𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum malam muna maka fatan alkhairi Dan Allah Malam meye yakesa mace bushewa a lokacin da take mu’amala da mijinta bayan lokacin da suka fara ba haka bane sannan malam me yake saurin kara ruwan maniyyi kuma malam Ina fitar da iska yayin saduwa malam a taimaka yadda ka saba taimako Allah ya kara girma ngd.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa’alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
To abinda yake sa bushewa idan ana saduwa rashin
wadatacciya ni’ima ne indai ana tsaka da saduwa ne kike Bushewa, Amma indai
kafin saduwa ne toh matsalar sanyi ne ko rashin wasa na motsa sha’awa, amma
wasu kuma jumawa ana gurzarsune yake sawa ruwan yake qafewa musamman idan
namijin gwarzo ne, amma ba matsala bane, abinda zakiyi shine kisamu magani masu
kyau na qara ni’ima, sai yawan shan kayan marmari da kayan ganye sune wanda
zasu taimaka miki sosai wajen tabbata ciyar ni’ima.
Sanann kidinga samu kankana ki ferayeta kamar
kabewa sai ki yayyyanka ki sata a blender ki markadeta sai ki saka garin
kaninfari kamar cokali 1 bayan kin markada sai qara zuba madararki gwangwani 1
kamar peak, luna ko wacce kike da Iko, sai ki qara markadawa su haɗe gaba ɗaya, Sai ki samu
mazubi mai kyau ki juya ki ajjiye a firji kidinga sha wanan zai sakar miki ni’ima
kamar fanfo sai kin gaji da zuba.
Sannan abinda zai qara yawan ruwan maniyyi shine
ki samu yayan kabewa ki dake kidinga shansa da zuma ko ki markada dabino da
madara kina sha duk suna bada wadattacen ruwan maniyyi ga mata da maza.
Matsalar fitan iska yayin ya danganta da yanayin
kwanciya da kukeyi musanmam ana samun fitar iska wajen saduwa ta baya domin
iska na samin shiga da fita, wani lokacin kuma buɗewa ga mace na saka fitar iska ta gabanta yayin saduwa,
wani lokacin kuma gaskiya ba matsala bane domin indai ana saduwa a wajen da
akwai iskar fanka takan sa iska na shiga da fita wajen zurawa da cirewa sai
adinga jin iska na fita wannan ba matsala, amma ga magani a jarrrraba in Shã
Allah Zaki dace.
Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
Ganyen magarya sassaqen danya,Yayan hulba
,Gishiri. waɗannan kayan hadin sai ki
haɗesu guri guda ki tafasa
bayan kin sauke ki zuba gishiri kina zama a cikin ruwa na tsawon minti
goma Kuma ya zama ruwan da kike tsarki dashi Amma ko yaushe ya zama da dumi.
Allah ta’ala yasa mudace
WALLAHU A’ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.