Ticker

Iddar (Takabar) Mai Cikin Da Mijin Ta Ya Mutu Kafin Ta Haihu, Sai Ta Haihu Bayan Mutuwar Sa

TAMBAYA

Assalamu alaikum warahmatullah malan bambaya ta itace mace ce tana nakuda zata haihu sai mijin ta ya futa ya siyo kayan haihuwar sai mota ta kade mijin nata sai ya rasu bayan ya rasu sai matar ta haihu shin iddar ta da takabar sun yake tunda ta haihu bayan mujin nata ya rasu, ko kuma takabane za tayi iddar ta yanke mata tunda dai mijin nata ya MUTU kafin ta haihu ko doka zatayi

AMSA

YA kamata mufara sanin Nau'ukan {IDDAH}

Iddodin da mata ke yi sun kasu kashi biyu

(1) Iddan mutuwa (takaba)

(2) Iddan rabuwar aure.

Na farko: Iddan mutuwa (takaba): Wannan kuma shine: iddar da take wajaba ga matar da mijinta ya rasu ya bar ta, (kenan zamu fahimci  iddar itace takabar kuma takabar ita ce iddar kenan duk abu daya ne ga wace mijin ta ya rasu) shi kuma halin  matar da mijin ta ya rasu baya fita daga dayan halaye guda biyu:

(1)Ko wannan matar ta zama tana da ciki.

(2)Ko kuma ta zama bata da ciki.

Idan har ta kasance tana da ciki: To iddarta zata qare ne in ta haife abinda ke cikinta; koda kuwa bayan wassu 'yan-dakiqoqi ne daga rasuwar mijin nata, wannan kuma saboda faxin Allah madaukakin sarki

وَأُولَاتُ الْأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَنْ يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ ۚ  (الطلاق 4:65)

Ma'ana: (Su kuma ma'abota ciki lokacinsu na idda shine su sauke cikinsu) {dalaaq 4:}

kuma saboda da hadisin Almiswar dan Makhramata (r.d) yana  cewa

"أَنَّ سُبَيْعَةَ الأَسْلَمِيَّةَ(رضي الله عنها) نُـفِسَتْ بَعْدَ وَفَاةِ زَوْجِهَا بِلَيَال، فَجَاءَتِ النَّبِيَّ, فَاسْتَأْذَنَتْهُ أَنْ تَنْكِحَ، فَأَذِنَ لَهَا فَنَكَحَتْ" رواه البخاري (رقم/5320).

Ma'ana: (Haqiqah Subai'ah al-aslamiyyah {r.d} ta haihu bayan rasuwar mijinta da 'yan kwanaki, sai ta zo wajen annabi {s.a.w} tana neman izininsa akan za ta yi aure, sai yayi mata izini, sai kuma ta yi aure) {bukhari ne ya rawaitu shi a hadisi mai lamba ta 5320}.

kenan zamu fahimci ita mace mai ciki da zaran mijin ta ya mutu sai kuma ta haihu to ita ta gama takabar ta (iddar ta).

wannan ita ce  fahimtar dukkan malaman sahabbai (Allah ya kara yarda da su) ban da (abdullahi dan abas da aliyu dan abi dalib) hakama  dukkan malamai fahimtar su kenan, {Allah yai musu rahama)Ban da malan sahnuun almaalikey" {A duba sharhin muslim juz'i na 10 shafi na 109}

=Idan kuma ta kasance bata dauke da wani ciki: To iddar ta zata  kasance ne tsawon watanni huxu da kwanaki goma,(wato kwana dari da talatin 130) lallai matar da mijinta ya mutu ya barta ba tada ciki dole ne zata yi wannan takabar, da daya ne ya sadu da ita, ko kuma bai taba saduwa da ita ba; saboda gamewan fadin Allah ta'alah

وَالَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنْكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا ۖ فَإِذَا بَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا فَعَلْنَ فِي أَنْفُسِهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۗ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ (البقرة 234:2)

(kuma Wadanda suka rmutu daga cikinku, suka kuma bar mata na aure, (su mata) za su yi zaman jira na watanni gudu da kwana goma. (A matsayin takaba) to idan sun cika wa'adinsu, babu laifi a kanku (waliyyan su) cikin duk abun da suka aikata game da kawunan su ta HANYAR da aka saba (a shari'a). Kuma Allah mai cikakken sani ne game da abun da kike aikatawa [Baqarah: 234].

Kuma babu wani dalili da ya zo da kebance wata mace daga hakan.

Allah she ne mafi sani

AMSAWA

{ABU ABDULLAH)

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments