Sarrafa Harshen Mawallafiya a Matsayin Dabarar Bayar da Labari a Wasu Kagaggun Rubutattun Labaran Hausa na Balaraba Ramat Yakubu

Citation: Zulyadaini, B. and Suleiman, Y. (2024). Sarrafa Harshen Mawallafiya a Matsayin Dabarar Bayar da Labari a Wasu Ƙagaggun Rubutattun Labaran Hausa na Balaraba Ramat Yakubu. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 54-66. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.007.

Sarrafa Harshen Mawallafiya a Matsayin Dabarar Bayar da Labari a Wasu Ƙagaggun Rubutattun Labaran Hausa na Balaraba Ramat Yakubu

 Balarabe Zulyadaini
Department of Languages and Linguistics, Uniʋersity of Maiduguri 

Da

Yusufu Suleiman
Department of Hausa, Aminu Saleh College of Education, Azare, Bauchi State

Tsakure: Wannan aiki yana ƙunshe da bayanai dangane da yadda mawallafiya ta yi amfani da dabarar sarrafa harshe domin ta yaɗa wasu al’adun Hausawa da kuma na wasu al’ummomin da ba Hausawa ba. Sannan ta yi amfani da wannan dabara domin ta yaɗa addinin Musulunci, da kuma yanayin zamantakewar iyali a gidajen Hausawa. Aikin bai tsaya nan ba, sai da ya taɓo yadda mawallafiyar ta yi amfani da dabarar domin ta yaɗa tattalin arziki irin na ƙasar Hausa, ta yadda wasu maza da mata suke gudanar da wasu sana’o’in.

Gabatarwa

Marubucin littafin ƙagaggen labari yakan yi amfani da dabaru iri-iri a lokacin da yake rubutu. Irin waɗannan dabaru suna da matuƙar tasiri ga mai karatu. Saboda haka za a iya cewa dabarun bayar da labari sukan taimaka wajen isar da saƙo cikin sauƙi, wato ta yadda mai karatu zai fahimce shi ba tare da ya sha wahala ba. Don haka mawallafi ke amfani da sarrafa harshe a matsayin wata dabara ta isar da saƙonni daban-daban a cikin labari. Akan yi amfani da irin waɗannan dabaru domin a yaɗa wasu manufofi da suka shafi mawallafin labari ko al’ummarsa ko kuma wata al’umma da ke maƙwabtaka da shi. Saboda haka marubuci yana da damar zaɓin irin dabarar ko dabarun da zai yi amfani da su domin su yi tasiri wajen isar da saƙo ga mai karatu.

Ɗangambo, (2007:38) ya bayyana cewa: “Zaɓin da duk mutum ya yi wajen isar da saƙon da yake so ya isar zai yi tasiri ga wanda ake isar da saƙon gare shi.” Saboda haka idan mawallafi ya yi amfani da wasu kalmomi na jan hankalin mai karatu, akan ce ya yi amfani da dabarar sarrafa harshe domin ya yaɗa wata manufarsa ko wasu manufofinsa ko na al’ummarsa. Irin waɗannan manufofi da mawallafi ke ƙoƙarin yaɗawa ta hanyar sarrafa harshe aka duba, kuma aka yi nazarinsu a cikin wannan bincike.

Ma’anar Salo Da Sarrafa Harshe

Idan ana maganar sarrafa harshe za a ga cewa yawanci yakan zo ne tare da salo wajen bayani. Saboda haka salo da harshe tamkar magani ne da abin haɗa shi. Domin a tabbatar da irin kusacin da ke tsakanin salo da harshe, sai Gusau (2003) a cikin Tsoho (2013:30) ya bayyana cewa: “Salo da harshe kamar jini ne da tsoka, wato ba a iya raba su.” Zai fi dacewa a fara ba da ma’anar salo daga bakin wasu masana da manazarta, kafin a dubi sarrafa harshe a matsayin wata dabara ta bayar da labari kamar yadda aka yi amfani da shi a cikin Mukhtar, (2004).

Masana da manazarta sun yi ta bayyana ma’anar salo gwargwadon fahimtar kowanensu. Duk da cewa yawancin masana da manazarta sun nuna cewa shi salo abu ne mai wuyar ganewa, amma sun taka rawar gani wajen fito da ma’anoni daban-daban waɗanda za su sa a fahimci inda aka dosa idan ana maganar salo. Yanzu za a duba yadda wasu masana da manazarta suka bayyana ma’anar salo.

Yahaya, da Ɗangambo, (1986: 114) sun bayyana ma’anar salo da cewa:

“Salo yana nufin hanyar da aka bi aka isar da saƙon littafi, wato dabarun jawo hankali, da sarrafa Hausa, misali amfani da Hausa mai kyau, amfani da kalmomi cikin hikima, gina jimloli da dai sauransu.”

A wani binciken kuma Ɗangambo, (2008: 34) ya bayyana cewa:

“Salo wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci. Wannan yana nufin yin amfani da wata kalma, lafazi, yanayi, hanya ko tunani a maimakon wani. Zaɓin da duk mutum ya yi wajen isar da saƙon da yake so ya isar zai yi tasiri ga wanda ake isar da saƙon gare shi. Ana iya cewa armashin zance/saƙo ya danganta da irin batutuwa (kalmomi da yadda aka yi zaɓin sarrafa su) na wanda ke isar da saƙon.”

Har ila yau Ɗangambo, (2008: 82) ya fayyace mana bambancin da yake akwai tsakanin ma’anar salo da ta sarrafa harshe, inda ya nuna cewa:

“Salo dabaru ne na isar da saƙo cikin armashi; sarrafa harshe kuwa ya ƙunshi yadda aka yi amfani da kalmomi bisa dokokin nahawun harshe (Hausa), ko saɓanin haka.”

Shi kuwa Tsoho (2013: 31) ya bayyana ma’anar salo da cewa:

“Yawancin salailan da manazarta suka fi duba a ƙirƙirarrun labarai da sauran ayyukan adabi na Hausa, sun haɗa ne da salon sarrafa harshe, inda ake bayani kan adon magana, da kirari, da karin magana, da habaici, da kwalliya, da kamance da aron kalmomi da amfani da wasu harsuna da ba Hausa ba, misali Larabci da Turanci (Ingilishi), da dai sauransu.”

A wani binciken da aka gudanar, Bunza, (2017) ya tofa albarkacin bakinsa dangane da ma’anar salo, inda ya bayyana cewa:

“Salo kalma ce mai faɗin ma’ana gwargwadon manufar da aka yi amfani da ita. Kalma ce da a taƙaice take nufin dabara ko hanya ko wayo ko iyawa da sauransu.” (Bunza, 2017: 3).

A wani binciken kuma Aliya Adamu Ahmad (2013: 81) ta bayyana cewa:

“Kalmar salo na nufin amfani da hanyoyi da dabarun jawo hankalin mai karatu ko mai sauraro da marubuci ya yi amfani da shi, domin ya ƙara ma rubutunsa armashi. Wato ke nan “Salo” hanya ce ko dabara ta yin wani abu, ko bayyana wani abu.”

Har ila yau ta ƙara da cewa:

“Dabarun sarrafa harshe dabaru ne kuma da suka ƙunshi dokokin sarrafa harshe (nahawu) da ake amfani da su wajen isar da saƙo. Waɗannan dokoki su ne mawallafa ke sarrafa su ta hanyoyi mabambanta, wasu lokutan ma sukan karya dokokin don su sami cim ma manufar da suke buƙata, kuma su gamsar da jama’a cikin ban sha’awa.” (Ahmad, 2013: 84-85).

 A taƙaice dai za a iya cewa salo da sarrafa harshe na nufin yadda marubuci ya zaɓi yin amfani da dabaru iri-iri domin ya isar da saƙon cikin labarin da ya rubuta ga mai karatu ko mai sauraro. Don haka kowane marubuci yana iya ɗaukar dabarar sarrafa harshe da ya ga za ta kai shi ga cim ma manufarsa. Abubuwan da za a duba nan gaba su ne yadda marubuciyar littattafan (Budurwar Zuciya da Alhaki Kwikwiyo Ne da Matar Uba Jaraba) ta yi amfani da dabarar sarrafa harshe domin ta isar da saƙonnin cikin waɗannan littattafai ga mai karatu ko mai sauraro.

 

Sarrafa Harshen Mawallafiya

Amfani da sarrafa harshe yana daga cikin dabarun da mawallafin ƙagaggen labarai ke amfani da su domin jan hankalin mai karatu. Wannan ya nuna cewa amfani da sarrafa harshe na mawallafi yakan taimaka masa wajen yaɗa al’ada irin tasa ko kuma al’adar ƙabilarsa a cikin labari. Wani lokaci kuma ya yi amfani da sarrafa harshe domin ya yaɗa addininsa ko siyasarsa ko tsarin rayuwa da na tattalin arzikinsa ko na al’ummarsa, da dai dangogin waɗannan, (Mukhtar, 2004: 50).

Wannan ya nuna cewa a cikin ƙagaggen labari ana iya samun tasirin addini da na tsarin rayuwar al’umma da na tattalin arziki da kuma na al’adun ƙabilar marubuci ko na wata ƙabila ta kusa ko ta nesa (baƙuwar al’ada). Saboda haka a nan za a duba irin wannan dabara ta sarrafa harshe kamar yadda mawallafiyar ta yi amfani da ita a littattafan da ake nazari.

Sarrafa Harshe Domin Yaɗa Al’ada

 Dangane da ma’anar al’ada an sami masana da manazarta da suka kawo bayanai dalla-dalla. Saboda haka a nan za a bayyana ra’ayoyin wasu daga cikin masanan da manazartan dangane yadda suka fito da ma’anar.

 Umar, (1981) ya bayyana cewa: “Al’adu dai su ne dukkan hanyoyin rayuwar al’umma…. Sun ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi zaman al’umma.” (Umar, 1981: 263).

Shi kuma Bunza, (2006) ya ƙara faɗaɗa ma’anar al’ada inda ya bayyana cewa:

“Al’ada tana nufin dukkan rayuwar ɗan Adam tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa. A ko’ina mutum ya samu kansa duk wata ɗabi’a da ya tashi da ita tun farkon rayuwa ya tarar a wurin da ya rayu, ko yake rayuwa, ita ce al’adarsa da za a yi masa hukunci a kai.” (Bunza, 2006: xxxii).

Shi kuma Ibrahim, (2016) cewa ya yi:

“Al’ada ta shafi dukkan abubuwa waɗanda al’umma take aiwatarwa a rayuwarta ta yau da kullum, ta kuma lamince wa ‘ya’yanta da su ma su gudanar da su. Hasali ma al’ada aba ce mai numfashi (rai) mai yaɗo, mai sassauyawa lokaci bayan lokaci.” (Ibrahim, 2016: 137).

A taƙaice za a iya cewa al’ada tana nufin abubuwan da ɗan Adam ya tashi cikinsu kuma ya saba yinsu, ya rayu a cikinsu har zuwa ƙarshen rayuwarsa. Kowace al’umma ta duniya tana da irin nata al’adun da suka bambanta ta da na sauran al’ummomi. Yawancin marubuta ƙagaggun labarai sukan yi ƙoƙari wajen fito da al’adunsu a cikin rubuce-rubuce domin su yaɗa su a idon duniya.

A cikin littafin Budurwar Zuciya, mawallafiyar ta fito da al’adar nan ta kayan lefe da ake yi a lokacin aure a ƙasar Hausa. Wannan ya faru ne a lokacin da Alhaji Usman ya auri Sa’adiya, yarinyar da ya hana ta ƙarasa karatunta a makarantar sakandare. A cikin labarin an bayyana cewa:

“Kada ka so ka ga irin abin da ya kashe mata da iyayenta kafin a yi bikin. Har saitin nan na gwal ya saka mata a kayan lefe, wato zannuwan aure.” (Yakubu, 1987: 18).

A ma’ana ta asali in an ce kashe, to ana nufin raba abu mai rai da ran nasa, ko kuma kawo ƙarshen wata magana a kotu ko a wurin ‘yansanda da makamantan waɗannan. Shi kuma kuɗi ba abu ne mai rai ba, amma sai aka danganta shi da kisa. A maimakon a ce “kada ka so ka ga abin da ya ɓatar mata,” sai aka yi amfani da kashe domin a ƙayatar kuma a ƙarfafa irin ɓatarwar da aka yi. Kamar yadda ake kisan maciji ko wani abu mai rai, haka nan aka kashe mata kiɗi tare da iyayenta. Duk inda aka ambaci kasha kuɗi, to an san cewa ba kuɗi kaɗan ake magana ba. Saboda yawan kuɗin ne ya sa aka ce kada ka so ka ga abin da aka kashe. Wato idan ka gani abin zai iya ba ka tsoro ko mamaki saboda yawansa.

Idan aka sake dubawa za a ga cewa mawallafiyar ta yi amfani da kayan lefe a maimakon kayan aure domin ta fito da wata al’adar Bahaushe, ta ƙara wa zancen armashi kuma ta burge mai karatu. Kalmar lefe tana nufin wani abu da ake saƙawa da kaba wanda ake amfani da shi don saka kayan kaɗi ko kayan aure. Duk da cewa a zamanin da muke ciki ba a yin amfani da lefe wajen saka kayan aure, amma har yanzu sunan yana nan kamar yadda aka sani a matsayin abin da ake amfani da shi wajen sanya kayan aure, don haka ake kiransa kayan lefe. A wasu garuruwan ƙasar Hausa akan kai kayan lefen ne kafin a ɗaura aure, yayin da a wasu garuruwan kuma sai an ɗaura aure da a kai kayan.

Idan kuma aka duba cikin littafin Alhaki Kwikwiyo Ne, nan ma an yi ƙoƙarin yaɗa al’adar Bahaushe ta kaiwa kayan toshi, wato yadda ake haɗa kaya a cikin kwalla domin ‘yan uwan saurayi ko mai neman aure su nuna cewa ɗansu ko ɗan uwansu yana son wannan budurwar. Irin wanna ta kasance a lokacin da Alhaji Abubakar yake hira tare da Saudatu, lokacin da yake tambayarta cewa:

Ɗazu da rana kin ce akwai kwallaye a ajiye. To, tun da yake an amince da ni, ai sai a yi ƙoƙarin mayarwa da waɗannan nasu, don kuwa a gobe zan kawo nawa, ko yaya kika gani?” (Yakubu, 1990: 80).

A nan an yi amfani da kwalla a matsayin abin da ake zuba kayan toshi. A zamanin da idan ana zancen neman aure, to za ka ji yawan kwallayen da aka kai gidan su budurwa. A nan an nuna cewa yawan kwallayen da aka kai gidan su budurwa shi ne gwargwadon farin jininta a wajen samari. A cikin kwallayen akwai wasu kayayyaki, kamar tufafi da man shafawa da turare da kayan ƙarau da kuma sauran kayan kwalliya. Abin da ake so a bayyana dangane da kwalla a nan shi ne amfaninta wajen sanya kayan toshi saboda canje-canje da aka samu na zamani.

A taƙaice dai ta nuna cewa akwai al’adar nan ta kai kayan toshi gidan su yarinyar da saurayi yake nema da aure. Wannan ba baƙuwar al’ada ba ce a ƙasar Hausa. Sannan kuma tana nuna shaidar cewa lallai saurayi da gaske yake son yarinyar ba da wasa ba, kuma ba domin ya yaudare ta ba. Wannan kalma tana nuna cewa kai kayan toshi yana daga cikin al’adun da suka shafi neman aure a ƙasar Hausa.

Idan kuma aka duba littafin Matar Uba Jaraba, nan ma za a ga wata al’ada ta Bahaushe da aka yi ƙoƙari wajen fito da ita, wato yadda ake haɗa kayan ƙauri a lokacin da aka sami ƙaruwa ta haihuwa. Akan haɗa kayan ƙauri kamar ƙafafun saniya da kayan yaji domin yi wa mai jego biƙi. Irin wannan al’adar an kawo bayaninta ne a lokacin da Ladidi matar Sa’idu ta haifi ‘ya’ya maza tagwaye, inda aka bayyana cewa:

“Ranar ƙauri kuwa ƙafofin sa ya sa aka sayo daga Kano, aka yi ƙauri da shi, ban da alawa da goro huhu guda ɗan Shagamu.” (Yakubu, 2006: 47).

A ma’ana ta asali idan ce ƙauri ana nufin irin warin da ake ji idan an ƙona gashi ko tsumma (C.N.H.N. 2006). A nan mawallafiyar ta yi amfani da kalmar ƙauri domin ta fito da alaƙar da ke tsakanin nama da wuta a wajen gashi ko dafi. Saboda haka ƙauri a cikin labarin yana nufin wani nau’i na nama da ake dafawa a bayar wa maijego ta ci domin ta kwantar da kwaɗayinta. Haka zalika akwai ranar da ake warewa domin dafa wannan ƙauri.

Abin da ya shafi alawa da goro kuma, ana amfani da su ne wajen hidimar bukukuwa a ƙasar Hausa. Shi kansa goron da ake magana, ba kowanne ne ba sai wanda aka kawo daga Shagamu. Shagamu gari ne da ya shahara wajen kasuwar goro, sannan garin yana nan a kudu maso yammacin Nijeriya, wato yankin Yarabawa.

A taƙaice dai mawallafiyar ta yi amfani da kalmar ƙauri ne domin ta nuna gwanintar harshe kuma ta burge mai karatu, sannan ta tallata al’adar a idon duniya. Saboda haka kayan toshi da na lefe sun shafi al’adar neman aure a ƙasar Hausa. Shi kuma kayan ƙauri ya shafi al’adar haihuwa a gargajiyar Bahaushe.

Sarrafa Harshe Domin Yaɗa Addini

Wani lokaci a cikin wasu rubutattun ƙagaggun labarai akan sami abubuwan da suka jiɓanci addini. Wasu mawallafan sukan yi haka ne domin su tallata addininsu, su yaɗa shi a duniya domin a san irin wasu dokoki na shari’a da ke cikinsa. Irin wannan yakan taimaka wa mai karatu har ya fahimci irin addinin da shi mawallafi ko al’ummarsa ke bi. Sannan wani mawallafin yakan nuna yadda addinin ya yi tasiri a cikin rayuwar wasu daga cikin taurarin labarin.

Idan aka duba labarin cikin littafin Budurwar Zuciya za a ga yadda addinin Musulunci ya yi tasiri a cikin rayuwar wasu daga cikin taurarin, wato kamar yadda aka bayyana matsayin mahaifin Asama’u inda aka ce:

“Mahaifinta yakan yi tamsiri a unguwarsu, kuma duk wani abu da ya faru a unguwar, ko aure ko jana’iza ko suna, shi ake kira.” (Yakubu, 1987: 3).

Idan aka duba za a ga cewa kalmar tamsiri an samo ta ne daga kalmar “Tafsir” wadda ta samo asali daga Larabci. Mawallafiyar ta canja wa kalmar suna daidai da yadda Bahaushe yake faɗa. Saboda haka a nan za a gane cewa kalmar tamsiri kamar yadda ta yi amfani da ita, tana da alaƙa da addinin Musulunci. A cikin addinin Musulunci ne aka san cewa akwai tamsiri da ake yi domin a yi bayani tare da sharhi a kan ayoyin Alƙur’ani mai tsarki. Idan ana tamsiri, yawanci ana bayani ne kan horo da hani ko kuma wani abu na tarihi da ya gabata domin wata koyarwa. Don haka a nan mawallafiyar ta fito da wannan kalma ta tamsiri ne domin ta ƙara yaɗa addinin Musulunci.

Idan kuma aka duba cikin littafin Alhaki Kwikwiyo Ne za a sake samun yadda mawallafiyar ta ƙara yaɗa addinin Musulunci domin ta ƙara fito da shi fili, kamar yadda ta bayyana cewa:

“Ita Rabi ba ta ce musu komai ba. Maimakon ma ta bi su ɗakin, sai kawai ta ɗauki butar da ke nan ƙofar ɗaki, ta nufi ban ɗaki abinta. Lokacin da ta fito, sai ta ji an yi kiran sallah daga nan babban masallacin Juma’a, sai kawai ta yi alwala, ta shiga ɗaki, don ta yi sallah.” (Yakubu, 1990: 92).

Domin a ƙara fito da addinin Musulunci a cikin labarin, sai mawallafiyar ta yi amfani da kalmomin ‘kiran sallah’ da ‘Masallacin Juma’a’ da ‘alwala’ da kuma ‘sallah.’ Dukkan waɗannan kalmomi suna da alaƙa da addinin Musulunci kai tsaye, kuma sun shafi aikata ibada ta hanyar yin sallah.

Kowane musulmi ya san cewa sallah tana ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci. Hasali ma idan sallah ta inganta, sauran ayyuka ma sun inganta. Saboda haka idan lokacin sallah ya yi, to, ba sauran wani aiki sai ita. Idan an idar da sallah, sai a shiga sauran hidindimun duniya. Yin sallah ne ke bambanta tsakanin musulmi da wanda ba musulmi ba.

Idan kuma aka duba cikin littafin Matar Uba Jaraba an sake kawo wasu abubuwan da suka jiɓanci addinin Musulunci, wato lokacin da Safiya ‘yar gidan Daso ke fama da rashin lafiya na taɓuwar hankali. A nan an bayyana cewa:

“An tattaro wasu malamai da suka duƙufa a kan Safiya, ana ta faman addu’a da sauke Alƙur’ani, masu karanta Dala’ilu na yi, ga ɓangaren masu karanta Ashafa suna karantawa.” (Yakubu, 2006: 61).

Wannan ya nuna cewa an yi amfani da wasu littattafai da kundaye da suka shafi addinin Musulunci. Waɗannan sun haɗa da ‘Alƙur’ani’ da ‘Ashafa’ da kuma Dala’ilu.’

A ma’ana ta zahiri, kalmar ‘sauke’ tana nufin a ɗauke abin da yake sama a mayar da shi ƙasa. Amma a cikin labarin mawallafiyar da ta ce sauke Alƙur’ani, tana nufin karance dukkan ayoyin Alƙur’ani mai tsarki gaba ɗaya da nufin neman waraka daga cutar da ke addabar mutum. Har ila yau Alƙur’ani ana karanta shi a matsayin neman lada ko ibada lokacin da ake yin sallah. Haka kuma ana karanta shi domin neman tsari daga sharurrukan ɗan Adam da na aljannu da sauransu. Ana karanta Ashafa da Dala’ilu domin neman waraka daga wasu cututtukan Kamar yadda aka yi amfani da su a cikin labarin.

A taƙaice dai za a iya cewa wasu marubutan sukan sanya abubuwa na addini domin su yaɗa shi a idon duniya. Wannan ya nuna cewa addinin mawallafi yakan           iya yin tasiri matuƙa a cikin rubuce-rubucensa, kamar yadda abin ya faru ga marubuciyar waɗannan littattafan.

Sarrafa Harshe Domin Nuna Tsarin Rayuwa

Al’ummomin duniya suna da hanyoyi daban-daban na tafiyar da rayuwarsu. Sannan ko da a tsakanin al’ummomin da ke maƙwabtaka da juna, akan sami wasu ‘yan bambance-bambance na tsarin tafiyar da rayuwa. A cikin littafin Budurwar Zuciya an sami irin wannan tsarin rayuwa na yanayin zamantakewar iyali, musamman ma yadda Alhaji Usman ke zaune da matarsa Asama’u, sannan da irin matsalar da ta taso tsakaninsu a sakamakon shirinsa na ƙara aure, lokin da Asama’u ta bayyana masa cewa:

“Babu inda za ni. Aurenka kuwa, ba zai hana ni zama in lura da ‘ya’yana ba, wata ta zo, ta wulaƙanta mini su. Ga gidan nan ta zo. Kai kanka ka san sai ranar da ka mutu sannan za a haifi wata ‘ya maccen….” Alhaji ya tashi da fushi, ya fita daga gidan ma gaba ɗaya. Da ma dai haka irin wannan yake faruwa tsakanin Alhaji Usman da matarsa Asama’u.” (Yakubu, 1987: 1).

Wannan ya nuna cewa lallai akwai abin nan da Hausawa kan ce “kishi kumallon mata.” Mawallafiyar ta yi amfani da wasu jimloli da ke nuna kishi. Sannan an nuna cewa wasu matan Hausawa kan wulaƙanta ‘ya’yan kishiyoyi, musamman ma idan mahaifiyar yaran bat a gidan. Sauran jimlolin da aka yi amfani da su domin a fito da kishi sun haɗa da:

1.“Ga gidan nan ta zo.” Ana so ne a bayyana cewa idan ma aka auro wata matar ai za ta zo ta ga irin zaman gidan idan ma da daɗi ko ba daɗi.Sannan ko da ta zo ma, ba yadda ta iya da ita domin ita ce ta fara haihuwar ‘ya’ya a gidan. Don haka ai na gaba ya yi gaba.

2.“Sai ranar da ka mutu sannan za a haifi wata ‘ya maccen.” Wannan ma wata magana ce ta hikima wadda ke bayyana cewa mata masu kyau ba sa ƙarewa. Sai ya ƙare aure-aurensa ya bar mata masu yawa kuma kyawawa. Wannan ya nuna cewa waɗannan maganganu ne na kishi da ake samu a tsarin rayuwar zaman aure a tsakanin kishiyoyi a ƙasar Hausa.

Bugu da ƙari, daga wannan jayayya da aka yi tsakanin Alhaji Usman da matarsa Asama’u, za a gane cewa yawanci a cikin al’ummar Hausawa akan sami matsala tsakanin miji da mata lokaci-lokaci, kamar yadda Bahaushe kan ce “Zo mu zauna, zo mu saɓa,” musamman ma idan ya nuna sha’awarsa ta ƙara aure. Saboda haka mawallafiyar ta fito da wannan matsala ta rashin fahimtar juna da ake samu a yanayin tsarin rayuwar zaman aure tsakanin mata da miji a ƙasar Hausa.

 A cikin littafin Alhaki Kwikwiyo Ne an sami kishi a tsakanin matan Alhaji Barau, saboda ɗaya daga cikin matan, wato Fatima, ta sami juna biyu. Daga wannan lokacin ne sauran matan suka fara kishi da ita, musamman uwargidan. A lokacin da ta sami Alhaji Barau da Fatima a ɗaki, sai aka bayyana cewa:

“Tana shiga kuwa sai ta fara yi wa Alhaji surutai cewar mene ne abin ɓoye-ɓoyen da ake yi, ai ba shi da wani amfani, su ma masu taya shi murna ne, don Allah bai ba su ba, ai bai kamata ya ƙi su har ya ware su ba. Ta dai shiga surutu iri-iri na ɓacin rai, don kuwa kishi ya cika ta a lokacin.” (Yakubu, 1990: 21-22).

 An fito da wasu zantukan kishi domin a nuna wani salon magana na ƙorafe-ƙorafen da ake samu daga wurin matan da ba su sami haihuwa ba a gidan miji. Dangane da irin waɗannan zantuka na kishi da suka bayyana a cikin labarin sun haɗa da:

(1) “….mene ne abin ɓoye-ɓoyen da ake yi?”

Wannan ya nuna cewa an yi amfani da wani salon magana domin a fito da ƙorafi a kan ɓoye ciki. Akan yi irin wannan ɓoye zancen ciki domin gudun sharrin kishiyoyi. Duk da cewa dole ne daga baya cikin ya fito fili, amma akan ɓoye saboda gudun wasu matsaloloin da ke iya faruwa na asirce-asirce na kishiyoyi.

 (2) “….don Allah bai ba su ba, ai bai kamata ya ƙi su har ya ware su ba.”

 A nan ma an yi amfani da sarrafa harshe ne domin a sake fito da wani ƙorafi na wariya tsakanin matar da ta sami juna biyu da sauran matan da ba su samu ba. Yawancin kishiyoyin da Allah bai ba su haihuwa ba, sukan nuna kishi ga wadda ta samu. Wani lokaci ma akan sami matan da ke yunƙurin kashe kishiyar ko lalata cikin da aka samu ta hanyar yin asiri. Mawallafiyar ta nuna cewa yawanci irin wannan matsalar takan haifar da rashin jituwa tsakanin matar da ke haihuwa da wadda ba ta haihuwa a gidan miji.

 Idan kuma aka duba labarin cikin littafin Matar Uba Jaraba , nan ma za a ga wani irin kishi, wato yadda aka bar kishi a kan miji, aka koma kishi a kan sana’a. Irin wannan kishin ya samu ne tsakanin Daso da Ladidi, wato a lokacin da Ladidi ta fara abincin sayarwa ana kai mata kasuwa. A nan an bayyana cewa:

“To wannan ciniki da Ladidi ta kama gadan-gadan, sai kishin miji ya saki Daso, na ciniki ya kama ta. Saboda in yau ta ce an cika gida da hayaƙi, gobe sai ta ce almajirai sun cika gidan da surutu, jibi ta ce ‘yan aikin Ladidi sun yi mata rashin kunya.” (Yakubu, 2006: 50).

Idan aka duba za a gane cewa an yi amfani da wasu maganganu masu nuna kishi kamar haka:

(1) “….an cika gida da hayaƙi.”

An jefa magana ce ba tare da an kama suna ba. Wannan ya nuna cewa an ɓoye sunan wadda ta cika gidan da hayaƙin. A maimakon a fito fili a kama sunan Ladidi, sai aka sakaye sunan. Ana so a nuna cewa Ladidi ce ta cika gida da hayaƙi saboda abincin sayarwa da take yi. Saboda haka wannan wani salo ne na magana wanda ya shafi gugar zana. Ita kuma Daso ba ta sayar da abinci, sai dai abubuwan sha waɗanda ba sai an yi amfani da wuta ba wajen sarrafa su.

 (2) “….almajirai sun cika gidan da surutu.”

Wannan wata magana ce da ke nuna alamar kora da hali. Wato an fake da surutun almajirai a cikin gida domin Alhaji ya hana su shiga ɗauko kayan tallen abinci.

