Salon Amfani da Karin Magana a Waka Bisa Fahimtar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya: Nazari Daga Wasu Rubutattun Wakokin Hausa

    Citation: Hassan, H. and Yankara, M.M. (2024). Salon Amfani da Karin Magana a Waƙa Bisa Fahimtar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya: Nazari Daga Wasu Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 24-32. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.004.

    Salon Amfani da Karin Magana a Waƙa Bisa Fahimtar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya: Nazari Daga Wasu Rubutattun Waƙoƙin Hausa

    Dr. Hussaini Hassan

    07039283077, hussainihassan387@gmail.com
    Department of Hausa, Federal College of Education, Pankshin

    DA

    Muhammad Musa Yankara

    08062367496, mymuhammad@fudutsinma.edu.ng
    Department of Hausa, Federal University, Dutsin-Ma

    Tsakure: Salon amfani da karin magana a waƙoƙin Hausa na baka, ko rubutattu, wani tsalli ne daga cikin salailan da Yahya, (2001 da 2016), ya bayyana, ya kuma tsattsefe shi tare da zaratan misalai. A wannan takarda an dubi wannan salo na amfani da karin magana, kamar yadda ya kawo shi, kana aka yi nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa, sannan aka ɗora nazarin bisa wannan fahimta ta Shehin Malamin. A fahimtar masanin, ya ce marubuta waƙoƙin Hausa suna amfani da karin magana ta hanyoyi guda uku da ya haɗa da faɗaɗa karin magana, da gutsure karin magana da kuma ƙirƙirar karin magana. Har ila yau, sai ya nuna cewa dukkan karin maganar da ake amfani da ita a waƙa ana yi ne ko dai don yin ishara, ko ƙarin bayani ko nuna ƙwarewa a harshen, ko kuma adana karin maganar. An zaƙulo misalai daga waƙoƙinHausa da suke nuni ga faɗa ta wannan masani, kuma Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, ta hanyar amfani da dabarar bincike ta bibiyar rubutattun bayanai, da kuma sauraren waƙoƙin da aka nazarta. A ƙarshen nazarin, wannan takarda ta ƙara tabbatar da wannan fahimta ta Shehin malamin na yadda marubuta waƙoƙin Hausa suke amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsu, tare da sun sani ko ba su sani ba.

    Fitilun Kalmomi: Salo; Karin Magana; Abdullahi Bayero Yahya; Rubutattun Waƙoƙin

    Gabatarwa

    Ɗangambo, (1984) da Zarruƙ, da wasu (1987) da Yahaya da wasu (1992) da Gusau, (2003) da Mukhtar, (2005) da Sarɓi, (2007) da ‘Yar‘aduwa, (2010) Yahya, (2013, 2016) da Auta, (2017) da sauransu da yawa sun bayyana waƙa da magana ko lafazi wanda ake yi cikin tsarin da ya saɓa wa maganar yau da kullum.

    Waƙa a duniyar Bahaushe kamar gishiri ne cikin miya, domin, rukuni ne kuma ginshiƙi ne babba ga harkokin zamantakewarsu. Hanya ce ta isar da manufofi da saƙonni ga jama'a, musamman kan abin da ya shafi harkar ilimi ko faɗakarwa kan sha’anin zamantakewa ko siyasa ko tarbiyya ko lamarin addini da makamantansu. A kowane harshe na duniya, waƙa ita ce kan gaba wajen bunƙasa da ɗaukakar adabin wannan harshe, domin ita ke nashe dukkan sassa na rayuwar al’ummar da ke magana da harshen. Waƙa tana da tasirin gaske cikin jinin mutane. Don haka ne wasu lokuta mawaƙan Hausa suke amfani da ita wajen cim ma burin duk wani al’amari da suka tunkara.

    Masana da manazarta sun yi rubuce-rubuce masu yawa kan abin da ya shafi salo a waƙoƙin Hausa, na baka da kuma rubutattu. Mafi yawan rubuce-rubucen da aka yi, ba a cika ba salon amfani da karin magana kulawar da ta da ce ba, kamar yadda Farfesa Abdullahi Bayero Yahya ya tsettsefe cikin littafinsa na Salo Asirin Waƙa (2001, 2016).

    Salon amfani da karin magana a waƙa, fage ne da mawaƙa ke aiki da basira wajen yi wa waƙa kwalliya da sanya waƙa ta yi armashi da daɗin saurare a kunne. Duk da irin wannan matsayi da tagomashi na salon amfani da karin magana, sai ga shi mafi yawan manazarta ba su faye ba fagen kulawa a nazarce – nazarcensuna salo a rubutattun waƙoƙi ko na baka ba. Wasu masanan ma irin su Gusau, (2003), da Bunza, (2009), da sauransu da dama ko kawo wannan salo ba su yi ba, balle a ga inda suka sanya shi. Wannan ya ja hankali ga yin rubutu a kan wannan salo domin ƙara fito da shi da jan hankalin masu nazari kan su riƙa kula da shi saboda muhimmancinsa, musamman ma a yau da kusan mawaƙa na wannan ƙarni suka fi amfani da kare-karen magana sama da kowannen irin salo a waƙoƙinsu.

    Salo

    Ma’anar salo kamar yadda masana suka bayyana shi ne “dabara ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya bayyana.

    Salo a nazarin waƙa kuwa yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda mawaƙi ya bi domin isar da saƙon da yake son ya isar. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatu (Yahya 2016:29).

    Salo yana nufin hanyoyi ko dabarun da marubuci ya yi amfani da su wajen isar da wannan saƙo nasa. Ya kuma ƙara da cewa za a iya fassara salo ta waɗannan siffofi da suka haɗa da: salo wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci, salo ƙari ne na daraja ko armashi a cikin rubutu ko furuci, salo ya shafi kaucewa daidaitacciyar ƙa’ida, salo harshen wani mutum ne, wato kowane mutum da irin yadda yake tunani kuma tunanin mutane biyu babu ta yadda za a yi ya zama iri guda (Ɗangambo, 1982:1, 2007:37).

    Salo wata dabara ce da za a iya yi wa harshe ado da ita kuma hanya ce ta sarrafa harshe a jujjuya shi ta yadda za a iya taƙaita manufa ko a sakaya ma’ana ko kuma kaifafa tunani (Gusau 2003:54).

    Ta duban waɗannan ma’anoni da aka kawo, ana iya cewa salo dabara ce ta isar da saƙo ta hanyar amfani da kwalliya da sarrafa harshe domin ganin an isar da saƙon cikin armashi da ban sha’awa.

    Karin Magana

    Wasu daga cikin masanan da suka tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar karin magana sun haɗa da: Finnegan (1970) a inda ta ce:

    Karin magana jerin kalmomi ne mai dubun hikima da zalaƙa wanda ke zuwa a gajarce, tare da ma’ana mai gamsarwa idan aka tsaya aka yi sharhi.

    Tudun wada (1982) yana ganin ba wani abu ne karin magana ba illa, magana ce wadda ake lanƙwasa ta, ta yi daɗin ji a kunne ta kuma yi ma’ana.

    Shi kuwa Bichi (1997) ya nuna cewa:

    Karin magana magana ce da take ƙunshe da hikima a cikinta, kuma tana bayyana hoton rayuwa da tunanin al’ummar da ke amfani da ita.

    Gwammaja (2010) shi ma ya bayyana ma’anar karin magana da cewa:

    Salo ne na yi wa mutum nasiha a kan wani abu da ya yi marar kyau, domin kada a fito ɓaro – ɓaro a sanar da shi halayensa musamman idan akwai kunya a tsakaninsu.

    Bugaje (2014) kuma sai ta bayyana cewa:

    Karin magana, magana ce mai tsawo wadda aka dunƙule ta, ta zama gajera cikin hikima, da zalaƙa kuma ta ƙunshi ma’ana mai yawa in za a tsaya a warware ta.

    A taƙaice za a iya cewa karin magana tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaƙa tare da bayar da ma’ana gamsasshiya mai faɗi, mai yalwa, musamman in aka tsaya aka yi bayani daki-daki. Wato karin magana taƙaitacciyar magana ce `yar ƙil wadda ta ƙunshi hikima da zantukan ma’ana.

    Farfesa Abdullahi Bayero Yahya

    Farfesa Abdullahi Bayero Yahya wanda mafi yawan abokai da ɗalibansa suka fi sani da Fafesa A.B. Yahya haifaffen garin Sakkwato ne a unguwar Giɗaɗawa. An haifi Farfesa a shekarar 1953. Kamar yadda yake a al’adar ƙasar Hausa an tura shi makarantar allo yana da shekara uku zuwa huɗu, a ƙarƙashin malaminsu Malam Haliru. Lokacin da ya cika shekara bakwai sai aka sanya shi a makarantar Firamare ta Waziri Ward Primary School, wadda daga baya aka sauya mata suna zuwa Waziri Model Primary School, a inda ya yi shekara shida saɓanin bakwai da ake yi a Firamare a wancan lokacin. Hakan ya faru ne a dalilin ciyar da shi gaba da aka yi da ƙarin aji guda, wanda galibi akan yi wa yara masu hazaƙa ko girma. A shekara 1967 ne ya samu shiga makarantar Sakandirn gwamnnati da ke Birnin Kebbi, a inda ya kammala a shekarar 1971. Da kammala makarantar sakandire sai ya fara aikin koyarwa a farkon shekarar 1972, a inda ya fara aikin koyarwar a makarantar Firamare da ke Kware, duk da cewa abokansa sun fi son da su haɗu su nema gurbin karatu na fagen share shiga Jami’a a Bayero, wadda a lokacin ake kira da Abdullahi Kwalejin Bayero, amma shi kuma ya fi sha’awar shiga Babbar makarantar horon malamai Adɓance Teachers College Sokoto, domin samun takardar Shaidar aikin Malanta. A cikin shekarar ne kuwa ta 1972 a watan Oktoba ya samu gurbin karatu a Kwalejin Ilimi Ta Shehu Shagari da ke nan Sakkwato, a inda ya kammala a shekarar 1975. Abdullahi ya yi gwajin koyarwa da ake tura ɗalibai masu neman ƙwarewa a fannin koyarwa a a Makarantar horon Malamai ta Gusau da kuma ta Bida a shekarat 1974 da 1975.

