Ticker

Hukuncin Alwalar Wanda Gabansa Ya Tashi Ba Tare Da Ya Fitar Da Komai Ba Da Kuma Yayin Da Ya Ke Sallah

Assalamu alaikum warahmatullah

Minene hukuncin Alwalar Wanda gabansa ya tashi ba tare ya fitar komai bh da Kuma a yayin sallah

AMSA

ALHAMDULILLAH

Sallah bata baci saboda tashin gaban mutum ko motsawar sha'awar sa ayin da ya ke sallah, domin hakan ba ya daga cikin abubuwan da suke bata sallah, matukar dai mazi bai futa ba, amma idan mazi ya futa to alwala ta lalace kuma wajibi ne mutum ya fita da ga sallar, kuma ya wanke gaban sa da abun da mazi din ya taba na tufafin sa ko jikin sa, sannan mutum ya sake alwala kuma ya sake sallah.

wajibi ne ga mai sallah ya kautar da dukkan wani waswasi da tunanin da yake sabbaba masa hakan (wato tunanin da yake sa gaban sa yake tashi ko sha'awar sa take  motsawa), kuma ya fukanci sallar sa da khushu,i da tadabbarin ma'anonin ayoyin da ya ke karantawa, idan kuma ya ji wani abu daga haka to ya nemi tsarin Allah daga shaidan, kuma yayi tofi a bangaran hagun sa Sau uku, kamar yan da ya zu  a cikin hadisi

أنَّ عُثْمَانَ بنَ أَبِي العَاصِ أَتَى النَّبيَّ صَلَّى اللَّهُ عليه وسلَّمَ، فَقالَ: يا رَسولَ اللهِ، إنَّ الشَّيْطَانَ قدْ حَالَ بَيْنِي وبيْنَ صَلَاتي وَقِرَاءَتي؛ يَلْبِسُهَا عَلَيَّ، فَقالَ رَسولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عليه وسلَّمَ: ذَاكَ شيطَانٌ يُقَالُ له: خَنْزَبٌ، فَإِذَا أَحْسَسْتَهُ فَتَعَوَّذْ باللَّهِ منه، وَاتْفِلْ علَى يَسَارِكَ ثَلَاثًا. قالَ: فَفَعَلْتُ ذلكَ، فأذْهَبَهُ اللَّهُ عَنِّي.

{رواه مسلم في صحيح مسلم الصفحة أو الرقم : 2203}

haqiqa usmaana dan baban aas {r.d} ya je wajan annabi {s.a.w} sai yace : ya manzan Allah haqiqa shaidan yana shiga tsakanina da sllah ta  da karatuna yana rikita ta akai na (ma,'ana ya na rikita ni da samin waswasi da tunanuka ta tayan da zan rasa ko raka'a nawa na sallata ko  yaya na karanta fatiha ko wanin ta) sai annabi {s.a.w} ya ce: ai wanchan da yake sa ka haka wani shaidan ne da ake kiran sa da suna [KHANZAB] idan kaji hakan (ko hakan ya riske ka) ta kanimi Allah ya tare ka daga gare shi (wato kace: A'UUZHU BILLAHI MINASH-SHAIDAANIR-RAJIIM) sannan kayi tofi a bangaran  hagun ka Sau uku. Sai usman dan abul aas ya ce: sai na aikata abin da annabi (s.a.w) ya ban umarnin in aikata, sai Allah ya tafiyar min da bin da na ke ji da ga gare ni. (wato na abun da shaidaanin nan ya ke Saka min a sallah ta). {imam muslim ne ya rawaito shi a cikin ingantaccan littafin sa wato sahihu muslim a lamba ta ko shifi na 2203}.

ALLAH SHINE MAFI SANI

AMSAWA

{ABU ABDULLAH}

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments