Abu ne sananne cewa; Salaf sun yi Ijma’i a kan haramcin tawaye wa shugaba fasiki. Rashin yin tawayen shi ne Mazhabar Salaf Ahlus Sunna, da Akidarsu da suka hadu a kanta, har hakan ya zama daga cikin “usul” na Mazhabar Ahlus Sunna, wato ginshikin da duk wanda ya saba ya fita daga cikin Ahlus Sunna ya zama dan bidi’a. Saboda babu wadanda suka saba a wannar mas’ala sai ‘yan bidi’a; Khawarijawa da Mu’utazila d.s.
To ganin haka ya sa kungiyoyin zamani ‘yan siyasa, kamar
Kungiyar Ikhwan da rassanta, suke ta kwakwule-kwakwale da laluben neman
shubuhohi da za su halasta ma kawunansu fada da shugabanni da gomnatoci a
kasashensu. Sun yi kwashe-kwashe, sun tara shubuhohi a kan haka, sun zo suna
kafa hujja da su a kan halascin tawaye wa shugaba Musulmi fasiki.
To babbar shubuharsu ita ce: sukar Ijma’in da aka hakaito
daga Salaf, ta hanyar nuna cewa; lallai akwai wadanda suka saba wannan Ijma’i
cikin Salaf.
Don haka babbar shubuharsu na sukar Ijma’in shi ne raya
cewa: Hussain (ra) da Abdullahi bn Zubair (ra) sun yi tawaye wa Yazidu, Ibnu
Zubair ya cigaba da tawaye har zamanin Abdulmalik bn Marwan.
To wannan ya sa za mu yi nazari a kan wannan batu, ta
fiskoki kamar haka:
1- Menene tawayen?
2- Shin ya tabbata Hussain (ra) ya yi tawaye?
3- Shin ya tabbata Ibnu Zubair (ra) ya yi tawaye?
4- Tawayen wasu cikin Tabi’ai da Malamai masu falala a yakin
Madina, da fitinar Ibnul Ash’ath d.s.
Ta hanyar amsa wadannan tambayoyi ne kadai za mu fahimci
hakikanin abin da ya faru a zamanin magabata.
Tambaya ta farko: Menene tawayen?
Tawaye wa shugaba, wanda yinsa yake fitar da mutum daga
Sunna, ya zama dan bidi’a shi ne wanda ya hada abubuwa guda biyu:
1) Mulki ya tabbata a hanun shugaba, wanda masu ruwa da
tsaki suka yi masa bai’a.
Imamu Ahmad ya ce:
"والسمع والطاعة للأئمة وأمير المؤمنين البر
والفاجر ممن ولي الخلافة، واجتمع الناس عليه ورضوا به".
طبقات
الحنابلة (1/ 244)، شرح أصول اعتقاد أهل السنة والجماعة (1/ 180)
Shaikhul Islam ya ce:
"ولا يصير الرجل إماما حتى يوافقه أهل الشوكة
عليها الذين يحصل بطاعتهم له مقصود الإمامة".
منهاج
السنة النبوية (1/ 527)
2) Daukar makami a tawayen don yakar shugaba. Imamu Ahmad ya
ce:
"والصبر تحت لواء السلطان على ما كان فيه من
عدل أو جور، وأن لا نخرج على الأمراء بالسيف وإن جاروا".
طبقات
الحنابلة (1/ 130)
Saboda haka dan tawaye shi ne wanda ya dauki makami ya yi
tawaye wa shugaban da mulki ya tabbata a hanunsa, masu ruwa da tsaki suka yi
masa bai’a, ya zama shi ne mai iko da garuruwan da suke karkashinsa.
Ko kuma idan ya yi bai’a wa shugaba, sai kuma ya warware
bai’ar, ya fita daga da’a, don ya raba kan al’umma.
Saboda haka ba za a ce wani Sahabi ya yi tawaye ma wani
shugaba ba, har sai wadannan abubuwa guda biyu sun tabbata.
To sai mu isa kan tambaya ta biyu:
Shin ya tabbata Hussain (ra) ya yi tawaye?
Za mu amsa wannar tambaya da wadannan abubuwa masu zuwa:
1- Hussaini (ra) bai yi bai’a wa Yazeedu ba:
Lallai ya tabbata cewa; Yazeedu ya aika wa mutanen Madina
wasika don su yi masa bai’a, Sahabbai ‘ya’yan Sahabbai da suke raye a lokacin
duk sun yi masa bai’a, irin su Ibnu Umar (ra), Ibnu Abbas (ra), da kuma
Muhammad bn Hanafiyya (r). Amma Hussain (ra) da Abdullahi bn Zubair (ra) ba su
yi masa bai’a ba. Al-Balazariy ya ruwaito cewa:
"فلما توفي معاوية - رحمه الله - للنصف من رجب
سنة ستين وولي يزيد بن معاوية الأمر بعده، كتب يزيد إلى عامله الوليد بن عتبه بن أبي
سفيان، في أخذ البيعة على الحسين وعبد الله بن عمر، وعبد الله بن الزبير، فدافع الحسين
بالبيعة ثم شخص إلى مكة".
أنساب
الأشراف للبلاذري (3/ 155)، الطبقات الكبرى (1/ 442)، تاريخ خليفة بن خياط (ص: 232
- 233)
Shi Hussain (ra) yana ganin cewa: bayan Mu’awiya (ra) shi ya
fi cancantar Khalifanci. Wannan ya sa ya ki yin bai’a wa Yazeedu.
Saboda haka asali Hussain (ra) bai yi Bai’a wa Yazeedu ba,
balle a ce ya yi tawaye ya warware Bai’a.
2- Mulkin Yazeedu dukkan mutane ba su shiga karkashinsa a
Hijaz ba:
A wannan lokacin al’amarin mulki a Hijaz bai tabbata wa
Yazeedu ba, shi ya sa Ibnu Umar da ya hadu da su (Hussain da Ibnu Zubair) a kan
hanyar Makka, sai ya yi musu Nasiha. Ibnu Sa’ad ya ruwaito cewa:
"ولقيهما عبد الله بن عمر وعبد الله بن عياش
بن أبي ربيعة بالأبواء منصرفين من العمرة. فقال لهما ابن عمر: أذكركما الله إلا رجعتما
فدخلتما في صالح ما يدخل فيه الناس، وتنظرا؛ فإن اجتمع الناس عليه لم تشذا، وإن افترق
عليه كان الذي تريدان".
الطبقات
الكبرى (1/ 444)
A ciki sai yake cewa: “…Ku bari a gani, idan mutane suka
yarda da mulkinsa kar ku yi ware, idan kuma mutane ba su goyi bayansa ba shi
kenan za ku samu abin da kuke so”.
Haka kuma har ya Yazeedu ya mutu, haka wadanda suka biyo
bayansa, mulkinsu bai yi karfi a Hijaaz ba, sai da Abdulmalik bn Marwan ya zama
khalifa. Shi ya sa khalifancin Ibnu Zubair (ra) ya fi karfi a Hijaz.
3- Mulkin Yazeedu dukkan mutane ba su shiga karkashinsa a
Iraqi ba:
Haka Mutanen Kufa sun aika wa Hussaini (ra) cewa; su fa ba
su da shugaba, don haka ya zo su yi masa bai’a. Daga cikin abin da suka rubuta
masa akwai cewa:
"...وليس علينا إمام، فاقدم علينا لعل الله يجمعنا
بك على الحق. واعلم أن النعمان بن بشير في قصر الإمارة، ولسنا نجمع معه جمعة، ولا نخرج
معه إلى عيد، ولو بلغنا إقبالك إلينا أخرجناه فألحقناه بالشام. والسلام".
تاريخ
الطبري (5/ 352)، أنساب الأشراف للبلاذري (3/ 157 - 158)
Sai suka bayyana masa cewa; ba su da shugaba. Suka nuna masa
cewa; Gomnan Yazeedu, wato Nu’uman bn Basheer (ra) ba shi da wani tasiri, ba
shi da wani iko na shugabanci. Ba ya jagorantar Juma’a balle Eidi.
Shi ma Hussain (ra) sai ya yi musu wasika, a ciki ya nuna
cewa; zai zo ne saboda sun ce: BA SU DA SHUGABA. Ga wasikar tasa kamar haka:
"بسم الله الرحمن الرحيم، من حسين بن علي إلى
الملإ من المؤمنين والمسلمين، أما بعد، فإن هانئا وسعيدا قدما علي بكتبكم، وكانا آخر
من قدم علي من رسلكم، وقد فهمت كل الذي اقتصصتم وذكرتم، ومقالة جلكم: إنه ليس علينا
إمام، فأقبل لعل الله أن يجمعنا بك على الهدى والحق وقد بعثت إليكم أخي وابن عمى وثقتي
من أهل بيتي، وأمرته أن يكتب إلي بحالكم وأمركم ورأيكم، فإن كتب إلي أنه قد أجمع رأي
ملئكم وذوي الفضل والحجى منكم على مثل ما قدمت علي به رسلكم، وقرأت في كتبكم، أقدم
عليكم وشيكا إن شاء الله، فلعمري ما الإمام إلا العامل بالكتاب، والآخذ بالقسط، والدائن
بالحق، والحابس نفسه على ذات الله. والسلام".
تاريخ
الطبري (5/ 353)
Don haka Hussain (ra) bai fara tunanin fita zuwa ga Kufa ba
sai da suka tabbatar masa cewa ba su da shugaba. Wannan yake nuna ashe mulkin
Yazeed a Kufa bai yi karfi ba.
4- Taraju’in Hussain (ra) daga tafiya zuwa Kufa:
Asali da ma Hussaini (ra) ya nufi zuwa Kufa ne don suna so
ya zo ya shugabance su, don ba su yarda da shugabancin Yazeedu ba. Amma da ya
ga ha’incinsu, sai ya fara Taraju’i. Wannan Taraju’i nasa kashi biyu ne:
A- Taraju’insa bayan kashe Muslim bn Aqeel:
A lokacin da labarin kisan Muslim bn Aqeel ya same shi sai
ya yi niyyar fasawa, zai koma Madina:
"وبلغ الحسين قتل مسلم وهانئ فقال له ابنه علي
الأكبر: يا أبه ارجع فإنهم أهل..... وغدرتهم وقلة وفائهم ولا يفون لك بشيء. فقالت بنو
عقيل لحسين: ليس هذا بحين رجوع. وحرضوه على المضي. فقال حسين لأصحابه: قد ترون ما يأتينا
وما أرى القوم إلا سيخذلوننا فمن أحب أن يرجع فليرجع. فانصرف عنه من صاروا إليه في
طريقه وبقي في أصحابه الذين خرجوا معه من مكة ونفير قليل من صحبه في الطريق".
الطبقات
الكبرى - متمم الصحابة (1/ 463)
Al-Maqdisiy ya ce:
"ولما بلغ الحسين قتل مسلم بن عقيل هم بالرجوع
إلى المدينة".
البدء
والتاريخ (6/ 10)
Ibnul Jauziy ya ce:
"قال علماء السير: لما علم الحسين، بما جرى لمسلم
بن عقيل هم أن يرجع، فقال أخو مسلم: والله لا ترجع حتى نصيب بثأرنا. فقال الحسين: لا
خير في الحياة بعدكم. فسار فلقيته أوائل خيل عبيد الله، فنزل كربلاء، فضرب أبنيته،
وكان أصحابه خمسة وأربعين فارسا ومائة راجل".
المنتظم
في تاريخ الملوك والأمم (5/ 329)
Wannan ya sa bayan kashe Muslim bn Aqeel sai Hussain (ra) ya
sallami magoya bayansa wadanda suka hadu da shi a hanya suka biyo shi, duk don
nuna ya fasa neman khalifancin.
"بسم الله الرحمن الرحيم أما بعد، فإنه قد أتانا
خبر فظيع، قتل مسلم ابن عقيل وهانئ بن عروة وعبد الله بن بقطر، وقد خذلتنا شيعتنا،
فمن أحب منكم الانصراف فلينصرف، ليس عليه منا ذمام.
قال:
فتفرق الناس عنه تفرقا، فأخذوا يمينا وشمالا حتى بقي في أصحابه الذين جاءوا معه من
المدينة".
