Ticker

Me Ya Sa Addinin Muslunci Ya Tsole Ma Turawa Ido?

Wata rana mun yi rubutu, a ciki sai muka yi ishara cewa; Muslunci shi ne Addinin da Turawa suke yaka. To sai wani daga cikin yaran Turawan masu izgilanci ga Addinin Muslunci yake cewa; ta yaya Turawa za su tsaya su bata lokacinsu wajen yakar Addinin jahilci da cibaya?!

To abu ne sananne cewa; Yaki da yake gudana a yau yaki ne a kan Madogaran tsarin rayuwa. Yaki ne tsakanin tsarin rayuwa da ya ginu a kan Addini, da kuma tsarin rayuwa da ya ginu a kan watsi da Addini (secularism & modernism).

Ita madogarar tsarin rayuwa ta Addini, Addinin Kiristanci da Addinin Yahudanci sun fadi warwas a gaban tsarin rayuwa bisa madogara ta watsi da Addini (secularism & modernism). Ma'ana; Addinin Kiristanci da Yahudanci duka sun gaza wajen tunkarar tsarin watsi da Addini (secularism & modernism), saboda Addinai ne da aka lalata su aka gurbata su, aka gurbata littatafan da aka saukar musu.

Shi dai Yahudanci da ma Addini ne na gado da kabilanci ba Addini ne na kiran mutane su shiga cikinsa ba, mutum ba zai zama Bayahude ba sai in iyayensa Yahudawa ne, musamman uwarsa mahaifiya. Don haka Addini ne na kabilanci. Wannan ma yana daga cikin dalilai da suka sa Yahudancin ya kasa tunkaran tsarin rayuwar watsi da Addini (secularism & modernism).

Amma shi kuma Kiristanci tun tuni ya fadi a gaban madogarar watsi da Addini (secularism & modernism), tun lokacin da aka gurbata shi aka shigar da almara masu yawa cikinsa. Babbar almarar da suka kirkira ita ce cewa; Allah uku ne Allah daya. Da almaran cewa; Allah ya shiga jikin Annabi Isa (as). Har kuma lokacin da aka shata fagen yaki tsakanin Malaman Coci da Malaman Kimiyya da Fasaha, inda Coci ya yaki duk wani binciken Kimiyya da aka yi aka gano Nazariyya da abubuwa na hakika da suka saba ma karantarwan Coci da Bible.

To a nan ma dai Kiristanci ya gaza a wannan dagar da suka yi da Malaman Kimiyya, wannan ya sa aka yi watsi da Kiristanci a Turai, a koma tsarin rayuwa bisa madogarar watsi da Addini (secularism & modernism).

Don haka daga nan babu Addinin da ya saura ya tsaya a gaba tsarin rayuwa bisa madogarar watsi da Addini (secularism & modernism) sai Addinin Muslunci kawai. Shi ya saura a tsaye tsayin daka babu girgiza a gaban tsarin watsi da Addini. Saboda babu tufka da warwara a cikinsa, kuma Addini ne na da'awa da yake kiran mutane a shiga cikinsa, kuma Allah ya tsare Littafinsa daga gurbata, kuma har yau babu wani binciken Kimiyya na hakika da ya zo ya ci karo da tabbataccen Nassi na Addinin Muslunci. In kuwa ka samu abin da ya ci karo da tabbataccen Nassin, to Nazariyya ce kawai ba ta tabbata a bisa hakika ba.

Amma babu binciken Kimiyyar da aka tabbatar da hakikaninsa amma kuma ya saba ma tabbataccen Nassi na Addinin Muslunci.

Sa'annan kuma kasancewar Addinin Muslunci cikakke ne ya shafi dukkan fagagen rayuwa, ya iya yin jawabi a kan dukkan matsalolin rayuwa gaba daya; fagen Siyasa da Tattalin arziki da Zamantakewa. Kuma Addini ne da dalilansa dalilai ne na yakini masu karfi da ingancin da babu shakka a cikinsa.

Wannan ya sa tsarin watsi da Addini (secularism & modernism) ya tabbatar da cewa; lallai babu kalu-bale a gabansa sai Addinin Muslunci kawai shi kadai. Wannan ya sa ta ko'ina Muslunci aka sa a gaba, saboda shi ne wanda ya tabbata a tsaye a bisa hakika, babu shiririta ko tufka da warwara a cikinsa, shi ne Addinin da ba a gurbata shi ba, kuma binciken Kimiyya da fasaha na hakika ba ya cin karo da shi.

Saboda haka a yau babu yaki na hakika face tsakanin tsarin rayuwa bisa Madogarar Addinin Muslunci da kuma tsarin rayuwa bisa madogarar watsi da Addini (secularism & modernism). Don haka Turawa suka tabbatar cewa; ba su da abin da za su yaka sai Addinin Muslunci.

Babban abin da ya ba da karfi wa madogaran Addinin Muslunci shi ne saboda Allah ya kare shi, ba a gurbata shi an yi tahrifin Littafinsa ba, kamar yadda aka samu cikin wadancan Addinai. Kuma Allah ya yi alkawarin kare wata Kungiya da za ta dawwama a kan wannan Addini, babu abin da zai girgiza su har sai Alkiyama ta tsaya.

✍️ Dr Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments