Nazarin Amfani Da Kalmomin Aro Na Larabci Da Na Ingilishi a Cikin Wakoki Makada Sa’idu Faru

    Citation: Lawal, S., Garba, A. & Abubakar, U.S. (2024). Nazarin Amfani Da Kalmomin Aro Na Larabci Da Na Ingilishi a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 243-249. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.031.

    Nazarin Amfani Da Kalmomin Aro Na Larabci Da Na Ingilishi a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru 

    Daga

    Sulaiman Lawal
    Zamfara State College of Education, Maru
    Email: Sulaimanlawalgus131gmai.com
    Phone no: 08168214203 

    Da

    Ashafa Garba
    Zamfara State College of Education, Maru
    Email: ashafagarbagusaumail.com
    Phone no: 07032137674 

    Da

    Usuman Sanusi Abubakar
    Federal College of Technical Bichi, Kano State
    Email: usmansanusi73gmail.com
    Phone no: 08036407638

    Tsakure

    Wannan takardar da aka gabaatar mai kanu ‘’Nazarin Amfani da Kalmomin Larabci da na Ingilishi a Cikin Wasu Wakokin Sa’idu Faru. Babbar manufar wannan takardar ita ce, fito da wuraren da Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da kalmomin aro na Larabci da Ingilishi a cikin wakokinsa wajen isar da saƙonsa ga jama’a masu sauraran. Waɗannan kalmomin da aka yi nazari a cikin ɗiyan wasu waƙoƙinsa su ne kalmomin Larabci da na Ingilishi tare da yin sharhi a kansu. Haka kuma, wannan takardar an yi amfani da wasu muhimman hanyoyi wajen tattara bayanai domin a samu nasara kamamala ta. Sannan kuma, an yi amfani da waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru guda biyar (5) waɗanda aka samu a cikin ayyukan Gusau, (1988) Diwanin Waƙoƙin Makaɗan Fada da Gusau, (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka inda aka tantance su aka yi amfani da wasu ɗiyan waƙoƙinsa wajen fito da dabarar amfani da kalmomin aro. Waɗannan waƙoƙin da aka yi amfani da su sun haɗa da: Waƙar ‘Sarki Musulmi Muhammadu mai Tura Haushi da Koma Shirin Yaƙi da Muzakarin Sarki Ɗan’audu da Farin Cikin Musulmin Duniya da kuma Gwabron Giwa na Shamaki Baba Uban Gandu. Daga ƙarshe wannan takardar ta gano cewa an yi amfani da kalmomin Larabci (26) da kalmomin Ingilishi (14) a cikin ɗiyan wasu waƙoƙi daban-daban da aka nazarta.            

     

    1.0 Gabatarwa

    Wannan takardar da aka gabatar akwai ma’anar waƙar baka daga bakin masana da taƙaitaccen tarihin makaɗi Sa’idu Faru da ma’anar kalmomin aro da sharhin kalmomin Larabci da na Ingilishi a cikin ɗiyan waƙoƙin da aka nazarta da kammalawa da manazarta da kuma ratayen kalmomin Larabci da Ingilishi da aka yi sharhi a kansu. Waƙar baka wani ɓangare ne na adabin baka (gargajiya). Kowace al’umma ta duniya tana da waƙar baka. Al’ummar Hausawa ma na ɗaya daga cikin al’ummar duniya waɗanda suke da waƙar baka. Akwai ilmantarwa da nishaɗantarwa da faɗakarwa da gargaɗi da wa’azantarwa a cikin waƙoƙin baka na Hausa. Haka kuma, a cikin waƙoƙin baka na Hausa makaɗa suna amfani da aron kalmomi daga wasu harsuna daban-daban domin su isar da saƙonninsu zuwa ga jama’a musamman masu sauraransu. Masana da manazarta sun yi rubuce-rubuce akan ma’anar waƙar baka. Kaɗan daga cikinsu akwai: Waƙar wani furuci ne wato lafazi ko saƙo cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko ƙa’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi. (Ɗangambo, 1982). Waƙa tana zuwa ne a sigar gunduoyin zantuka waɗanda ake kira baibaitoci ko ɗiyoyi kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman (Umar, 1980:3) Waƙa magana hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke da wani saƙo da ke ƙunshe cikin wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu (Yahaya: 1984: 2-3) Waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa, a rera cikin sautin murya da amsa-amo na kari da kiɗa, sau da yawa kuma da amshi (Gusau, 2011: 2) Waƙar baka ita ce wadda ake rerawa don jin daɗi, a ajiye ta a ka a kuma yaɗa ta a baka (Sa’id 1981:235)

    Ana samun baƙi ko kalmomin aro a cikin waƙar baka kuma kalmomi aro na ɗaya daga cikin abin da ke taka muhimmiyar rawa a cikin waƙoƙin baka na makaɗa Sa’idu Faru musamman wajen isar da saƙonsa cikin sauƙi.

    2.0 Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru   

    An haifi Makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru ta cikin ƙasar Maradun, ƙaramar Hukumar Talatar Mafara Jihar Zamfara a wajejen shekarar ta 1932. Ana kuma yi masa laƙabi da ‘Ɗan’umma’ wanda matar ƙanen ubansa ta sanya masa, saboda ba ya faɗin sunanta, sai dai yana kiran ta Umma, amma wannan laƙabi bai shahara a tsakanin mutane ba, balle ya danne sunansa na yanka wato Sa’idu. Sunan mahaifin Sa’idu Faru shi ne makaɗa Abubakar Ɗan Audu shi kuwa makaɗa Audu, Alu mai Kurya ya haife shi. Ashe ke nan Sa’idu Faru shi ne ɗan Abubakar Ɗan’audu da Alu mai Kurya. Dukkan waɗannan makaɗan an yi su ne a garin Faru, sai dai mahaifiyar Sa’idu mutumiyar Banga ce ta cikin ƙasar Ƙaura-Namoda, kuma a can ne aka haife ta. Sa’idu Faru ya yi gadon kiɗa ne wajen mahaifinsa. Kakansa na sama makaɗa Alu makaɗan Kurya ta kiɗin yaƙi ne wanda ake yi wa kirari ‘Kurya gangar Mutuwa’.

    Yawanci ƙuruciyar Sa’idu Faru ya yi ta a garin Banga ta Ƙaura-Namoda inda aka haifi uwarsa, amma kafin ya girma ƙwarai sai ya koma wurin tsohonsa makaɗa Abubakar a Faru. Makaɗa Sa’idu bai sami ilimin Muhammadiyya da yawa ba, sai dai an sa shi makarantar allo inda ya yi zurfi ga karatun Alƙur’ani mai tsarki. Haka kuma, ba a sa shi makarantar boko ba, don haka bai san komai ba game da sha’anin boko. Alahaƙiƙa tun yana yaro sha’anin kiɗa da waƙa ya ɗauke masa hankali. Makaɗa Sa’idu Faru ya koyi waƙa wurin mahaifinsa makaɗa Abubakar, waƙoƙinsa suka daɗa kyautatuwa ta hanyar fasaha da hikima tare da ƙwaƙwalwar da Allah ya ba shi. Tun Sa’idu Faru yana da shekaru goma aka fara zuwa yawon kiɗa da shi gari-gari. Bayan da ya cimma shekaru goma sha shida ya soma karɓi a wannan lokaci ne kuma aka haɗa su tare da ƙanensa Ma’azu wanda shi ne Ɗangaladima a halin yanzu. Baya ga tsohonsa Abubakar makaɗa Sa’idu bai koyi kiɗa ga kowane makaɗi ba, dukkan salailai iri-iri da yake sakawa a waƙoƙinsa tushensu mahaifinsa da baiwar da Allah ya ba shi ta gane fasalin waƙa. Da tsohon Sa’idu Faru ya rasu, sai ya ɗauki gabatar waƙa, ya sa himma da ƙwazo yana ta yi har zuwa rasuwarsa.

