Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Manta Da Sallah Guda Bai Yi Ta Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum mlm barka da sapiya. Tambaya ce dani akan mutumin daya mance baiyi sallar Isha'i ba har saida gari ya waye bayan sallar asubah sannan ya tuna yaza'ayi. Bissalam

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

Wanda ya manta da wata sallar farillah bai tuna da wuri ba, har sai bayan ya sallaci sallar dake gaba da ita, yadda zai yi shine

Yayi alwala (idan bashi da ita) ya rama sallar da ya manta ɗin nan, sannan ya sake sallatar ta biyu nan wacce yayi.

Wato ka rama sallar isha'i ɗin sannan ka sake sallatar sallarka ta asubahin da kayi. Wannan haka hukuncin yake saboda wajibcin jeranta dukkan salloli yaseerul fawa'iti. (sallolin da basu kai biyar ba).

Kuma ita sallar ramuwa ya halatta ayita a kowanne lokaci ba sai an jira zuwan irin lokacinta na ainahi ba.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments