Yan Uwan Miji Na Suna Shigowa Gidanmu Ba Tare Da Izini Ba

    TAMBAYA (162)

    Slm Allah ya karawa Malan imani da lapia Allah yakareka dakai da iyalan ka ya karamaka ilimi mai albarka Malan tambayana shine mijina yana bari yan uwansa maza suna zuwa gidanmu sukanzo suyi wata 1 2 harfi Malan kuma gidan ba babba bane hasalima ga dakina ga wanda suke kwana aciki kuma ina shayarwa Allah yasani idan sukazo da farko ina kare kanna idan zanshayar da babyna amma idan suka kwana biyu nakansaki jikina sabida zafi wata sa'i kuma Allah yasani suna takurani yanzu haka kusan shekara biyar kenan suna haka Kumafa baligaine maza idan nacemasa bakyau zuwansu saiyace bazai iya hanasuba dan Allah Malan ina neman karin bayani da zan tinkari mijina dashi  yazanyi

    AMSA

    Ki same shi ki ce masa My sweetheart me zaka fada gameda wannan ayar da Allaah ya saukar ?

    ( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَدْخُلُوا بُيُوتَ النَّبِيِّ إِلَّا أَن يُؤْذَنَ لَكُمْ إِلَىٰ طَعَامٍ غَيْرَ نَاظِرِينَ إِنَاهُ وَلَٰكِنْ إِذَا دُعِيتُمْ فَادْخُلُوا فَإِذَا طَعِمْتُمْ فَانتَشِرُوا وَلَا مُسْتَأْنِسِينَ لِحَدِيثٍ ۚ إِنَّ ذَٰلِكُمْ كَانَ يُؤْذِي النَّبِيَّ فَيَسْتَحْيِي مِنكُمْ ۖ وَاللَّهُ لَا يَسْتَحْيِي مِنَ الْحَقِّ ۚ وَإِذَا سَأَلْتُمُوهُنَّ مَتَاعًا فَاسْأَلُوهُنَّ مِن وَرَاءِ حِجَابٍ ۚ ذَٰلِكُمْ أَطْهَرُ لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ ۚ وَمَا كَانَ لَكُمْ أَن تُؤْذُوا رَسُولَ اللَّهِ وَلَا أَن تَنكِحُوا أَزْوَاجَهُ مِن بَعْدِهِ أَبَدًا ۚ إِنَّ ذَٰلِكُمْ كَانَ عِندَ اللَّهِ عَظِيمًا )

    الأحزاب (53) Al-Ahzaab

    Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada kũ shiga gidãjen Annabi, fãce fa idan an yi izni a gare ku zuwa ga wani abinci, bã da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma idan an kira ku, to, ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku wãtse, kuma bã da kun tsaya kunã masu hĩra da wani Iãbãri ba. Lalle wannan yanã cũtar da Annabi, to, yanã jin kunyarku, alhãli kuwa Allah bã Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan zã ku tambaye su waɗansu kãyã, to, ku tambaye su daga bãyan shãmaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukãtanku da zukãtansu. Kuma bã ya halatta a gare ku, ku cũci Manzon Allah, kuma bã ya halatta ku auri mãtansa a bãyansa har abada. lalle wannan a gare ku yã kasance babban abu a wurin Allah.

    Asbabin nuzul (dalilin saukar ayar) yana da alaqa da yanda wasu Sahabbai suke shiga gidan Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ba tareda izininsa ba

    Ki bincika Littattafan tafisiri irinsu: Ibn Khathir (dalibin Ibn Taimiyya), Tafsir na Ibn Jarir at-Tabari da Tafsir Imamul Qurtubi da sauran malaman Salaf

    Malamai sunyi Ijma'i, ba kyau shiga gida saida izinin masu gida. Wannan ayar itace hujja a kansa. Ki nuna masa kiji me zai ce

    Rashin koyi da SUNNONIN fiyayyen halitta ne yasa muketa tafka kura kurai a lamuranmu

    Karin bayani Kuma zai zo filla filla a cikin karatun da muka Fara last 2 weeks na littafin SUNNONI 1,000+ da sauransu

    Mai buqatar shiga USMANNOOR ONLINE ACADEMY, sai yayi magana ta private don kada karatun da muka fara yayi maka nisa

    Wallahu taala a'alam

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa:

    ✍️ADMIN: ZAUREN TAMBAYA DA AMSA:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

     ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.