A Wani Ƙauye Da Ake Kira Kalausar Lugge'eri Ne Aka Dasa Ɗambar Fara Bikin Kamun Kifi Na Argungu (Argungu Fishing & Cultural Festival) Shekaru 99 Da Suka Wuce

    Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sama wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1920 zuwa 1934 akan hanyarsa ta zuwa wani taron Sarakuna a Kano, a cikin shekarar 1925 ne ya yada zango a wani Ƙauye da ake kira "KALAUSAR LUGGE'ERI" dake Kilomita 8 kan titin Dange /Danchad'i /Bod'inga, a cikin gundumar Dange ta Masarautar Sakkwato. 

    Ya na tafe da ayari mai ƙarfin gaske da ya  ƙumshi hikimai da masu hidima akan Dawaki da kayansu na abinci da na sauran buƙatun rayuwa a lokacin wannan tafiya. A lokacin, Malam Muhammadu Tambari ne  ke Sarautar Sarkin Musulmi ( ya yi Sarauta daga shekarar 1924 zuwa 1931).

    Da Uban Ƙasar /Hakimin Gundumar Dange na wannan lokacin, Sarkin Bauran Dange Malam Hassan Mu'azu (wanda ya zamo Sarkin Musulmi a shekarar 1931, watau Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu'azu) ya samu labarin saukar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sama  a wannan Ƙauye dake cikin gundumarsa sai ya nemi a yi masa iso domin ya je su gaisa. 

    Aka yi masa iso, ya tafi wannan wuri suka yi musabaha da tattaunawa mai tsawo domin dukansu masu ilmin addini ne gwargwadon hali har ma suka taɓo yanayin zamantakewa tsakanin Sakkwato da Argungu. Sarkin Bauran Dange Malam Hassan Mu'azu ya yiwa Mai Martaba Sarkin Kabi Muhammadu Sama hidima sosai a wannan lokaci. 

    Ana kyautata zaton wannan haɗuwar tasu a Kalausar Lugge'eri ce silar ziyarar da Malam Hassan Mu'azu ya kai a Argungu a cikin shekarar 1934, shekaru 3 bayan zamowarsa Sarkin Musulmi, domin kuwa sun ci gaba da hulɗa da zumunci bayan wannan haɗuwa da suka yi a wannan wuri a shekarar 1925. 

    Kafin wannan ziyara ta Mai Alfarma Sarkin Musulmi Hassan ɗan Mu'azu a Argungu da ta haifar da bikin kamun kifi na Argungu a shekarar 1934, masu mulkin Sakkwato da Argungu sun yi iya nasu ƙoƙari domin daidaita zamantakewa tsakanin Masarautun biyu, amma abun ya yi ta haɗuwa da tasgaro ko cikas. Saboda haka ne ake ganin wannan haɗuwar ta Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sama  da Sarkin Bauran Dange, Hassan Mu'azu a Kalausar Lugge'eri a Shekarar 1925 ta zamo sanadiyar ɗinke ɓarakar da ta daɗe tana illa a tsakanin waɗannan manyan Masarautu guda biyu. 

    Duk da yake kafin rasuwarsa ya yi ƙudurin rama wannan ziyara zuwa Sakkwato, Allah bai nufi Mai Martaba Sarkin Kabi Muhammadu Sama  da ya kai  irin wannan ziyara a Sakkwato ba har ya yi wafati. 

    Bisa ga amincewa da umurnin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Dr. Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR da Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama'ila Muhammad Mera CON ne aka tantance wannan wuri, aka kuma killace shi domin taskace  Tarihi na magabatansu da suka yi wannan aikin alheri da ƙulla zumunci a tsakanin Masarautunsu. 

    ABIN LURA:
    A rubutun da na fitar akan wannan lamari ranar Asabar, 27/07/2024 na ambaci Marigayi Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Malam Muhammadu Sani(1934-1942) a matsayin Sarkin da aka fara bikin kamun kifi na Argungu a lokacinsa, wannan kuskure ne duk kuwa da yake a shekarar da aka fara bikin ne ya zama Sarkin Kabi, amma a lokacin wanda ya gada  ne kuma wanda ya zama silar ziyarar da ta haifar da bikin ne ta hanyar yada zangon da ya yi a Kalausar Lugge'eri a shekarar 1925, watau Mai Martaba Sarkin Kabi Muhammadu Sama  aka soma shi wannan bikin ya zuwa yau. 

    Allah SWT ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, ya yalwata bayanmu, amin. 
    Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sama wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1920 zuwa 1934 akan hanyarsa ta zuwa wani taron Sarakuna a Kano, a cikin shekarar 1925 ne ya yada zango a wani Ƙauye da ake kira "KALAUSAR LUGGE'ERI" dake Kilomita 8 kan titin Dange /Danchad'i /Bod'inga, a cikin gundumar Dange ta Masarautar Sakkwato.

    Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya. 
    08149388452, 
    08027484815. 
    birninbagaji4040@gmail.com 
    Litinin, 29/07/2024.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.