Kwanakin baya na yi rubutu da Ingilish a kan sunayen Hausawa na gargajiya. Mutane da dama sun nema in fassara zuwa Hausa domin ƙaruwar al’umma. To gashi nan!
Kusan shekaru 45 da suka wuce, matar wani amini na ta haifar mu su da ɗa. Aminin nawa ya ce da magabantan sa a sawa yaron suna Maikuɗi. Duka ɓangaorin – na matar sa da na sa – suka tirje kan cewa ai ‘Maikuɗi’ ba suna ba ne. Shi kuma bai ga wani aibu da sunan ba, tunda sunan gargajiya ne na Hausawa. Kuma shi Bahaushe ne. Ya cije. Suka cije.
Kwanaki uku kafin ranar sunan jaririn dole ya haƙura,
ya bada wani sunan. Ya ce a raɗawa
yaron Ibrahim. Wannan suna ne mai daraja
wajen Musulmai, Kiristoci da kuma Yahudawa. Hankalin kowa ya kwanta da
wannan sunan. Sai da suka farga cewa ashe sunan uban maihaifiyar yaron ne. To
kaga kuwa ba wanda ya isa ya kira sunan yaron Ibrahim batso-batso saboda kunya
da kara. Ala dole a ka dinga kiran yaron da sunan da uban ya so a ba shi tun
asali: Maikuɗi. Yanzu
dai Maikuɗi cikakken ɗan kasuwa ne a ƙasashen
Gabas to Tsakiya. Allah Ya ba shi nasara sosai, kuma ya ci sunan sa – domin a Hausance Maikuɗi na nufin wanda aka haifa
ranar sa’a, ko kuma wanda a ka haifa ranar Talata.
Amma ba a rabu da Bukar ba, wai an haifi Habu. Bayan shekaru
kaɗan, matar aminin
nawa dai ta haifar masa da ƴa mace. Kamar ka sani, sai ya ce a raɗa mata suna Tabawa, sunan Hausawa. Nan ma a ka
ce ba a yarda ba. Tabawa ba suna ba ne. Kamar wancan lokacin, dole amini na ya
haƙura,
ya ce a sakawa yarinyar suna Hajara. Shi ma suna ne mai daraja. Hasali ma dai,
Hajara sunan matar Annabi Ibrahim ne. Sai dai kuma sunan babbar yayar amini na
ce, kuma mahaifiyar su ba ta furta sunan, saboda kunya irin ta mutanen da. Dole
a ka haƙura
aka dinga kiran jaririyar da Tabawa. Sunan asali a cikin al’ummar Hausawa wanda ke
nufin uwar sa’a. Ko
kuma wacce a ka haifa ranar Laraba (a Kano, a Katsina kuma ranar Talata). Yanzu
haka tana koyarwa a babbar makaranta a Kano, kuma ta kusan gama PhD a ɗaya daga cikin jami’o’in
Najeriya. Yara guda biyu. Kowanne ya
taki sa’a a rayuwa. Sunayen su suka zama jagora gare su.
Tambayar ita ce, mai ya sa muka tsani sunayen Hausawa na
gargajiya? Ko don saboda “Aƙidar Danniya”
ce, watau Cancel Culture inda ake ta rurutawa duk wani sunan da ya samo asali
daga gargarjiyar Hausawa za a ce ai na Maguzawa ne?
Watau ba za ka raɗawa
ɗan ka suna Maikuɗi ba, amma da zarar ka ce
sunan sa Yasar sai a ce ka yi daidai, duk da cewa Yasar, sunan Larabawa, na
nufi mai arziki. Ko Kamal (daidaito). Kira ɗan
ka Damisa, ka shiga uku, in ka canza zuwa Fahad, ka gyara, duk da cewa sunan
wani nau’i na damisa (panther) da Larabci. Mai ya sa Fahad ya fi Damisa daraja
duk da cewa ma’anar su ɗaya?
Sunaye da yawa da mu ke amfani da su ba du da wata nasaba da
Musulunci – kawai zaƙi ne da su; sai mu ɗauka
mu ƙaƙabawa
kan mu. Yanzu dubi waɗannan
sunayen Larabawan, sannan ka kwatanta abin da zai faru in ka yi amfani da sunan
fassarar su da Hausa: Fawaz (Nasara – Mainsara?), Farid (kaɗaitacce), Haydar (Zaki),
Mumtaz (mai inganci), Usama (Zaki), Zafer (wanda ya yi nasara), da dai sauran
su.
Kar ka ce Tabawa, amma ka ce Mahjuba (lullubabbe), ko Samira
(surutu). “Dare? Sunan mace? Haba malam, menene haka?”, “Afuwan, na canza, zan kira ta Laila” (dare,
da Larabci).
Abin da nake son in nuna shi ne da yawa daga cikin sunayen
da Hausawa Musulmai ke alfari da su ba su da wata dangantaka da Musulunci. Bama
ma sanin ma’anar sunayen, kawai saboda zaƙin sunan da kuma Larabcin sa, sai mu ɗauko mu jibga wa ƴaƴan mu.
An tirsasawa Hausawa yin amfani da sunayen Larabawa saboda Cancel Culture ta
gama shelantawa duk sunan da ba na Larabawa ba ne (ko da ba shi da asali a Qur’ani ko Hadisi), to na ‘Haɓe’ (watau Hausawan asali) ne, kuma in dai na
Haɓe ne, to Maguzanci
ne. Wannan kuwa an yi ne domin a nunawa Hausawa ba su da tasiri a rayuwa tun
daga 1804.
Ganin haka ya sa ni da aminin na, da kuma wani abokin mu
muka ce gara mu yi fargar jaji a kan
sunayen Hausawa, duk da cewa mu kan mu daga baya ambaliyar Cancel Culture ta
mamaye sunayen da muka bawa ƴaƴan mu. Amma duk da haka mukace bari mu
zauna mu yi wani yunƙurin ankare mutane game da Cancel Culture a kan sunayen
Hausawa na asali. Mun futo daga sinadiran halitta dabam-dabam (Kanuri,
Balarabe, Fulani), amma mun watsar da wannan muna alfahari da cewa mu Hausawa
ne, ba wani shashancin ‘Hausa-Fulani’.
Sai da mukayi shekaru fiye da goma muna tattaro sunayen
Hausawa na asali waɗanda
ba su da wata alaƙa da Maguzanci (rukunin da ƴan Cancel Culture ke saka duk Bahaushen
da ba Musulimi ba ne, an manta akwai Hausawa da kuma sauran ƙabilu
ma su bin addinin Kirista –
su ma Maguzawa ne?). Sai muka haɗa
da ƙalilan
daga sunayen da suke da nasaba da Musulunci. A ƙarshe muka samu sunaye 1001 da Hausawa ke
amfani da su. Daga ciki, 869 zunzuruntun
sunayen asali ne na Hausawa. Sannan sai 132 waɗanda suka samo asali daga zuwan Musulunci,
harda waɗanda Hausawa
suka narkar da su. Bari na yi bayanin kaɗan
daga cikin duk rukunayen biyun.
Rukuni Rayuwa, Cututtuka da Mutuwa. A wannan rukunin,
Hausawa na bawa ƴaƴan su sunayen da suka danganci akasin rayuwa. A wannan rukunin
za a fahimce yadda Hausawa suka ɗauki
rayuwa. Misalai sun haɗa
da waɗannan:
Barbushe (wanda ba ya barci). Wannan shi ne sarkin Kano na
farko kafin mulkin mallakar Daudawa (Bagauda da ayarin sa). Wataƙila
ganin cewa wannan shi ne babban mai jagorancin bauta a tsakanin Kanawan da suka
yarda da addinin sa a farkon samuwar alƙarya su ya sa ake danganta ire-iren waɗannan sunayen da wannan
nau’in bautar.
Abarshi. An samo wannan da daga lafazin ‘Allah Ya bar shi’.
Mace kuma Abarta.. Idan an haifi yaro, a kan rabu da shi, watau a bar shi shi
kadai wani tsahon lokaci ta yadda ko iskokai ba za su kula da shi ba. Ana yin
haka ne saboda kare shi. Dangogin sunan sun haɗa
da Mantau, Ajefa, Barmani, Ajuji, Bawa, da Barau.
Ga kuma Shekarau, wanda aka samo daga Shekara. Wannan yaro
ne wanda aka haifa bayan ya wuce lokacin haihuwa, watau kamar ya shekara a ciki
kenan. Wani juyin sunan shi ne Ɓoyi (ɓoyayye).
Ana kiran jaririya da wannan martabar Shekara. Shawai kuma sunan da a ke bawa
yarinyar da ta sha wuya bayan haihuwar ta (ana sawa maza ma sunan). Anini
yarinyar da ke ƙananuwan gaɓoɓi ne.
Sai kuma Tanko. Wannan jariri ne wanda ya biyo haihuwar mata
uku a jere. Makamantan sunan sun haɗa
Gudaji, Tankari, Yuguda/Iguda/Guda. Macen shi kuma ita ce Dela (da kuma Duduwa,
Baranka, Kande) macen da ta biyo maza a haihuwa, kamar Tanko da matan da ya
biyo.
Dukiya da kuma Bauta: Wannan rukunin sunayen da Hausawa ke
gudu saboda dangantasu ta mummunar muzantawa al’umma ta hanyar bautarwa. Bayi
na da muhimmanci a masarautun Kano, Zariya, Daura da Katsina. Kuma ana juya su
yadda iyaygen gidan su suke buƙata.
