Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu
Yayin da kayi/kikayi reply ta priɓate hakan na nufin kana da buƙatar Karin ilimin iya mu’amalar auratayya kan
tafarkin koyi da Sunnah kuma a shirye kake da ka gyara ibadarka tsakanin ka/ki
da matarka/mijinki
Idan wayarka ta lalace wajen Engineer zaka kai domin a gyara maka, idan bakada lafiya asibiti zaka garzaya don likita ya baka magani. Gyara mu’amalar auratayyar mu yafi muhimmanci fiyeda waɗancan abubuwan guda biyu
Ina son duk wanda yake karanta wannan saƙon, yayiwa kan sa
tambaya:
"SHIN MU’AMALAR AUREN DA NAKE YI A KO DA
YAUSHE IRIN TA CE ANNABI YA KOYAR A ADDINANCE KO KUMA INA YI NE KAMAR YANDA
ZUCIYA TA TAKE SO❓
Ka maimaita tambayar kanka kamar sau 3. Anan take
zaka ji hankalin ka ya dawo jikin ka sannan zaka fara kwokwanto akan anya kuwa
irin yanda fiyayyen halitta ya gudanar da mu’amalar auratayya nakeyi ?
Sanin kanki ne cewar komai da zamu aikata saida
musulunci ya koyar da mu, hatta shiga bandaki to ina kuma ga rayuwar auratayya
wanda wallahu a’alamu a nan ne za’a samu shugaban kasa ko gwamnan gobe wanda
zai jagoranci miliyoyin al’umma. Kinga kenan komai zaki gudanar sai an koma ga
hadisai da suka yi bayani akan yanda Annabi SAW ya koyar da matan gidansa a
lokacin rayuwarsa tare dasu
Wannan littafi mai suna: "Guidelines To
Intimacy In Islam" ma’ana: Shiriya akan alaƙar auratayya a musulunce, wallafar Mufti Ahmad Ibn
Adam Alkautary), na zaƙulo shi ne (a matsayin zababbe) daga cikin Littattafan da suke a cikin
wayata (Library folder) wadanda suke da alaƙa da mu’amala kamar irinsu: "Nisa’ Hawul
Rasul" ma’ana: "Mata A Lokacin Ma’aiki" na Amany Abul Fadi Farag
da littafin: "Rijal Hawlur Rasul" ma’ana: "Maza A Lokacin Ma’aiki"
na Khalid Muhammad Khalid. Da littafin Emotional Intelligence" zamu iya
fassara shi a: "Yanda Zaka Iya Sarrafa Shauƙi" wallafar Daniel Goleman da littafin:
"The 5 Loɓe Languages" wato:
"Yaren Soyayya guda 5" na Gary Chapman
Da wani littafi mai suna "Men Are From Mars -
Women Are From Ɓenus" ma’ana: "Maza daga duniyar Mars suke - Mata Kuma daga
duniyar Ɓenus" wallafar Dr.
John Gray, abin da yake nufi Kuma ya fada a littafin shine duniyar Ɓenus da muke Kira da
Zara matar Wata ta kasance tana da tsananin zafi saboda kusancin ta da Rana,
mata daga can suke shiyasa suke da yawan fada ga mazansu da tsananin Kishi ga
kishiyar su
Ita Kuma duniyar Mars sanyi ne da ita, Maza
dagacan suke shiyasa suke da sanyin hali da raunin zuciya ga matansu, babban
makamin da su kuma Mata suke kwato yancinsu a wajen mazajensu shine ta hanyar
yin kuka. Yace ka ƙaddara wataran maza sun saka abin hangen nesa daga duniyar Mars suka hango
Mata a duniyar Ɓenus, suka hau rocket suka je wajen su, suka aure su, zama ya kasa yiwuwa a
Ɓenus saboda zafi ita
Kuma duniyar Mars tayi sanyin da Mazan bazasu iya zama a kanta ba, karshe aka
yanke shawarar da Mazan da Matan za’a dawo sabuwar duniyar al-Ard (Earth)
saboda tana da yanayin sanyi da zafi, watarana da safe kowa ya tashi da cutar
zafi da sanyi hakan ya sa maza basa jin dadin zama da matan suma kuma suke ta
complain akan halayen mazan wannan ne dalilin da ya sa suka manta asalinsu,
shiyasa har yanzu ake ta samun Rikici a zamantakewar auratayya kowa ya manta
asalinsa: duniyar Mars da Ɓenus. Ammanfa wannan shaci fadi ne na Dr. John
A karshe sai na ga dacewar na zabi littafin:
"Shiriya akan alaƙar auratayya a musulunce" domin kuwa Muna son koyi ne da Abinda Annabi
(Sallallahu alaihi wasallam) ya koyar gameda mu’amalar aure
Babbar manufarmu itace mu gyara mu’amalar da muke
musamman ta saduwar aure, muyi koyi da Sunnah don mu gudu tare mu tsira tare
Manufata itace: na zama silar da zan bawa shaidan kunya
kada ya raba auren masoya
Bansan adadin aure nawa na zama silar gyarawa ba
wasu sukan Kira a waya. Ba iya magana ta bane ba (balagar zance) ko ilimi na ba
saidai hakan baiwace daga Allaah Kuma muna ƙara gode Masa domin kuwa yace idan ka gode Masa to
zai ƙara maka. Kuma sasanta
mutane shine yafi alkhairi fiye da abaka jajayen raƙuma
Ko da akwai gudunmawa saboda gudanar da program
din Kamar irinsu Registration Fee❓
Na’am. Dalilin da yasa mukayi maganar gudunmawa
shine: saboda DATA din da zamu dinga siya don gudanar da karatun - da an tsara
za’a bada wasu adadi amman don maslahar wasu sai muka ga dacewar kowa ya bada
abinda zai iya bayarwa. Sanin kanku ne cewar shekara da shekaru babu Wanda muka
taba tambaya gudunmawa a dalilin TAMBAYOYIN da kuke turowa kuma in Sha Allaahu
bazamu taba tambayar ka/ki wani abu ba don zamu bada AMSA domin kuwa wannan mu
ne muka sa kanmu shekara da shekaru Kuma da aljihunmu muke saka DATA don ganin
mun amsa muku TAMBAYOYIN ku da hujja daga: Ƙur’ani, Hadisi, Ijma’i ko Ƙiyasin malamai Kuma zamu ci gaba da hakan matuƙar muna raye, in Sha
Allaah
To saidai wannan tsarin kune kuka bada shawarar a
fara da kanku shiyasa muka ga dacewar neman gudunmawar ku ta yanda baza’a
takure mu ba
Kamar Yanda kuka buƙata Ni kuma nayi alƙawarin cewar Zan ware lokaci daga cikin lokuta na
don tabbatuwar hakan, da akwai dokoki guda 3 ga duk Wanda yake son zama
halastaccen member na Zauren "MU’AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI":
1️⃣Maida hankali wajen bibiyar karatun da akai (ana iya
sauke karatuttukan da akayi, wadanda zamu dinga hadasu da ɓideos na karatuttukan malamai don a Kara fahimta)
2️⃣Zaka iya zama member ne kadai ta hanyar yin Registration
. Wanda ya kasu gida 3:
i} Regular = N3,000 (Sefa jaka 2)
ii} Intermediate = 5,000 (Sefa jaka 4)
iii} Special = 10,000 (Sefa jaka 6)
3️⃣Duk ƙarshen kowanne wata zaka dinga bada tuition fees, shi kuma wannan bamu ƙayyade abinda za’a bayar
ba tukunna, saidai ko nawa ka bayar za’a karba don ci gaba da gudunar da
karatun. A yanzu haka da akwai wadanda suka bada gudunmawarsu ta shekara daya
(Watanni 12), idan mutum ya ga dama zai dinga badawa duk karshen wata, ko ka
dunƙule ka bayar da na
watanni, gwargwadon ikon ka. Ba takurawa
Da akwai dubunnan mata da miji daga group dinmu na
TAMBAYA DA AMSA daga group na 1 har zuwa na 23 da suke yawan turomin tambayoyi
akai akai Wanda bansan adadin wadanda na zama silar gyaruwar aurensu ba, Kuma
tabbas zasuyi farin cikin wannan program din, don haka ga duk wanda ya zama
ready, yake da ra’ayi da Kuma niyyar shiga wannan group:, zai iya tura
gudunmawar ta Opay ko Zenith Bank kamar haka:
Opay/Moneypoint Account;
Usman Danliti
7035387476
Ko
Zenith Bank
Usman Danliti
2118853750
Masu amfani da Sefa Kuma zaku turo ta NITA:
07035387476
A turo eɓidence of
payment (shaidar an turomin: receipt ko screenshot)
Duk bayan wata 3 zamu tsara ƘUESTIONNAIRE ta tambayoyi, ka cike kayi submitting
ta priɓate
Muna roƙon Allaah ya bamu ikon amfana da ilimin muyi aiki dashi har ma wasu su
amfana
Ku sanar da sauran mutane gameda wannan sabon
program din ku kafa musu hujja da maganar Uwar Muminai, Nana Aisha (Radiyallahu
anha) da tace: "Madallah da matan Madina wadanda kunya bata Hana su yin
tambaya gameda addininsu"
Annabi {Sallallahu alaihi wasallam} yace:
"Idan Allaah Yana son bawa da alkhairi sai ya fahimtar dashi addini"
Bukhari da Muslim
Zaku iya sharing saƙon (batareda kun canza harafi ko guda 1 ba) domin
kuwa duk Wanda ka zama silar gyaruwar addininsa to zaka samu share na ladan d
zai samu. Bonanza akan Bonus kenan
💞DOKOKIN SHIGA MAKARANTAR: "MU’AMALAR
AURATAYYA A MUSULUNCI"📚
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.