Mas’alar Gado A Tsakanin ’Yan’uwa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Na saya wa mahaifiyarmu gwalagwalai na ba ta a matsayin aro domin ta riƙa ado da su. Yanzu dai ta rasu, kuma yanuwana ba su san wannan yarjejeniyar a tsakaninmu ba. Wace shawara malam zai ba ni a kan gadon waɗannan gwalagwalan nawa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    Ya danganci yadda ’yan’uwan za su ɗauki wannan labarin ne idan suka ji shi a yanzu. Idan kin tabbatar cewa za su gaskata ki a kan maganar, to kina iya gaya musu. Har kuma a ware waɗannan ɗin daga cikin kayan gadon marigayiyar.

    Amma idan kin tabbatar ko kina shakkar amincewarsu da maganar, to abin da ya fi sai ki yi shiru kawai, kar ƙilu ta jawo bau. Wato kar a yi tsammanin so kike kawai ki rage musu kayan gadonsu.

    Wanda hakan kuma shi zai iya haifar da saɓani a tsakanin ’yan’uwa, saɓanin da zai iya kai wa ga asarar da ta fi ta miliyoyin kuɗi, wataƙila ma sama da farashin gwalagwalan.

    A fahimtata gara ki yi haƙuri da neman wannan gwalagwalan kawai, musamman dayake tun asali ba ki sanar da kowa ba, kuma ba ki sanya kowa sheda a kan hakan ba.

    Ba abin mamaki ba ne idan kika yi haƙuri, daga baya Allaah ya musanya miki da abin da ya fi shi alkhairi, musamman idan kika sanya kyakkyawar manufar kawar da rashin jituwa da janyo fahimtar juna a tsakanin ’yan’uwa.

    Allaah ya taimaka.

    Wal Laahu A’lam.

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    +2348021117734

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.