    Bayan kammala karatun da ya yi na Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari sai ya fara aiki inda aka tura shi Sakandirin Gwamnati ta garin Anka, inda ya zauna har zuwa shekarar 1978, a inda ya samu gurbin karatu a jami’ar Bayero Kano. Farfesa ya kammala karatun digirinsa na farko a fannin Hausa da Ilimin addinin Musulunci, a shekarar 1981, sannan ya yi aikin yi wa ƙasa hidima a shekarar 1982, wanda bayan ya kammala ya sake samun gurbin karatu a Jami’ar ta Bayero domin karatun digiri na biyu a fannin Hausa. Farfesa ya fara aiki a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo a shekarar 1983. Bai jima da soma aiki a jami’a ba ya soma karatun digiri na uku. Wanda ya kasance cikin mutum uku na farko da aka fara yaye wa a matakin digiri na uku a wannan sashe na Hausa, a shekarar 1987.

    Tafiya ta yi tafiya, Farfesa Yahya tun daga matakin Assistant Lecturer har ya kai Farfesa a shekarar 2003, yau shekara ashirin ke nan. Shehin malamin ya riƙe muƙamai da dama tun a ciki da wajen ƙasar nan. Daga cikin muƙaman har da shugaban Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da Sakkwato. Farfesa ya ba da gudummuwa mai tarin yawa, ya yaye ɗalibai tun daga masu digiri na uku, wanda yanzu haka daga ɗalibansa akwai masu matakin farfesa da ma gwamnoni da ‘yan majalisu na tarayya da sauran manyan ma’aikatan gwamnati a mataki daban-daban. A fannin rubuce-rubuce ya rubuta littattafai da har zuwa yau ana amfani da su a duniyar ilimi, ban da tarin maƙalu masu dama, a shahararrun mujallu na ƙasa (Department of Nigerian Language, UDUS 2023).

    Salon Amfani da Karin Magana a Waƙa

    Shehin Malami Farfesa Abdullahi Yahya ya bayyana cewa daga cikin salon da mawaƙa suke amfani da shi a waƙoƙinsu har da amfani da karin magana. Ya nuna salo a matsayin wata dabara wadda mawaƙa suke sarrafawa don isar da saƙonsu ga mai karatu ko sauraren waƙarsu ba tare da ƙosawa ko gajiyawa ba. Akwai hanyoyi guda uku waɗanda ya ce da a kan su ne mawaƙa suke ɗora karin magana a cikin waƙarsu.Ga waɗannan hanyoyi guda uku kamar yadda masanin ya bayyana.

    Faɗaɗa Karin Magana

    Kalmar faɗaɗa tana nufin ƙara wa abu faɗi (CNHN, 2006: 129). Mawaƙa suna amfani da karin magana a waƙa domin su faɗaɗa wannan karin magana, su kambama ta domin ya zama sun ƙara fito da saƙon sarari yadda za a fahimta. Sai dai wani abin luara a game da wannan salo shi ne, da yake idan Bahaushe ya tashi faɗaɗa abu yakan yabe shi ne ya kururuta shi ya kuma kambama shi ya nuna ya fi kowanne, wannan ya sa maganar takan zama tamkar kirari, amma idan aka ɗora zancen bias faifan nazari, sai a ga karin magana ne, illa dai kawai an jirkita ta sannan aka sarrafa ta wata sigar daban. Dubi misalin wannan baiti da Shehin Malamin ya bayar a littafinsa:

    Ana iya shafa kan mussa,

    Na jibda ba ka farawa.

    Ana iya kama ɗan buku,

    Mijirya ba ka damƙowa.

     

    Fura aka kwankwaɗa amma,

    Kunu kam sai da kurɓawa.

    Mutum in ya biɗo canji,

    Abinai an na renawa.

    (Alƙali Haliru Wurno: Ko ba ka Raƙumi ka San Cau)

    Baitukan cike suke da karuruwan magana waɗanda suka yi kama da kirari, amma ba kirari ba ne. Sannan dubi ƙarin wannan misalin wanda ya yi kamada kirari, amma dai karin maganar tana nan a baitin:

    Giwa du’abin da tah haifa,

    Ai an shedi bai zamma taffa,

    Domin ya wuce shiga kwalfa.

    (Alhaji Garba Gwandu: Waƙar Makaman Gwandu Balarabe)

    Idan aka duba waɗannan misalai da ya Yahya, (2016:14) ya kawo sai a ce wannan ai kirari ne a saboda siffofin kirari da ya bayyana cikin baitin, amma abin da ya fito fili na karin magana shi ne ‘Ɗan giwa, giwa ne’ wanda hakan ya yi kama da kirari. Wato dai karin maganar ita ce ta faɗaɗa saƙon da ake son a isar. Wannan kuwa ba wani abin mamaki ba ne, domin a cewar Zarruk da Alhassan, (1982:3-10), akan iya canza karin magana a mayar da shi kirari, saboda lanƙaya shi da mai yin kirarin yake yi ga kan sa. Misali:

    4. Yaro da goriba sai lasa,

    Ba gurgurar ta ko gutsura ba.

    (Rabi’u Nguru: Faɗi Sosai)

    A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da karin maganar nan da Hausawa suke cewa “Yaro da goruba sai lasa”. Bai bar karin maganar haka ba, sai ya faɗaɗa ta domin ya ga ya fito da asalin ma’anar karin maganar. Faɗaɗawar a nan ita ce inda ya yi ƙoƙarin nuna cewa goriba gurgura akeyi, ko a gutsura idan an gurgura, amma a wajen yaro marar haƙoƙi bai iya gurgurar balle kuma ya gutsura. Wato dai mawaƙin ya yi amfani da wannan karin magana wajen gwarzanta gwaninsa jagoran gwagwarmayarsu da kuma kambama shi, ta hanyar kamanta yadda yaro marar haƙoƙi ba ya iya yin komai da goruba, in ba ya lasa ya bari ba, haka maƙiya abokan adawa ba za su iya yin komai da shi ba, balle su ci galaba a kan sa.

    Dubi yadda kuma aka kawo wannan salo a baitin da ke cewa:

    Shiru an faɗa ai ba kwa tsoro ba ne,

    Kamar ja wurin rago misalinmu ne,

    Ku duba kunama ga ta ‘yar ƙanƙane,

    Idan har ta harbi amale sai ka ga yai makuwa.

    (Mustapha Umar Baba: Fito – na – Fito)

    A wannan baitin kuma mawaƙin ya sarrafa karin maganar nanne da Hausawa suke cewa “Shiru-shiru ba tsoro ba ne, gudun magana ne” da kuma “Ja da baya ga rago ba tsoro ba ne, shirin faɗa ne”. Mawaƙin ya yi amfani da karin maganar ne wajen kambama masu gwagwarmaya da nuna cewa a bar ganin suna ƙyale duk wani abin da ake yi musu na musgunawa da zalunci, ba fa wai tsoro ba ne, ba su da tsoro. Wataƙila, idan da a magana ce ta yau da kullum ake son faɗa wa wani ana iya ce mashi ka bar ganin ana ƙyale ka, idan kayi zalunci, akwai abin da muke dubawa, amma maimakon haka sai ya ce “ja da baya ga rago ba tsoro ba ne, shirin faɗa ne” wannan zai sa abokin adawa ya kaɗu ya shiga tunanin ko wane irin mataki za su ɗauka nan gaba. Har ma a a wani ɗango na baitin yake kambama maganar da ba da misali da cewa ka dubi dai duk girma na raƙumi amma kunama sai ta sabauta shi, to su ma fa a bar ganin su ‘yan ƙalilan yara, idan suka taso to sai sun sa abokin adawa ɗimuwa.

    Har wayau dangane da amfani da salon faɗaɗa karin maganam akwai:

    Gobarar dare ta watan bakwai ga rani kan kore,

    Ta kama ta tsaya gidan su mai wa Amo takkai.

    (Audu Makaho: Waƙar Mai wa Amo Takkai)

    Nufin mawaƙin yin baƙar addu’a ga abokin adawarsa kamar yadda baitin ya nuna. A maimakon haka, sai ya yi amfani da karin magana nan na Hausawa da suke cewa “Watan bakwai, maƙarar rani”. Ya yi hakan ne don ya kambama addu’ar tasa inda ya roƙi Allah kan gobara ta taho ta kama gidan abokin adawarsa, kuma ya nuna yadda yake son gobarar ta kasance mai muni; ta zo cikin dare kuma a watan bakwai. Shi kuwa watan bakwai tsakiyar rani ne, ga ba isasshen ruwa a gulabe da tafkuna da za a iya ɗiba a kai gudummuwa domin a kashe, ga shi kuma lokacin rani lokaci ne na iskar bazara, da ke kaɗawa. Ita kuwa gobara da iska ba a shiri, ana kashewa ne, iska na ƙara yaɗa ta da rura ta.

    Gutsure Karin Magana

    Mawaƙasukan yi amfani da karin magana a waƙa ta hanyar gutsure shi. Za a samu cewa mawaƙi yakan faɗi muhimman kalmomin da karin maganar ya ƙunsa ya bar sauran domin mai saurare ko karatu ya cike su. Waɗannan kalmomi da mawaƙi yake gutsurewa kan iya zama kalma ɗaya ko sama da haka, gwargwadon yadda ba zai shige wa mai sauraro ko karatu duhu ba. Rubutattun waƙoƙin Hausa sukan zo da wani abu makamancin haka, kamar yadda aka samuwani mawaƙi yana cewa:

       9.   Idan ko kun ƙi ji,

    To wallahi kun shiga ukku.

