Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Diyan Wakokin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari Daga Wakar Turakin Kano Alhaji Ahmadu

    Citation: Abdu, A.M. (2024). Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Saidu Faru: Nazari DagaWaƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 250-254. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.032.

    Turken Zuga da Yabo a Zubin Wasu Ɗiyan Waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru: Nazari Daga Waƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu

    Daga

    Amina Mbaruma Abdu Ph.D
    Sashen Koyar da Ilimin Firamare
    Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Fasaha), Potiskum, Jihar Yobe
    08031319789
    aminambaruma@gmail.com

    Tsakure

    Babbar manufar wannan takarda ita ce fayyace yanayin turken zuga da yabo a waƙar Turakin Kano. Don haka zuga ko yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, musamman ma, makaɗan fada. Ra’in da aka yi amfani da shi wajen ɗora wannan bincike, an gudanar da shi bisa kwatance kawai, an yi ƙoƙarin fito da ɗiyan waƙoƙin da suka dace da binciken ne, sannan aka yi sharhi a kansu ta yadda za fito da ma’anar da suke ɗauke da ita, wadda ta dace da binciken. Wannan bincike an gudanar da shi ta hanyar nazarta waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru waɗanda aka rubuta su a wasu littattafai da kundayen bincike da aka gabatar a matakai daban-daban, sai dai binciken ya taƙaita ne ga waƙa guda ɗaya ta Alhaji Ahmadu Turakin Kano. A wajen kawo ɗiyan waƙar da aka yi magana a kan su, an cire gindin waƙar sannan aka yi sharhi kan manufar gindin waƙar. Dukkanin ɗiyoyin da aka kawo an juya su ne kamar yadda aka rubuta su a littattafan da aka yi nazari a cikinsu. Takardar ta gano Alhaji Sa’idu Faru yakan yabi duk wani wanda ya yi masa alkhairi ko aka yi masa alkhairi saboda shi. Haka kuma an gano irin zuga da yake yi wa wanda ya zaɓi ya yi masa waƙa, yakan nuna hazaƙarsa da bajintarsa da fasaharsa wajen kwarzanta da zuga duk abin da ya so ya yi wa waƙa. Takardar ta yi ƙoƙarin sharhanta wasu daga cikin ɗiyan da ya bayyana zuga da yabo a cikinsu.

    Gabatarwa

    Zuga da yabo wasu abubuwa ne daga cikin turakun waƙoƙin baka, musamman waƙoƙin baka na Hausawa. Zuga tana da tasiri akan dukkan wani babba ko mai sarauta, musamman na gargajiya, domin ko yaya aka yi wa mutum sai yaji daɗi kuma ya nuna gamsuwarsa. Yabo kuwa yana taka muhimmiyar rawa wajen fito da turken waƙa da ma nuna inda waƙa ta sa gaba. Makaɗa, musamman na fada sukan ɗauki zuga da yabo da muhimmanci wajen wasa mai gidansu. Wasu lokutan makaɗa sukan zuga ko yaba wasu da ba sarakuna ba kamar attajirai ko wasu haziƙai ko zaƙaƙuran mutane da suke taimakawa al’umma, musamman waɗanda suke tare da su. Haka kuma, wasu sukan yi ma wasu masoya ko makusanta waɗanda suka yi wa waƙoƙinsu nuna irin alaƙar da take tsakanin su da kuma irin bajintar da mukusantan suka yi domin wanda ake yi wa waƙa. A wannan takarda an bibiyi yadda Makaɗa Sa’idu Faru ya baje fasaha wajen zugawa tare da yaba Turakin Kano da fito da matsayinsa da martabarsa a wajen al’ummarsa. Haka kuma waƙar ta fito da tarin abubuwan ci gaban rayuwa da garin Kano yake da su wanda ya tsere sauran jihohin ƙasar nan.

    Turke shi ne manufar da take cikin waƙar da akan isar zuwa ga masu sauraro, haka kuma turke yana nufin jigo a rubutacciyar waƙa. Turke a ƙa’idar masu nazarin waƙar baka na nufin saƙon da waƙa take ɗauke da shi. Idan an ce saƙo kuma ana magana ne kan manufa da ta ratsa waƙa tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kansa ba. Ashe ke nan saƙon da makaɗi yakan zaɓa ya gina waƙarsa, ya tauye kansa da kansa ya zuba ɗiyanta bisa wasu zaɓaɓɓun kalmomi da za su doshi wata babbar manufa ɗaya, shi ne ake kira turke (Gusau, 2008:370).

    Turken waƙar baka shi ne saƙon da aka gina ko ɗaure waƙa a jikunsa aka tsayar da ita da shi. Manazarta waƙar baka sun bayyana ma’anar turke da cewa shi ne saƙon da waƙa take ɗauke da shi (Gusau, 2003). Anan saƙo ana nufin manufar da ta sa aka ƙera wannan waƙa a kanta, kuma wannan manufa ta ratsa waƙar tun daga farko har ƙarshenta. Makaɗa da mawaƙan baka na Hausa sukan shirya waƙoƙi da dama a bisa mabambanta turaku, kamar turken zuga da yabo ko ta’aziyya. Wasu lokuta kuma sukan surka turaku guda biyu a waƙa guda biyu a waƙa guda, kamar turken zuga da na yabo. Kowanne ɗaya daga cikin turakun ya keɓanta da wasu tubalai da ake amfani da su wajen wajen gina shi, (Sani & Aliyu, 2018).

    Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Sa’idu Faru

    An haifi makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru da ke ƙasar Maradun, ƙaramar Hukumar Talatar Mafara a wajejen shekara ta 1932. Ana yi masa laƙabi da “Ɗan’umma” wanda matar ƙanen mahaifinsa ta sanya masa, saboda ba ya faɗin sunanta, sai dai yana kiran ta Umma, amma wannan laƙabi bai shahara a tsakanin mutane ba, balle ya danne sunansa na yanka watau Sa’idu. Shi kansa Sa’idu Faru yakan yi wa kan shi kirari yana cewa:

    Ɗan Umma rungumi

    Ɗan Tumba rungumi

    Sunan mahaifinsa makaɗa Abubukar ɗan Abdu, shi kuwa makaɗa Abdu, Alu mai kurya ya haife shi. Don haka nasabarsa ita ce Sa’idu ɗan Abubakar ɗan Abdu da Alu mai kurya. Dukkan waɗannan makaɗa an yi su ne a garin Faru, sai dai mahaifiyarsa mutumiyar Banga ne ta cikin ƙasar Ƙaura-Namoda. Makaɗa Sa’idu Faru bai samu ilimin Muhammadiyya da yawa ba, sai dai an sa shi makarantar allo in da ya yi zurfi ga karatun Alƙur’ani mai tsarki, haka kuma ba a sa shi makarantar boko ba. Alal haƙiƙa tun yana yaro sha’anin kiɗa da waƙa ya ɗauke masa hankali.

    Makaɗa Saidu Faru ya koyi waƙa ne a wajen mahaifinsa makaɗa Abubakar, waƙoƙinsa suka daɗa kyautatuwa ta hanyar fasaha da hikima tare da ƙwaƙwalwar da Allah ya ba shi. Tun ya na da shekaru goma aka fara zuwa yawon kiɗa da shi gari-gari. Bayan ya ɗan tasa ya fara yin waƙar kan sa a lokacin yana da shekaru goma sha shida, ya fara da wata waƙa da take cewa:

    Gindin waƙar: Bi da maza ɗan Joɗi na Iro

    : Iro magajin Shehu da Bello.

    (Gusau, 1996:119).

    Daga nan Sa’idu Faru ya ci gaba da yi wa sarakuna da ‘ya’yan sarakuna waƙoƙi, har zuwa lokacin da ya sadu da Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar. Makaɗa Sa’idu Faru yana da matan aure uku tare da ‘ya’ya maza da mata da jikoki masu yawa.

     

    Yanayin Turken Zuga da Yabo a Waƙar Turakin Kano Alhaji Ahmadu

    Makaɗa Sa’idu faru kan yi amfani da hikima da dabara wajen yin zuga da yabo tare da kwarzanta iyayen gidansa da kuma mutanen da suka yi masa wata kyauta ta bajinta ko makamancin haka a rayuwarsa. Har ila yau yana amfani da ƙwarewa ta fuskoki daban-daban domin yabo da zuga ga wanda ya so. Haƙiƙa makaɗa Sa’idu Faru ya waƙe Turakin Kano tare da bayyana nasarorin da ya cimma a rayuwarsa.

    Turken Zuga

    Zuga dabara ce ta ɗaukaka abu sama wadda ta ƙunshi wasu kalmomi da ake amfani da su a koɗa mutum a cicciɓa shi a nuna fifikonsa a kan wasu. (Muhammad, 2015:395). Zuga takan tsuma mutum ta sa masa kuzari da ƙwarin gwiwa.

    Kalmar “zuga” tana iya ɗaukar ma’anar koɗa mutum, ko wasa shi, ko ingiza shi ya yi wata bajinta, ko ma ya yi wani abin da yafi ƙarfinsa don ya burge wanda yake sa shi. Zuga na sa mutum in ya saurare ta, ya ji ta, to ya yi Imani da abin da aka ce kuma ya aikata abin da aka ce.

    Makaɗa Alhaji Sa’idu Faru ya buɗe wannan waƙa ta Turakin Kano Alhaji Ahmadu ne da nuna zuga watau gidin waƙar ma zuga ta fara da shi domin ya saka masa ƙaimi ga Turaki tare da zaburar da masu sauraron waƙar don su san ƙima da darajar wanda ake yi wa waƙar, ga abin makaɗa Sa’idu faru yake cewa:

    Mai waƙa: Turakin Kano Alhaji Ahmadu

    G/W: Tsakin tama na abashe,

    : Ana shakka haye ma Amadu

    Jagora: Toron giwa ba togewa ɗ2

    ‘Y/Amshi: Ɗan Hashim ƙanen Sarkin Kano.

    (Gusau, 2009, sh.161)

    A nan ya nuna daraja da kwarjini na Turakin Kano don wasu na shakkar tunkararsa saboda ƙimarsa da daraja ta gidan sarauta. Shi ya sa ya kwatanta shi da toron giwa, mai tunkararsa sai ya shirya, sannan ya bayyana alaƙarsa da sarkin Kano watau ƙani yake gare shi. Watau ba wai kawai sarauta ce ta haɗa su ba, a a ɗanuwan sarki ne na jini sannan babban ɗan kasuwa ne a garin Kano haka kuma mai faɗa a ji ne a fada shi ya sa makaɗa ya zuga shi da cewa: ana shakka haye maka.

    Haka kuma, wannan ɗiyan da ke tafe ya bayyana irin iko da mulki da Turaki yake da shi a fadar sarkin Kano da nuna cewa duk abinda ba na Turaki ba ne ƙarya ake yi, inda ya ke zuga shi da cewa:

    Jagora: Sa’idu faru ka waƙa iko

    ‘Y/Amshi: Komi kaj jiya ƙarya akai

    Jagora: Sa’idu faru ka waƙam mulki

    ‘Y/Amshi: Komi kaj jiya ƙarya a kai

    (Gusau, 2009, sh.162)

    Ana ya bayyana kan sa da cewa shi ne da kansa yake yi wa Turaki waƙa ba saƙo ba, don nuna girmansa da martabar wannan waƙa ta shi, ya ƙara kwarzanta kan sa da cewa waƙar mulki yake yi wa mai mulki, watau ba ɗan haye ba ko ɗan karere, ya ƙara da cewa komai kaj jiya ƙarya akai. Watau waƙa idan ba ta Turaki ba ne ba za a kamanta shi da na Turaki ba.

    Har wa yau akwai wasu ɗiyan da makaɗa Sa’idu faru ya sake fito da martabar Turaki da bayyana irin matsayinsa wurin al’umma. A in da yake cewa:

    Jagora: Toron giwa ba togewa

    ‘Y/Amshi: Ɗan Hashim ƙanen sarkin Kano

    Jagora: Toron giwa ƙi fasawa

    ‘Y/Amshi: Ɗan Hashim ƙanen sarkin Kano

    Jagora: Turakin Tama na Abashe

    ‘Y/Amshi: Ana shakkah haye ma Amadu,

    : Mai daraja na wambai,

    : Ɗan Hashim ƙanen sarkin Kano

    (Gusau, 2009, sh.161-162)

    Haka kuma, ya zayyano abubuwa muhimmai wanda Allah ya albarkaci jihar Kano da su, tun daga abubuwa na more rayuwa da ci gaban ƙasa da sana’o’i da ilimi da mulki da masa’antu da sutur da kayayyakin abinci, a cewarsa duk suna a birnin Kano, ga yadda ya jero ɗiyoyin kamar haka:

    Jagora: In

    ‘Y/Amshi: Nijeriya ta arewa babu jiha irin birnin Kano

    Jagora: Lallai shina birnin Kano

    ‘Y/Amshi: Yadi shina birnin Kano

    Jagora: Kuɗi shina birnin Kano

    ‘Y/Amshi: Ilimi shina birnin Kano

    Jagora: Kyauta tana birnin Kano

    ‘Y/Amshi: Mulki shina a birnin Kano

    Jagora: Injimin yin motoci

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    Jagora: Injimin yin jirgin ƙasa

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    Jagora; Injimin yin mashin hawa

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    Jagora: Injimin yin famfon ruwa

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    Jagora: Injimin yin motoci

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    Jagora: Injimin yin keken hawa

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    Jagora: Injimin yin kwaɗon ɗaki

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    Jagora: Injimin ƙera makamai

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    Jagora: Injimin yin tasoshi

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    Jagora: Injimin yin kwanoni

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    Jagora: Injimin shirya agogo

    ‘Y/Amshi: An ce shina a birnin Kano

    (Gusau, 2009, sh.163-164)

     

    Waɗannan ɗiyan duk an yi su ne domin zuga jihar Kano da abubuwan da suke da shi da ma waɗanda ba su da shi, haka na bayyana ƙauna ga Turakin Kano da al’ummar Kano gaba ɗaya. Idan aka duba akwai abubuwan da ba a da su a Nijeriya ma gaba ɗaya amma saboda zalaƙa irin ta makaɗa Sa’idu Faru, ya bayyana da cewa akwai su a garin Kano kamar misali, injinan ƙere-ƙere da ya Ambato kamar na ƙera motoci da mashina da kekuna da na ƙera makamai duk babu su. Amma da yake ya yi amfani da salo mai ƙayatarwa na kambama abin da ake wa waƙa ya sa ya zauna daram kuma ya karɓu.

    Har wa yau, makaɗan ya nuna zuga a birnin Kano ta fannin kayayyakin abinci, amma hakan ba makawa haka yake domin jihar Kano tana ɗaya daga cikin jihohin arewa da suke samar wa ƙasar nan kayayyakin abincin, kama daga gyaɗa da dawa da masara da gero da wake dasauransu, kamar yadda makaɗa Sa’idu faru yake faɗi a cikin waɗannan ɗiyoyi:

    Jagora: Babban abincin arewa

    ‘Y/Amshi: Gero shina birnin Kano

    Jagora: Gero yana birnin Kano

    ‘Y/Amshi: Dawa tana birnin Kano

    Jagora: Gero yana birnin Kano

    ‘Y/Amshi: Dawo tana birnin Kano

    (Gusau, 2009, sh.162)

    Haka kuma, makaɗan ya sake zuga Turaki tare da kururuta shi da girmama shi da nuna isar sa da kambama shi a duniya a in da yake cewa:

    Jagora: Tsaye da kyawo, zamne da kyawo

    ‘Y/Amshi: Ahmadu kamfaragin Sarkin Fada ɗ2

    : Karsanin galadiman Kano

    : Kurum kake mai ban tsoro

    : Ɗan Hashim ƙanen sarkin Kano

    Jagora: Baba kware kake

    ‘Y/Amshi: Da faɗawa ɗan Hashim ƙanen Sarkin Kano

    (Gusau, 2009, sh.162)

    Turken Yabo

    Turken yabo ɗaya ne daga cikin turakun waƙoƙi baka, wanda ya fi kowanne turke fice a waƙoƙin Hausawa (Gusau, 2008:376). Ya ƙara da cewa turken yabo ya haɗa da “ambaton kalmomin sambarka da nufin nuna amincewa da hali ko wani abin da mutum ya yi nagari”. Kowanne turke yana da tubalan da akan yi amfani da su wajen gina shi, misali a turken yabo a kan samu ƙananan tubala da suka haɗar da ambaton nasaba da kyawawan halaye da kyauta da makamantansu.

    Haƙiƙa makaɗa Sa’idu Faru ya yabi Turaki Ahmadu yabo mai yawa, ta yadda ya nuna irin girma da martabar Turaki wajen al’umma, har da yadda yake nuna mararinsa na son zuwa Kano, kamar yadda yake cewa:

    Jagora: In ban yada zuwa Kano ba, ina shawak Kano

    Y/Amshi: Amma ciki ɗan Hashim Kano shi nis sani

    Jagora: In ban yada zuwa Kano ba, ina murnak Kano

    Y/Amshi: Amma ciki ɗan Hashim Kano shi nis sani

    (Gusau, 2009, sh.162)

    A nan mawaƙin ya nuna ba zai je Kano ba sai don dalilin Turaki don a ganinsa babu kowa ma cikin Kano sai Turakin, don haka wannan yabo ne da wani bai yi wa wani sai masoyi na asali, wanda ya cancanci haka.

    Haka kuma, cikin yabon da ya yi masa ya ce bai ma san Turaki ba, domin mafarki kawai ya gan shi, amma hakan bai hana ya yabe shi ba, domin zuciyarsa ta yi nisa wajen ƙaunarsa, a in da yake cewa:

    Jagora: Cikin mahwalki nikan ga shi.

    Y/Amshi: Ko shi ba sanina yay yi ba.

    (Gusau, 2009, sh.162)

    A ƙa’ida ta makaɗa da mawaƙan baka sukan yaba kyauta tun kafin a yi musu kyauta don hakan ma salo ne na roƙo tare da yabawa ga mutumin da suke so ya yi musu wannan kyautar, shi ya sa, ya yaba kyautar kujerar Makkah da mota marsandi domin yana da yaƙinin za a yi masa kyautar tun kafin a yi ta, kamar yadda yake cewa:

    Jagora: Amadu cika ni aza ni k aba ni kuɗi in tai haji.

    Y/Amshi: In hawo bisa marsandi, ina rabkak kiɗi.

    Makaɗa Sa’idu Faru tare da Daudun kiɗi Mu’azu sun nuna cewa duk wata kyauta idan ba daga wajen Turaki ba ne ba su karɓar ta, sun ƙara da cewa duk wata kyauta daga wajen Turaki take kamar kyautar kuɗi da ta riga da ta bawa da ta mota, kamar haka:

    Jagora: Ɗan sarkin da ka kyautaj jikka

    Y/Amshi: Ɗan Hashim Kano ɗai a haka

    Jagora: Ɗan sarkin da ka kyautar riga

    Y/Amshi: Ɗan Hashim Kano ɗai a haka

    Jagora: Ɗan sarkin da ka kyautab bawa

    Y/Amshi: Ɗan Hashim Kano ɗai a haka

    Jagora: Ɗan sarkin da ka kyautam mota

    Y/Amshi: Ɗan Hashim Kano ɗai a haka

    : Duk wanda yaz zam irin haka

    : Ko ba daɗe shin a sarkin Kano

    (Gusau, 2009, sh.163)

    Baya ga waɗannan yabo da kirari da makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Turakin Kano ya ƙara da yi masa fata ta gari, a inda yake masa addu’ar ya zama sarkin Kano kamar yadda yake cewa:

    Jagora: In Allah ya yi ma babban rabo,

    : Turaki a ce ma San Kano.

    (Gusau, 2009, sh.163)

    Sannan baya ga yabon da makaɗa Sa’idu faru suka yi wa Turakin Kano, sun haɗa da yabo ga jihar Kano ƙwarai zai je gidajen rediyoyi na jihohi mabambanta domin ya yabi jihar Kano duk don albarkacin Turakin Kano Ahmadu, ga yadda ya zayyano ɗiyoyin waƙar:

    Jagora: za ni gidan rediyo na sakkwato

    ‘Y/Amshi: In yi yabon Jihab birnin Kano

    Jagora: Za ni gidan rediyo na Kaduna

    ‘Y/Amshi: In yi yabon Jihab birnin Kano

    Jagora: Za ni gidan rediyo na Ikko

    ‘Y/Amshi: In yi yabon Jihab birnin Kano

    Jagora: Za ni gidan rediyo na Niger

    ‘Y/Amshi: In yi yabon Jihab birnin Kano

    (Gusau, 2009, sh.163)

    Wannan yabo ne da makaɗan ya yi wa jihar Kano albarkacin Turaki aka yi shi, watau a nan, ba Turaki ne kawai abin bege ba har da jihar da ya fito, haƙiƙa ƙauna ce ta kawo haka, don idan ba ka son abu ba za ka yabe shi ba, ballantana har wasu su ci albarkacinsa.

    3.0 Kammalawa

    Zuga da yabo abubuwa ne da suke da muhimmanci a cikin harkar makaɗan baka na Hausa, makaɗan suna girmama kyauta ko yaya take sannan kuma ba sa wasa da ita, shi ya sa duk wanda ya ba su sai sun faɗa sun kuma yabe shi, wani lokaci zugan da suka yi wa mutum shi yake sa a ba da kyautar, wani lokaci kuma ganin dama ce kawai ta mai wadata ko mai sarauta yake yin kyautar. A wannan takarda an fito da wasu ɗiyan waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru wanda ya yi wa Turakin Kano Alhaji Ahmadu. Wannan waƙa an yi ta ne don yabo tare da nuna zuga gare shi, shi kuma Turaki ya kyautata masa ne, domin kowa ya yi wa mawaƙi kyauta ɗayan biyu ne ko dai ya yi masa ne don ya faɗa ko kuma ya yi masa ne don soyayya kawai, shi kuma mawaƙi alhakinsa ne ya yaba kyautar da aka yi masa don ya biya kyautar da aka yi masa. A wannan nazari an fahimci wasu kalmomi da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen bayyana zuga da yabo ga Alhaji Ahmadu, wannan salo da ya yi amfani da su, haƙiƙa ya yi armashi ƙwarai, domin ya nuna zalaƙarsa da gwanancewarsa wajen iya waƙa musamman ta fada, kamar in da yake cewa:

    Jagora: In Allah ya yi ma babban rabo,

    : Turaki a ce ma San Kano.

    Haka kuma ya nuna matsayi da girma na Turaki ta hanyar bayyana rashin sha’awarsa ta zuwa birnin Kano ma gaba ɗaya in ba don dalili na Turaki ba. In da yake cewa:

    Jagora: In ban yada zuwa Kano ba, ina shawak Kano

    Y/Amshi: Amma ciki ɗan Hashim Kano shi nis sani

    Jagora: In ban yada zuwa Kano ba, ina murnak Kano

    Y/Amshi: Amma ciki ɗan Hashim Kano shi nis sani

    Manazarta

    CNHN (2006). Ƙamusun Hausa. Jami’ar Bayero Kano. Zaria: ABU Press.

    Gusau, S. M. (1996). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kano: Fisbas Media Services.

    Gusau, S.M (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu Da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishes Limited.

    Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka Zaɓaɓɓu: Matannoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Century Research and Publication Limited.

    Muhammad, A. S. (2015) Nazarin Ayyukan Makaɗa: Sa’idu Maidaji Sabon Birni (1938-2000). Kundin Digiri na Biyu. Zaria: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Ahmadu Bello University.

    Oxford, (1999). Mini Dictionary. Oxford: Oxfort University Press.

    Sani, Y. S. & Aliyu, A. (2018). Ingiza Mai Kantu Ruwa: Nazarin Zuga a Waƙoƙin Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina. Takardar da aka gabatar a Taron Ƙara wa Juna Ilimi a Kan Rayuwa da Falsafar Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina, Jami’ar Bayero, Kano.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.