Ticker

Gadon Mata Ta Biyar

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Miji ne yana mata huɗu sai bayan ya rasu ne aka gano cewa yana da wata mace ta biyar har da ’ya’ya! To, yaya za a yi maganar gado?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Alƙalin kotun musulunci ne zai bincika har a tabbatar da gaskiyar wannan daawar: Musulmi ya auri mace ta biyar! Alƙali ne zai gano: Yaushe aka ɗaura masa aure da ita? Da gaske a lokacin yana tare da auren matansa guda huɗu, ita ce ta biyar?

Idan ya gano haka ne, to wannan aure lalatacce ne. Kuma shari’ar musulunci ba za ta yarda da shi ba. Don haka babu wata alaƙa ta gado a tsakanin wannan matar da mijin da ya rasu.

Matsalar da ta rage kawai sai batun gadon ’ya’yan da aka samu a ƙarƙashin wannan ɓataccen auren.

Maganar da ta fi dai ita ce: Waɗannan ’ya’yan ba su da wani laifi domin samun su ta wannan hanyar da shari’a ba ta amince da ita ba. Don haka laifin mahaifinsu bai kamata ya shafe su ba. Kamar dai ɗan zina ne. Menene laifinsa?

A ƙarƙashin wannan bayanin, sai a tabbatar musu da dangantuwarsu ga mahaifinsu, kuma a saka su a cikin masu gadonsa.

Allaah ya tabbatar da mu a kan hanya.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

+2348021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments