TAMBAYA (161)❓
Assalamualaikum. Malam Barka da yini Mlm Inada Tambaya Malam yahalata Inje wajen Wadda Ba musulmaba Wanki Kai saboda Anan Bida Bamusulmai masuyi. Ngd
AMSA❗
Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu
*_Akwai kyakkyawar alaqar kasuwanci tsakanin
Kafiran Medina da Musulmai a zamanin Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam
An haramta kashe Kafirin Amana wanda ya biya Jizya
Yin kitso a wajen Wanda ba musulmi ba ko wani abu
makamancin hakan ba laifi bane ba indai har akwai kyakkyawar alaqa tsakaninki
dasu
Kuma Albishinki - Da nice ke to da Da'awah zanyi
Mata !
Zaki iya amfani da wannan damar wajen kwadaitar da
ita ladubban addininki na musulunci
Misali: Idan zata fara yi Miki kitson sai ke kiyi
Bismillah (taji Bismillar) sannan kice Mata ta fara ta bangaren dama domin koyi
da Sunnar Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam ta damaitawa
Idan farce ne Kuma sai ki furta (Bismillahi ala
sunnati Rasulullah) ki fada yanda zata ji daganan sai a fara yanke manuniya
(yatsa) sai a damaita, bazaa yanke babban dan yatsa na dama ba tukunna don
gudun kada a dawo hagu, sai a dauko yatsun hagu a damaita su a qare da babban
yatsan Daman. Kinga kinyi koyi da Matan Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam da
Kuma Matan sahabbansa (Radiyallahu anhuma)
Idan Kuma Lalle/Kunshi ne ko Subqa zatayi Miki sai
shima kiyi Bismillar sai ta fara miki da kafar dama a kammala da ta hagu
Zaki Sha tambaya a wajenta kam. Sai ka bata amsa
da ai wannan shine Sunnar Dan uwan Annabi Isah (Alaihis Salam) da aka turawa
Nasara yan kauyen Nazreth dake kasar Palestine shekaru sama da 2,000 da suka
shude
Daganan sai hira ta barke !
Ki rufe ta da hujjoji !
La'alla ta musulunta a hannunki tunda suna yunwar
neman hujjar da zata sadasu zuwa ga Gaskiya sabanin Yahudawan da sun san
gaskiyar musulunci amman suka take silar hakan suka bata. Nasara suna cuna
cikin duhun jahilci shiyasa suka zamo batattu su Kuma Yahudu Kuma son zuciya da
take qarya shiyasa Allaah Azzawajallah yayi fushi dasu. Kuma shiyasa a kullum a
kalla muke maimaita ayar dake cikin Suratul Fatiha su 17 (Farillai):
( اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ )
الفاتحة (6) Al-Faatiha
Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
( صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ
عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ )
الفاتحة (7) Al-Faatiha
Hanyar waɗanda Ka yi wa
ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba,
kuma ba ɓatattu ba.
Bawai dole bane ki fada Mata hakan Amman koyi da
Sunnah ne domin kuwa Babu dole a addini kamar yanda Allaah Azzawajallah ya fada
( لَا إِكْرَاهَ فِي الدِّينِ ۖ قَد تَّبَيَّنَ الرُّشْدُ مِنَ
الْغَيِّ ۚ فَمَن يَكْفُرْ بِالطَّاغُوتِ وَيُؤْمِن بِاللَّهِ فَقَدِ اسْتَمْسَكَ بِالْعُرْوَةِ
الْوُثْقَىٰ لَا انفِصَامَ لَهَا ۗ وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ )
البقرة (256) Al-Baqara
Bãbu tĩlastãwa a cikin addini, haƙĩƙa shiriya tã bayyana daga ɓata; Sabõda haka wanda ya kãfirta da dãgũta kuma ya yi
ĩmãni da Allah, to, haƙĩƙa, yã yi riƙo ga igiya amintacciya, bãbu yankẽwa agare ta. Kuma Allah
Mai ji ne, Masani.
Karin bayani Kuma zai zo filla filla a cikin
karatun da muka Fara last week na littafin SUNNONI 1,000+ da sauransu
Mai buqatar shiga USMANNOOR ONLINE ACADEMY, sai
yayi magana ta private don kada karatun da muka fara yayi maka nisa
Wallahu taala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha
illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa:
✍️ADMIN: ZAUREN TAMBAYA DA AMSA:
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.