 (3) “….’yan aikin Ladidi sun yi mata rashin kunya.”

An yi amfani da rashin kunya domin a bayyana rashin kara tsakanin Daso da ‘yan aikin Ladidi. Ai ka ga a nan idan har ‘yan aiki za su yi wa matar gida rashin kunya, wataƙila idan maigidan ya ji labari zai iya dakatar da su. A taƙaice idan aka duba waɗannan jimloli guda uku, za a ga cewa suna nuna alamun kishi ne da ke gudana tsakanin Daso da Ladidi. Wannan ma wani tsarin rayuwa ne na zamantakewar aure tsakanin matan Hausawa kuma kishiyoyi.

Wani kishin da aka samu a cikin littafin Matar Uba Jaraba shi ne a sakamakon samun haihuwar ‘ya’ya maza. A lokacin da Ladidi ta haifi tagwaye maza, sai Daso ta fito da kishi a fili. A sanadiyyar haka ne ta tafi wani gari wai shi Ningi a cikin Jihar Bauci domin ta sami maganin da za ta yi amfani da shi ta kashe ‘ya’yan Ladidi. Bayan boka ya nuna mata magunguna iri uku, na mutuwa da na haukacewa da kuma na shiga duniya, nan take sai ta bayyana masa cewa:

“Ai malam duk gaba ɗaya nake so ka ba ni. Da ɗaiɗai sai na talauta mata zuri’arta gaba ɗaya…. Malam ka ba ni kawai. Duk abin da kake tunani ma ni na ɗauka, kuma ko nawa zan biya ka kuɗinka. Kada ka damu ba ni kawai.” (Yakubu, 2006: 56).

An yi amfani da wasu kalamai domin a nuna yadda wasu matan Hausawa ke furta wasu miyagun kalamai domin neman biyan bukatunsu na son rai. Irin waɗannan kalamai, kamar yadda aka yi amfani da su a cikin labarin, sun haɗa da:

(1) “Da ɗaiɗai sai na talauta mata zuri’a.”

A ma’ana ta zahiri kalmar ‘talauta’ tana nufin ƙarewar dukiyar kuɗi ko wata kadara ko kuma wani da aka mallaka. A cikin labarin an yi amfani da kalmar domin a nuna wani salon magana na kishi kan yadda za a salwantar da ‘ya’yan Ladidi, su ƙare kamar yadda dukiya ke ƙarewa a wurin mai ita. Wannan ya nuna cewa ‘ya’ya ma ai dukiya ce, domin ba a sa kuɗi a saye su. Saboda haka an yi amfani da zancen talauta zuri’a nuna za a lalata ko a ɗaiɗaita ‘ya’yan da aka haifa tamkar yadda kuɗi ke lalacewa. Irin wannan yakan faru ne ko dai ta hanyar yi musu asiri su mutu, ko su haukace ko kuma su shiga duniya.

(2) “Duk abin da kake tunani ma ni na ɗauka”

An yi amfani da wani salon a ɓoye wani al’amari, wato tunani a kan irin nauyin da mutum zai ɗauka. A nan ana ƙoƙarin bayyana cewa abin da ake tunani bai wuce zunufi ba. Shi zunufi abu ne mai nauyin gaske. Idan idon mace ya rufe, takan ce ta amince ta ɗauki zunufin ko da mene ne zai faru da ita.

Idan aka duba wannan bayani za a gane cewa a lokacin da kishi ya ratsa mace, idonta kan rufe, sannan tunaninta ya gushe har sai ta aikata abin da take so, ko da kuwa za ta yi nadama daga baya. Zafin kishi kan sa mace ta yi kisan kai ko ta haukatar da mutum ko kuma ta sa a shiga duniya ba shiri ta hanyar amfani da asiri. Irin waɗannan abubuwan akan same su a wasu rubuce-rubuce na ƙagaggun labaran Hausa domin a nuna tsarin rayuwar wasu matan Hausawa masu tsananin kishi da ƙulle-ƙullen makirce-makirce a gidan miji.

A cikin littafin Alhaki Kwikuyo Ne an sami wani tsari na rayuwar Hausawa, yadda ake bayyana yanayin rayuwar gidan Alhaji Abdu dangane da ƙunci da ƙazantar gidan da kuma irin rashin kulawa ta a-zo-a-gani da yake yi kamar yadda aka bayyana cewa:

“Da ka shiga gidan za ka san cewa lallai babu wani jin daɗi a tare da masu wannan gida. Igiyar tsumma ma daban take a gidan. Ga wata rariyarsu ta kwatami a tsakiyar gidan. Sannan a gefe ɗaya kuma, ga wurin da suke yin girki, hayaƙin girkin ya baƙanta gidan gaba ɗaya.” (Yakubu, 1990: 2).

An bayyana yanayin ƙunci a cikin wasu gidajen da ke cikin birni saboda yawan jama’a ko ƙarancin fili a cikin gidajen. Haka kuma an bayyana yanayin cikin irin waɗannan gidajen ta yadda aka kawo maganar ‘igiyar tsumma’ da ‘rariyar kwatami’ da kuma ‘hayaƙin girki’ da ya baƙanta gidan. Dukkan waɗannan abubuwa da aka ambata suna da nasaba da ƙazanta. A nan an yi amfani da wani salon magana ne domin a nuna irin tarin ƙazantar da ke cikin gidan da kuma kusacin wurin dafa abinci da wuri mai ƙazanta.

Daga wannan bayani za a gane cewa wasu mutanen suna zaune ne a cikin ƙunci da matsi a unguwanninsu. Saboda haka duk lokacin da jama’a suka sami kansu cikin irin wannan yanayi na ƙunci, to ba shakka akan sami matsala ta ƙazanta da rashin walwala sosai. Daga ƙarshe idan ba a dace ba sai a kamu da wasu cututtuka.

A cikin littafin Matar Uba Jaraba an fito da wani tsarin rayuwar Hausawa, wato yadda abinci bai rufe idon Bahaushe ba. An sami irin wannan a lokacin da Sani ya tarar da Sa’idu da Musa sun gama cin abinci, inda yake cewa:

“Salamu alaikum. Kai amma na daki gurbi, ina ta sauri kada dai a ce an mai da kwanukan abincin gida?” “Wa’ alaikumu salam Sani, sannu da zuwa. Shiga gidan ka ce su zuba maka abinci, mun cinye wanda aka fito da shi.” (Yakubu, 2006: 17).

A nan an yi amfani da salon magana domin a nuna gwanintar harshe, wato inda aka ce “Kai amma na daki gurbi.” Manufa a nan ita ce rashin sa’a ko rashin dacewa. Wato an sami gurbin da aka ajiye abincin, amma babu shi an cinye. Saboda haka ba a dace ba ke nan.

Wannan ya nuna cewa a cikin tsarin rayuwar Hausawa akwai wasu abubuwan ban sha’awa, musamman ma yadda za ka tarar da maigida ya fito da abinci daga gidansa domin ya sami waɗanda za su ci tare. Ba kasafai Bahaushe ke son zama ya ci abinci shi kaɗai ba. Yawanci yakan so ya ci tare da abokansa ko ‘yan uwansa ko kuma duk wanda Allah ya kawo. Wannan tsari ne mai kyau a cikin rayuwar al’ummar Hausawa. Don haka a nan an nuna cewa Hausawa mutane ne masu son kyautatawa, ba masu rowa ga duk wanda Allah ya haɗa su zaman tare ba. A taƙaice mawallafiyar ta nuna cewa a tsarin rayuwar Hausawa akwai ƙauna da mutuntawa da kuma taimakon juna, musamman ma a shekarun baya.

