka tabbata/.
Ɗaya kuwa ta Ɗanƙwairo mai cewa,/Ga Giwa ga hili tsakak karkara//Mahalba ina masu son
suna/.
[11:19am, 31/05/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Ranka ya daɗe barka da kwana dafatar Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.
Ta
Kurna Waƙar Sarkin Ƙayan Maradun Abubakar/Bubakar ce wanda ya yi Sarauta
daga shekarar 1939 zuwa 1960 lokacin da aka cire shi. Ɗayar kuma ta Yandoton Tsafe Aliyu II ce wanda ya yi
Sarauta daga shekarar 1960 zuwa rasuwarsa a shekarar 1991. Allah ya kyauta
makwanci, amin.
In
Shaa Allahu za a lalubo su Ranka ya daɗe.
[11:24am, 31/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ina godiya Hon sir. Dalilin biɗar su gare ka
shi ne kular da kake yi da yaren da mawaƙa suka yi waƙoƙinsu.
[8:15pm, 31/05/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: Makada
Alhaji Musa Dankwairo yana harzuka Maimartaba 'Yandoton Tsafe idan ya zo kan
wannan dan waƙar. Wata
rana da ya je a lokacin Sarki na cikin wata rashin lafiya amma sai da Sarki ya
sa aka yi shela duk aka hadu garkar Sarki. Ko da ya zo nan ya ce "ga giwa
ga hili tsakak karkara mahalba ina masu son suna? Sarki kuwa ya mike tsaye ya
bude hannuwansa kamar mai kirari! Sai da aka rirrika shi ya zauna.
[9:20pm, 31/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Lalle irin wannan turken ko tubalin waƙa take yake yamutse Basarake. A nazarin waƙa ana kiran sa "zuga".
[9:22pm, 31/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Ashe da Ɗankwairo
ya yi ɓarna
[9:32pm, 31/05/2024] Prof. A.B. Yahya:
Haka nan kuma an taɓa faɗa mini cewa
akwai lokacin da 'Yandoto ya fita tanadi, an kai wani ƙauye sai aka ji wani gida an sa kaset mai dauke da
wannan waƙa, to da
'Yandoto ya waƙar kuma
wannan dan da ke ɗauke da tubalin sai kuwa nan a kan doki 'Yandoto ya
harɗa tamatele!, ya ce ma bafadensa "Sarkin fada a'a
muke?"
[5:36am, 01/06/2024] Dr Yusuf Gama: To ai
wadannan bayanai abubuwa ne masu amfani ga daliban ilimi da manazarta, domin za
a iya rubuta makala sukutum da guda a kan irin wannan batutuwan, misali:
Dangantakar Sarki da Waƙa da kuma
Makadi/Mawaki: Tasirin Wakokin Dankwairo Ga Jin Isar Sarautar Aliyu Yandoto, ko
wani taken makamancin wannan, musamman ma in za a iya tattaro ire-iren wadannan
al'amura da suka faru.
[6:50am, 01/06/2024] Dr. H.U. Bunguɗu: A waƙar Sarki Ibrahim na Suleja Dankwairo yana cewa " waƙar da na yi maka tai ma daɗi,
Ko
ni da niy yi ta tai man daɗi.
[3:32pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya:
Sa'idu Faru ya ce, cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Yawuri, ko baya ga wannan waƙa akwai wasu tara gida, idan sarki ya yi na'am da
wannan to yana aikawa gida su zo.
Wannan
magana tubalin roƙo ne cikin
salon kambamawa/kambame/kambame zulaƙe domin Sa'idu Faru ya samu babbar kyauta daga sarkin.
Ga
alamu wannan salo mai tagomashi ne ga mawaƙan sarauta. Ɗanƙwairo ma yakan yi amfani da shi. Misali cikin wakoƙin da ya yi wa 'Yandoton Tcahe akwai wata da yake faɗin,/In dai ana hidda hakkinmu daidai/ Sai an ji launi
iri banban/.
