Sannu Ba Ta Hana Zuwa Ko Za A Dade Ba A Je Ba: (Farfesa Abdullahi Bayero Yahya Nawawi a Farfajiyar Karatun Hausa)

Citation: Bunza, A.M. (2024). Sannu Ba Ta Hana Zuwa Ko Za A Daɗe Ba A Je Ba: (Farfesa Abdullahi Bayero Yahya Nawawi a Farfajiyar Karatun Hausa). Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 1-5. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.001.

Sannu Ba Ta Hana Zuwa Ko Za A Daɗe Ba A Je Ba: 
(Farfesa Abdullahi Bayero Yahya Nawawi a Farfajiyar Karatun Hausa)

Aliyu Muhammadu Bunza
Dept. of Nigerian Languages, Faculty of Arts, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto

Gabatarwa

Jawabin shimfiɗa Buzun Karatu (Inaugural Lecture) wata irin gagarumar hidima ce a tsarin karatu, da koyarwa, da bincike, da renon ɗaliban ilmi, Jami’o’i da cibiyoyin bincike. Buki ne na nuna wa gwarajen da suka yi fice a fannoni daban-daban na ilmi. Maƙasudinsa, suna Jami’a ya yi zara; a duniyar ilmi, sunan Tsangaya ya yi fice a farfajiyar Jami’a, Sashe ya yi kere cikin takwarorinsa. A ɓangaren wanda aka yi bukin dominsa, wata dama ce ta tabbata, cewa, ba a wane bakin banza; tabbas! Zomo ba ya kamuwa daga zaune; wurin da babu ƙasa nan ake gardamar kokuwa. Sanin kumbo kamar kayanta, na zaɓi , raɗa wa wannan jawabi suna: “Sannu ba ta hana zuwa ko za a daɗe ba a kai ba.” Na ɗora binciken wannan ɗan jawabi a kan wata fatawa ta Sani Aliyu Ɗandawo da ke cewa:

Jagora:   Tafiya sannu-sannu sai giwa,

Yara:      Ina waɗanga masu gaugawa.

Gindi:    Shehu sauran mazan farko,

                Mu je Gwambe in gano Sarki.

Wane Ne Abdullahi Bayero Yahya Nawawi Giɗaɗawa Sakkwato?

Da gangan na yi riɓinjin sunayen na shida, domin feɗe biri har wutsiya. Sunaye biyu na farko, Abdullahi Bayero, su ne nasa. Abdullahi babban suna ne da masana ke cewa, ko’ina da ruwanka. Akwai shi gabanin Musulunci, da Musulunci ya bayyana ya ƙara tabbatar da shi, mu lura da sunan Annabinmu Muhammadu bin. Abdullahi. Bayero Bafulatanin suna ne, da dangantakar jini wato (Ba) na wakiltar (Uba/Baba), a jerin sunayen iyaye ga fulani matakai uku ne: Badikko, Basambo da Bayero. Ke nan, Bayero shi ne Babangida ƙarami.

Yahya Nawawi sunan mahaifinsa ne (Alƙalin Lardi). Giɗaɗawa, suna unguwarsu ce, da ta samo suna daga kakansa Waziri Usman Giɗaɗo. Ga al’adar Sakkwatawa, ‘yan cikin garin Sakkwato, suna sa sunayen unguwowin da suka fito a ƙarshen sunansu ya kasance musu laƙabi, misali a ce “Bagiɗaɗe.” Mu kuwa na na bayan fage muna ƙara “Sakkwato” don wanwancewa kawai. A kan wannan taliyo na kira shi: Abdullahi Bayero Yahya Nawawi, Giɗaɗawa, Sakkwato. A wajensa “AB Yahya” yake, a wajen abokan aiki “Bayero” yake. Ni dai ban taɓa jin wanda ya kira shi da sunansa na yanka “Abdullahi “ ba. Domin “Bayero” ya amshe. Haka kuma, ban taɓa tsintuwar “Giɗaɗawa” ko “Sakkwato” a tsarin sunansa ba. Yau da buƙatar ta taso an ambace su. Allah Ya yi muna jagora.