Sarrafa Harshe Domin Nuna Tattalin Arziki

Wani lokaci mawallafa sukan yi amfani da wata dabara ta sarrafa harshe domin su nuna irin tattalin arzikinsu ko na al’ummar da suke tare da ita. Irin wannan yakan shafi harkar kasuwanci ko ta noma da kiwo ko haƙar ma’adinai ko kuma aikin gwamnati da makamantansu. Balaraba Ramat Yakubu ma ba a bar ta a baya ba wajen ƙoƙarin nuna tattalin arziki irin na al’ummar da ta fito daga cikinta, wato al’ummar Hausawa.

Idan aka duba cikin littafin Budurwar Zuciya za a ga yadda mahaifin Usman (wato Alhaji Aminu) ya buɗe masa shago domin gudanar da harkar kasuwanci kamar yadda aka bayyana cewa:

“….kwanan Asama’u bakwai a gidan aka buɗe wa Usman ƙaton shago, duk an cika masa shi da tasa. Daga nan arziki sai gaba yake yi, sai ma ya daina zama a kantin, sai yaransa yake bari, don shi yana zuwa ƙasashen kusa da mu saro kaya, kamar su Ghana da Togo. Ba dai ya zama a gida sosai. Bayan wannan shagon ma ya buɗe wasu.” (Yakubu, 1987: 4).

Buɗe ƙaton shago ga Usman ba ana nufin cewa da shagon a rufe yake ba, ana nufin sabon shago da aka buɗe domin gudanar da harkar kasuwanci. Ana so a bayyana cewa an zuba masa kaya domin gudanar da harkar saye da sayarwa. Sannan kuma an ambaci tasa domin a nuna nau’in kayan da ake sayarwa a cikin shagon. Haka nan kuma an ambaci kalmar kanti domin a fito da wani sunan da ake kiran shagon sayar da kaya. Haka zalika an ambaci ‘saro kaya’ domin a nuna cewa akan sayo kaya daga wasu wurare daban domin a sayar a ci riba.

 Idan aka duba wannan zance za a ga cewa mawallafiyar ta bayyana wa mai karatu irin tattalin arzikin al’ummar da take ciki. Kasancewar Kano gari ne na kasuwanci, sai mawallafiyar ta fito da harkar saye da sayarwa a cikin labarin domin ta nuna babbar hanyar tattalin arzikin al’ummar da ke garin Kano da kewaye. Mawallafiyar ta yi amfani da wannan dabara domin ta nuna cewa kasuwanci wani ɓangare ne na bunƙasa tattalin arziki a ƙasar Hausa.

Idan kuma aka duba cikin labarin Alhaki Kwikuyo Ne za a ga cewa an ƙara fito da wani nau’I na kasuwanci da ke bunƙasa tatalin arziki, kamar yadda aka bayyana cewa:

“Alhaji Abdu ɗan kasuwa ne, yana da jarinsa daidai gwargwado, kuma rumfarsa a nan kasuwar Sabon Gari take. Yana sayar da yadudduka, atamfofi da ‘yan kwalaye. Ba za dai a ce rumfar Alhaji Abdu a cike take da kaya tab ba, sai dai akwai kaya na sama da Naira dubu ɗari da ashirin a ciki.” (Yakubu, 1990: 1).

Kasuwanci sai da jari. Duk kasuwancin da ba jari, to akwai sauran zance a baya. An fito da wasu kalmomi kamar ‘jari’ da ‘rumfa’ da ‘kasuwa’ da ‘yadudduka’ da ‘atamfofi’ da kuma ‘yan kwalaye’ domin su ne suka haɗu suka gina irin kasuwancin da ake magana a kansa. Daga samun jari sai rumfa, sai kuma kayan da za a zuba ciki domin fara harkar saye da sayarwa. Wannan ya nuna cewa a wajen harkar kasuwanci, akwai nau’o’in kayan sayarwa daban-daban kamar yadda aka gani a cikin bayanan da suka gabata.

A ƙasar Hausa , harkar saye da sayarwa tana ɗaya daga cikin tsofaffin sana’o’in da ake da su. Wannan ya nuna cewa an yi amfani da sarrafa harshe a matsayin dabara ta bayar da labari domin nuna irin wannan tattalin arziki na al’ummar Hausawa.

Abin bai tsaya nan ba, sai da mawallafiyar ta ƙara nuna irin wani tattalin arziki na kasuwanci da ake da shi a cikin al’ummar da ta fito. Idan aka duba labarin cikin littafin Matar Uba Jaraba za a ga yadda aka sake fito da wani tattalin arzikin ta hanyar kasuwancin sayar da kayan koli. A cikin labarin an bayyana cewa mahaifin Ladidi ne sanadiyyar samun arzikin Sa’idu, wato bayan ya aurar masa da ita Ladidin, kamar yadda aka bayyana cewa:

“Ya kawo kuɗi wuri na gugar wuri har sule talatin ya ba shi, ya ce ya dinga bin sa Kano saro kayan koli. Da haka ya samu ya zama ɗan koli cikakke, duk ƙauyukan ƙasar in ana cin kasuwa zai je. Tun yana kasa kayansa a tabarma ranar kasuwa, har ya samu ya yi teburin katako a kasuwar, tafi-tafi sai ga shi da ginanniyar rumfa.” (Yakubu, 2006: 12).

An yi amfani da wani salon magana inda aka ce ‘wuri na gugar wuri’ domin a nuna yawan kuɗin ko adadinsu da aka ba wa Sa’idu a matsayin jari domin ya yi harkar kasuwanci. Wuri wani nau’i ne na kuɗi da aka taɓa amfani da shi domin harkar kasuwanci, wato a ba ka kaya, ka ba da wuri. Duk da cewa a yanzu ba a amfani da wuri a wajen cinikayya, amma sai aka kawo shi domin a nuna cewa yana da muhimmanci a ɓangaren tarihin tattalin arziki a wani lokaci da ya gabata.

A nan an kawo harkar saye da sayarwa, wato kasuwancin sayar da kayan koli. Sana’ar koli tana ɗaya daga cikin sana’o’in da Hausawa ke tinƙaho da su, domin sana’a ce da ke kawo riba mai dama. Domin a nuna irin ci gaban da aka samu a wannan harka ta kasuwancin, sai aka kawo zancen kasa kaya a tabarma da farko, sannan daga baya aka koma kasawa a kan teburin katako. Daga ƙarshe kuma da harkar ta ƙara bunƙasa, sai aka gina rumfa. Bahaushe kan ce “gaba-gaba ƙwaryar roro.”

A harkar kasuwanci, mata ma ba a bar su a baya ba. Wasu matan sukan yi kasuwanci ne domin su sami ɗan abin biyan buƙatunsu na cikin gida. Har ila yau a cikin littafin Matar Uba Jaraba, an bayyana yadda matan Sa’idu ke irin nasu harkokin kasuwancin, inda aka bayyana cewa:

“Daso na da ƙaton firji inda take sayar da zoɓo da ruwan sanyi, kullum za a cika manyan robobi a kai mata ƙofar rumfar Alhaji Sa’idu, a sayar mata da shi tas, a ƙirgo mata kuɗinta a kawo mata da yamma.” (Yakubu, 2006: 49-50).

Da ganin jerin sunayen abubuwan da aka ambata an san cewa abokan tafiyar juna ne, ko kuma a ce magani ne da abin haɗi. Kalmomin “firji” da ‘zoɓo’ da kuma ‘ruwan sanyi’ suna tafiya ne tare. Duk wanda zai yi kasuwancin sayar da zoɓo da ruwa, har ma da sauran kayan shaye-shaye sai ya haɗa da firji idan yana so harkar ta bunƙasa. Akan sanya irin waɗannan kayayyakin cikin firji domin ya ba da sanyi. Mutane sukan saya, su sha, musammamn ma lokacin zafi.