[5:54pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya:
Akwai wata dabbar daji da Kassu Zurmi ya yi amfani da kirarin da ake yi mata
wato, "Awakin banza". Wace dabba ce Kassu ke nufi cikin waƙarsa ta Garugaru? Don me ake ce mata "Awakin
banza"?
[6:06pm, 01/06/2024] Dr Rabiu Ba shir KASU:
Allah gafarta Malam kirarin biri ne. Akan ce biri awakin banza/tumakin banza
Komai
yawansu ba sa taki.
[6:12pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Haƙiƙa! Kuma birai ne da suka fi yawa a nan ƙasar Hausa, jajjaye ne masu yawo cikin gungu kamar
awakinmu. Hasashena ne kurum.
Alhamdulillahi!
Muna godiya sosai da fatan alheri da addu'o'inku zuwa ga Ɗan Uwa, Makaɗa
Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo
Yauri a kan wannan abun alheri da ya samu na mayar da aikinsa zuwa Ƙasar Morocco da Hukumar Shige Da Ficen Nijeriya ta yi
masa. Allah ya karɓa, amin.
A
wata tattaunawa da na yi dashi ta wayar salula Ranar Asabar, 01/06/2024, na
tambaye shi ko ba za mu sake jin motsinsa a fagen Kiɗa da waƙa ba domin yanayin aikin da zai samu kansa a ciki nan
gaba kaɗan? Makaɗa
Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo
Yauri ya amsa mani cewa "In Shaa Allahu bani da ƙudurin barin wannan sabga ta gidanmu dake da zummar ci
gaba da kariya ga al'adunmu, ko da wane irin girma na samu a cikin wannan aikin
hukuma da nike yi".
Da
wannan muke yi masa godiya akan wannan tunani nasa da kuma ƙara yi masa addu'ar samun cikakkiyar nasara mai
albarka a kowane fanni, amin.
Ibrahim
Muhammad Ɗanmadamin
Birnin Magaji, Jihar Zamfara. Asabar, 01/06/2024.
[6:41pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya:
Salon Kinaya ne Kassu ya yi wa wani Musa cikin mutanen Jangerawa a waƙar GARUGARU. Kassu yana nufin Musa bai da amfani, ko a
cikin sana'ar tauri ko sana'ar farauta, ban dai fahimta ba. Amma dai ai duk
wadanda suka taru a dajin nan in ba Garugaru ba duk birai ne awakin banza ga
Kassu saboda Garugaru ne kurum ya yi masa ƙwazo mai daɗi
kamar ya dama zuma ya sha!
[6:46pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Ma
sha Allahu. Ina murna da jin haka. Ina malaman boko da suka karanta Hausa amma
suna ɓoyon a ce Hausa suka karanta?
[7:28pm, 01/06/2024] Dr Rabiu Ba shir KASU: Ma
sha Allah da wannnan gagarumar nasara da aka samu, Allah ya saka masa da alheri.
Kai kuma Allah ya ƙara maka
kwarin guiwa na ƙoƙarin ganin Waƙar baka ta habaka.
Zan
so in samu Wakokin makadin, domin ban taba jin su ba gaskiya.
[7:51pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya: Waƙar GARUGARU da Kassu Zurmi cike take da salon Kinaya
kamar "biri awakin banza* da "jan zakara" da sauransu. Fito da
da sauran kana mai bayanin abin da Kassu ke nufi da kowane.
[8:08pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya:
Nuna salailan kinaya da alamtarwa/alamu da ke cikin waƙar Garugaru ta Kassu Zurmi kana mai bayyana manufar
mawaƙin da
kowane salo
[8:34pm, 01/06/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
Shi ne Ɗansa na
biyu, mace ce ta farko shi ke bi ma ta, saboda haka shi ne babba a cikin sauran
'ya'yan maza.
Bai
kuma yi biyar Mahaifin wajen Waƙa ba, hasali ma yana yi masu faɗa
cewa su ci gaba da neman ilimi. Cikin ƙaddarawar Allah SWT sai gashi Suferitandan na Shige da
fice, Alhaji Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo Yauri ya gade/gaje gida.
Kenan
tarihi ne ya maimaita kansa domin Kakansa Makaɗa Aliyu Ɗandawo
Shuni (duk da yake shi baya gaji/gadi Kiɗa
da waƙa ba ne)
ya sha tsangwama daga Mahaifinsa akan shigarsa wannan sabga ta Kiɗa da waƙa.
Da
tsangwamar ta yi masa yawa ne ya dinga gudu zuwa wani gari da ake kira Augie a
cikin Masarautar Argungu, Jihar Kabi ta yanzu ya ci gaba da wannan sabgar.
A
can ne ma ya yi auren fari, ya auri Hajiya Hauwa'u (Laraba) wadda ita ce ta
haifar masa Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo Yauri a garin Argungu a cikin shekarar 1943 (tana raye a gidan ɗan ta, Marigayi Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo a Yauri, a halin yanzu), shi ne ya haifi Makaɗa Ibrahim Sani Aliyu Ɗandawo Yauri. Allah ya jiƙan magabatanmu, amin.
[8:43pm, 01/06/2024] Prof. A.B. Yahya:
Allahu Akbar! A kullum na karanta irin wannan tarihi nakan ji an ƙarfafa iƙrarina da ke nufin waƙa baiwa ce ba koyon ta ake yi ba.
[1:27pm, 18/06/2024] Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara: Daular Zamfara:
1300 Zuwa Yau A Takaice
Daular
Zamfara samu ne a cikin 1300 ta hanyar jagorancin wani mutum da ake kira
"Dakka" da ake kyautata zaton ya fito da jama'arsa ne daga Gabas ta
tsakiya. Sun fara yin hedikwata a wani wuri da ake kira "Dutci/Dutsi"
dake cikin Masarautar Zurmi ta Jihar Zamfara ta yau.
Daga
nan ne ɗansa da ake kira "Bakurukuru" ya ɗauke hedikwatar daga Dutci/Dutsi zuwa Birnin Zamfara
dake cikin Gundumar Isa ta Jihar Sakkwato ta yau a cikin ƙarni na 15. Anan ne Gobirawa suka tarad dasu a cikin ƙarni na 18 har ma suka nemi su ba su wurin zama
domin a lokacin su Gobirawa sun daɗe
da samar da Ƙasarsu
bayan fitowarsu daga inda ake kira "Gobur"/Gubur" da ake
kyautata zaton a cikin yankin Saudi Arabia ta yau ne.
Zamfarawa
sun ba su Gonar Alƙalinsu da
ake kira Alƙalawa a
lokacin mulkin Sarkin Zamfara Malo, kafin daga baya Gobirawan su mamaye su a
lokacin mulkin Sarkin Zamfara Maroƙi a shekarar 1764 har ma su mayar da Gonar Alƙalin Zamfara a matsayin sabuwar hedikwatarsu da suka
kira "Alƙalawa/Alkalawa"
a zamanin mulkin Sarkin Gobir Ibrahim Babari.
Daga
lokacin har zuwan Fulani masu jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular
Usmaniya a cikin ƙarni na 19,
Zamfarawan nan da Gobirawa suka mamaye sun yi ta yawo suna kafa
hedikwatoci na wucin gadi a Kiyawa ta Masarautar Birnin Magaji da Banga da
Kuryam Madaro dake Masarautun Birnin Magaji da Ƙaura Namoda a Jihar Zamfara ta yanzu da Sabongarin
Damri/Sabongarin Bakura kafin tsakanin 1815 zuwa 1824 Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo ya ɗauko hedikwatar daga Sabongarin Damri/Sabongarin
Bakura zuwa Anka inda take ya zuwa yau. Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura na
cikin Masarautar Bakura, Anka kuma ta na cikin Masarautar Anka duka dai a Jihar
Zamfara ta yau.
Akwai
jinsin Zamfarawa na biyu da suka ƙirƙiri Talata Mafara da Bukkuyum da Gummi dake Jihar Zamfara ta yau. Su
kuma sun fito ne daga Rano/Kano ne a cikin ƙarni na 18, a lokacin Daular Gobir ta mamaye waɗan can jinsin Zamfarawan da suka zauni Dutci/Dutsi da
Kiyawa da Banga da Kuryam Madaro da Sabongarin Damri/Sabongarin Bakura da Anka.
Haka
nan zaman ya ci gaba har bayyanar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi a cikin ƙarni na 19 a lokacin da jihadin jaddada Addinin
Musuluncin da ya jagoranta na Daular Usmaniya ya mamaye Gobirawa da sabuwar
hedikwatarsu ta Alƙalawa/Alkalawa
a cikin 1804 zuwa 1808 wanda shi ne abun da ya karya ƙarfin Daular Gobir har ma ya yi sanadiyar samar da
sabuwar hedikwatarsu a Tcibiri ta Jamhuriyar Nijar ta yau daga baya kuma suka
samar da Sabon Birnin Gobir ta Nijeriya a lokacin mulkin Sarkin Gobir Hassan Ɗan Halima.
Tsakanin
ƙarni na 17 da ƙarni na 18 da ƙarni na 19 wasu jinsin mutane sun shigo wannan yanki
da ake kira Zamfara suka ƙirƙiri Masarautu.
Misali,
Katsinawa zuriyar Ƙauran
Katsina Mayaƙi Gemun
Dodo sun ƙirƙiri Kwatarkwashi da Tsafe, wasu Katsinawan kuma suka
samar da Ƙasar Ɗansadau. Fulani Ashafawa daga yankin Yandoto suka
samar da Gusau a ƙarƙashin jagorancin Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa.
Fulani
Kasarawa daga Katsina ta hannun Malam Ibrahim Ɗan Zundumi suka samar da Bunguɗu, Fulani Adarawa daga yankin Nijar ta yau, watau su
Malam Muhammadu Daɗe/Da'e da ɗansa
Ummaru wanda ya zamo Sarkin Maru na farko da laƙabin Banaga suka samar da Maru, Fulani Alawa ta hannun
Malam Muhammadun Aya daga Mali ta yau suka samar da Birnin Magaji.
Fulani
Alibawa daga Nijar ta yau a ƙarƙashin
jagorancin Abu Amil da Muhammadu Namoda da Ummaru Ɗan Jeka da Gatari da Makauru suka samar da Zurmi da Ƙaura Namoda da Moriki da Kware da Kuryad Dambo.
Borno
- Fulata/Fulata - Borno ta hannun Muhammadu Wauni suka samar da Bazai/Jangeru, Fulani
daga Gwandu ta hannun Malam Muhamman Ballo suka samar da Badarawa/Shinkafi. Ɓurmawa suka fito daga Tsohuwar Daular Borno suka ƙirƙiri Bakura.
Fulani
Jallawa daga yankin Jamhuriyar Nijar ta yanzu ta hannun Malam Muhammadu Ɗan Naɓore da Malam
Madaro suka samar da Rawayya da Kuryam Madaro. Zamfarawan da ake kira "Ƙayatawa" a ƙarƙashin jagorancin Malam Abarshi suka samar da Masarautar Ƙaya/Maradun kafin Fulani Torankawa ta hannun Malam
Muhammadu Mu'alliyeɗi ɗan Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio su karɓi ƙasar a 1870.
Haka
aka yi ta wannan zama har bayan Jihadin Daular Usmaniya na shekarar 1804 har
kuma zuwan Turawa. Bayan Turawa sun ci Sakkwato, Cibiyar Daular Usmaniya Ranar
15/03/1903 sai duka waɗan nan wurare suka zama ƙarƙashin mulkin Ingila har zuwa samar da Ƙasar Nijeriya a 1914 da samar da Jamhuriyar Tarayyar
Nijeriya mai yancin kanta a shekarar 1960, kenan a ƙarƙashin Lardin Nijeriya ta Arewa.
A
shekarar 1967 aka yi Jihar Arewa maso yamma mai hedikwata a Sakkwato (Sokoto, Niger,
Kebbi, Zamfara na yau). A shekarar 1975/76 aka yi Jihar Sakkwato mai hedikwata
a Sakkwato (Sokoto, Kebbi, Zamfara), a Shekarar 1991 aka yi Jihar Kebbi daga
Tsohuwar Jihar Sakkwato, sai kuma a shekarar 1996 aka yi Jihar Zamfara daga
Tsohuwar Jihar Sakkwato inda aka tattara waɗan
can wurare da muka ambata a sama, Anka, Talata Mafara, Bukkuyum, Gummi, Gusau, Yandoto,
Maradun, Tsafe, Kwatarkwashi, Ɗansadau, Zurmi, Ƙaura Namoda,
Moriki, Bunguɗu, Maru, Birnin Magaji, Shinkafi, Kware, Kuryad Dambo,
Rawayya da Kuryam Madaro da Bakura aka ba su Jihar Zamfara da hedikwata
a Gusau.
Wadan
nan wuraren/yankunan ne aka mayar Masarautun yanka guda 19 bayan an ƙirƙiro Jihar Zamfara. Guda 11 masu daraja ta ɗaya, guda 8 masu daraja ta biyu.
Anka,
Gusau, Zurmi, Ƙaura Namoda,
Tsafe, Bunguɗu, Maradun, Talata Mafara, Bukkuyum, Gummi da Bakura
sune masu daraja ta ɗaya.
Birnin
Magaji, Moriki, Shinkafi, Kwatarkwashi, Maru, Ɗansadau, Jangeru/Bazai da Birnin Yandoto sune ke da
daraja ta biyu.
A
duba Tarihin Zamfara na Dr. Kurt Krieger wani Bajamushe da aka wallafa a
shekarar 1959 da The Rise and Collapse of Zamfara Kingdom (PhD Thesis Na Dr. Garba
Nadama, ABU Zaria, 1976) da Muƙalar Prof. Kabir Suleiman Tsafe mai Taken "Jihar Zamfara:
Tarihinta Da Ƙalubalenta
Da Ribatarta A Tarayyar Nijeriya" da ya gabatar a Taron Bikin Cika shekaru
20 da Ƙirƙiro Jihar Zamfara da aka gudanar a Gusau, Babban
Birnin Jihar Zamfara a watan Oktoban 2016.
A
duba Kundin PhD na Dr. Sanusi Shehu Gusau (UDUS, duk da yake ban tantance
take/tittle da shekara ba) da Kundin Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Daular Zamfara na UDUS, 2020 da
Kundin Taron Ƙasa da Ƙasa akan Tarihin Daular Gobir na UDUS (ban riƙe shekara ba) da Littafin Infakul Maisur na Amirul
Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio da Littafin Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau na
Jami'ar Bayero, Kano akan Masarautun Katsinar Katsinar Laka dake cikin Daular
Usmaniya da kuma The Fascinating Zamfara Emirates na Malam Ibrahim
Tambuwal (dake jiran ɗaɓi) domin samun ƙarin bayani akan wannan batu.
[7:52pm, 28/06/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
LAƘABIN SARAUTAR BANAGA DAGA
TSOHUWAR DAULAR ZAMFARA NE ASALINTA:
Banaga
sunan wani Mayaƙi ne da ya
fito daga jinsin Zamfarawan da suka samar da Masarautar Mafara/Talata Mafara ta
yau. Waɗan da ke da zumunci da Zamfarawan Masarautar Bukkuyum
da Gummi dukan su dai suna a Jihar Zamfara ta yau ne.
Malam
Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau muzakkarin gaske ne da ya fito daga tushensa
tun suna zaune a Tunfafiya (Tunfafiya tana akan Titin Gusau zuwa Sakkwato, yan
kilomitoci kaɗan kafin zuwa garin Talata Mafara, hedikwatar
Masarautar Zamfarawan Mafara ta yanzu a Jihar Zamfara) a ƙarshe ƙarshen ƙarni na 18.
Ya
tasarwa Kudu maso gaba shin Tunfafiya/Mafara sai da ya ƙirƙiri gari da ya kira da Birninsa, watau " Birnin Banaga". Anan
ya zauna har zuwa bayyanar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da mataimakansa
da suka shigo yankin daga wajensu na asali, kenan su Malam Muhammadu Daɗe/Daɗi/Da'e wasu
Fulani Adarawa da suka fito daga wani yanki na Jamhuriyar Nijar ta yau.
Daga
Birnin Banaga ne (a halin yanzu wannan Birni ne ake kira "Tsohon Birnin
Banaga dake cikin Masarautar Maru a Jihar Zamfara) ya dinga kai samame ya zuwa
iyakar Daular Katsina ta yamma (gabas da shi kenan) ya kuma matsawa Masarautar
Maska lamba da hare-hare, uwa uba ya hana sakewa ga masu jihadin jaddada
addinin musulunci na Daular Usmaniya.
Da
al'amarinsa ya yi tsanani ne Malam Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya umurci Malam
Muhammadu Daɗi/Daɗe/Da'e da
zuriyarsa da a lokacin suke zaune a yankin Jabaka (Jabaka hedikwatar gunduma ce
a Masarautar Maru ta yau) da Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa dake zaune a yankin Yandoto da Malam
Muhammadu Bachiri dake Bunguɗu da Malam
Karaf dake Kannu (Kannu gunduma ce a halin yanzu a cikin Masarautar Birnin
Magaji) da su fitar da shi daga wannan yanki.
Da
wannan ne sai suka yi masa taron dangin da ya sanya ya fice daga wannan Birni
nasa, watau "Birnin Banaga". Ya je yamma ya ƙirƙiri sabon mazauni da ya kira "Murai"/"Morai" ya ci
gaba da mulkinsa da laƙabin
"Banagan Murai" (Murai/Morai hedikwatar gunduma ce a Masarautar
Talata Mafara a Jihar Zamfara).
Ya
sake fita daga Murai ya je yamma ya ƙirƙiri garin Anka ya ci gaba da rayuwa tare da jama'arsa har zuwa shiyoyin
1815 zuwa 1824 lokacin da Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo daga zuriyar Sarkin Zamfara Abarshi (Zamfarawan da suka zauni
Dutci/Dutsi ta Ƙasar Zurmi,
Jihar Zamfara tun a shekarar 1300 da Birnin Zamfara a Ƙasar Isa, Jihar Sakkwato har zuwa 1764 da Kiyawa a
Masarautar Birnin Magaji da Banga da Ƙuryam Madaro dake Masarautar Ƙaura Namoda da Sabongarin Damri a Masarautar Bakura
duka a Jihar Zamfara) suka sake fitar dashi da jama'arsa duk da yake ba ta
hanyar yaƙi ba.
Daga
Anka ne ya fita ya sake girka wani gari da ya kira "Sabon Birnin
Banaga" da ke Kudu maso gaba shin Anka (wannan gari hedikwatar gundumar
Sabon Birnin Banaga ne a Masarautar Anka, Jihar Zamfara) inda a nan ne Allah
SWT ya yi masa wafati.
Kenan
daga Tunfafiya zuwa Birnin Banaga zuwa Murai zuwa Anka zuwa Sabon Birnin Banaga
ne Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau ya yi rayuwarsa.
Daga
baya ne masu jihadi suka mayar da garin Maru a matsayin sabuwar hedikwatar
wannan yanki da Birnin Banaga yake, suka naɗa
Malam Ummaru ɗan Malam Muhammadu Daɗi/Daɗe/Da'e a matsayin jagora da laƙabin "Banaga" a matsayin Sarautarsa domin
taskace Tarihin wannan muzakkari watau Malam Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau.