    Makaɗa Sa’idu Faru bai yi wa kowa waƙa sai sarki ko wanda ya jiɓinci jinin sarauta. Sa’idu Faru yana cewa; ‘Sai su sarakuna nike yi wa waƙa, saboda shi talaka idan ka sami kuɗi in ka yi mashi waƙa yana jin daɗi bare ma idan ka ce mashi ɗan wane jikan wane yana yiwuwa kakansa talaka ne. In ka ambaci kakansa bai ji daɗi ba, in ko ya ɓata maka rai sai dai ka yi haƙuri domin talaka ne. Makaɗa Sa’idu yana shirya waƙarsa a gida kafin ya fita zuwa ga wanda zai yi wa ita, Sannan zai dinga bitar ta kimanin kwana biyu domin ta zauna a ƙirjinsu da isa wurin wanda zai yi wa waƙar ya san wadda zai yi masa kai tsaye. Makaɗa Sa’idu Faru yana da matan aure guda uku (3) tare da ‘ya’ya ishirin da shida (26) maza da kuma mata a cikinsu goma sha ɗaya (11) sun rasu goma sha biyar (15) suna nan da kuma jikoki kimanin ashirin (20) (Gusau: 1987: 117-125).

    3.0 Ma’anar Kalmomi Aro

    Ɗaukar kalma daga wani harshe, a shigar da ita cikin jerin kalmomi wani harhe na daban (Garba, 1984: 43). Wannan wata fasaha ce da Ɗan’adam ke amfani da ita ta hanyar ɗauko gudar kalma ko gudajin kalmomi daga wani harshe a shigar cikin jerin kalmomin wani harshen a daban. Sai dai irin wannan aron ya saɓa da aron da ake mayarwa domin shi akan yi wa kalma kwaskwarima ta dace da tsarin ginin kalmomin harshen da ya yi aron. Aron kalmomi ya ƙunshi hanyoyin da masu magana da harshe suke bi su ari waɗansu kalmomi daga wasu harsuna. Kalmomin aro ko baƙin kalmomi sun ƙunshi kalmomin da Hausawa suka saƙa su cikin furuci ko rubutu a kalmomi da suke kalmomin harshen Larabci da na Turanci da waɗansu harsuna waɗanda Hausawa suke cuɗanya da su. Don haka, a sanadiyyar wannan zamantakewa ta haifar da are-aren kalmomi a tsakaninsu, musamman harshen Hausa wadda tafi fa’idantuwa da waɗannan harsunan kuma ta ribanta da kalmomin nasa da dama.

    3.1 Amfani da Kalmomi Aro a Cikin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    An sami kalmomin aro da dama a cikin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru cikin waɗanda aka nazarta sannan kuma, waɗannan kalmomin aro dukkansu kalmomi ne da makaɗin ya yi amfani da dabarar aro na kai-tsaye inda aka yi wa wasu kalmomin kwaskwarima domin su dace da harshen Hausa yayin da wasu kalmomin aka yi amfani da su kai-tsaye.

    3.2 Aro na Kai-tsaye

    Shi wannan nau’in na aron shi ne, wanda za a ɗauko kalma tare da ƙwayar ma’anarta a yi amfani da ita tamkar yadda take a harshen asali, sai dai wasu kalmomin akan yi masu kwaskwarima domin su dace da tsarin ginin harshen Hausa.

    3.3 Kalmomin Aro na Larabci a Cikin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru

    Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru cike suke da kalmomin aro na Larabci. Wannan kuma bai rasa nasaba da kasancewar al’ummar Hausawa sun jima suna hulɗa ta kasuwanci da Larabawa sannan kuma, daga baya Addinin Musulunci ya zo masu. Waɗannan dalilai sun taimaka wajen samun baƙin kalmomin aro na Larabci a cikin al’ummar Hausawa. Akwai kalmomin aro na Larabci da aka fito da su kuma aka nazarta da Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a cikin wasu daga ɗiyan waƙoƙinsa wajen isar da saƙonsa ga masu saurare. Kaɗan daga ciki akwai:

    Misali:

    Jagora: Na marafa ɗanbaba ai tura haushi,

    Y/Amshi Na sarkin Gabas duniya hori-wawa,

    Bai gadi sakwe ba mama na Baura,

    Toron giwa uban Bello Mado,

    Ɗan Hausa ba mai irin haƙuri nai.

    (waƙar Sarkin Musulmi MuhammaduTure Haushi ɗa na 1).

