Ibnu Abdilbarr Ya Hakaito Sabani A Kan Tawaye Wa Shugaba Fasiki

    Imam Ibnu Abdilbarri ya hakaito sabani a kan mas’alar tawaye wa shugaba fasiki, yayin da yake fassara jumlar

    "ألا ننازع الأمر أهله"

    Ya hakaito fassarori guda biyu

    (1) “Ahlin shugabanci” su ne adilai masu falala da riko da Addini.

    (2) A son samu “Ahlin shugabanci” su ne adilai masu falala da riko da Addini, amma idan fasiki azzalumi ya zama shugaba to wajibi ne a yi hakuri, kada a yi masa tawaye.

    Fassara ta farko ita ce fassarar da ‘yan bidi’a cikin Mu’utazilawa da Khawarijawa suka rike, suke tawaye wa shugaba azzalumi. Ibnu Abdilbarri ya fadi haka inda ya ce

    "وبهذه اللفظة وما كان مثلها في معناها مذهب تعلقت به طائفة من المعتزلة، وهو مذهب جماعة الخوارج".

    الاستذكار (5/ 16)

    Wannan lafazi da mai irin ma’anarsa shi wasu cikin Mu’utazilawa suka rike a matsayin Mazhabarsu (ta tawaye wa shugaba). Kuma shi ne Mazhabar Khawarijawa”.

    A cikin “al-Tamheed” kuma ya ce

    "وإلى منازعة الظالم الجائر ذهبت طوائف من المعتزلة وعامة الخوارج".

    التمهيد لما في الموطأ من المعاني والأسانيد (23/ 279)

    Wasu kungiyoyin Mu’utazilawa da gamayyar Khawarijawa sun tafi zuwa ga ra’ayin tawaye wa shugaba azzalumi”.

    Fassara ta biyu ita ce fassarar da Ahlus Sunna suka gina Mazhabarsu a kanta. Ibnu Abdilbarri ya ce

    "وأما جماعة أهل السنة وأئمتهم فقالوا هذا هو الاختيار أن يكون الإمام فاضلا عالما عدلا محسنا قويا على القيام كما يلزمه في الإمامة، فإن لم يكن فالصبر على طاعة الإمام الجائر أولى من الخروج عليه، لأن في منازعته والخروج عليه استبدال الأمن بالخوف وإراقة الدماء، وانطلاق أيدي الدهماء وتبييت الغارات على المسلمين والفساد في الأرض وهذا أعظم من الصبر على جور الجائر".

    الاستذكار (5/ 16)

    Amma Jamaar Ahlus Sunna da Limamansu sai suka ce: wannan shi ne zabi abin so, shugaba ya kasance mai falala, mai ilimi, mai kyautatawa, mai karfi a kan riko da shugabanci. Amma idan ba a samu haka ba to hakuri a kan da’a wa shugaba azzalumi shi ya fi a kan yi masa tawaye, saboda yi masa jayayya da yi masa tawaye canza zaman lafiya da rashin zaman lafiya ne, da kuma zubar da jinane, da since ma wawaye hanaye su yi ta barna, da kuma bude wa kafirai kofa su yi ta kawo wa Musulmai farmaki, da barna a bayan kasa, wannan kuwa shi ya fi girman sharri a kan hakuri da zaluncin azzalumin shugaban”.

    Saboda haka sabanin da Imam Ibnu Abdilbarr ya hakaito a kan tawaye wa shugaba fasiki sabani ne tsakanin Ahlus Sunna da ‘yan bidi’a, Khawarijawa da Mu’utazila.

    To amma kasancewar kafin sabanin ya takaita tsakanin Ahlus Sunna da ‘yan bidi’a an samu wasu cikin Sahabbai da Tabi’ai sun yi tawaye wa shugabanni azzalumai, sai ake ba su mafita da wannan Hadisi. Wato su Hussain (ra), Abdullahi bn Zubair (ra) da wasu cikin Tabi’ai. Shi ya sa Ibnu Abdilbarrin ya ce

    "ذهب إلى هذا طائفة من السلف الصالح واتبعهم بذلك خلف من الفضلاء والقراء والعلماء من أهل المدينة والعراق".

    الاستذكار (5/ 16)

    Wasu cikin magabata na kwarai (Hussain “ra”, Abdullahi bn Zubair “ra”), kuma wasu masu falala cikin ‘yan bayansu, da makaranta Alkur’ani (gardawa) da Malamai a Madina da Iraq suka bi su a kan haka”.

    Lallai hakan ya faru, amma an yi musu inkari, kuma wasu sun janye daga yin tawayen, kamar Hussain (ra). Wadanda kuma suka yi tawayen daga baya sun yi nadama. Don haka ra’ayin bai samu gindin zama a cikin Ahlus Sunna ba, tun da sun yi taraju’i daga wannan ra’ayin.

    Daga karshe dai sai sabanin ya takaita tsakanin Ahlus Sunna da ‘yan bidi’a, Khawarijawa da Mu’utazila da sauransu, suka tafi a kan tawaye wa shugaba azzalumi. Abul Hassan al-Ash’ariy ya fadi game da Khawarijawa

    "ولا يرون إمامة الجائر".

    مقالات الإسلاميين ت ريتر (ص: 125)

    (Khawarijawa) Ba sa ganin halascin shugabancin azzalumi”.

    Haka al-Bagdadiy ya nakalto daga Abul Hassan al-Ash’ariy din ya ce

    "قال شيخنا أبو الحسن: الذى يجمعها إكفار على وعثمان، وأصحاب الجمل، والحكمين، ومن رضي بالتحكيم وصوب الحكمين، أو أحدهما، ووجوب الخروج على السلطان الجائر".

    الفرق بين الفرق (ص: 55)

    Ya ce: Daga cikin abin da kungiyoyin Khawarijawa suka yi Ijma’i a kansa akwai

    "ووجوب الخروج على السلطان الجائر".

    Wajabcin tawaye wa shugaba azzalumi”.

    Ahlus Sunna kuma suka yi Ijma’i a kan haramcin tawayen. Don haka duk wanda ya yi tawayen to ya fita daga Sunna, ya koma cikin ‘yan bidi’a, kamar yadda Imamu Ahmad da Ibnul Madeeniy suka fada

    "ولا يحل قتال السلطان ولا الخروج عليه لأحد من الناس، فمن فعل ذلك فهو مبتدع على غير السنة والطريق".

    شرح أصول اعتقاد أهل السنة والجماعة (1/ 181) طبقات الحنابلة (1/ 244)

    Bai halasta a yaki shugaba ba, haka yi masa tawaye, duk wanda ya yi haka to shi dan bidi’a ne, ba ya kan tafarkin Sunna da hanyar Ahlus Sunna”.

    Saboda haka da wannan za ka san cewa: danganta tawaye wa shugaba azzalumi ga Mazhabar Ahlus Sunna babban kuskure ne.

    ✍️ Dr Aliyu Muh'd Sani (H)

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.