Daga
wannan ne wasu Masarautun Arewancin Nijeriya suka ari laƙabin wannan Sarauta ta "Banaga" suka ci gaba
da amfani da ita/shi.
Allah
SWT ya jiƙan
magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, ya yalwata
bayanmu, amin.
Ana
iya duba "Tarihin Zamfara" na Dr. Kurt Krieger wani Baturen Jamus da
aka buga a shekarar 1959 da "The Rise and Collapse of Zamfara
Kingdom" PhD Thesis na Dr. Garba Nadama (ABU Zaria, 1976) da "The
History of Zamfara from 1764 to 2013" PhD Thesis na Dr. Sanusi Shehu Gusau
(UDUS, 2017) da Littafin Infaƙul Maisur wallafar Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da kuma Littafin
Shaihin Malami Sa'idu Muhammad Gusau na Jami'ar Bayero, Kano da ya wallafa
akan rawar da masu jihadi suka taka a Katsinar Laka domin samun ƙarin bayani.
[3:42pm, 29/06/2024] Mal. I.M. Ɗanmadamin B/M:
FITAR BANAGA ƊAN BATURE ƊAN DANAU DAGA ANKA ZUWA SABON WURIN DA YA KAFA, WATAU
" SABON BIRNIN BANAGA.
Akwai
magana/maganganu guda biyu game da wannan fitar ta Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau daga Anka da suka fi shahara a Tarihin samar
da Anka a matsayin hedikwatar ƙarshe ta Zamfarawan da suka zauni Dutci/Dutsi da Birnin Zamfara da
Kiyawa da Banga da Ƙuryam
Madaro da Sabongarin Damri tsakanin 1300 zuwa 1815/1824.
Ta
farko ita ce wacce/wadda Dr. Kurt Krieger ya tafi akai cewa Sarkin
Zamfara Ɗan Baƙo (1815-1824) ne ya yi wa Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau sammu da aka haɗa a kaɓakin Tuwo aka ɗauka
daga Sabongarin Damri zuwa Anka. Har Bawan Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo wanda ya ɗauki sammun zuwa Anka ya ambata a cikin aikinsa
"Tarihin Zamfara" (wanda akasari daga rubutun magabata ne da suka
mulki Daular Zamfara da aka rubuta a cikin Ajami da ya karɓe daga Fadar Sarkin Zamfaran Anka a cikin 1940s/50s)
ya tafi dashi Ƙasar su, Jamus.
A shekarar 1959 kuma ya wallafa wannan Littafi nasa mai suna "Tarihin
Zamfara" wanda kusan shi ne madogara ta biyu akan Tarihin Daular Zamfara
bancin Infaƙul Maisur
na Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan
Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio
tagammadahullah birahamatihi.
A
ciki ya bayyana cewa bayan wannan Bawa ya girke wannan kaɓakin tuwo a Ƙofar gidan Banaga Ɗan Bature a Anka (a gidan ne Sarakunan Zamfara tun
daga Sarki Ɗan Baƙo, 1815-1824 ya zuwa yau suke sarauta) da ya fito
Sallar Asuba ya yi kiciɓis da shi sai sammun ya shige shi.
Da
hantsi ya tara hakimansa da manyan mutanen garin ya sanar dasu cewa zasu tashi
daga Anka ba tare da ɓata lokaci ba, ya yanke shawara umurni ne ya ke basu. Saboda
haka a ranar suka kimtsa kayansu, su ka fice daga garin, suka tsallaka Kogin
Zamfara dake Kudu da Anka ya sake kafa sabon zama da ya kira "Sabon
Birnin Banaga" inda na ambata a cikin rubutun da ya gabata cewa anan ne
Allah ya yi masa wafati. Na je garin a cikin farko farkon shekarar 2011.