    Wannan ɗan waƙar an samu kalmomin aro guda uku waɗannda makaɗa Sa’idu Faru ya yi amafni da su wajen isar da saƙonsa ga masu sauraro. A cikin ɗan waƙar makaɗin ya yi amfani da w Kalmar aro daga harshen Larabci inda ya yi yabo ga sarkin gabas. Wato Kalmar ita ce duniya wadda take nufin wani sarari da Allah ya yi hallita sannan kuma samar da abubuwa daban-daban a ciki.

    Sai kuma: Faɗi gaskiya Bello kai Shehu ya ce,

    Jagora: Bari masu son duk su maishe ka yaro,

    Da kyauta da ilimi da neman dalili,

    Y/Amshi:  Da gode wa Allah da istingifari,                

    Da su Bello ɗan Shehu yat ma kowa,

    Ka kai kamab Bello ka gadi Moyi,

    Saur aka kai inda mai Hausa yak kai.

    (waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Ture Haushi ɗa na 3).

    Idan aka duba wannan ɗan waƙar da ya gabata za ga makaɗan ya yi amfani da kalmomin aro guda huxu inda ya nuna Shehu mutum ne mai gaskiya yayin da ya aro kalmomin Larabci ya yi amfani da su domin isar da saƙonsa ga masu sauraro. Kalma ta farko ita ce ilimi da yake nufi mutum ya tashi ya je ya neme ilimi domin ya kore jahilci a rayuwa. Akwai kalmar dalili wadda take nufin wani abu da zai sa mutum ya aikata wani abu. Sai kalmar Allah tana nufin Ubangiji ko kuma mahallici. Sai istingifari wanda yake wani nau’in ibada na neman gafarar Allah zunuban da aka aikata bisa kuskure ko kuma da gangan.

    Akwai kuma:

    Jagora: Muhamman dalilinka niz zo Talata,

    ‘Y/Amshi: Muhamman dalilinka niz zamni Hausa,

    Kwas san mu gidan ga na anka san mu,

    Kuma ba mu wuce nan ba nan munka dage,

    Ban zo gidan ɗanbita niy yi roƙo,

    Ko ya raba lafiya ba ruwana

    (waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Ture Haushi ɗa na 6)

     

    Wannan ɗan waƙar da ya gabata makaɗin ya yi amfani da kalmar aro guda ɗaya domin ya samu ya isar da saƙonsa cikin sauƙi. A nan makaɗin ya yi amfani wannan kalmar ne domin nuna dalilin da ya sa ya zo ranan Talata. Ita dai kalmar Talata tana ɗaya daga cikin jerin sunayen ranaku na mako da makaɗin ya yi amfani da ita wajen isar da saƙonsa.

    Sai kuma wannan:

    Jagora: Shi wane girman kai bai da wayo,

    ‘Y/Amshi: Wane girman shi kai bai da wayo,

    Ya toge daidai shi ne nan ban i na,

    Ya bar azumi da kono da sunna,

    Sai shisshirye benci matsata su zanna

    (waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu mai Ture Haushi ɗa na 8).      

    A cikin wannan ɗan waƙar Sa’idu Faru ya yi ƙoƙarin amfani da kalmomin aro na Larabci guda uku inda yake nuni da wanda yake wa ba ya aikata su wato kalmomin azumi da kono da kuma sunna. A nan kalmar azumi tana nufi wani nau’in ibada ne da al’ummar Musulmi suke yi ko dai azumin ya kasance na farilla ne (watan Ramadan) ko kuma na sunna da ake aiwatarwa a lokuta daban-daban domin neman lada wajen Allah (SWA). Sai kalmar sunna wadda take magana a kan koyi da abubuwan da Annabi Muhammadu (S.A.W) ya bayar da umurni a aikata musamman abin da ya shafi ibada. Hikimar da za gani a nan dukka waɗannan kalmomin da makaɗin ya aro daga Larabci suna magana ne a kan abin da ya shafi ibada.

    Sai kuma:

    Jagora: Tsaye da kyawo zamne da kyawo,

    ‘Y/Amshi: Macciɗo jikan Ma’azu makaye,

    Babban jerin duniya uban Alhaji Salihu.