Haihuwa

An haifi Abdullahi Bayero Yahya Nawawi a Unguwar Giɗaɗawa, Sakkwato, a shekarar (1953). A yau shekarar (2021), Bayero ne da shekara 68 (Sittin da takwas) a duniya. In an ɗebe shekaru 7 (bakwai) na ƙuruciya da cikinsu aka yi hidimomin koyon zama, da rarahe, da tahiya, da koyon magana na tatarniya da taƙadarun sautuka da sautuka masu ƙugiya, da tagwaye, har zuwa karatun allo. A cikin shekarun za mu ga, Abdullahi Bayero Yahya Nawawi, ya share shekara sittin da ɗaya (61) cikin yi wa ilmi hidima. Sunan mahaifin Yahya Nawawi, sunan mahaifiyarsa Hadizatu Basharu. Ga al’adarmu, diddigin salsalar uba ake bi wajen tabbatar da salsalar ɗa. Bayero ɗan Yahya Nawawi; jikan Waziri Abdulƙadir Macciɗo; kama kunnen Waziri Buhari; Tunkuɗa hauɓin Waziri Ahmadu; Taka kusheyin Waziri Usman Giɗaɗo; Ihm! Na Nana Asma’u ‘yar Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, Allah Ya gafarta musu, ya gafarta wa Malamin kiɗi Narambaɗa da ya tabbatar da:

Jagora:                   Ɗan bajini shi ka zama bajini,

Jagora/Yara:       Yai bobakali yai tozo,

Yara:                      Ɗan akuya na kallo.

Gindi:                    Na yaba da girma Abdu ƙanen mai daga,

Kanda mu san kowa kai mun ka sani Sardauna.

Matakan Karatu

Abdullahi Bayero Yahya gidan karatu da karantarwa ya tashi. Matakin farko na karatunsa shi ne, makarantar karatun Alƙur’ani ta Malam Haliru Giɗaɗawa ya shiga (1958). Daga shekarar (1961) ya shiga makarantar Firamare ta Waziri Ward, ya ƙarasa (1966). Da ya kammala Firamare, ya samu nasarar shiga makarantar Sakandare ta Gwamnati, Birnin Kabi daga shekarar (1967 - 1971). Ya ci nasarar cin jarabawa mai daraja ta biyu (Division II). Jarabawar da ya ci ta ba shi damar shiga Makarantar Horon Manyan Malamai ta Sakkwato daga shekarar (1972 - 1975). Kammalawarsa ke da wuya, ya samu karɓuwa Jami’ar Bayero, Kano (1978 - 1985). Ya karɓi digirinsa na ffarko da darajar Babban Mataki na Biyu (2/1). Ya sake komawa Jami’ar Bayero, Kano ya ƙara karatun digirin ƙwarewa (MA) (1982 - 1982). Da ƙafa ta tsayu sosai, ya sake sabon shirin karatun digirin sauka (PhD) a shekarar (1982) ya kammala a shekarar (1987), Jami’ar Sakkwato. Wanda duk ya samu waɗannan digirori a boko, ya samu layun tsari katta’u na samun kowane irin aiki irin na Sani Ɗanbolɗo da ke cewa:

“              :Kun san layun tsari gare ni,

“              :Mi al layun tsarinka Mamman,

“              :Dunƙullan dawo gami da nono,

“              :Kowas sha su ba shi jin kasala,

“              :In ko an yi gardama a dama.

Gindi:    Rabbana Allah ka taimake mu,

“              :Mu samu fitar kai cikin tukunya.

Takardun Cancanta

Abdullahi Bayero Yahya, ba shigan ƙadangare shantu ya yi wa karatun boko ba. Kowane mataki ya hau, ya sauka lafiya, kuma an tabbatar masa da haka. Ga takardun cancanta da ya mallaka na zamunan karatu da ya ratsa:

i.         Cancantar Kammala Firamare 1956

ii.       Cancantar Jarabawar (WASC) Mataki II, 1971

iii.     Cancantar Koyarwa (NCE) Ingilishi da Musulunci 1975

iv.     Digirin Hausa da Musulunci, Matakin 2/1 1981

v.       Digirin Ƙwarewa Hausa 1983

vi.     Digirin Sauka (PhD) 1987

vii.   Farfesa a Adabin Hausa 2003.

Daga shekarar (1956) da Abdullahi Bayero Yahya ya karɓi takardar cancanta da kammala Firamare zuwa yau (2021) an share shekara sittin da biyar (65) ana koyo da koyarwa da daa juna sani, da bincike, da jagora, da jamakafi cikin ilmi. Tunanina a nan shi ne, shin tsakanin Bayero da karatu wa ya ratsi wani? Bayero ya ratsi karatu? Ko karatu ya ratsi Bayero? Na harari batun irin rigimar nan ta cewa, tsakanin ƙwai da kaza, wa ya fara zuwa duniya? Ga yadda Sarkin Gardi Ƙyanƙyashe Mijin ‘Yartsito da Bela Sarkin Gardi suka ba juna amsa. a muƙabalarsu fadar Gwandu ga yadda suka ce:

Ƙyanƙyashe:       Ai sai an kai ga ƙyanƙyashe,

                                :Sannan bela ka bayyana.

Bela:                       Sai bela ta ci ta wuce,

                                :Sannan aka kai ga ƙyanƙyashe.

Gindi:                    Sa maza gudu,

                                :Sa arna sake shawa.

Wuyar Aiki ba a Fara ba

A zamanin da Abdullahi Bayero Yahya ya yi karance-karancensa, karatu na da daraja babba ga idon gwamnati, wanda duk ya same shi, za a ba shi abin yi. Daga lokacin karatunsa na Sakandare ya zuwa yau, ya taka muhimmiyar rawa a wurare goma sha shida (16) da suka haɗa da:

1.       Malami a makarantar Garin Kware 1972

2.       Malami a makarantar Gwamnati ta Anka 1975-1978

3.       Malami a makarantar Sakandare ta Gwamnati, Anka 1981-1982

4.       Mai Duba Malaman Hausa a Ma’aikatar Ilmi Sakkwato 1982

5.       Malami a Jami’ar Sakkwato 1983

6.       Malami a Jami’ar Sebha, Libya 1998-2002

Daga 1972-2021 shekara 49 Abdullahi Bayero ya yi na koyarwa.

Mulki

7.       Mataimakin Shugaban Tsangayar Fasaha da Nazarin Addnin Mususlunci, Jami’ar Sakkwato 1988-1992

8.       Shugaban Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya 1992-1997

9.       Daraktan Tsare-tsaren karatu 1993-1996

10.    Ɗanmajalisar Zartarwa na Jami’ar Sakkwato 1993-1996

11.    Ɗanmajalisar Zartarwa na Kwalejin Ilmi, Sakkwato 1994-1995

12.    Darakta Cibiyar Nazarin Hausa 2005-2007

13.    Shugaban Kwamitin Kula da Lafiya, Jami’ar Sakkwato 2002-2005

14.    Shugaban Kwalejin Ilmi, Sakkwato 2007-2012

15.    Shugaban Jaha na Harkokin Ilmi Arewa 2008

16.    Ɗankwamitin Daidaita Ilmin Firamare 2008.

Babu wai, Farfesa Abdullahi Bayero Yahya gogaggen Malami ne da ya koyar tun daga makarantar Firamare har ya zuwa Jami’a. Ya shugabanci matakan kula da ilmi, da renonsa, tun daga Firamare har ya zuwa Jami’a babu matakin da bai riƙa ba ga shugabanci, sai shugabancin Jami’a kawai. Wannan ya tabbatar da cewa, Jami’armu cancanta ta bi wajen ɗora Abdullahi Bayero Yahya a kujerar Farfesa. Kujerar Farfesa ba ta ƙarfi, da wayo, da fadanci ba ce, ai kamar sarauta ce, in ji malamin kiɗi Narambaɗa:

Jagora:   Sarauta ban da nufin Allah ce,

Yara:                      Da ɗibat ta akan yi da ƙarfi.

Jagora:   Waɗanga da nag gaza ganewa,

Yara:      Da sun ga ana haka nan da sun yi.

Jagora:   Wane a dangana tun ga uwaye,

Yara:      Ba duka ɗan sarki ba ka samun sarki.

Gindi:    Gogarman Tudu jikan Sanda,

                Maza su ji tsoron ɗan Maihausa.

Kyautukan Sambarka

Maƙamin Farfesa ba naɗin je-ka-na-yi-ka ba ne na a-ja-ta-haka-nan. Kujera ce da tun ba a kai ga hawanta ba, mai ita zai samu karɓuwa wurare daban-daban da kyautukan yabo, da girmamawa, waɗanda za su koran fage ga masu mamare, da tababa. To, Farfesa abdullahi Bayero Yahya ya ci nasarar:

1.       Samun Fullbright Research Award na Cibiyar Musayar Gaggan Masana, USA 1991

2.        Takardar Yabo ta musamman daga Jami’ar Sebha, Libya 2002

3.       Kyautar Cancanta daga Sashen Larabci Kwalejin Ilmi ta Kumbotso, Kano 2007

4.       Takardar Yabo da cancantar Jagoranci “Dubai UAE, 2011.

Ta tabbata, ba a wane bakin banza.Lallai Jumu’ar da ke albarka tun ranar Larba ‘Yankoli ke baje kayansu. Ashe Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto cikon sunna ta yi makaho da waiwaya.

