Jinin Haihuwa Yana Dawo Min

    TAMBAYA (164)

    Aslm alaikum Malan da fatan an wuni lfy tambaya ta itace n'a haihu yaw kimanin Wata biyar anma tun bayan haihuwar jini na ya kasa daidaituwa yakan zo kuma bayan ya kwanaki ya dawkewa kuma ya sake dawowa to Malan dan Allah miye hukunci wannan jini kuma zan bar ibada ne yayin da ya dawo ko zan ci gaba da yi da fatan za a amsa mini tambaya ta da gaggawa nagode

    AMSA

    Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

    Jumhurin malaman mazhabobi guda 4 sunce babu taqamaiman adadin kwanakin da mai jinin nifaas take yi

    Saidai sunce mace zata ci gaba da ibadar ta ne bayan kwanaki 40 ko da ace jinin ya ci gaba da zubowa

    Jinin da ya ci gaba da zubowa bayan kwanaki 40 din shi ake Kira da jinin Istihaadah Kamar yanda hadisi ya tabbata daga Umm Salama (Radiyallahu anha)

    _Ahmad, Abu Dawood, al-Tirmidhi da ibn Maajah haka Kuma a cikin Massah al-Azdiyyah wanda Shaikh Muhammad Nasiriddin Al-Albani ya sahhahashi_

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.