تاريخ
الطبري (5/ 398 - 399)
B- Taraju'in Hussain (ra) a haduwarsa da Hurr bn Yazeed al-Bu'iy, wanda aka aiko
shi don ya tafi da shi zuwa Kufa wajen Ibnu Ziyad:
"...قال له الحسين: فما تريد؟ قال الحر: أريد والله
أن أنطلق بك إلى عبيد الله بن زياد، قال له الحسين: إذن والله لا أتبعك، فقال له الحر:
إذن والله
لا أدعك، فترادا القول ثلاث مرات، ولما كثر الكلام بينهما قال له الحر: إني لم أومر
بقتالك، وإنما أمرت الا أفارقك حتى أقدمك الكوفة، فإذا أبيت فخذ طريقا لا تدخلك الكوفة،
ولا تردك إلى المدينة، تكون بيني وبينك نصفا حتى أكتب إلى ابن زياد، وتكتب أنت الى
يزيد ابن معاوية إن أردت أن تكتب إليه، أو إلى عبيد الله بن زياد إن شئت، فلعل الله
إلى ذاك أن يأتي بأمر يرزقني فيه العافية من أن أبتلى بشيء من امرك، قال: فخذ هاهنا
فتياسر عن طريق العذيب والقادسية، وبينه وبين العذيب ثمانية وثلاثون ميلا ثم إن الحسين
سار في أصحابه والحر يسايره".
تاريخ
الطبري (5/ 402 - 403)، أنساب الأشراف للبلاذري (3/ 170)، الطبقات الكبرى - متمم الصحابة
(1/ 463 - 464)
A karshe dai sai Hussain (ra) ya fasa zuwa Kufa, kuma ya
fasa komawa Madina. Abin da yake nuni ga cewa: ya fasa kudurinsa na khalifanci
a Kufa.
C- Taraju'in Hussain (ra) a Karbala:
Hatta a Karbala Hussain (ra) ya yi Taraju’i, inda ya ba su
zabin abubuwa uku: Imma su bar shi ya koma Madina, ko su bar shi ya tafi wajen
Yazeedu, ko su bar shi ya tafi kan iyaka wajen Jihadi. Ga maganar Hussain (ra)
kamar haka:
"إنه قال: اختاروا مني خصالا ثلاثا: إما أن أرجع
إلى المكان الذي أقبلت منه، وإما أن أضع يدي في يد يزيد بن معاوية فيرى فيما بيني وبينه
رأيه، وإما أن تسيروني إلى أي ثغر من ثغور المسلمين شئتم، فأكون رجلا من أهله، لي ما
لهم وعلي ما عليهم".
تاريخ
الطبري (5/ 413)، تاريخ دمشق لابن عساكر (45/ 51)، أنساب الأشراف للبلاذري
(3/ 182)
Don haka wannan shi yake tabbatar da cewa; hatta abin da
Hussain (ra) ya fito yi na a nada shi Khalifa a Kufa, ya yi Taraju'i, saboda da
ma mutanen Kufan sun ce masa ne ba su da shugaba, ya zo ya shugabance su. Sai
da ya zo ya akasin abin da ya yi zato.
To ka ga ashe saboda wadannan dalilai babu yadda za a yi a
siffanta Hussain (ra) da Tawaye wa shugaba. Saboda da ma asali bai yi bai'a ba,
kuma mulkin Yazeedu ba shi da karfi a yanki na Hijaz, da kuma Kufa inda mutanen
Kufan - jama'ar Babansa da dan'uwansa - suka nemi ya je ya shugabance su.
Kuma hatta wannan din daga karshe ya yi Taraju'i.
6- Ra'ayin Ahlus Sunna game da jingina Tawaye ga Hussain
(ra):
Game da jingina Tawaye wa Hussain (ra) mutane sun kasu kashi
uku:
1) Masu cewa ya yi Tawaye, kuma hakan dadai ne, don shi ne
shugaba na gaskiya. Wannan shi ne ra'ayin Rafidha 'yan Shi'a, da wadanda suka
dace da su a kan haka.
2) Masu cewa ya yi Tawaye, shi dan tawaye ne, wanda ya saba
Hadisai da suka hani a kan tawayen, don haka kashe shi da aka yi daidai ne.