Duba Manyan Digiri na MA da PhD

A ƙa’idar Jami’a, babu mai hawa kujerar muƙamin Farfesa, sai ya shuka wanda zai gaje shi. Ana kula da irin ƙwazon malami, na zaburar da ƙanana su zo su dafi kafaɗarsa, su miƙe a ga tsawonsu. Bisa ƙa’ida, ba mu yarda da , an haife ka, ka ƙi haihuwa don ƙeta ba, ƙwazon da Farfesa Abdullahi Bayero Yahya ya nuna a nan shi ne:

1.        Duba digirin MA da PhD a matsayi daban-daban. A Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ya duba MA da PhD fiye da goma (10).

2.        Ɗaliban da ya yi wa jarrabawar kundayen MA da PhD a Jami’ar Bayero, da Ahmadu Bello sun kai talatin da takwas (38) daga cikinsu tara (9) PhD ne, ashirin da tara (29) MA.

3.        Ya jarraba ayyukan Farfesoshi uku (3) a matsayin mai jarrabawa na waje.

4.        A jimlace, manyan ɗaliban babban digirin MA da PhD arba’in da takwas (48) suka daga kafaɗar Farfesa Bayero tare da Farfesoshi uku, hamsin da ɗaya ke nan (51). Tirƙashi! A sha’anin ilmi, Farfesa Bayero ya isa ya kafa babban gari na kansa domin Allah Ya yi wa aiki albarka.

Manyan Ɗalibai

Haƙiƙa ɗaliban MA da PhD manyan ɗalibai ne, amma a fagen kujerar Farfesa, da ɗaliban da suka zama Farfesa ake kirari. Farfesan duk da ya kai ga yaye ɗaiban da suka kai ga kujerar Farfesa to, komai ya yi, an ba gwauro ajiyar mata. Daga cikin Farfesoshin da Abdullahi Bayero Yahya ya yaye muna da:

1.       Farfesa Sani Yusuf Birnin Tudu (Adabi: Waƙa)

2.       Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa (Adabi: Waƙa)

3.       Farfesa Hamza Ainu (Adabi: Waƙa)

4.       Farfesa Abdullahi Sifawa (Islamic Studies)

5.       Farfesa Alhaji Mahmood Yakubu (History)

6.       Farfesa Salihu Bala Aljannare (Arabic)

7.       Farfesa Kamal Babikir (Arabic)

8.       Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza (Al’ada: Magani)

Madalla da samun baya mai kyau. Farfesa Bayero, bari in ranto karin waƙar Narambaɗa da ya yi wa Sarkin Gobir Amadu in saƙa tunana a ciki:

Jagora:   Bayero sai godiya Allah,

Yara:      Komi akai duniya ka yi.

Gindi:    Amadu Bubakar Gwarzon Yari,

                Dodo na Alkali.

Kowa Ya Ci Zomo Ya Ci Gudu

Dukkanin abubuwan da muka lissafa; da ake ratsawa a kai ga kujerar Farfesa, wannan fasali ya fi su. A wannan fasalin, za a binciko karance-karancen da aka ce an yi, da ayyukan da aka yi, da ɗaliban da aka yaye, ina rubuce-rubuce da aka yi, da suka tabbatar da kowa ya ci zomo ya ci gudu? Ga yadda Farfesa Abdullahi Bayero ya yi wasan kura da rubuce-rubuce, da bincike-bincike, da wallafe-wallafe.

1.       Ya gabatar da takardu a tarukan ƙara wa juna sani na Sashe da Tsangaya, da Jami’a, a cikin gida, da waje, fiye da talatin (30).

2.       Ya wallafa fitattun takardun ilmi, guda arba’in da biyu (42).

3.       Ya wallafa littattafan bincike kimanin goma (10).

4.       Ya tattaro bincike wurare daban-daban, da ba a wallafa ba guda goma sha biyu (12).

5.       A jimalce, Farfesa Abdullahi Bayero Yahya ya gadar da mu ayyuka kimanin tis’in da biyu (92), da za mu amfana da su komai tsawon rayuwa. Lallai Farfesa Bayero ba ƙyalle ba ne cikin sha’anin Adabin Hausa. Alhaji Muhammadu Gambo Fagada ya faɗi gaskiya:

Jagora:   Dole nakiya ta yi zaƙi Sanda Ummaru,

                Don da zuma aka fara yin ta.

Ƙaƙale da Gudunmuwa Ta Musamman

Hadisin Hausawa na, buƙatar dara a kasa, ko ba a inganta shi ba, ba ya da alamun rauni gabansa da bayansa. A karatu, idan mai shi ya kai ga kujerar Farfesa ana son a ga ɗan abin da ya ƙaƙalo sabo daga cikin ayyukan magabata; da kuma gudunmuwar da za a yi bugun gaba da ita, ga kujerar da yake a kanta. A namu sani na ɗalibai.