An kasa bayi rukuni biyu a Kano: na gida, da kuma na gona.
Yardaddun bayi aka fi bari a gidan Sarki
saboda sadaukarwa su ga mai sarautar. Bayin gona kuwa waɗanda ana kamo su ne lokacin rarumar yaƙi, ko
kuma ba a yarda da su ba saboda ganin cewa za su iya tsere wa da zarar sun samu
dama. Irin waɗannan
bayin an fi samun su a gidajen attajirai, ko kuma manyan manoma.
Duk da dai cewa ba a cinikin bayi yanzu (hasali ma kifar da
cinikin ne ginshiƙin zuwan Turawan mulkin mallaka a 1903 zuwa Kano) amma har
yanzu bauta na nan da ranta a gidajen Sauratar ƙasashen Hausa.
A Kano dai bayin an sake raba su gida biyu – kammmun bayi
(rukunin farko wanda kamo su a ka yi a raruma) da kuma cucunawa ƴaƴan
bayi, waɗanda su ma
bayi ne). Sunayen da ake danganta su da bayi sun haɗa da:
Nasamu. Wannan bawan farko ne da matashi ya mallaka a kan
hanyarsa ta zama hamshafin attajiri. Sai Arziki, baiwar farko da mutum ya
mallaka. Ga kuma Nagode, baiwar da a ka bawa mutum kyauta. Idan mahaifi na son
kyautatawa ɗan sa, sai
ya ba shi bawa namiji, wanda ake kira Baba da Rai. Suna Dangana na da tushe
biyu. Na farko shi ne yaron da ƴan uwansa suka rasu da jaririntaka (sunan
macen shi ne Nadogara). Na biyu shi ne bawan da manomin da ya fara nasara bayan
ya sha wahalar noman. Sai Baubawa, bawan da ke daga addini dabam da na mai shi.
Tun zuwan Turawa aka fara zaizaye sunayen da ke da
dangantaka da cinikin bayi. Amma duk da haka, akwai sunayen da ke alamta ko
sana’a ko matsayin bawa. Misalai sun haɗa
da sarautun bayi a gidajen Sarauta, duk da ba a cika yawan amfani da su ba. Kaɗan daga cikin sun haɗa da:
Shamaki (mai kula da bayin sarki da kuma dawan sa). Ɗan
Rimi (Babban bawan sarki, kuma yana kula da makaman yaƙin sarki). Kasheka (mai
kula da cikin gidan sarki, akasari ‘baba’ ne, watau dai ‘zarmalulu no work’ saboda gudun raɗe-raɗen shaiɗan),
Jarmai (shugaban runduna), Kilishi (mai kula da kujerar Sarki). Waɗannan sunayen a gidan
Sarauta kawai ake samun su ba jama’ar gari ba sai dai a matsayin laƙabi.
Rukunayen Sunayen Yanayi. Hausawa na bawa ƴaƴan su
sunaye da ke da alaƙa da yanayi na shekara, sati, ko zagoyawar yanayin. Misali,
Sammako (wanda aka haifa da asuba), Ranau (haihuwar rana), Na-Hantsi (da
hantsi), Dare (cikin dare), Shuka (lokacin shukar gona), Nomau (da kuma Ɗankaka,
Kakale, Kaka duk lokacin girbi), Marka (kamar damina).
Musulunci bai hana baiwa mutum sunan da ya dace ba. Illa dai
ba a son abin da ya yi nuni ga wani abun da Musulunci ya haramta. Zuwan
Musulunci sai ya kawo sunayen da aka fi danganta su da Musuluncin kamar sunayen
Annabawa, ko Sahabbai. Waɗansu
sunayen kuma sai Hausawa suka lanƙwasu zuwa nasu furucin. Misali Guruza
(Ahmad), Da’u (Dawud),
Gagare (Abubakar), Auwa (Hauwa), Daso (Maryam), Babuga (Umar), Ilu (Isma’il), Jibo (Jibrin),
Dijangala, Dije (Khadijah), Unku (Amina), Jibaje (Jibrin), Hansai (Hafsat),
Burungu (Amina), Abba (Abun).
Wannan taƙaitaccen bayani ne a kan waɗannan sunayen. Ga cikakken
jerin sunayen a rariyar kasa in mutum ya na so ya samu. Sannan kuma akwai
cikakkiyar maƙala ta Ingilishi da a ka buga bayanai masu zurfi a kan
lamarin. Rariyar ta na ƙasa ita ma.
Suna Linzami: Hausa Names as Ethnographic Identifiers: https://bit.ly/3XHmf1I
1001 Authentic Traditional Hausa Names: https://bit.ly/4e42es2
Daga shafin
Prof. Abdalla Uba Adamu
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.