    (Abdullahi Lushi: Laƙad Ja’al haƙƙu)

    Wannan karin maganar ba ta cika ba, mawaƙin ya katse ta, bai ƙarasa ta ba, da niyyar mai saurare ya ƙarasa. Karin maganar nan ce da Hausawa suke cewa “In an ƙi ji, ba a ƙi gani ba”. A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da karin maganar ne domin jan kunnen ‘yan sanda waɗanda a waƙar ya ce su ne ake tura wa suna dukansu idan suna tarurrukansu ko wa’azozinsu na addini. Wato yana gargaɗinsu da cewa ranar da za su fara rama dukkan abin da suke yi masu, to su ma sun shiga uku, don kuwa ba za su sassauta masu ba.

    Ƙirƙiro Karin Magana

    Mawaƙa suna amfani da ƙirƙirarrun karin magana a waƙoƙinsu domin nuna ƙwarewa da iya sarrafa harshe gami da naƙaltarsa. Irin waɗannan karin magana sun samu ne daga baya sakamakon wayewa ta cuɗanya da wasu al’ummu. Mawaƙan sukan ƙirƙire su ne domin su dace da manufar waƙar ko kuma baitin waƙa. Ga wasu misalai kamar haka:

     

     

    43. Allah shi ne yai badame sannan yai bahago,

    Ba ka tanƙwaruwa kwamandan yaƙi gamji go,

    Ga jirgin tsira yana ta sanarwa I will go,

    In ba san banza ba wane ne zai hau jirgin salula.

    51 Dubi halittar doki Allah ne yai ba wani ba,

    Dubi irin sukuwarsa bai sa mai shak – zoba ba,

    Duba yadda yake gudu kuma ba da karan-shaf ba,

    Ba sitiyari babu hon motar ƙudurar Allah ta’ala.

    (Mustapha Umar Baba: Waƙar Tauhidi)

    Abin lura a waɗannan baituka shi ne, mawaƙin ya yi amfani da wasu karin magana guda biyu da a iya cewa ƙirƙirarru ne, kuma domin su dace da saƙon da yake so ya fitar cikin baitocin. A baiti na43, mawaƙin ya yi amfani da karin maganar da ya kira ‘son banza mai sa a hau jirgin salula’. Ma’anar abin da mawaƙin ke nufi da jirgin salula ya fito a ɗango na uku, wanda ke nufin shi jirgin salula kishiya ne na jirgin tsira. Wannan kuwa ya yi canjaras da hikimar Hausawa da suke cewa motar ƙwaɗayi ba ta da masauki sai tashar walaƙanci, shi kuwa kwaɗayi da son banza duk tushensu ɗaya ne, Ɗanjuma ne da Ɗanjummai.

    Haka abin ya kasance abaiti na 51 inda ya yi amfani da ƙirƙirarriyar karin magana domin ta yi daidai da manufar waƙarsa, wato inda ya ce “Ba sitiyari babu hon motar ƙudurar Allah ta’ala”. A zahiri wannan magana ce a dunƙule, wanda in an fassara za a samu faffaɗar ma’ana. Mawaƙin ya yi amfani da wannan magana wajen nuna ƙudura ta ubangiji, yadda ya halicci doki ake amfani da shi tamkar yadda ake amfani da mota abin hawa. Sai ma ya nuna shi ya fi ma mota, domin shi ba sitiyari ba karan – shaf da sauran abubuwa da in suka lalace mota za ta tsaya.

    A gaba an samu baitin da ke ɗauke da wannan salo kamar haka:

    7. Kasuwa da gida gun kwanciya duk kuna jin tsoro,

    In ka hau mota tsautsayinka kake sauraro,

    To barejirgin sama makarar sama ce jirgin Nijeriya.

                (Nura Shahidi: Waƙar Talakan Nijeriya)

    Mawaƙin ya yi amfani da zance na hikima a dunƙule da take ɗauke da wata ɓoyayyiyar ma’ana, wanda shi ne abin da ake nufi da karin magana. Wannan magana da za a iya cewa ƙirƙira ya yi, ita ce inda ya nuna jirgin sama ba komai ba ne ga talakawan Nijeriya face akwatin gawar su, wato“makarar sama ce jirgin Nijeriya”. Mawaƙin yana nuna irin taɓarɓarewar tsaro a ƙasar Nijeriya, wanda yawan haɗarin da jirage suke yi a saboda rashin gyara ko nagarta tamkar mutum ya shiga makararsa ta mutuwa ce. Wato ke nan idan jirgin sama ya yi hatsari akan ce wannan jirgin sama ne kuwa ko dai makarar sama.

    Dalilan Amfani da Karin Magana

    Ta wannan ɓangare kuwa, Shehin Malamin ya bayyana cewa ana amfani da karin magana a waƙa a saboda wasu dalilai da suka haɗa da yin ishara da ƙarin bayani da nuna ƙwarewa ga harshe da kuma adana karin magana. Da yawan marubuta waƙoƙi suna amfani da karin magana saboda waɗannan dalilai da ya bayyana, kamar yadda aka tsinakayi misalai daga waƙoƙi.

    Yin Ishara

    An bayyana ma’anar Ishara da cewa “An Illustration; indication; adɓice; fore-warning” (Bargery, 2016: 480). Wato daidai ne ace tana nufin misali, ko nuni ko kuma shawara mai kyau ko hani. An kuma ƙara bayyana ma’anar kalmar ishara da cewa tana nufin nuni, ko sanarwa (CNHN, 2006:208). Wato abin nufi shi ne nuni zuwa ga wani abu, la’alla abin da ake gani ne kurum ko ake iya taɓawa, ko nuni ga wata magana ko zuwa ga gaskiya. Misali:

    69. Burazas ku sa ƙaimi haba ‘yan uwa,

    Haƙa ta yi nisa tun da ta kai ruwa,

    Haƙiƙa akwai nasara da ba makawa,

    Ku dage ku cije babu shakkar uban kowa.

    (Mustapha Umar Baba: Waƙar Fito-na-fito)

    A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da karin maganar da ke cewa “haƙa ta cim ma ruwa” wajen yin ishara ga abokan gwagwarmayarsu a kan su ƙara tashi tsaye su ƙara ƙoƙari kuma su zage damtse domin kuwa burinsu ya soma cika, nasara za ta samu a wannan fafutika da suke yi. Wato dai kai ka ce wani albishir ne mawaƙin yake yi wa ‘yan gwagwarmayarsu.

    Sannan kuma akwai:

    11. Ai ƙofar Allah da yawa take ta ma fi ƙofar cali,

    Don mun riƙe Allah ake bugunmu ana ta cin zali,

    Ya ‘yan uwa kui haƙuri Allah shi ne fa alƙali,

    In mun tsaya gaban kotun Allah ma gane mai raki.

    (Mustapha Umar Baba: Maganin Mayu)

    Karin maganar Hausawa da suke cewa “ƙofar Allah ta fi ƙofar cali yawa” ita ce ta zama ƙumshiyar wannan baiti. Shigowarta cikin baiti shi ya nuna ishara ce mawaƙin yake kan cewa duk wata musgunawa da azzalumai suke yi musu saboda sun ce Allah za su bi, to mabiya su yi haƙuri akwai ranar sakayya. Ka da su ɗauka kamar wannan abu da ake yi musu ya wuce a banza, a’a yana musu ishara da cewa akwai ranar da azzaluman za su koka, ranar da za su tsaya a kotun Allah wanda ba a afil.

    Ga yadda misalin ya sake bayyana a gaba:

    27.  In da rabon a sha dukabari ba ta maganin komai,

    Ɗan tsako ya sami abinci sai ya guje wa dangi nai,

    Sai ran da shirwa ta yi mamaya ya ga za ta dai cim mai,

    Zai zo gurin uwarsa yana ki rufe ni na tuba na biki.

    (Mustapha Umar Baba: Maganin Mayu)

    Nan kuma mawaƙin ya yi amfani da kare-karen magana guda biyu da nufin yin ishara ga waɗanda suka fita daga cikin gwagwarmayarsu suka musu tawaye. Su ne mutanen da suke ce musu ‘yan tawayiya. Kare-karen maganar su ne “mai rabon shan duka ba ya jin bari sai ya sha”. Sai kuma“Ɗan tsako samu ka ƙi dangi”.Wato dai mawaƙin yana sanar da abokan gwagwarmayarsu cewa ka da su damu waɗannan da suka yi tawaye, rana tana zuwa da za su yi nadama, wataƙila ma ranar da nadamar ba za ta yi amfani ba. Don kuwa Hausawa suna cewa wanda bai ji bari ba to zai ji hoho.

    Ƙarin Bayani

    Ana amfani da karin magana a cikin baitocin waƙa domin ƙarin bayani ga babbar manufar baiti ko baitocin da ya fito. Karin maganar kan iya fitowa kamin ko bayn ko kuma cikin baitocin da ya fito. Marubuta waƙoƙin gwagwarmaya suna amfani da irin wannan salo a inda sukan yi amfani da karin magana domin ƙarin bayani a kan saƙon da yake son ya isar. Duba wannan misalin:

    3.  Dalilin tsara ƙasidar yanzu asirin zan yaye,

    Kwanan can mun kai ziyara wani baƙin ƙauye,

    Sai na ji suna faɗin su ma sun zam ‘yan tawaye,

    Kai nasu ya waye sun daina biyar ƙatti sun amsa saƙo.

    Da jin haka ke da wuya da ɗai a kujera na kimtse,

    Sai na yi farat nai firgigi har na rantse,

    Ina faɗa ko yau kasuwa ta zamto ta watse,

    Shi dai ɗan koli da ribar nan da yac ci yake ta taƙo.

