Ticker

Maras Hankali Kawai

Shi fa wannan hankali da kake gani, wanda kullum zaka ji ana cewa; wane ya yi hankali, wane yana da hankali, wane ba shi da hankali,,, kowa ya san a jikin Dan Adam yake, amma abin mamaki abu ne da mutane suka yi sabani mai tsanani wajen bayanin hakikaninsa. Tun daga kan Musulmai har zuwa Mulhidai 'Yan Falsafa. Kowa ya yi bayaninsa bisa mahangar sana'arsa da bukatarsa gare shi. Har aka nakalto cewa; an samu ra'ayi kusan dubu a kan ma'anarsa.

Su 'Yan Falsafa iya iliminsu shi ne bincike a kan abu samamme, saboda haka suka kasance jahilai a kan abin da yake bayan halitta (Metaphysics). Haka likitoci su ma sun yi nasu bayani, haka Malaman nazari masana Ilmul Kalam, mabiya hankali a Addini, haka Malaman Fiqhu, sun yi bincike kan hankali, don bayanin sharadin hawan Shari'a kan Mukallafi.

Wasu 'Yan Falsafan suka ce Hankali abu ne da yake tsaye da kafafunsa "Jauhar", suka mayar da hankali tamkar mutum mai tafiya ko dabba mai tafiya, -abun dariya- 😅. Iya iliminsu kenan.

Alhali shi hankali Gaibi ne kamar yadda Ruhi yake gaibi, su kuma 'Yan Falsafa sun fi kowa jahilci game da gaibi, ba su san komai ba sai abin da yake a zahiri, wanda za a iya taba shi ko ganinsa ko jinsa ko... Wannan ya sa 'Yan Falsafa suka wayi gari Mulhidai, masu inkarin samuwar Allah, saboda hankalinsu ba ya iya riskar gaibi.

Amma mu kuma Musulmai, Ubangijinmu Allah abin bautarmu, ya sanar da mu cewa; hankali wata sifa ce -ba jiki ba- da take jikin Dan Adam, wanda yake sanin wasu abubuwa da ita, wacce za ta banbance tsakaninsa da Mahaukaci. Kamar sanin cewa; daya rabin biyu ne, baki da fari ba sa haduwa kamar yadda haske da duhu ba sa haduwa, da makamancin irin wannan ilimi da duk mai shi za a kira shi Mai hankali bisa ma'anar sabanin Mahaukaci.

Kuma a kan wannan Allah ya dora Shari'a. Ma'ana; Allah bai dora Shari'a ga wanda bai san akwai banbanci tsakanin haske da duhu, sanyi da zafi, da sanin cewa; sama ba za ta rikito ba, ko sanin cewa; ba za a yi ruwan naira daga sama ba, d.s.

Haka kuma Allah ya nuna mana cewa; hankali yana zuwa da ma'anar aiki da ilimin sanin gaskiya da sanin abun da zai amfani mutum amfani na hakika, da wanda zai cutar da shi cutarwa ta hakika. Don haka duk halakakke cikin Mulhidai, Kafirai da Zindikai da Munafukai 'Yan Boko Aqida ba su da hankali bisa wannar ma'ana.

Da wannan za ka san cewa; Mulhidai, Kafirai da Munafukai 'Yan Boko Aqida, duka suna da hankali da ya banbance tsakaninsu da Mahaukaci, amma ba su da hankali na aiki da ilimin abin da zai amfanar da su ko ya cutar da su ta hakika.

Wannan ya sa a Ranar Lahira za su yi nadama a cikin wuta su ce:

{لَوْ كُنَّا نَسْمَعُ أَوْ نَعْقِلُ مَا كُنَّا فِي أَصْحَابِ السَّعِيرِ } [الملك: 10]

"Da mun kasance muna ji, kuma muna hankalta da ba mu kasance cikin 'yan wutar Sa'ira ba".

Ya Allah ka mana tsari da rashin hankali.

✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments