𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
shin Mallam yakamata mutum ya auri mace domin tanada arziki Shikuma bayida abinda zai ciyar da Wanda bata komai yasa ya auri mai arziki domin taringa taimaka masa wajen ciyar da gida shikuma yasamu hanyan dena zina kasancewar auren nata.
Auren Mace Don Arzikinta
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa’alaikum salam CHAB DIN!!!. Amma dai akwai
matsala, kasan mata kuwa? to da yawansu ban nace gabaki ɗayansu ba, mace bazata baka kuɗi wai ka ciyar da kishiyarta ba.
Lalle kwata-kwata baka fahimci mace ba, akan
kishiya bakasan suna kashe miji Sabida kishiya ba, kowa ma ya rasa, ita ta
rasa, kishiyar ma ta rasa? Kuma kake tunanin zata ɗauki kuɗi ta baka kana
ciyar da kishiyarta abinci?
Wallahi wata ta gaya min cewar, duk lokacin da
mijinta ya kuskure yayi Mata kishiya, ta dena masa duk abinda yake masa,
alhalin ma’aikaciya ce, tana ɗaukar Albashi,
shi kuma baya ɗaukar Albashi. Kuma da
idona naga wadda ta siyawa mijinta mota yake yin haya, daga baya ya sami wadata
sai ya kara aure, yana kara auren nan kuwa ta karɓe motarta ta baiwa wani. Sabida haka kabi a hankali,
lalle zaka yaudari kanka indai mace ce, ai Su mata karfen nasara ne.
Amma dai Akwai masu kirki a cikinsu, sai dai duk
kirkinsu ba zasuyi Maka akan kishiya ba. Haka duk hakurin mace, Baza tayi Maka
akan kishiya ba.
Allah ta’ala yasa mudace
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.