Ticker

𝐙𝐀𝐍 𝐈𝐘𝐀 𝐘𝐈𝐍 𝐒𝐀𝐋𝐋𝐀𝐇 𝐀 𝐙𝐀𝐔𝐍𝐄 𝐒𝐀𝐁𝐎𝐃𝐀 𝐊𝐀𝐓𝐎𝐍 𝐂𝐈𝐊𝐈?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Ina da tsohon ciki, idan ina Sallah sunkuyo da tashi yana bani wahala, zan iya yi a zaune?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum as salam. Za ki iya yi a zaune, in har ba za ki iya yi a tsaye ba, saboda Hadisin Imran ɗan Hussain lokacin da ya faɗawa Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) Basir ɗin da yake damunsa, sai yace masa: "Kayi Sallah a tsaye, in ka kasa kayi a zaune, in ka kasa yi a zaune kayi da gefenka", kamar yadda Bukhari ya rawaito a Hadisi na (1066).

Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: wanda yake da lalurar da zata hana shi yin Sallah a tsaye, zai iya yi a zaune, saboda addinin Musulunci mai sauƙi ne, ba ya ɗorawa rai abin da ba zai iya ba.

Allah ne mafi sani.

𝑨𝒎𝒔𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu... 

Post a Comment

0 Comments