Dole Ne Musulmi Ya Yarda Da Haddi Na Shari'a

    Asali Addinin Muslunci ya ginu ne a kan tushe guda biyu; imani (ikirari da gaskatawa) da kuma yin aiki:

    1- Imani da gaskata dukkan abin da Allah ya saukar a Littafinsa da kuma ta harshen Manzonsa (Hadisai).

    2- Aiki da abin da Allah ya saukar (Alkur'ani da Sunna/ Hadisai).

    Na farko ba a dauke ma kowa ba. Na biyu kuma an dora shi ne a kan mai iko kawai.

    Shi ya sa Allah ya ce:

    {فَاتَّقُوا اللَّهَ مَا اسْتَطَعْتُمْ } [التغابن: 16]

    "Ku ji tsoron Allah gwargwadon iyawarku (samun iko)".

    Haka Annabi (saw) ya ce:

    «ما نهيتكم عنه فاجتنبوه، وما أمرتكم به فافعلوا منه ما استطعتم»

    صحيح البخاري (9/ 94) صحيح مسلم (4/ 1830)

    "Duk abin da hane ku to ku nisance shi, abin da kuma na umurce ku to ku aikata shi gwargwadon iyawarku".

    Saboda haka, daga cikin abin da Allah ya saukar sawa'un a Littafinsa ne ko a Sunnar Manzonsa (Hadisai) akwai Jihadi da Haddodi na Shari'a:

    (1) Kisa haddin ridda.

    (2) Kisa haddin zina bayan aure.

    (3) Yanke hanun barawo.

    (4) Kisa ko yanke hanaye da kafafu ga 'Yan Fashi da Makami.

    (5) Jihadi na yakar kafirai masu yakar Musulmai, ko na kiransu su shiga Muslunci ko su biya jizya.

    Duka wadannan da ire-irensu Allah ya saukar da su a Shari'ar Muslunci, imma a cikin Alkur'ani ko a cikin Sunnar Annabi (saw), kuma al'umma ta yi Ijma'i a kansu.

    To kasancewar aiki da wadannan abubuwa ba a hanun daidaikun mutane suke ba, a hanun hukuma mai shugaba da sojoji da alkalai da jami'an tsaro suke, to ba a dora ma daidaikun mutane ko wata kungiya yin aiki da su ba. Saboda Allah ya dora mana abin da za mu iya ne gwargwadon ikonmu.

    Abin da ake bukata a wajen kowane Musulmi mai imani da Allah da Manzonsa shi ne; ya yi imani da wadannan; Jihadi da haddodi na Shari'a, ya yarda da su, ya yi ikirari da su ya gaskata su, ko da kuwa ba a zartas da su a yanzu, saboda abin a hanun Gomnati yake. Don haka duk da cewa; Gomnatin da take mulkanmu ba ta zartas da wadannan hukunce - hukunce to amma dole ne Musulmi ya yi imani da su, ya yarda da su ya gaskata su.

    Da wannan za ka fahimci bacin hanyoyi guda biyu:

    1. Hanyar Boko Haram masu daukar doka a hanunsu, masu zartas da hukunce - hukuncen Shari'a alhali su ba Gomnati ba ne.

    2. Hanyar Boko Aqeeda masu yakar Addini, masu rushe hukunce - hukuncensa, masu karyata Allah da Manzonsa, masu hana Musulmai yin imani da gaskata hukunce - hukunce da haddodin Shari'ar Allah.

    Saboda haka, hanya madaidaiciya ita ce hanyar Muminai masu gaskata Allah da yin imani da haddodin Shari'a, kuma ba sa daukar doka a hanunsu, ba sa fita daga Jama'ar Musulmi su dauki makami a kansu kamar yadda kungiyoyin ta'addanci suke yi, saboda sun san cewa; zartas da hukuncin Haddi da yin Jihadi a hanun Shugaban Gomnati yake ba hanun daidaikun mutane ko kungiyoyi ba.

    Saboda haka matakin da 'Yan Boko Aqeeda suke dauka, na yakar Addini, da hana mutane yin imani da yarda da haddodin Shari'ar Muslunci, tsattsauran ra'ayi ne da Ta'addanci a kan Musulmai da hana su bin Addininsu.

    ✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.