    (Abdullahi Lushi: Ya sharafuddini Haƙiƙa Mun Shaida ka ida saƙo)

    Duba da abin da baitin ya ƙumsa, mawaƙin ya yi amfani da karin maganar nan na Hausawa da suke cewa “ko yau kasuwa ta watse ɗankoli ya ci riba”. Mawaƙin ya yi amfani da karin maganar ne wajen fito da bayani na baitin da ya gabaci wannan, a inda ya nuna cewa ya ji daɗi ya yi murna ya kuma yi farin ciki yadda ya ga cewa bukatarsu na kiran al’umma kan su yi wa gwamnatin da ba ta Allah ba tawaye, to ya yi nasara, haƙa ta cimma ruwa, tun da ga shi har a cikin ƙauyen ƙayau, an samu wasu sun fahimci abinda suke kira a kan sa. Wato dai wannan karin magana mawaƙin ya yi amfani da ita wajen bayyana abin da baiti na sama ya ƙunsa.

    Haka kuma a gaba an samu cewa:

    25.  Maƙi gani sai ka kau da idonka don kuwaga shi nan,

    Ya fito ga shi nan kuma ras har kun ji yai magana,

    Ina su kulɓa ina su kurege? ‘Yan dakon fitina?

    Marmaza ku naɗe tabarma don ko ga mai gurin ya dawo.

    26.  Malaman fada maƙiya to yaya ranku yake,

    Kun yi sharrin kun ɓatancin duk a banza yake,

    Kun ta kushe malam ga jama’a ta son sa suke,

    Ku ƙara yin himma don sharrin naku ma jama’a ya kirawo.

     

    27. Kun rubuta takardu kar a sake shi kun yi kira,

    Ahaf! Ulama’us su’i ai fa kun makara,

    Duk ku gane idan Allah ya nufaci ɗan zakara ,

    Zai yi cara sai ya yi ko da muzuru shaho suna kai kawo.

    (Tabarmar Kunya: Mustapha Umar Baba)

    Waɗannan baitoci cikin su mawaƙin ya yi amfani da karin magana wajen ƙarin bayani game da manufar da yake son ya isar. Karin maganar ita ce inda Hausawa suke cewa “Mai guri ya zo mai tabarma ya naɗe”, da kuma karin maganar nan ta Hausawa “Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi. A baitukan mawaƙin ya nuna cewa shugaban gwagwarmayarsu yana da maƙiya, da suka yi ta ƙulle–ƙulle na kar a sake shi lokacin da gwamnati ta ɗaure shi. To da ya fito shi ne mawaƙin ya yi amfani da wannan karin magana na nuna cewa to mai guri ya zo fa mai tabarma sai ya naɗe. Sannan ya ƙara fito da manufarsa ta waccan baiti na farko da wata karin maganar a baiti na gaba da cewa duk wannan makirce-makirce da ake masa in Allah ya nufa, to lallai ba makawa sai ya kai ga cin nasara. Wato zakaran da Allah ya nufa da ya yi cara ko ana muzuru dashaho sai ya yi.

    Nuna Ƙwarewa ga Harshe

    Ana gane ƙwarewar mai amfani da harshe ta yadda yake amfani da karin magana da sarrafa ta yadda yake so. Waƙar da aka yi amfani da kare-karen magana takan ba mai sauraro sha’awa, takan kuma yi armashi. Sannan shaida ce ta nuna cewa mawaƙin ya laƙanci harshen da al’adun masu harshe. Dubi waɗannan misalai:

    Don ana taƙamar ɗinki ai ba a fasa ƙwarya ba,

    Don hangen hadarin nesa ai ba a yi wanka da kashi ba,

    Wanda ya ƙyale malam ban ga abin da zai kama kuma ba,

    Don haka mu komai wuya muna nan bayanka Zakzaky.

    In da rabon a sha duka bari ba ta maganin komai,

    Ɗan tsako ya sami abinci sai ya guje wa dangi nai,

    Sai ran da shirwa tai mamaya ya ga za ta dai cimmai,

    Zai zo gurin uwarsa yana ki rufe ni na tuba na bi ki.

    (Mustapha Umar Baba: Waƙar Maganin Mayu)

    Lokaci guda a cikin baiti ɗaya kacal mawaƙi ya yi amfani da karin maganabiyu, wanda wannan ba ƙaramar burgewa ba ce da nuna ƙwarewa. A baiti na 24, da na 25, ya kawo waɗannan kare-karen magana na Hausawa da suka haɗa da:“Ba a fasa ƙwarya don taƙamar iya ɗinki”, da kuma “Ka da hangen hadari ya sa ka wanka da kashi”.Dukkan waɗannan karin maganganu sun zo a waƙar ne da nufin nusar da mutane cewa abin da bai wadace ka ba, ko bai zamo naka ba, ba za ka yi saurin sakin na hannunka ba, kamar dai yadda mutum ba za ya ɗebo kashi ya yi wanka da shi don ya hangi hadari ba. Ko kuma ya fasa ƙwaryarsa don yana taƙamar ya iya ɗinki ba.

    Wato dai manufar mawaƙin shi ne yi wa masu da’awar tawaye ga kiran malaminsu jagorar gwagwarmayarsu shaguɓe da cewa sun saki reshe ne fa sun kama ganye, wato sun bar tsira sun nufi halaka.