Idan aka sake duba cikin labarin Matar Uba Jaraba za a ga yadda aka ƙara fito da wata sana’ar mata da ke bunƙasa tattalin arziki, inda aka bayyana cewa:

“Farawar Ladidi ke da wuya sai ciniki ya tashi. Ba ta shekara da farawa ba, da tana da yaro ɗaya sai ga shi yaranta masu kai abinci Kwari su shida ne. Kowa da irin abin da yake sayarwa, mai ɗaukar taliya daban, sai mai ɗaukar doya da shinkafa, farfesun kayan ciki, soyayyar kaza da ƙwai.” (Yakubu, 2006: 50).

An yi amfani da wasu kalmomi da ke nuna wasu nau’o’in abinci daban-daban kamar ‘taliya’ da ‘doya’ da ‘shinkafa’ da ‘farfesun kayan ciki’ da ‘soyayyar kaza da ƙwai’ domin a nuna ire-iren abincin Hausawa da aka faye amfani da su a zamanin da muke ciki. Irin wannan sana’a takan taimaka wa matan da ke cikin gidajensu wajen bunƙasa tattalin arzikinsu. Saboda haka mata ma suna da rawar da suke takawa wajen kawo bunƙasar tattalin arziki a ƙasar Hausa. An ga irin kasuwancin da wasu matan aure ke yi a cikin gidajensu, kuma yakan taimaka musu wajen samun abin biyan ƙananan buƙatunsu na cikin gida ba tare da sun ɗora nauyinsu gaba ɗaya a kan maigida ba.

A taƙaice dai mawallafiyar ta yi amfani da wannan dabarar bayar da labari ta hanyar sarrafa harshe domin ta fito da wasu nau’o’in kasuwanci a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin bunƙasar tattalin arziki a ƙasar Hausa, musamman ma a garin Kano da kewayenta. Har ila yau kasancewar mawallafiyar ta tashi ne a wurin da ake harkar kasuwanci, sai harkar kasuwancin ta yi tasiri ainun a cikin rubuce-rubucenta da aka nazarta.

Sarrafa Harshe Domin Nuna Baƙin Al’adu

Al’umma takan ci gaba ta hanyar samun sauye-sauye na rayuwa a sakamakon cuɗanya da wasu baƙi. Irin waɗannan baƙi sukan bar matsuguninsu na asali, su koma wani saboda wasu dalilai. Sukan tafi tare da al’adunsu, sannan su yi cuɗanya da mazauna wurin da suka tarar. Wannan ya nuna cewa kowace al’umma ta duniya ba ta cika ta tumbatsa ta fuskar ci gaba sai tare da cuɗanya da wasu al’ummomi daban-daban. Irin wannan cuɗanya ta al’ummomi mabambanta al’adu takan haifar da gwamatsuwar al’adun. A sakamakon irin wannan cuɗanya ce ake samun gaurayar wasu baƙin al’adu na kusa ko na nesa a cikin al’ummar da aka tarar a wuri.

Mu’azu, (2013) ya bayyana baƙin al’adu da cewa:

“Idan aka ce baƙin al’adu na nesa, ana nufin al’adun al’ummomi waɗanda suka zo suka riski Hausawa daga uwa duniya mai nisa.” (Mu’azu, 2013: 52).

Wannan ya nuna cewa a sakamakon cuɗanya da aka samu tsakanin al’ummar Hausawa da baƙi, sai al’adun baƙin suka fara gauraya da na Hausawa, wanda ya haifar da kutsen da suka yi cikin rubuce-rubuce na ƙagaggun labaran Hausa da ake da su a wannan zamani.

Idan kuma aka duba cikin ƙamusun Hausa, (C.N.H.N. 1981: 32) an bayyana cewa:

“Tarihi ya nuna dukkan inda aka sami wata al’umma ta shigar wa wata al’umma, waɗanda tilas ne ya zamana al’adunsu sun sha bamban; to za ka taras al’adar al’ummar da ta fi ƙarfi ta yi tasiri a kan rarraunar. In ma ba an mai da hankali ba sai a wayi gari a tarar ƙaƙƙarfar ta mamaye rarraunar baki ɗaya.”

Saboda haka a duk inda aka sami al’adun al’ummomi mabambanta sun gauraya a wuri guda, to galibi wadda ta fi ƙarfi ita ce ke rinjaye a kan mai raunin. A irin wannan yanayi ne ake nuna wa mai karatu cewa al’ada mai ƙarfi takan iya mamaye wadda ba ta kai ta ƙarfi ba, ko da a wurin aka tarar da ita. Daga ƙarshe sai a wayi gari ba ita ba alamarta.

Idan aka duba cikin littafin Budurwar Zuciya za a ga yadda baƙin al’adu suka shigo cikin labarin kamar yadda aka bayyana cewa:

“Ummi da Hadiza kuwa, suka je, suka fece kwalliya. Ba su sa ma kayanmu na gargajiya ba, watau zani da riga ba. Ummi dai wani wando ta sa da ƙaramar riga. Kanta kuwa sai ta taje gashin kawai, kamar mai zuwa London. Ita kuwa Hadiza sai ta sa wata ‘yar riga, ko gwiwa ma ba ta rufe mata ba. Ga ɗankwali; amma sai ta ɗaura shi a wuya, kamar za ta shaƙe wuyan nata da shi. Kuma suka kawo wata irin hoda, suka shafa a ido da fuska.” (Yakubu, 1987: 45).

Abin lura a nan shi ne yadda aka ce “Ba su sa kayanmu na gargajiya ba….” To ai ka ga a nan ya nuna cewa sun yi amfani ne da kayan da ba na Bahaushiyar al’ada ba. Wannan ya nuna cewa an yi amfani da tufafin sanyawa da kayan kwalliya irin na matan Turawaba na matan Hausawa ba. Don haka a nan an shigar da baƙuwar al’ada ƙarara domin a nuna yadda wasu ‘yan mata Hausawa ke cin karensu ba babbaka a makaranta ko a gida idan suka zo hutu. Wani lokaci akan ga ‘yan mata na sanya tufafin da ba su dace ba a cikin makarantu, musamman a manyan makarantu. To, amma saboda “rashin mafaɗi, wai abin da ya sa ungulu cin kashi,” in ji Bahaushe, sai su riƙa yin abin da suka ga dama.

Har ila yau idan aka duba cikin littafin Matar Uba Jaraba za a ga nan ma yadda aka shigo da wata baƙuwar al’ada, wato yadda Aminu ya kama hannun Shola a gaban mahaifanta, kamar yadda aka bayyana cewa:

“A nan ubanta ya buɗe ƙofar gida ya ga Aminu a tsaye. Nan da nan ya kama Aminu ya rungume shi kamar ɗansa….Tana shigowa ya miƙe, ya kama hannunta. Za ta sa kuka sai ya girgiza mata kai, ya yi murmushi, ya zaunar da ita kusa da shi.” (Yakubu, 2006: 91-92).

Idan aka duba wannan bayani za a ga cewa a al’adar Bahaushe, abu ne mawuyaci a ce saurayi ya kama hannun budurwarsa, musamman ma a gaban iyayenta. To, amma sai ga shi an sami haka a lokacin da Aminu ya je gidan su Shola, yarinyar da yake so ya aura. To, ai ka ga a nan abin ya saɓa da al’adar Bahaushe. Ko da su iyayen abin bai saɓa da al’adarsu ba, to, ai shi ya kamata ya ji kunya saboda saɓa wa tasa al’adar. Don haka ake kallon al’amarin a matsayin baƙuwar al’ada. Wannan ya nuna cewa mawallafiyar ta sanya baƙuwar al’ada a cikin rubutunta na labarin cikin littafin domin ta nuna wa mai karatu cewa zaman Aminu a ƙasar Yarabawa ne ya haifar da haka. Wato ya ɗauki al’adar Yarabawa ya sanya ta cikin wani al’amarin rayuwarsa.