    (waƙar Farin cikin Musulmin Duniya ɗa na 3)

    Akwai kalmar aro guda ɗaya da aka yi amfani da ita cikin wannan ɗan waƙar ta ‘Farin Cikin Musulmin Duniya’ wato kalmar alhaji wadda take nufin mutumin da ya je aikin hajji ƙasa mai tsarki wato Saudiyya ya sauke farali wanda yake sauke farali na ɗaya daga cikin abubuwa da Allah ya sharɗanta ga Musulmin da ya samu iko aƙala sau ɗaya a rayuwarsa. A nan kalmar da Sa’idu Faru ya aro ta Larabci ta shafi fannin ibada da ake kiran wanda ya yi aikin hajji.

    Akwai kuma:

    Jagora: Sa’idu malamin waƙa

    ‘Y/Amshi: Mai kwana lazumin na Mamman Balarabe

    (waƙar Farin cikin Musulmin Duniya ɗa na 4).

     

    An yi amfani da kalmomin aro guda biyu cikin wannan ɗan waƙar wajen isar da saƙo inda makaɗin ya kira kansa malamin kuma mai kwana yana lazumi. A nan makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da kalmar malamin wadda ma’anarta take nufin mutum masani mai koyar da wani fannin na ilimi. Sai kalma ta biyu da ya yi amfani da ita cikin ɗan waƙar wato, lazumin wadda ita kuma take nufin roƙon Allah a samu biyan buƙata. A nan makaɗin kalmomin da ya yi amfani da su, sun shafi ibadun da ake aiwatarwa cikin Addinin Musulunci.

    Akwai kuma:

    Jagora: Manya ma’aikatan gwamnati,

    Manyan ma’aikatan En/e

    Almajirinku na an nan,

    Don bisa garai ta Allah ya shirya muna abinci,

    Na roƙe inda hali,

    Don shirya muna kujera tamu mu tai hajji

    Na yi mahwalki nai sallah Makka ɗawahi,

    ‘Y/Amshi: Kuma na rungume turame a bagaruwa da tasbahohi

    An ce mani Alhaji nai kyaun fasalin kiɗi,

    Wanga mahwalki in Allah ya nufa,

    A shirye shi ya zan haka.

    (waƙar Farin cikin Musulmin Duniya ɗa na 17).

     

    Idan aka duba wannan ɗan waƙar makaɗa Faru ya yi amfani da kalmomin aro na Larabci guda takwas wajen isar da saƙonsa zuwa ga masu sauraro, inda ya yi amfani da waɗannan kalmomin ya roƙa abin da yake da buƙata.Waɗannan kalmomin sun ƙunshi: Almajirinku da hajji da sallah da Makka da ɗawahi da tasbahohi da fasali. Kalma ta farko ita ce ta almajirinku wadda take nufin mutumin da bar garinsu ko yankinsu ya je wani gari neman ilimi. Akwai kalmar hajji ziyartar ɗakin Allah domin yin ibadun da aka shimfiɗa. Sai. Sai sallah nau’i ne na ibada da Allah ya wajabta wa dukkan Musulmi wadda ake gabatarwa sau biyar a rana ko kuma salolin nafila da ake aiwatarwa ko kuma sallah da ake yi bukin ƙare Azumin Ramadana ko bukin sallah layya. Akwai kalmar Makka wadda take ƙasa ce daga daulolin ƙasashen Larabawa. A nan hikimar da za a ga kalmomi guda bakwai sun shafi ibada.

     

    Sai kuma wannan:                                                                                

    Jagora: Tanƙwahau na Alƙalin Alƙalai,

    ‘Y/Amshi: Bello uban Sarkin dogarai

    (waƙar Farin cikin Musulmin Duniya ɗa na 23).

     

    Akwai kalmar aro ta harshen Larabci a cikin wannan ɗan waƙar guda wato alƙalin da alƙalai. A nan kalmar alƙalin na matsayin mutum guda. Sai kuma alƙalai wadda take nufin alƙalai biyu ko fiye da haka. Wannan kalmar ta alƙali da makaɗi ya aro a harshen Larabci ta shafi fannin shari’a.

                       

    Sai kuma wannan:

    Jagora: Zaure mijin gida,

    ‘Y/Amshi: Ɗan Amadu koway yi gum da kai bai ci riba ba.

    (waƙar Koma Shirin Yaƙi ɗa na biyu)

     

    An samu kalmar aro a cikin wannan ɗan waƙar na “Koma Shirin Yaƙi” inda aka samu kalma guda wato riba inda makaɗin ya kira Sa’idu Faru ya nuna duk wanda ya yi karo da shi bai ci riba ba. Wannan kalmar ta riba tana nufin qarin kuxi da xan kasuwa ke samu bayan ya sayar da kaya sama da farashin da sayo. Hikimar da za a gani kalmar riba da aka yi amfani da ita ta shafi sha’anin kasuwanci. Akwai kuma:

    Jagora: Na gaishe ka da aikin ilimi,

    ‘Y/Amshi: Na gaishe ka da yaƙin mulki,

    Na kuma gaishe ka da kyauta.

    (waƙar Muzakkarin Sarki ɗan Audu ɗa na 5).                                       

    Wannan ɗan waƙar da ya gabata an samu kalmomin aro guda biyu inda makaɗin ya ambaci kalmomin mulki wadda take nufin tafiyar da shugabanci na jama’a. Sai kuma kalma ta biyu ita ce kyauta tana nufi ka ba wa wani, wani abu.

    Jagora: Don ku san,

    ‘Y/Amshi: Sai an ci Talata sannan Narba ka isowa.

    (waƙar Muzakarin Sarki Ɗan’audu ɗa na 10).

     

    Wannan ɗan waƙar an samu kalmar aro guda da aka yi amfani da su wajen isar da saƙo wato kalmar Narba wadda makaɗin ya ambata kuma kalmar tana nufin ɗaya daga cikin kwanaki da ake da su cikin mako.

    Akwai kuma:                                                                       

    Jagora: Su ungulu na son riƙon muƙami,

    ‘Y/Amshi: Amma bai bari ƙazanta.

    (waƙar Muzakarin Sarki Ɗan’audu ɗa na 12).

     

    A nan cikin wannan ɗan an samu kalmar aro ta Larabci guda guda ɗaya da aka yi amfani da ita wajen isar da saƙo ga jama’a wato kalmar muƙami. Kalmar muƙami tana nufin samun wani iko ko kuma dama tafiyar da wani abu.

    3.4 Kalmomin Aron na Ingilishi a Cikin Ɗiyan Wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru

    Turawa wasu al’ummomi ne da Hausawa suka daɗe suna mu’amala da su ta fuskar zamantakewa da sauran harkokin rayuwa. Don haka, al’ummar Hausawa sun daɗe suna amfani da kalmomin Turanci masu tarin yawa waɗanda suka aro suka shigar da su cikin kalmominsu kuma suke amfani da su musamman a ɓangararori da dama na rayuwa waɗanda suka haɗa da ɓangaren da ya shafi kimiyya da fasaha da siyasa da al’adu da dai sauransu. A cikin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru akwai wurare da ya yi amfani da hikimar kalmomin aro na Ingilishi domin ya isar da saƙonsa cikin sauƙi musamman zuwa ga jama’a masu sauraronsa. Ga kaɗan daga ɗiyan waƙoƙin da ya yi amfani da irin wannan hikimar kamar haka:

    Misali:

    Jagora: Baba ya ba mu bandura guda duk na lailai,

    ‘Y/ Amshi: Yaba mu bandura guda duk na yadi,

    Yaba mu fam goma ya ce mu ɗunke,

    Ga takalma na fam shidda-shidda,

    Hula kalabus guda goma yab ban,

    Kyauta irin taka jikan Ma’azu,

    Don ba a cewa mutum ba kama tai,

    Sai Larabawan Masar masu girma.

    (waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Ture Haushi ɗa na 4)

    Wannan ɗan waƙar Makaɗa Sa’idu Faru ya nuna irin giman kyautar da aka yi masu inda ya yi amfani da kalmomin aro na Ingilishi waɗanda suka haɗa da: Kalmar bandura da yadi da fom. A nan kalmar bandura da harshen Ingilishi tana nufin ƙunshin wani abu da yake cure wuri ɗaya. Akwai kalmar yadi wadda wani nau’i ne na sutara (tufafi) da ake amfani da shi domin suturta jiki. Sai kalmar fam wato wasu nau’in kuɗi ne da ake amfani da shi a ƙasar Ingila. Idan aka lura a wannan ɗan waƙar za ga cewa saƙon da makaɗin yake buƙatar isawa ya fito fili.