Magana
ta biyu kuma akwai bayanin da ke nuna cewa umurnin Amirul Muminina Muhammadu
Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne Sarakunan
Zamfara na wancan lokaci da ke zaune a Sabongarin Damri su ka bi wajen
fitar da shi daga Anka da zummar su zauni wurin a matsayin sabuwar hedikwatarsu
duk da yake ba a bayyana ko ta wace hanya suka bi ba wajen aiwatar da
wannan umurni ba, ban kuma ci karo da wannan bayani a rubuce ba. Allahu
Wa'alam!!!
Fatsa/Hwatsa
[11:21am, 01/07/2024] Prof. A.M. Bunza: Mamari/ƙugiya sai an saka zare za ta zama fatsa.
[11:32am, 01/07/2024] Dr. Ali Usman Umar Lafiya:
Madalla da wannan ƙarin haske,
garnaƙaƙin Farfesa. 🙏🏼
[11:36am, 01/07/2024] Sarkin Rafin Gobir
Nikuma atawa mahanga wannan aikin na jafa mamari da zare da iccen da akeyi wato
sigar wannan ta kama kihin itace Hwatsa/fatsa,
Domin
ko'an handa mamari da zare ba'akiransu hwatsa Sai dai akirasu mamarin
hwatsa ko zaren Hwatsa
Misali
idan mutun nadaniyar yin hwatsa zakaji ya ce wannan mamari zaiyi hwata
ko wannan zaren zaiyi hwatsa kokuma wannan iccen zaiyi hwatsa ko zankama hwara
hwatsa
Kenan
Sai anhada abubuwa guda hudu 4 sannan za'aiya hwatsa
Mamari
Zare
Icce
Hwara/fara
Saboda
haka wannan sigar ta kamun kihin itace Hwatsa/fatsa
Maassalam,
[11:43am, 01/07/2024] +234 703 232 2222: Sosai
Sai an saka zare Da DanKaru Da Sanda Zata Zama Hwatsa/fatsa
Sannan
Akwai Roka Hwatsa/Fatsa wadda akeyi da zare Mai Wanda Daga karshe inda mamari
yake a daure Sai a daura mata adaura mata Dutse Domin mamarin ya nutse a kasa
sosai..........
[11:53am, 01/07/2024] Sarkin Rafin Gobir
Dan uwana malan Abdullahi idan ansaka zare da mamari ba'akiransu hwatsa Sai dai
akirasu anhada kayanyin hwatsa
Domin
wanda yatahi wajen yin hwatsa bacemashi yatahi wurin sun kihi Sai dai ace wane
yatahi wurin hwatsa
Amman
wanda yatahi da Homa Sai ace wane yatahi wurin su, sunkihi
[11:58am, 01/07/2024] Dr. Ali Usman Umar Lafiya:
Madalla da waɗannan bayanai naku. Ni, a karan kaina, na ƙaru sosai. Daga cikin abubuwan da suke samar da fatsa
kenan akwai:
Ic
(c)e/sanda
Zare
Fara
Mamari
Dutse*
Tambayata
ita ce, mene sunan abincin (mis: tana, ko gayan tuwo da akan maƙala a jikin mamarin) da ake yaudarar kifi da shi? Don
Allah, kuma ina son ƙarin
bayani game da laƙa/ɗaura dutse a jikin mamarin. Na gode.
[1:05pm, 01/07/2024] Sarkin Rafin Gobir
Wato atawa fahimta sigar kama kihi Gabaɗaya
kusan kowane ɓangare na ƙasar Hausa Akansamu Babancin yanayin da kowa ke
irin tashi dabara kamun kihi.
Wasu
lokutta ma Akansamu Banbancin yanda wasu ke kiran shikanshi wani kalan kihin da
kayan kamun kihin,
Misali
mu awajanmu bama amfani da kowane irin Dutci a wajen yin hwatsa kawaidai idan
mukasamu mamari da zare da icce/sanda da Hwara shikenan komi yahadu, Sai
bakin Gulbi wurin hwatsa/fatsa,
Yanzu ga maganar tuwo ka kawo nidai atamu Al'ada ta hwatsa bansan Anayin amfani da tuwo ba. Maassalam.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.