1.       Farfesa Bayero shi ne ya fara rubuta kundin digirin PhD a fannin Madahu cikin rubutattun waƙoƙin Hausa.

2.       Shi ya fara rubuta littafi a kan “salo’ cikin waƙoƙin Hausa mai suna “Salo Asirin Waƙa” har ya zuwa yau (2021) ba a sa shi mala ba.

3.       Shi ya fara ƙago wa waƙa mujallar kanta mai take: “Zauren Waƙa.” Ta yi fitowa (4) na biyar na kan hanya (2021).

4.       Cikin duniyar nazarin waƙa Bahaushiya, Farfesa Bayero na da Salailai huɗu da ba a gabace shi da su ba: Salon Tsattsafi, da salon Tunƙa, da Kiɗa da Amshi da Dibilwa.

5.       Farfesa Bayero manazarcin waƙa ne, marubucin waƙa ne, mai rubuta wa mawaƙa waƙa ne. Abin nufi, shi ke rubuta wa Garba Gwandu waƙoƙi, domin Garba ba ya gani, ga riwayar Garba Gwandu (GG) a kan aikin Farfesa Bayero ke yi masa a waƙarsa ta: “Haɗin Kai”:

Tammat kun ji ƙarshenta,

Haɗin kai kun ji sunanta,

Da an tambai ko way yi ta,

G.G Gwandu yay yi ta,

Bayero yar rubuta.

 

Mamaren Manazarci

Jawabin da Farfesa Bayero zai gabatar a yau Larba 30 ga Yuni, 2021 a matsayin Jawabin Shimfiɗa Buzun karatu shi ne ta farko da aka gabatar cikin harshen da aka karɓi digiri, karance-karancen xzama Farfesa. Madalla da wannan ƙwazo na fitar da harsunanmu na gado cikin baƙin marin mulkin kama-karya, da ya ƙasƙantar da harsunanmu na gado, domin daƙushe muna basira da tunani. Masu son su ji mene ne mamare? Ga Narambaɗa gabanin Farfesa Bayero:

Jagora:   Maƙiyan sha da arna,

                Ban san su ba mamare nikai.

Yara:      Da na san su yanzu da na muzanta su,

                Da bana ba su shekara sai Gurbin Ɓore,

                Sun san Garba Ɗanhassan kai yab ba Ƙaura.

Gindi:    Kai bajinin Namoda gagara gago na zagi,

                Iya gaba na Sanda baban Yarin Ƙaura.

Naɗewa

Yau Larba, 30 ga Yuni, 2021 Farfesa Abdullahi Bayero Yahya Nawawi na da shekara (68) a duniya. Bayan ƙuruciyar shekara (7) ya share shekara (61) yana yi wa ilmi hidima. Ya karɓi takardar cancantar karatu (7) a matakan karatu (7) daga shekarar 1956-1987. Ya riƙa muƙamai da matsayi (16) a cikin Jami’a da wajenta. Ɗalibai (51) ya yi wa tsanin karɓar manyan digirorin MA da PhD. Farfesa (8) suka dafi kafaɗarsa aka tabbatar da cancantarsu. Ya yi aikace-aikace da wallafe-wallafe (92). Farfesa Abdullahi Bayero Yahya, ya bayar da cikakkiyar gudunmuwa ga duniyar karatun Adabin Hausa. Ya ci nasarar ƙaƙalo abubuwa (4) da ba a gabace shi da su ba, a cikin ƙarni ɗaya da ‘yan kai na karatun Hausa a Nijeriya da wajenta. Duba zuwa ga adadin manyan ɗalibansa, da aikace-aikacensa, da wallafe-wallafensa, da gudunmuwarsa ta musamman, Farfesa Abdullahi Bayero Yahya Nawawi ya ba da gudunmuwa ɗari da saba’in da ɗaya (171) ga cigaban harshen Hausa, da ɗaukakarsa, da yau muke cin moriyarsa, da mu da iyalanmu. Babu shakka, sunan mijin iya baba. Da Bagudu, da Ƙigudu, duk Sagudu ne yayansu. Haƙiƙa sannu ba ta hana zuwa; kuma ta wuce raini ga gaggawa, domin gaggawa nawa take haifarwa. Jama’a mu miƙe tsaye mu kartɓi saƙon Alhaji Gambo:

Jagora:   Ashe kura ko ta yi kwance,

:Ko an yanke ba ta motci,

                :Ɗan akuya bai ƙetarar ta,

                :Yana aza kura lahiya take,

                :Ba shi isa kusa, ba shi yarda.

Download the article:

Post a Comment

0 Comments