𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam Khamis. Shin Akwai Addu'ar Da Mutum Zaiyi Yashawo Kan Budurwa Tasoshi Saboda Allah Suyi Aure?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.
Babu wata addu'a keɓantacciya cikin abunda muka sani wacce mutum zai lazimci
yinta idan yana neman aure, wacce ta tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi
wasallam, Saidai wajibine ka roki Allah ya azurtaka da mace tagari.
Hakika Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yakoyar
damu Addu'ar "ISTIKARA" Ma'anarta shine kanemi Allah ya zaɓa maka abunda yake shine alkhairi agareka, cikin al'amura
gaba ɗaya duniya da lahira, wannan addu'a itace wacce jabir bin
Abdullahi Allah yakara masu yarda yaruwaito Yace: Annabi sallallahu Alaihi
wasallam yakasance yana koyar damu "ISTIKARA" acikin dukkan al'amura
gaba ɗaya, kamar yanda yake koya mana surah daka Alqur'ani,
Yace: Idan ɗayanku yai niyyaci wani
al'amari, yayi sallah raka'a biyu, bata farillah ba, saiyace:
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيـرُكَ بِعِلْمَكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ
بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيمِ، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلَا أَقْدِرُ،
وَتَعْلَمُ وَلَا أَعْلَمُ، وَأَنْتَ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ، اللَّهُمَّ إِنْ كُنْتَ
تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الَأمْرَ (وَيُسَمِّي حَاجَتَه) خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي
وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ
كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأَمْرَ شَرٌّ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ
أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ عَنِّي وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ
كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ
FASSARA: Ya Allah! Ina neman zaɓinka domin iliminka, kuma ina neman Kabani iko domin
ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko, ni
kuwa ba ni da iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin
abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al'amari (sai ya ambaci bukata
tasa) alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen
al'amarina a wata rayuwar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa Ka
kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikinsa. Kuma
idan Ka san wannan al'amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata da
karshen al'amarina a wata ruwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsar
Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka
kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi".
Bukhari ( 1109).
Duk wanda ya nemi zaɓin mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma
ya yi azama acikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah maɗaukakin sarki Yace:
...وَشَاوِرْهُمْ فِي الْأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى
اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُتَوَكِّلِينَ
FASSARA: "Kuma ka shawarce su cikin
lamarinka, idan kuma ka kuduri aniya, to ka dogara ga Allah. Lailai ne Allah
Yana son masu tawakkali". (Suratul Imran Aya ta 159)
Dangane da miji Annabi sallallahu Alaihi wasallam
Yace: ( idan wanda kuka yarda da addininsa da halayensa yazo neman auren 'yarku
ku aurar masa, idan ba hakaba fitina zata auku aban qasa da fasadi mabayyani,)
Turmuzi ( 1084) da ibnu majah ( 1967).
Dangane da Mace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam
Yace: ( Ana auren mace saboda abubuwa huɗu:
1. kyawunta.
2. Nasabarta.
3. Dukiyarta.
4. Addininta.
Kanemi ma'abociyar addinin zata hutar da
hannuwanka ) Bukhari (4802) da Muslim ( 1466).
Alhafiz ibnu hajar rahimahullah Yace: Ma'anar mace
takasance mai addini, addini yakasance shine abunda mutum yake dubawa akan komai, musamman akan
abunda zaka daɗe kana zama dashi, Sai
Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya Umarceshi da ma'abociyar addini, wanda
shine kololuwar abun nema, fat-hul bari ( 9/135).
Wannan shine abunda zaka maida hankali akansa
wajan dacewa dasamun mace tagari maisonka don Allah kuyi aure.
WALLAHU A'ALAM.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.