Hajiya Luba Da Hajiya A'i Da Hajiya Inno

    Hajiya Luba Da Hjaiya A'i Da Hajiya Inno

    "Mai girma ɗan mai girma,
     Uban Luba baban A'i da Inno,
     Amadu kai ɗai kake gwarzo...."

    Haka Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya ambatawa Marigayi Mai girma Firimiyan Jihar Arewa na farko kuma na ƙarshe, Sir Ahmadu Bello GCON KBE Sardaunan Sakkwato a cikin Waƙar da ya yi masa mai amshi "Ya wuce reni ba a yi mai shi, Amadu jikan Garba sadauki".

    Farko daga gefen hagu daga sama (mai bulan kaya) na wannan hoton Hajiya Luba ce, sai Hajiya A'i  a ƙasa a gefen hagu na wannan hoton, da  kuma Hajiya Inno a gefen dama na wannan hoton. Sune waɗanda Makaɗa Musa ke nufi a cikin waɗannan☝️ ɗiyan Waƙar.

    Sune ya'yan/ɗiyan Marigayi Sir Ahmadu Bello GCON KBE Sardaunan da ya bari a duniya. Kenan jikokin Marigayi Mai girma Sarkin Raɓah Ibrahimu ne ɗan Sarkin Musulmi Abubakar II/Abubakar Mai Raɓah ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi  a gefen Mahaifinsu, saboda shi Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello ɗan Sarkin Raɓah Ibrahimu ne.

    A gefen Mahaifiyarsu kuma jikokin Dagacin Bichi Abubakar ne, shi kuma ɗan Dagacin Bichi Almustapha ne wanda ya fito daga tsatson Arɗo Abdullahi Gorgel, Bafulatani daga jinsin Danejawa wanda shi ne ya ƙirƙiri Bichi a shekarar 1672, saboda dukan su ya'yan /ɗiyan Marigayiya Hajiya Amina (Gwaggon Kano) yar Dagacin Bichi Abubakar ɗan Dagacin Bichi Almustapha ne.
     
    Hajiya Luba ta auri Marigayi Mai girma Marafan Sakkwato, Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi ɗan Alhaji Aliyu Bisije ɗan Dagacin Gasma dake Ƙaramar Hukumar Mulkin Karasuwa, Jihar Yobe Muhamman. Tana da ya'ya /ɗiya 2 tare dashi, Hafsat da Ahmad(Sardauna).

    Hajiya A'i ta auri Marigayi Mai girma Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Ɗanbaba ɗan Magajin garin Sakkwato Usman da ya fito daga tsatson Marigayi Mai girma Magajin garin Sakkwato na farko, Malam Abubakar Haruna Ɗanjada. Sun haifa  ya'ya /ɗiya da dama tare dashi kamar Hajiya Asma'u uwargidan Marigayi Mai girma Sarkin Sudan na Wurno, Alhaji Shehu Malami da Marigayi Mai girma Magajin garin Sakkwato, Alhaji Hassan Ahmadu Ɗanbaba da Hajiya Safiya wadda ta auri Alhaji Alhassan Abdullahi Mutassibi da Hajiya Khadija. 

    Hajiya Inno ta auri Marigayi Mai girma Wamban Kano, Alhaji Abubakar (Habu Ɗan Maje) ɗan Mai Martaba Sarkin Kano Sir Muhammadu Sanusi I, ɗan Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero, ɗan Sarkin Kano Malam Abbas, ɗan Sarkin Kano Malam Abdullahi Maje Karofi, ɗan Sarkin Malam Ibrahim Dabo. Sun haifi Hajiya Khadija (Hajiyayye) wanda ta auri Marigayi Mai girma Gwamnan farar hula na farko na Tsohuwar Jihar Sakkwato (Sokoto, Kebbi, Zamfara), Marigayi Alhaji Shehu Mohammed Kangiwa Turakin Kabi/Turakin Argungu na farko da Hajiya Fatima(Balaraba) wadda ke auren Alhaji Aminu Sulen Garo.

    Hajiya Inno da Hajiya A'i sun yi wafati, Hajiya Luba ce ke raye a halin yanzu. 

    Allah ya jaddada rahamarsa zuwa ga dukan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.
    08149388452, 08027484815.
    birninbagaji4040@gmail.com
    Alhamis, 24/10/2024.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.