Ganin Maniyi (Sperm) A Waje Bayan Mu’amalar Aure

    TAMBAYA (176)

    Snnn kuma Maye matsalar Idan nagana Tarawa da Iyalina, sai naga Sperm din a waje?. Ma’ana ya zuba a kan Gado?. Kodai Baya shiga ciki?. Sbd ni abin Yana Bai tsoro. Ko Idan na kawo gaban ne yake fitowa wajen ya zubar da maniyyin a waje?. Shine Abinda na kasa Ganewa. Wnnn itace tanbayata ya Sheikh.👍🏻

    AMSA

    Alhamdulillah

    Wannan ba matsala bane ai, dan uwa

    Saboda a duk digo 1 na sperm akwai at least 3 zuwa 5 milliliters na semen, wanda kowannen milliliter 1 yake dauke da ƙwayoyin halittu masu rai (sperm cell) daga Miliyan 20 har zuwa Miliyan 300

    Kaga kenan digo 1 na maniyyi (one drop) kadai zai zama silar samun juna biyu. Sai ka tuno da hadisin da Annabi Sallallahu alaihi wasallam yacewa Sahabbansa ko da kunyi azalo (coitus interruptus) ma’ana fitarda maniyyi a waje (outside the ɓagina) don tsawaita haihuwa, idan Allaah ya ƙaddara samun haihuwa a tsakaninku to ba shakka sai an samu ciki

    Kenan ba wai dole ne sai gaba dayan sperm din ya shige gaban macen ba kamar yanda kake thinking

    Wannan ikon Allaah ne Mai yanda ya so don ya nuna ikonSa akan yanda yake halittar Dan Adam daga ƙwayar halittar sperm cell wadda mutum bazai iya gani da idanunsa ba saida taimakon Microscope

    Allaah buwayi gagara Misali

    Sannan kuma idan mutum yana fama da matsalar ƙarancin Maniyyi to a shawarce ya dinga shan Lemo (orange) ko kuma grapefruit juice

    Idan mutum yana son cikakkun bayanai da suke da alaƙa da issue na aure to Albishirinku domin kuwa mun bude makarantar "MU’AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI", kuma karatunmu yayi nisa. Don haka duk wanda yake da ra’ayin shiga wannan makaranta sai yayimin magana ta Priɓate chat

    Wallahu taala aalam

     Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla’ilaha illa anta astaghfiruka wa’atubi ilayk

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.