Wannan shi ne ra'ayin Nasibawa makiya Ahlul Baiti cikin Banu Umayya.
3) Masu cewa Hussaini (ra) bai yi Tawaye ba, shi ba dan
tawaye ba ne, kuma ba shi ne shugaba ba, kuma an kashe shi ne bisa zalunci.
Wannan shi ne Mazhabar Ahlus Sunnati wal Jama'a.
Shaikhul Islami ya yi bayanin wadannan ra'ayoyi inda ya ce:
"وصار الناس في قتل الحسين - رضي الله عنه -
ثلاثة أصناف: طرفين ووسطا.
أحد الطرفين
يقول: إنه قتل بحق، فإنه أراد أن يشق عصا المسلمين ويفرق الجماعة.
وقد ثبت
في الصحيح عن النبي - صلى الله عليه وسلم - أنه قال: «من جاءكم وأمركم على رجل واحد
يريد أن يفرق جماعتكم فاقتلوه». قالوا: والحسين جاء وأمر المسلمين على رجل واحد، فأراد
أن يفرق جماعتهم. وقال بعض هؤلاء: هو أول خارج خرج في الإسلام على ولاة الأمر.
والطرف
الآخر قالوا: بل كان هو الإمام الواجب طاعته، الذي لا ينفذ أمر من أمور الإيمان إلا
به، ولا تصلى جماعة ولا جمعة إلا خلف من يوليه، ولا يجاهد عدو إلا بإذنه، ونحو ذلك.
وأما
الوسط فهم أهل السنة، الذين لا يقولون لا هذا ولا هذا، بل يقولون: قتل مظلوما شهيدا،
ولم يكن متوليا لأمر الأمة. والحديث المذكور لا يتناوله، فإنه لما بلغه ما فعل بابن
عمه مسلم بن عقيل ترك طلب الأمر، وطلب أن يذهب إلى يزيد ابن عمه، أو إلى الثغر، أو
إلى بلده، فلم يمكنوه، وطلبوا منه أن يستأسر لهم، وهذا لم يكن واجبا عليه".
منهاج
السنة النبوية (4/ 553 - 554)
Kuma ya ce:
"فهذا الغلو الزائد يقابل بغلو الناصبة، الذين
يزعمون أن الحسين كان خارجيا، وأنه كان يجوز قتله، لقول النبي - صلى الله عليه وسلم
-: «من أتاكم وأمركم على رجل واحد يريد أن يفرق جماعتكم، فاضربوا عنقه بالسيف كائنا
من كان» رواه مسلم.
وأهل
السنة والجماعة يردون غلو هؤلاء وهؤلاء، ويقولون: إن الحسين قتل مظلوما شهيدا، وإن
الذين قتلوه كانوا ظالمين معتدين. وأحاديث النبي - صلى الله عليه وسلم - التي يأمر
فيها بقتال المفارق للجماعة لم تتناوله، فإنه - رضي الله عنه - لم يفرق الجماعة، ولم
يقتل إلا وهو طالب للرجوع إلى بلده، أو إلى الثغر، أو إلى يزيد، داخلا في الجماعة،
معرضا عن تفريق الأمة. ولو كان طالب ذلك أقل الناس لوجب إجابته إلى ذلك، فكيف لا تجب
إجابة الحسين إلى ذلك؟ ! ولو كان الطالب لهذه الأمور من هو دون الحسين لم يجز حبسه
ولا إمساكه، فضلا عن أسره وقتله".
منهاج
السنة النبوية (4/ 585 - 586)
Saboda haka Mazhabar Ahlus Sunna ita ce: Hussaini (ra) bai
yi tawaye ba, kama bai raba kan mutane ba.
To da wannan za ka san cewa; jingina wa Hussaini (ra) tawaye
kuskure ne. Kuskure ne wanda Malamai da ya yawa sun afka cikinsa, suke danganta
masa tawaye wa shugaba, har Khawarijawan zamani da 'yan Ikhwan da Sururiyya
suke kafa hujja da shi, suke warware Ijma'in Salaf, suke rusa Akidar Ahlus
Sunna, suke halasta tawaye wa shugaba fasiki, suke janyo bala'i wa al'umma.
✍️ Dr Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.