    Sai kuma:

    Jagora: Da biskit da minti da taba sigari,

    ‘Y/Amshi: Biskit da minti da taba sigari,

    Da lemu da soda da kwalbat sitawut,

    Bai ya da aza su ko sau guda ba,

    Yanzu wasicin da Usumanu ya ce,

    Ya ce abincinsu daɗi gare shi,

    Awanci abincinsu daɗi gare shi,

    Kowane ne yai ta ci na ruwana,

    Wancan na ci ta ci bai ci can ba.

    (waƙar Sarki Muhammadu mai Tura Haushi ɗa na 7).

    Idan aka duba wannan ɗan waƙar da ya gabata za a cewa Sa’idu Faru ya yi amfani da kalmomin aro na Ingilishi guda biyar waɗanda suka haɗa da Biskiti wanda yake wani nau’i ne na abin maƙwalashe ne. Sai kuma minti wani abu ne ake sha ko tsotsawa da baki mai zaƙi. Ita kuma kalmar taba sigari wani nau’in abu da ake zuƙa daga baki ne wanda yake fitar da hayaƙi a cikinsa. Sai kuma kalmar lemu wanda yake wani abu ne da ake amfani da shi.

    Akwai kuma:

    Jagora: Wanda bai san daɗin doki ba,

    Sai ya ce jaki hikima garai,

    Wanda bai san daɗin mota ba,

    Sai ya ce Honda hikima garai,

    ‘Y/ Amshi: To, ni maganar zaƙi akai,

    Kowa na kurɓa ruwan zuma,

    Ba shi koma tad da batun maɗi.

    (waƙar Farin cikin Musulmin Duniya ɗa na 13).

     

    Ita wannan waƙar ta Farin Cikin Musulmin Duniya an samu kalmomin aro guda biyu da Sa’idu Faru ya yi amfani da su inda ya ɗaga darajasu fiye da wasu inda ya fifita doki fiye da jaki. Haka kuma, ya kawo mota wadda take wani nau’in abun hawa ne da Turawa suka samar da ake amfani da ita wajen sufurin jama’a ko kuma sufurin kaya daga wannan wurin zuwa wancan. Sai kalmar ta biyu ita ce honda wadda ita ma nau’in mota ce da ake amfani da ita ta alfarma.

    Sai kuma:

    Jagora: Ɗanbaba marafan kiɗi,

    Ni daudu daukin kiɗi,

    Ga Shehu makaman kiɗi,

    Ga su nan kuma ga Sarkin fada mun yi layi,

    ‘Y/Amshi: Yaran Sa’idu Faru namu,

    A zo a sha ta zak kyawo,

    In don kwaramniya ba fasali ba ce.

    (waƙar Farin Cikin Sarkin Musulmi ɗa na 15)

     

    An samu kalmar aro a cikin wannan ɗan waƙar da ya gabata guda ɗaya wato kalmar layi. Kalmar layi a nan tana nufin wani wuri da aka tsara. Makaɗin ya yi amfani da wannan kalmar ta aro ce inda yake bayar da labarin yanayin da suke ciki, shi da ‘yan amshin waƙarsa. A nan hikimar da za a gani ita ce yadda makaɗi ya yi amfani da hikimarsa ya yi amfani da wannan kalmar.

    Akwai kuma:                                                           

    Jagora: Majalisar ɗunkin duniya,

    A majalisar ɗunkin duniya,

    Ta yi ododi ga manoma a riƙa aiki da gaskiya,

    A aje abinci a gaskiya,

    A tar da gero a tar da dawa,

    Sai gujjiya a sai a kaɗa,

    A aje gero,

    So nai mukai babban abu Njeriya,

    Ko Bature ka kab ba shi girgizawa,

    Ko da ya sha,                                                                        

    ‘Y/ Amshi: Sai ka ji ya watsa Ingilishi,

    Kai nai ya fashe da ya tamni tsakin dawo,

    A sha hura a yi wasa Ɗantumba,

    Shan hura ba lahani ba ne

    (Waƙar Farin Cikin Sarkin Musulmin Duniya ɗa na 17)

    Wannan ɗan waƙar da ya gabata Sa’idu Faru ya yi amfani da kalmomin aro guda uku lokacin da yake bayar da labari a kana bin da majalisar ɗunkin duniya ta yin a kawo nau’o’in abinci zuwa ga al’umma. wato kalmomin ododi da Bature da Ingilishi. A nan kalmar ododi tana nufin a samar da wani abu da aka bayar da umurni a aikata wani abu. Akwai kalmar Bature wadda take nufi wani nau’i mutum ne farar fata. Sai kuma kalmar ingilishi wanda yake nufin wani harshe ne ƙasashen Turawa suke magana da shi.

    4.0 Sakamakon Bincike                                           

    Akwai abubuwa da dama da wannan sakamakon bincike ya gano kamar haka:

    1.An gano cewa dukkan kalmomin Larabci da makaɗa Sa’idu Faru ya aro ya yi amfani da su ya yi aro ne na kai tsaye, inda ya yi amfani da wasu yadda suke wasu kuma ya yi masu kwaskwarima.

    Haka kuma, kalmomin Ingilishi da makaɗin ya aro ya yi amfani da su wasu ya kira su yadda suke wasu kuma an yi masu kwaskwarima.

    2. Sannan kuma, wannan takardar ta gano an yi amfani kalmomin Larabci har guda ashirin da shida (26) a cikin wasu ɗiyan waƙoƙi da aka nazarta, inda takardar ta gano an yi amfani da kalmomin da suka shafi sha’anin ibada fiye da sauran fannoni na rayuwa.

    Kazalika, ta gano cewa an yi amfani da kalmomin Ingilshi da makaɗi Sai’idu Faru ya yi amfani da su cikin ɗiyan waƙoƙinsa har guda goma sha huɗu (14) na fannoni daban-daban na rayuwa.

    4.0 Kammalawa

    A taƙaice dai, wannan takardar ta yi bayani a kan ma’anar waƙar baka da taƙaitaccen tarihin Makaɗa Sa’idu Faru da ma’anar kalmomin aro da kalmomi aro a cikin waƙoƙin Sa’idu Faru waɗanda suka ƙunshi kalmomin aro na Larabci da na Ingilishi da sharhi a kan kalmomin aro da aka kawo da ratayen kalmomin aron da aka nazarta da kuma manazarta.

    Manazarta

    Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Faɗe Waƙa (sabon tsari) Kaduna: Amana

    Garba, C. Y. (1984). Nazarin Hausa a Ƙananan Makarantun Sakandare.

    Lagos: Nelson Pitman.

    Gusau, S. M (1987). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kano: Century Research and

    Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (1988). Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu Musamman a Ƙasar Sakkwato. Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

    Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka. Kano: Century Research and Publshing Limited.

    Gusau, S. M. (2011). Adabin Baka a Sauƙaƙe. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2014). Waƙar Baka Bahaushiya (The Hausa Oral Song). Kano: Century Reseach and Publishing Limited.

    Sa’id, B. (1981) Bambancin Waƙar Baka da Rubutacciya A cikin Studies in Hausa Language Literature and Culture. The Second Hausa Internatinal Conference. Kano: Center for the Nigerian Languages Bayero University.

    Umar, M. B. (1980). Nazarin Waƙoƙin Hausa. Zariya: Hausa Publication Center.

     

    Rataye na Ɗaya

    Jerin kalmomin Larabci da na Ingilishi da aka yi Aiki a Kansu

    Kalmomin Larabci

    1.      Ilimi

    11. Muƙami

    2.      Alhaji

    12 Tasbahohi

    3.      Hajji

    13. Alƙali

    4.      Sarki

    14. Sunna

    5.      Dalili

    15. Malam

    6.      Allah

    16. Mulki

    7.      Duniya

    17. Sallah

    8.      Istingifari

    18. Makka

    9.      Talata

    19. Ɗawahi

    10.  Salati

    20. Narba

    11.  Azumi

     


    Kalmomin Ingilishi

    1.      Yadi

    9. Mota

    2.      Bandura

    10. Honda

    3.      Biskit

    11. Gwamnati

    4.      Minti

    12. odda

    5.      Sigari

    13. Bature

    6.      Lemu

    14. Ingilishi

    7.      Soda

     

    8.      Benci

     

     Get the full PDF here:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.