Mummunar Sakar Zuci

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ina da matsalar mummunar zuciya mai faɗa min munanan abubuwa a kan Ubangiji Tabaaraka Wa Ta’aala. Yaya zan yi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    Hadisi ya tabbata daga Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ya ce

    جَاءَ نَاسٌ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَسَأَلُوهُ: إِنَّا نَجِدُ فِي أَنْفُسِنَا مَا يَتَعَاظَمُ أَحَدُنَا أَنْ يَتَكَلَّمَ بِهِ، قَالَ: «وَقَدْ وَجَدْتُمُوهُ؟» قَالُوا: نَعَمْ، قَالَ: «ذَاكَ صَرِيحُ الْإِيمَانِ»

    Waɗansu mutane sun zo wurin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) suka tambaye shi: Muna samun wani abu a cikin zuciyarmu abin da furta shi ke yi wa ɗayanmu girma matuƙa. Ya ce: Har kun same shi? Suka ce: E! Ya ce: Wannan tataccen imani ne. (Sahih Muslim: 132).

    Ma’anar wannan, kamar yadda Al-Khattaabiy ya faɗa shi ne

    أَنَّ صَرِيحَ الْإِيمَانِ هُوَ الَّذِي يَمْنَعُكُمْ مِنْ قَبُولِ مَا يُلْقِيهِ الشَّيْطَانُ فِي أَنْفُسِكُمْ، وَالتَّصْدِيقِ بِهِ حَتَّى يَصِيرَ ذَلِكَ وَسْوَسَةً، لَا يَتَمَكَّنُ مِنْ قُلُوبِكُمْ، وَلَا تَطْمَئِنُّ إِلَيْهِ نُفُوسُكُمْ

    Tataccen imani shi yake hana ku karɓar abin da sheɗan yake jefawa a cikin zukatanku, shi ya hana ku gaskata abin, ya hana shi tabbata a cikin zukatanku, kuma ya kasa natsuwa a cikin rayukanku, har dai abin nasa ya koma waswasi kawai. (Ma’aalimus Sunan, kamar yadda Al-Arnaa’ut ya ambata a ta’aleeqinsa ga Sunan Abi-Daawud:  7/435. Irin wannan maganar ce a cikin Ikmaalul Mu’lim Bi Fawaa’id Muslim: 1/431).

    Shiyasa a wata riwayar ma har kabbara ya yi, ya ce

    "اللهُ أكبرُ، اللهُ أكبرُ" الحمدُ لله الذي ردَّ كيدَه إلى الوسوسَةِ"

    Godiya da yabo sun tabbata ga Allaah wanda ya mayar da makircin sheɗan ya koma waswasi. (Sahih Abi-Daawud: 5112).

    Don haka samun irin wannan ba matsala ce ba, musamman idan muka fahimci cewa yawancin masu imani suna samun irin wannan

    Abu-Daawud As-Sajistaaniy ya riwaito da isnadinsa sahihi har zuwa ga Abu-Zumayl cewa: Shi ya tambayi Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) a kan wani abu da yake ji a cikin zuciyarsa, wanda kuma ba ya iya furtawa da bakinsa, sai ya ce

    أَشَيْءٌ مِنْ شَكَّ؟ قَالَ : وَضَحِكَ ، قَالَ : مَا نَجَا مِنْ ذَلِكَ أَحَدٌ

    Shin ko wani abu ne na shakka? Sai kuma ya yi dariya ya ce: Ai babu wanda ya tsira da wannan abin.

    Sai kuma ya bayar da maganin matsalar, ya ce

    إِذَا وَجَدْتَ فِي نَفْسِكَ شَيْئاً فَقُلْ : {هُوَ الْأَوَّلُ وَالْآخِرُ وَالظَّاهِرُ وَالْبَاطِنُ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ}

    Idan ka ji wani abu na wannan sai ka ce: {Shi ne Allaah na-farko, kuma na-ƙarshe, kuma na-bayyane, kuma na-ɓoye, kuma shi Masani ne game da dukkan komai}. (Surah Al-Hadeed: 3). (Sahih Abi-Daawud: 5110).

    Wal Laahu A’lam.

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.