Imam Hussain Da Yazid Dan Mu'awiya

TAMBAYA (163)

Assalamualaikum barka da safiya ya aiki Dan Allah menene a tsakanin imam Hussain da Yazid Dan Mu awiya kwanan Nan abun da yake ta trending kenan wasu na bayan imam Hussain wasu na bayan Yazidu menene gaskyar lamarin

AMSA

Waalaikumus salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Dukkansu bayin Allah ne wadanda Allah ya yarda dasu

Tarihin abinda ya faru tsakaninsu yana da tsayi kamar yanda na karanta a cikin Mukhtasar Minhajus Sunnah📗 na Ibn Taimiyya Rahimahullah

Matsala ce ta shugaban ci👑 ta shiga tsakanin su, bankado matsalar bashida faida ga musulmi😔

Muawiya Ibn Abu Sufyan ya kasance Sahabin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ne wanda daga baya ya zamo gwamna a garin Sham (Syria a yau) a zamanin khalifancin Sayyadina Umar da Uthman (Radiyallahu anhuma)

Shine ya zamo khalifan Umayyad na farko (661-680 CE) bayan rasuwar Sayyadina Ali Ibn Abi Talib, khalifa na 4

Sayyadina Yazidu Kuma, Dan Mu'awiya ne, Wanda ya zamo khalifan Umayyad bayan rasuwar Mu'awiya (680 - 683 CE)

Fadan⚔️ dake tsakanin Mu'awiya da Hussain ya samo asali ne silar sahalewar da Mu'awiya yayiwa dansa akan ya gajeshi a Khilafanci Wanda hakan ya saba da ala'adar Khilafa a addini (Wanda sai Committee din Shurah sun saka hannu). Wadanda suka yi bore sun hada da jikan Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam wato Hussain Ibn Ali. Shi Kuma yayansa Hassan shine ya sasanta fadan shiyasa Yan Shi'a Suka tsaneshi, zakaji sunfi ambaton ya Hussain akan ya Hassan🤔

Hussain Yana ganin bai kamata a dora Yazid a matsayin magajin Mu'awiya ba saboda hakan ya ci karo da tsarin addini. Wannan rigimar ta cikin gida itace ta zama silar yaqin Karbala a shekarar 680 Miladiyya Wanda ananne yan Shi'a suka kashe Hussain🥹

Kamar yanda kasan ilimin Masdalahul Hadith to Haka shima Ilimin "Masdalahul Tarih" wato yanda ake tace tarihi, shine ya zama silar da yan Shi'a suke ta Zagin abokan fiyayyen halitta 😳(Sallallahu alaihi wasallam). Yanzu don Allaah zaka so mutum ya dinga Zagin abokan mahaifinka🤢. To Ina Kuma ga Wanda zai zagi  Sayyadina Abubakar, Umar da Uthman😭ya fifita Sayyadina Ali da Hussain

Ki karanta karatun Marigayi Shaikh Albany Zariya mai taken: "Hiqbatun Minat Tarikh" muqaddimar: "Tasdidul Isaba Fi Ma Shajara Bainas Sahaba" wallafar al-allamatil Shaikh Ziyab Ibn Sahad Ali Hamdan al-Ghamidi, anan zakiga yanda ake tantance tarihi kamar yanda ake tace zuma farar saqa🐝

Yan Shi'a sun baude daga tafarkin Sunnah😭 sun rarrabu alhalin Allaah Azzawajallah yace kada ku rarrabe🙅‍♂️

( وَلَا تَكُونُوا كَالَّذِينَ تَفَرَّقُوا وَاخْتَلَفُوا مِن بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْبَيِّنَاتُ ۚ وَأُولَٰئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ )

آل عمران (105) Aal-Imran

Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka rarrabu kuma suka sãɓã wa jũna, bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu kuma waɗannan sunã da azãba mai girma.

Ko dayake ma su fa basu yarda da wannan Qur'anin da mu musulmai muke amfani dashi ba suna claiming ai an caccanzashi🤦🏼‍♂️. Ko ya zasuyi da ayar da Allaah yace Shi ya saukarda littafin Kuma zai Kare abinSa🤔

( إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا الذِّكْرَ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ )

الحجر (9) Al-Hijr

Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyaywane gare shi.

Allaah yace kada mu zamo ƙungiya ƙungiya

( مِنَ الَّذِينَ فَرَّقُوا دِينَهُمْ وَكَانُوا شِيَعًا ۖ كُلُّ حِزْبٍ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ )

الروم (32) Ar-Room

Wãtau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kõwace ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai.

Amman saboda sakarcin Shi'ah da Jahilci da biyewa son zuciya sai suke ma Kiran Kansu da ƙungiya din gaba daya (Wato Shi'ah)

Da akwai wani Malami Dan Shi'a Mai suna Shaikh Ali Khalil Ankantara Wanda gaba daya baya jin qishin ruwa💦 saidai yasha don marmari. Hakan ta faru a gaske silar mafarkin da yayi anyi tashin ALQIYAMA

Gashinan a tafkin ruwan Alkauthar 😍tareda Ma'aiki da Sahabbansa, sai ya tafi wajen Sayyadina Ali saboda bayason sauran Sahabban. Sayyadina Ali ya kauda kansa yaqi kulashi, can sai Ma'aiki ya kirashi, yace masa Zan shayar dakai ruwan Alkauthar amman kayimin alqawarin zaka dinga son Sahabbaina gaba daya. Nan take ya dauki alqwarin, Ma'aiki ya shayar dashi ruwan💦. Nan take ya farka daga baccin a tsorace😳

Daganan ya watsar da baqaqen kayannan nashi yacewa dalibansa da dubunnan mabiyansa su gaggauta barin Shi'ah babu alkhairi ko kadan a cikinta. Daganan ya riqe Sunnah gamgam. Tun daga mafarkin nan da Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam ya shayardashi ruwan Alkauthar, iyalansa sukace bai qara jin kishin ruwa ba. Allaahu Akbar !

Sahabbai ba maasumai baneba don sun fada cikin hadisin: Dukkan Yan Adam masu laifi ne saidai mafi alkhairinsu sune masu yawan tuba🤷‍♂️

عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «كلُّ بني آدم خَطَّاءٌ، وخيرُ الخَطَّائِينَ التوابون». 

[

رواه الترمذي (2499)، وحسنه الألباني، فهنا لم يتم استثناء أحد

Allaah yace

( يَا أَيُّهَا الرُّسُلُ كُلُوا مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَاعْمَلُوا صَالِحًا ۖ إِنِّي بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ )

المؤمنون (51) Al-Muminoon

Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.

( وَإِنَّ هَٰذِهِ أُمَّتُكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَأَنَا رَبُّكُمْ فَاتَّقُونِ )

المؤمنون (52) Al-Muminoon

Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa.

( فَتَقَطَّعُوا أَمْرَهُم بَيْنَهُمْ زُبُرًا ۖ كُلُّ حِزْبٍ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ )

المؤمنون (53) Al-Muminoon

Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu, kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su.

Son sahabbai wajibine saboda Allaah ya yarda dasu💞. Shaidan ne yake QOQARIN ya jefa mana qiyayyarsu a xuqatanmu kamar yanda ya jefawa Yan Shia tsanar su

Abinda yafi shine ka roqa musu Rahamar Allah 🤲sannan ka qyale abinda ya faru tunda ya riga da ya faru

Wallahu taala a'alam✒️

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku  kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments