Ga Wasu Akidu Guda Uku, Masu Kai Musulmi Aljanna Kai Tsaye

    Zaid bn Sabit ya ce: Annabi (saw) ya ce:

    «لا يعتقد قلب مسلم على ثلاث خصال إلا دخل الجنة». قال: قلت: ما هن؟ قال: «إخلاص العمل، والنصيحة لولاة الأمر، ولزوم الجماعة، فإن دعوتهم تحيط من وراءهم».

    سنن الدارمي (1/ 302 - 303)

    ((Wasu abubuwa guda uku, zuciyar Musulmi ba za ta kudurce su ba face sai ya shiga Aljanna)). Sai na ce: Wadanne ne su?

    Sai ya ce: ((Ikhlasin aiki, Nasiha ga shugabanni, da Lazimtar jama'ar Musulmi. Saboda addu'arsu tana kewaye wanda yake gefensu)).

    Wannan Hadisi ya kunshi bayanin hakkoki guda uku:

    1- Hakkin Allah:

    Ka bauta ma Allah shi kadai, kar ka hada shi da komai cikin bauta. Kuma ka yi Ikhlasi cikin bautar, kar ka yi riya ko nufin neman wanin yardar Allah.

    2- Hakkin shugabanni:

    Ka yi musu Nasiha, ka taimaka musu wajen inganta shugabancinsu da sauke nauyin da yake kansu, kar ka ha'ince su a amanar da suka ba ka, kuma kar ka ki yi musu gyara, ka ki taimakonsu don a samu gyara da shugabanci na gari.

    3- Hakkin Jama'ar Musulmai:

    Ka kasance tare da Jama'ar Musulmai, ka taimake su, ka yi kokarin yin duk abin da zai inganta rayuwarsu da Addininsu. Kar ka ware, ko ka zama dan tawaye, ka dauki makami kana kashe su, imma da sunan Addini da Jihadi, ko da sunan fashi da makami da kwacen Dukiya.

    Kishiyoyin wadannan kuma suna kai mutum wuta kai tsaye.

    Allah ya tsare mu.

    ✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.