A taƙaice wannan ya nuna cewa lallai mawallafa littattafan ƙagaggun labaran Hausa sukan yi amfani da irin wannan dabara ta sarrafa harshe domin su nuna wasu baƙin al’adu da suka cuɗanya da na Hausawa. Marubutan sukan sanya baƙin al’adun ne a cikin rubuce-rubucensu domin su nuna wa mai karatu cewa Hausawa mutane ne da ba sa ƙyamar wasu al’ummomin da suka zo domin su zauna, kuma su yi cuɗanya ko mu’amala tare.

Kammalawa

Idan aka duba za a ga cewa a cikin binciken an kawo bayayanai dalla-dalla a kan yadda wasu masana da manazarta suka yi ta bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar salo da sarrafa harshe tare da nuna irin dangantakar da ke tsakaninsu. Sannan an ga yadda mawallafiyar ta yi amfani da dabarar sarrafa harshe domin yaɗa wasu abubuwa daban-daban da suka shafi rayuwar Bahaushe ta yau da kullum, kamar addini da al’ada da tattalin arziki da kuma yanayin zamantakewa. Sannan an ga yadda aka sanya baƙin al’adu a cikin rubuce-rubucen nata na ƙagaggun labaran Hausa.

Manazarta

Adamu, G. (2002), “A Stylistic Study of Hausa Classic Noɓels: Shaihu Umar, Ruwan Bagaja and Kitsen Rogo.” Ph.D Thesis. Kano: Bayero University.

Ahmad, A.A. (2013) “ Salon Sarrafa Harshe A Cikin Littattafan Zube Na Hausa: Nazari Daga Littafin Ruwan Bagaja.” Humanities in the Sub-Saharan World. Ruwan Bagaja in Perspectiɓes. Eight Decades of a Hausa Masterpiece in Prose (1933-2013). UNICAIRO/UMYUK Special Research in Humanities.

Akporobaro, F.B.0. (2012), Introduction to Fiction. Lagos: Princeton Publishing Co.

Buhari, I.M. (1988) “Nazarin Jigogin Wasu Ƙagaggun Labaran Hausa.” Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa Studies), Sashen Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Bunza, U.A. (2017) Cigaban Mai Ginar Rijiya: Nazarin Wasu Salailan Warwara Cikin Littattafan Zben Hausa. Maƙalar da aka gabatar a babban ɗakin taro na tsangayar Fasaha, Katsina: Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Nuwamba, 2017.

C.N.H.N. (1981) Rayuwar Hausawa. Ikeja Lagos: Thomas Nelson (Nigeria) Limited 8 Ilupeju Bye-Pass.

C.N.H.N. (2006), Ƙamusun Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Ɗan’amarya, I.A. (2012) Tarihi Da Gudunmawar Gasa A Samuwa Da Bunƙasa Ƙagaggun Labaran Hausa.” Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa Studies), Kano: Jami’ar Bayero.

Ɗangambo, A. (2007) Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Kano: K.D.G. Publishers.

Ɗangambo, A. (2008), Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari). Kano: K.D.G. Publishers.

Ɗan’iya, D. (1997)“Adon Harshe Cikin Rubutaccen Adabin Hausa.” Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa Studies), Kano: Jami’ar Bayero.

Gusau, S.M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Kano-Nigeria: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2015) Mazhabobin Ra’i Da Tarke A A dabi Na Hausa. Kano-Nigeria: Century Research and Publishing Limited.

Hassan, G. (2013) “Kamar Kumbo Kamar Kayanta: Tarsashin Mutuntakar Abubakar Imam A Littafin Ruwan Bagaja.” Humanities in the Sub-Saharan World. Ruwan Bagaja in Perspectiɓes. Eight Decades of a Hausa Masterpiece in Prose (1933-2013). UNICAIRO/UMYUK Special Research in Humanities.

Hornby, A.S. (1995), Oxford Advanced Learner’s Dictionary. London:   Oxford University Press.

Ibrahim, M.T. (2016) “Waiwaye Adon Tafiya: Kwatanta Wasu Al’adun Hausawa Na Haihuwa Jiya DaYau.” Lautai Journal of the School of Languages, Vol.4 No.2 Gumel: Jigawa State College of Education.

Idris, Y. (2013) “Sigogin Kwaikwayo A Cikin Littafin Ganɗoki.” Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 1, No. 5. Department of Nigerian Languages, Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.

Isa, S.I. (2009) “Bunƙasar Rubutattun Ƙagaggun Labaran Hausa: Tsokaci Kan Labaran Bilkisu Salisu Ahmed Funtuwa.” KundinDigiri na Uku (Ph.D Hausa Studies), Sashen Harsunan Nijeriya da na Afirka, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

 

Magaji, A. (1982) “Tasirin Adabin Baka A Kan Rubutattun Ƙagaggun Labarai.” Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa Studies), Sashen Harsunan Nijeriya, Kano: jami’ar Bayero.

Maimota, A.S. (2010) “Kwatanta Wasu Dabarun Bayar Da Labari A Tauraruwar Hamada.” Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa Studies), Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Mu’azu, A. (2013) Baƙin Al’adu A Ƙagaggun Littaffan Soyayya Na Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Mukhtar, I. (1990) “A Stylistic Study of Sulaiman Ibrahim Katsina’s Hausa Novels.” Ph.D Thesis, Kano: Bayero University.

Mukhtar, I. (2004), Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai (Tsari na biyu). Kano: Benchmark Publishers Limited.

Mukhtar, I. (2010), Introduction to Stylistic Theories, Practice and Criticisms. Revised Edition. Usman Al’amin Publishers.

Tsoho, M.Y. (2013) “Salo Dokin Adabi: Nazari A Kan Barkwanci A Littafin Ruwan Bagaja.” Humanities in the Sub-Saharan World. Ruwan Bagaja in Perspectives. Eight Decades of a Hausa Masterpiece in Prose (1933-2013). UNICAIRO/UMYUK Special Research in Humanities.

The New Encyclopedia Britannica, Vol IX. Inc. William Benton, Publisher, 1943-1973.

Umar, A. (1981) “Taƙaitaccen Tarihin Hausa.” Hausa Language, Literature and Culture (The Second Hausa International Conference). Kano: Jami’ar Bayero.

Umar, M.B. (1987) Dangantakar Adabin Baka Da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph Publishing Company.

Yahaya, I.Y. da Ɗangambo, A. (1986) Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Yahaya, U. (2004), Sigogin Bayar Da Labari: Kamar Yadda Aka Yi A Kan Littattafan Amadi Na Malam Amah Da Tauraruwar Hamada. Kundin digiri na biyu (M.A. Hausa Studies). Sashen Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Yahaya, U. (2010), “Magana A Cikin Labari: Tsokaci A Kan Littafin Nagari Na Kowa, Na Jabiru Abdullahi.” Wazobia, A Journal Of Hausa Studies, Vol. 5, No. 1. Kano: Federal College of Education.

Yakubu, B.R. (1987), Budurwar Zuciya. Zaria: Gaskiya Corporation Limited.

Yakubu, B.R. (1990), Alhaki Kuykuyo Ne. Zaria: Gaskiya Corporation Limited.

Yakubu, B.R. (2006), Matar Uba Jaraba. Kano: Ramat General Enterprises.

Download the article:

Post a Comment

0 Comments