    Haka abin ya kasance ga baitina gaba wato na 25, inda ya sake amfani da wasu kare-karen maganar su ma guda biyu a jere don ƙara nuna ƙwarewa ga harshe. Waɗannan karin magana su ne inda Hausawa suke cewa “Idan da rabon a sha duka, bari ba ta magani” da kuma “Ɗan tsako samu ka ƙi dangi”. A wannan baiti mawaƙin ya ida warware zancensa da ya ƙullo a baiti na baya wato na 24, da cewa duk yadda za a nuna wa mutum tsira, to fa idan ba shi da rabo, ba za ya bi ba, wato idan da rabon a sha duka, to bari ba ta magani. Kuma idan har mutum ya bar danginsa to ba wayau ya yi ba, lallai wata rana zai yi da–na–sani, har ya zo neman gafara.

    Adana Karin Magana

    Za a ƙarƙare bayani da bayyana cewa ana amfani da karin magana a waƙoƙi domin ya zama an adana da taskace karin magana. Wato ke nan waɗannan kare-karen magana da aka kawo aka ba da misalai da su a wannan takarda sun samu takaskacewa, kuma za su zama masu amfani gaba tun da har zuwa yanzu suna nan cikin waƙoƙin, wanda hakan ne ma ya ba da dama har aka same su aka yi nazarin irin matsayin da suka fito da irin amfanin da aka yi da su, da moruwar da aka samu daga gare su.

    Kammalawa

    A wannan takarda kamar yadda aka gani, kuma bayani ya gabata, an dubi yadda masani Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, Farfesa Abdullahi Bayero Yahya ya bayyana yadda ya kamata a yi amfani da salon amfani da karin magana ne, a waƙoƙin Hausa, a inda aka gwada duba wannan hanya, aka yi amfani da misalai daga wasu waƙoƙin Hausa wajen bayar da misalai. Sai dai an gano cewa baya da waɗannan salalai da Shehin Malamin ya bayyana, na yadda ake amfani da karin magana, an gano cewa mawaƙa suna amfani da karin magana a waƙoƙinsu ta hanyar sarrafa karin maganar ya zama kirari. Idan mutum ya siffanta kansa da wani karin magana, to wannan karin maganar ya zama kirari ke nan.Wannan ma salo ne.

    Manazarta

    Auta, A. L. (2015). Faɗakarwa a rubutattun waƙoƙin Hausa, Kano: BUK Press

    Bunza, A.M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre Ltd.

    CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Zaria: Ahmad Bello University Press.

    Department of Nigerian Language, (2023). Flier for call of paper, for A Festschric in hounor of Professor Abdullahi Bayero Yahya, Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa.Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

    Ɗangambo, A. (1982). “Rikiɗar Azanci: Siddabarun Salo da Harshe Cikin ‘Tabarƙoƙo’ Tahamisin

    Ɗangambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa, Kano: Triumph Publishing Company Limited.

    Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa, Kaduna: Amana Publishers Limited.

    Gusau, S.M (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Hassan, M.B (1982). “Karin Magana da Salon Maganar Hausawa”, Nazari a kan Harshe, da Adabi, da Al’adu. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

    Koko, H. S. (2011). “Hausa Cikin Hausa”. (ba maɗaba’a).

    Lawal, N. (2016). Tarƙaƙƙen Nazarin Rubutattun Waƙoƙin Noma Na Gasar Argungu Ta 1982.Kundin digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Malumfashi, I. da Ibrahim, M. (2014). Ƙamusun Karin Magana. Kaduna: Makarantar Bambadiya Publishers.

    Mukhtar, I. (2005). Bayanin Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Area 7 Garki Abuja: Country Side Publishers Limited.

    Sarɓi S.A (2007). Nazarin Waƙen Hausa, Kano: Samrib Publishers.

    T/wada, Y. Y. (1982). “Tsari da Ma’ana a Karin maganar Hausa”, Nazari A Kan Harshe, da Adabi, da Al’adu. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

    Omar, S. (2013). Fasahar Mazan Jiya: Nazari a Kan Rayuwa da Waƙoƙin Malam Mu’azu Haɗeja.Sokoto: Garkuwa Media Services Ltd.

    Umar, M. B. (1987). Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph Publishers.

    Yahya, A.B. (2007). Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna: Fisbas Media Services.

    Yahya, A.B. (2016). Salo Asirin Waƙa. Sokoto: Guaranty Printers.

    Yahya, A.B. (2002). “Siffantawa Bazar Mawaƙi: Wani Shaƙo cikin Nazarin waƙoƙi”. Studies In Hausa Language, Literature and Culture the Fifth Hausa International Conference, Centre for the study of Nigerian Language, Bayero University Kano.

    ‘Yar’aduwa, T.M, da Junaidu, I. (2007). Harshe da Adabin Hausa A kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: Spectrum Books Limited.

    Zarruk, R. M. da Wasu (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Kananan Makarantun Sakandire. Littafi Na Ɗaya – Uku. Ibadan: University Press PLC.

    Zarruk, R. M. da Alhassan, H. (1982). Kirarin Duniya 222. Zaria: Ganuwa Publishers Limited.

    Download the article:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.